Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 70


Bibiyata Akeyi 70
Viral

Page 70

Page na farko taga anrubuta.” I LOVE HER.” abunda aka rubuta kenen, na biyu kuma SHE’S AN ANGEL.”
sake bud’e third Page d’in tayi, SHE’S STUBBORN, abunda aka rubuta kenen.”
Murmushi mai kyau *hanna* tayi sannan ta bud’e fourth Page d’in, SHE WAS BORN IN 29/MARCH/1998.”
Page na biyar tada bud’e ne taga rubutu mai yawa zama tayi sosai sannan ta fara karantawa Kamar haka.”
On 29/march/2007.” the day I first saw her.”
Runtse ido *hanna* tayi, sannan tacigabada karatu.”
Da misalin k’arfe 7:45.am.” na safiyar litinin, tushen aiki.” alokacin kowani d’alibi k’ok’arinsa yaga ya isa makarnta.”
Takowani lungu ka leqa dalibaine Da uniform kala-kala.”
New GRA sky crest d’alibaine birjik gaban makarnta assemly akeyi kowane d’alibi tsab-tsab dake kasancewar ranar farkon satii.”
Brown d’in skirt ne dakuma milk shirt sannan sai brown mini hijab.”
Yawancin student d’in kayanda ke jikinsu kenen.”
Sai kuma gefe d’aya dana ganii Brown skirt Da milk d’in hijab Da riga.” Alamu yanuna cewa junior ne masu wannan shiga.”
Daga can gefe kuma yarane Da green d’in check, bayan angama assemly d’in kowanne yanufii class d’insa.”
Motocii ne suketa wucewa hanyar.”
Wasu Motocii ne sukazo ajere da’amu akwai mai mulkii cikintq.” Motocii guda biyarne duka hud’u nagaba Da baya an musu paint na sojojii, yayinda d’aya Daga cikinsu takansace bak’a wuliik.” yarane makill, wanda suke jira su tsallaka, uniform d’insu ya ban tanta dana d’yqn skull d’in. Tsallaka titin sukesonyi, amma yawan motociin dasuke wucewa yahansu, tsaye suke cirko-cirko, MG ne dake cikin dake cikin bak’in motar yayiwa guard d’insa magana aka su kashe titin student su tsallaka.” tsayuwar motar ne yasa student suka fara tsallakawa, hanakalin MG ne yakai kan wata mota, stliet ce ta tsaya bakin sky crest ta sauke Wata yarinya, Da bazata wuce shekara tara ba.”
Sannan motar ta juya zuwaga makarantar dake opposite d’inta sa’adu zungur.”
Sauke sauran yaran yayi, wanda da’almu y’an uwan tane, amma abun yabashi mamaki ganin ita ansauke ta a private schooll sukuma y’an uwanta ansauk’esu a government schooll.”
Juyawa yayi zauwaga yarinyar dayaga ansuke.”
Gabansane yafad’ii da ganin yarinyar yarasa dalili kawai yakasa d’aga idanuwansa daga kanta.”
K’ura mata ido yayi tsam, magana takeyi wanda baijin mai take fad’a, amma kuma daga alamu yagane cewa magana ake mata akan sandal datasa, kowani student yawuce sandal na kafansu brown ne kokuma black.”
Ita kuma nata pink ne.”
Bayadda ba’ayi tacire sandal d’inba amma tak’ii, dariya abun yabashi ganin yanda yarinyar keda taurin kai.”
Ahaka har kusan 15 minute sukuma soldier’s d’in ganin haryanzu baiabsu order natafiya ba, yasa kowa yayi shiru.”
Gateman d’in ganin tak’ii cirewa ne yasa su cewa tom sai anmata bulala na latti, turjewa tafarayi tana kuka amma haka bbu imani, sanda ya zuga mata d’aya runtse idanuwa MG yayi danhar ajikinsa yajii zafin bulala.”
Bud’e idanuwa yayi yaga yanda take ihu.”
Ganin tana kuka yasa Gateman d’in yace ta wuce, tafiya takeyi tana kuka hankalin MG inyayi dubu yatshi ganin yanda tatafii tana kuka.”
Ahaka yatsaya harta shige.”
Juyawa yayi ya kalli driver ya nuna masa wani d’an waje anrubuta kobii senima asaman wajen duka sukayi parking.”
Yunwa sukeji duka dan saukarsu kenan zasu wuce zaranda hotel, su huta k’arfe biyu sunada meeting.”
Sai 1 aka tashi su *hanna* sunfito y’an primary kad’ai.”
MG leqe yakeyi amma baiganotaba Sai can wata yarinya tanata kwala kira *hanna* *hanna* direction d’inda take kallo ya kalla dan sunan yamasa sosai, idauwansa yayi tozali da yarinyar dayagani d’azu.”
K’arasawo tayi tace wai nii menene kiketa kirana?”
Bud’e baki MG yayi ganin k’aramar yarinya amma Sai shegen tsiwa.”
Yarinyar ce tafara magana tace d’azu anty tace muyi wshing d’inki is ur birthday today.”
Eh kawai *hanna* tace sannan takawarda kai tanufii wajan wani mai rake dake bakin titii, sayan raken tayi sannan ta koma ta zauna, bata dad’e dad’e zamaba wasu frnd d’inta sukazo, tsayawa sukayi cirko-cirko akanta, hqrara ta aika musu sannan tace menene kuma zaku wani tsayamun aka,,,,,,,, aibata k’rasaba suka juye mata bokitin ruwa.” Razana MG yayi ganin yanda tasa ihuu da kuma yanda numfashinta ke sama-sama.”
Had’e baki sukayi sunacewa Happy birthday, saurin fitowa MG yayi daniyar taimakonta, alokacin motar babansu ta danno wajan tsayawa yayi cakk, ganin babanta yafito dasaurii ya nufeta babbar riagarsa yacire yanad’eta yad’auketa zuwa mota.”
Ganin su MG yatsayayi yarasa dalilin dayasa Yarinyar tatsaya masa araii, baibai wajanba har saida ya ga yafiyansu.”
Juyawa yayi ya kalli captain bilal dake kusa dashi yace.”
Wancan mai raken kaje kabashi jaree, banso yak’ara sayarda rake.”
Dahaka suka isa masaukinsu, sannan suka wuce meeting.”
Washe gari yakamata MG yakoma amma haka yakoma washegarii da safe.”
Dai-dai lokacinda *hanna* tazo jiya.”
Sanda yaga shigarta har zuwa tashinta sannan ya koma.”
Alokacin *hanna* hawaye kawai take gogewa, ko batazo k’arshe ba tasan MG masoyintane.”
Share hawayen tayi tacigaba da karatuu.”
Sanda yayi kwana uku yana zuwa makaranta yana jiran tashinta.”
Ana hud’unne yabita har gida.”
Tun daga lokacinda yaga gidansu yabar captain bala da captain bilal masu jiranta.”
Koda yaushe suna k’ofar gidan idan anguwa zata tafii itqda yayyaunta to suna biye dasu.”
Ko shago *hanna* taje ta siya abu tom wannan mai shagon Sai anbashi jareenda zai iyayin uku ko hud’un nasa nad’a.”
Mutane daywa sun samu sauk’i daga talaucii ta dalilin *hanna* wanda ita kanta batasan anyi ba, shikuma wanda yakeyin shima baisanii ba.”
Koda gyada *hanna* taganii ahanya tasaya mai gyadanan Sai anbii har gidan iyayenta anmata kyauta.”
Alokacin da MG yake wannan abun shikansa baisan mai yake ji gameda *hanna* ba.”
Aranar juma’a *hanna* ta zo makaranta bbu P.E dress, abakin gate aka tsareta, MG na cikin mota dan dama yadad’e awajan.”
Duk yanda akayi da *hanna* qkan tasa tace ita bazata sakaba.”
Kamar yanda ya lura da *hanna* kullum Sai anyii rikici da ita akan pink d’in abuu.”
Ahaka bayanda suka iya suka barta dan idanda saboo yakamata su saba da halin *hanna*.”
Washe garii MG yakoma kano.”
Bayan yaje bai b’oyewa mahaifiyarsa abunda yake faruwa dashiba duk da dai bai shaida mata cewa wacece Yarinyar ba?”
Kuma bai fad’a mata shekrunta ba.”
Alokacin ummii ta shaida masa cewa sonta yakeyi.”
Bbu yanda batayi akan yafad’a mata gidansu da adress d’insu ba.”
Amma firr yak’ii yace mata dasauran lokaci.”

Zuwa sunday Sanda yakoma bauchii dan kwana biyu dayayi baiganta ba jiyakeyi Kamar ya shekara duk yavii ya susuce.”
Yana isa mai makarntarsu yafara nqima yashaida masa komai kan yanaso acanja uniform zuwa pink, mai makarantar ganin kud’ii nan danan ya amince.”
Monday dake student kowa yazo za’a bashi unifor kyauta.”
Pink colour *hanna* tayi murna sosai.”
A”inda iyayen yara sukayi mamakin ganin yanda mai makarntar yakeda son kud’ii amma harya iya kyautan uniform.”
Ahaka *hanna* tacigaba da karantawa har zuwa lokacinda suka shiga secoundry na dariya tayi dariya na kuka ma tayishi.”
Kukantane ya tsananta Alokacin da taga MG yarubuta sojojina sun dawo masu saida rake dan ta dalilinki, sojojina sun zamq masu shago ta dalilinki.”
Sojojina sun zama y’an taxi ta dalilinki.”
Duk wani taxi takika shiga iya tsayon girmanki, ina tsare dake, wannan abuun nayi shine dan kar ki had’u da wanda zai sayemun zuciyarki.”
*Hanna* sojojina har kwasan kwata na layinku sunyi dan tsaron lafiyarki.”
Aduk yanda kike sojojina *BIBIYARKI SUKEYI*.”
Aduk lokacinda da kike wani abuu idan kin cire mutanen gidanku tom ina *BIBIYE DAKE* k’arfin da kukan *hanna* yayinee yasata barin karatun Sanda tayi kukanta t koshi sannan kuma afili ta furta tabbas banyii laifii ba danace *BIBIYATA AKEYI* Share hawayenta tayi sannan tacigaba da karatun.”

To be continued

Ur’s
z33iiyyb3rw3r

*BIBIYATA AKEYI*

_Bismillahirrahmanirrahim_

Writing by
© _Zaynab Bawa_
( _z33iiyyb3rw3r_ )

_Like my page on Facebook :::Zaynab BAWA novels_

Followed me on instagram ::::mhiz_z33iiyyb3rw3r

*Manzon Allah tsirada amincin Allah su tabbata agareshi yace.” Duk wanda yakaranta wannan addu’a, la’ila ha illallahu wahdahu la sharika lahu, lahul hamdu wa lahul mulku yuhyi ayumitu ahuwa hayyul layamutu wahuwa ala kulli shai’in k’adir.” Allah zai rubuta masa lada dubu sau dubu sannan zai yaye masa zunubi dubu sau dubu.”*

*Yanada kyau karanta addu’ar nan bayan tashi daga bacci.” Alhmdllhillazii ahyana ba’ada ma amatana wa’ilaihinnushur.”*

================

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply