Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 73


Bibiyata Akeyi 73
Viral

Page 73

*
Gida suka nufa, suna shiga afeeya tataimakawa *hanna* ta shiga wanka itakuma tafita dan shirya musu breakfast.”
*Hanna* bata d’auki lokacii wajen wankan ba tafito dan ba k’arfiin jikinta takejii sosai ba.” abakin bed ta zauna ta had’a kai da gwuiwa hawaye na zubo mata, tunaninta d’aya awani hali MG yake ciki.” sallama afeeya rayi aqofar d’akin jin ba’a amsaba yasata shiga dan atunaninta bata futo awanka ba.” ganin *hanna* tayi tahad’e kai da gwuiwa alamun kuka takeyi, dasaurii tak’arasa wajenta, ta ta6a kafad’unta *hanna* tayi saurin d’agowa cikin muryar damuwa afeeya tace *hanna* wai meke damunki ne? Kinsan kuwa mai doctor yace? Plz kidena saka tunani acikin ranki, jin haka yasa *hanna* fashewa da kuka tace anty ya zanyii wallhy wayarsa bata shiga tunda yatafii ko sau d’aya bamuyi waya ba kuma haryanzu bbu wanda yasan halinda suke ciki, k’ara wani kukan take tana anty nashiga uku wallhy idan wani abu yasameshi bazan iya rayuwa bbu shiba, anty kitaimakenii yadawo.” wallhy inasaonsa anty duk abunda nafad’a k’aryane ban ta6a k’in saba, tasaka hannu akayi tana cewa nashiga ukuna.” idon afeeya tabb yacika da kwalla tausayin *hanna* dakuma tausayin kansu narashin sanin halinda d’an uwansu yake ciki yakamata, tabbas tasan aranda akace sun rasa MG tashin hankali yashigesu har iya k’arshen rayuwarsu, mutumne wanda yafii kowa soyuwa aran dangii.” bawai dan kud’insa ko mulkinsa ba a’a saidan kawai Allah yayishi dashiga ran alummah.” zama tayi abakin gadon ta rungume *hanna* tana tana bubbuga bayanta dan duk wani abunda zaifito abakinta yanzu kuka ne shiyasata yin shiru kawai.” hwaye tabb a’iidonta.”
D’iga hawayen idonta yafarayi abayaan *hanna* aikuwa *hanna* ta k’ank’ameta tsam taqara sake wani kukan.” shafa bayanta kawai afeeya takeyi dan bbu wata kalma dazatayi amfani da ita wajen nusarda ita, tasan dolene hanna ta damu, tausayinta ne ya dad’a malale zuciyar afeeyah,
Sunfii 15 minute ahaka sannan afeeya tasaka hannuwanta tashare hawayen idonta sannan ta d’ago *hanna* dake jikinta tasaka hannuwanta tana share hawayen tana mata murmushi cikin sigar lallashi tace kiyi shiru abunki kinji? jiya muna asibiti najii wasu soldier’s suna cewa next week zasu dawo, dan haka ki kwantarda hankalinki cikin, nan danan *hanna* tafara murmushi, cikin zumudi tafara murmushi hawaye nazuba mata tace, da gaske?” jijjjga kai afeeya tayi tana gaskanta mata zancen tace kwarai kuwa.”
Nana kaga fiskan *hanna* yahad’e hawaye dakuma murmushi riqo hannunta afeeya tayi tace maza tashi muje mucii abincii, *hanna* tace anty nak’oshi 6atarqi anty tayi tace hanna kina nufi idanya ganki ahaka zaiji d’ad’ine?” gara kicii abincii zuwa nanda satinn kya murmure sai yayi farin cikin ganinki, tashi muje tariqo hannunta, sai alokacin hanna tuna batada kaya ajikinta daga ita sai towel kunya ta kamata ta sunna kai ganinhaka afeeya ta gane mai take nufi, tasaketa tace kishirya saiki sameni afalo, sanna tamiqe tafuta, Tana gama shiri tafita falo tasamu anty afeeya tagama had’a musu komai zama tayi suka faracin abincin, batacii dayawaba tatashi da duk da damuwarta tad’an ragu amma fa haryanzu bawai dadin abincin takejii ba.”
Tashi tayi takoma kan kujera tazauna ta lumshe ido ita ba bacci takeyiba amma kuma hankalinta ba’a wajen yake ba, zuciyarta duk wani abunda yahad’a ta da MG yakeyi, abubuwane yashiga yi mata yawo acikin kwakwalwarta, na murmushi tayi murmushi, duk abunda takeyianty afeeya na kallonta, itama murmushin tayi tana girgirza kai, tarasa wani irin so sukeyiwa junansu.” wanda d’ayabazai iya rayuwa bbu d’aya ba.”
Wucewa anty tayi dan gabaatarda sallar walha, tabar *hanna* sai juye juye takeyi amma idanuwanta alumshe.” wani farin ciki ne acikin zuciyarta Jin cewa MG yakusa dawowa.” koba komai yanzu hankalinta xai kwanta, zata samu peace of mind.”

================

Hava mama yanzu dan Allah 1month hadda 2weeks kuma kice bazan fita ba.” dama su saleem d’in basu fita yawo bane dasai suje, dan Allah mama karkice a’a wallhy nagaji dazaman gida.” nisawa mama tayi tace toh karima tsoro nakejo gani nakeyi kamar idan kika futa wani abuu zai biyo baya.” wallhy bbu komai mama bbu wani abunda zai biyo baya.” yanzu zan sayo miki nadawo.” nisawa mama tayi sanna tace ok tom kishiga wuntii dan tafii kusa, sai ki dawo dawuri.”
Abida dake kusa dasu tace mama aike kika kulata, sai kace dole ance mata karta fita amma sai taurin kai.” harara karima ta galla mata tace banson rainii ansa dakene? Kawarda kai gefe abida tayi sannan karima tacigaba dacewa dan Allah mama wallhy yau haka kawai nakeda sha’awan fita, nisawa mama tayi sanna tace kid’auki kud’in amma kada ki dad’e.” toh tace sannan ta shiga ta zumbulo hijabii, tafito duk da haka hankalin mama bai kwanta taba tace, karima dawo kisa niqab bbu musu tadwo tasaka sanna tafice.”
Tana fita da wuce wuntii market, tayi sayyayanta tsab, sanna tad’auki hanyar dawowa, round about dake wuntii tana tsayae tana jiran keke napep, alokacin motan najeeb ya danno kai, ya juya titi kawai idanuwansa suka sauka kanta, sanye take da blue na hijab har k’asa sai niqab, bbu abinda kake kallo banda kwayar idanuwanta.” gabansane yayi mugun fad’uwa tun rabuwarsa da *hanna* bai ta6a ganin wanda takwanta masa araiba sai ita, bai k’ara tsintar kansa awannan yanayi ba sai yanzu, dukk da dacewa baiga fusknata amma taa kwanta masa.” ya nutsa cikin tunani harta tsari keke napep tafara tafiya.” sai lokacin yadwo cikin tunaninsa yana kallo tafara tafiya yayi saurin bin bayqn keke napep d’in.”
Ganin andoshi angiwarsu *hanna* sanda gabansa yafad’ii haka harzuwa k’ofar gidansu, alokacin yagama cinkewa, besan waceec ba, sanun kansane ba *hanna* bane to wacece, ita?”
Haka yayita zama awajen har kusan 1hour ganin bata k’ara fitowaba, yasashi jan motar yatafii.”

Waahe gari da 11:00am najeeb yaje gidansu *hanna* yadad’e ak’ofar gidan yana jira ko zata fito amma shiru.” yakusan 3day’s yana zuwa amma duk da haka bai ganinta, hakan yasa kawai yashare yacigaba da al’amuransa, amma kuma bawai dan yamanta da itaba yasa rai duk ranarda yaganta, in sha Allah sayya yi mata magana .”

_Plz kiyi hakurii da jina shiru kwana biyu, wasu y’an matsalolii ne amma nagode, da kiranku da massg d’inki, kj kwantarda hankalinku lpyna klau kawaidai y’ar matsalace.”_

_Kujira na dare yau biyu zanyi_

To be contiuned

Ur’s z33yy bawa

*BIBIYATA AKEYI*

_Bismillahirrahmanirrahim_

Writing by
© _Zaynab Bawa_
( _z33iiyyb3rw3r_ )

_Like my page on Facebook :::Zaynab BAWA novels_

Followed me on instagram ::::mhiz_z33iiyyb3rw3r

*Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace, ” *laula an aahukka ala ummatii* yace dabadan zan takurawa al’umma taba yace, “`la’artuhum bissuwak inda kullil salat“` *yace dana umurcesu dayin aswaki ako wace sallah.” yin suwak babbar sunnace ta Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi, yanadakyau bin sunnonin Manzon Allah Allah kabamu ikon bii.”*

*Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace, ” kullaa ummatii yadkulal jannata illa man abah, duk alummata zasu shiga aljanna, harsai wanda yak’ii, mamaki yaakama mutanen dake wajan sukace ya rasuliahi yanzu waye zaiqii shiga aljnnah?” sai Manzon Allah yace wanda yamun biyayya tabbas zaishiga aljannah, sannan yace wanda yasa6ani kuwa to tabbas yak’ii.” Allah kabamu ikon yin biyayya ga manzonka.”*

================

*Wannan shafin nakune ku kad’ai, sanda nijar, da QUEEN, nagode da k’aunarku garenii nijar inasonku sosai.” ILYSM.”*

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply