Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 75


Bibiyata Akeyi 75
Viral

PAGE 75

*
Kai tsaye gidan yayansa ya nufa, dan yayi kyewar gidan sosai, kobabu komai gidan na tariyo masa al amura dayawa.”
Yana isa yafito yabud’e gate kasancewar bbu mai gadii, ya shiga da motar sa, parking yayi sannan yafito yanufii k’ofar shiga gidan, entercorm ya danna, jin k’ara anty dake zaune tadubii karima tace je Ki bud’e kofa, bbu musu karima tatashi dake ita baimai surutu bane sosai.”
Hijab d’inta tad’auka tsumbulele har k’asa dake, dariya dukansu sukasa, anty tace saikace wata matar liman, cikin gidanma sai kinsa hijabii.” abida ne tace anty rabuda ita Allah lokacinda muna gida gyallalukanta ma k’ananune.” juyawa karima tayi ta nufii k’ofa ta rabu dasu dan ita yanzu, tafison manya manyan hijabai, zuwanta bauchi yasa tajii tana sha’awar canja d’abi’unta, duk da tunda d’abi’unta ba munana bane amma tanaso na yanzu yafii nada kyau.” k’arasawa k’ofar tayi ta bud’e.”
Shikuma kansa na k’ofa yana jira A bud’e, tana bud’ewa sukayi ido biyu gaban kowanne daga cikinsune yafad’ii, saurin yin k’asa da kanta tayi tanajin wani irin yanayi tace, kashigo, shiru yayi yatsaya yana kallonta itakuma ta sunkuyarda kanta tana wasa da yatsun hannunta, tunanine fall aransa yasan shakka bbu ita ce wannan yarinyar dayaganii, kasancewar, yanayin daya tsincii kansa irinna ranar, hijabin ta irinna yarinyar ranar, kuma gashi yau yaganta a gidansu *hanna* yau awajen anty hakan yanuna sunada alaqa da ita kenan.”
Ganin yak’i cewa komai yasata juyawa takoma ciki, tana shiga anty tace wayene?” cikin sanyin jiki tace umm anty bansan shiba, amma nace masa yashigo.” baisan tabar wajanba sanda yadawo daga dogon natsarinsa.” nisawa yayi sannan yace ya Allah kada ka jarabceni DA abunda zaifii k’arfiina, ya Allah kada kasa mun son yarinyar nan kamar yanda kasamun na *hanna* na azabtu da shii, Ya Allah kamun za6in alkhairii.”
Cikin sanyin jiki yasa kansa afalon had’eda yin sallama.” dasaurii anty tajuyo tace A’a uncle munyii fushi kakoma kawai, fara sosa kansa yayi yana dariya yace agafarcenii, kaina k’asa natuba, yana fad’ii yana k’arasowa.” dariya anty tayi tace dalili d’aya ne zanyafe maka.” Dai-dai lokacin ya k’araso yana zama yace ai ahakanma nagode.”
Kallon abida anty tayi tace tashi kije kidauko masa drinks da abincii.” saurin tsaida ita najeeb yayi yace a’a barshi kawai nagode, wucewa zanyii nace barina biyo, 6ata rai anty tayi tace badai baka huce ba?” murmushin dole yayi yace, ai dolena nayi hakurii, tunda bawani yajamunba.” nima kaina bansan dalilin yin hakanba, jikin anty ne yayi sanyi tausayin najeeb yakamata, tace A Allah zaimaka za6ii mafii alkhairii, nisawa yayi baice komai ba.” sai alokacin suka gaisheshi ya amsa idanuwansa nakan karima, yatashi yace ni barin wuce, zandawo akwai maganar zamuuyii, toh sqika dawo kawai anty tace, sannan yatashi yafita.”

================

Jin dawowarsu MG yahana *hanna* bacci kwana tayi tana sallolii da addu’oii, har gari yawaye *hanna* bata runtsa ba.”
Addu’a kawai takeyi, dakyar ta iya tashi tafara yiwa MG girki, sosai tagwada nata basirar, masu aikii dama kullum sukan shigo suyii gyara amma yau itada kanta ta tayasu suka Gyare ko ina sannan, ta turara gidan, kowani lungu da sak’o yad’auki kamshii.”
Shiga tayi itama ta fara nata wankan tadad’e tana wanka, sannan tafito turare kawai ta iya feshe jikinta dashi, amma ko powder kasa sawa tayi balle man le6e, fargaba tafii komai yawa aranta yanzu, doguwar riga ta zura, sai d’an kwalinta.” sannan tasauko palour ta zauna, bata dad’eba matar shahid taahigo dasaurinta tace, wa *hanna* ta tashi sutafii barrack, dan yanzu haka ance sun kusa sauk’a.” da Kallon tambaya *hanna* tabita tace dama banan zasu sauk’a ba.” girgiza mata kai tayi tace ainan gidajensu ne, zamuje taryanzu a barrack, mamakine yakama *hanna* ganin yanda bata damu sosai ba, hakan yana nufiin harsun fara sabawa kenan, waje sukayi sannan suka Shiga mota, ba’ad’auki lokacii ba suka isa.”
Sun shiga *hanna* *hanna* sai kallo take binsu dashi ganin yanda matan soldier’s da y’ay’ansu, tako ina ta leqa matane da yara, kusan duk matan fararen fata ne, d’ai-dai kune blacks, sai kuma soldier’s da suke barbarje a barrack d’in.” 12:00 alqrm yabuga na jirgi yasauk’a, kowacce sai raba ido takeyi wasu matan kuma wak’a sukeyi, ba’afii 12:30 ba sojoji suka fara shigowa wannna wajen, wasu na shigowa riqeda akwatin gawa ahannun su.” sai sunshigo ciki su ajiye.” duk wanda tahango mijinta aguje suke tafiya su rungumesu, wanda suka hango akwatii da pics na mijinsu kuma wasu zubewa sukeyi ak’asa, wasu na ihuu tashi d’aya wajen ya karad’e ga sojojii basu fasa shigaba, *hanna* kuwa gabanta yafara dukan taraa tara idanuwanta sunkawo ruwa, banda hawaye bbu abunda yake zuba.”
Aikuwa can saiga abid ya shigo, yaronshine yafara hangoshi, jan hannun mamansa yayi yace momma momma yana nuna mata abid yace pappa, ganinsa sukeyi gaban akwatin wata gawa, soldier’s dayawa sun d’aukota da alamu ta babbane, nan gaban *hanna* ta matar shahid yafad’ii dan tabbas acikinsu mijin d’ayane.” kasa zuwa matar abid tayi dan daga alamu hankalinsa atashe yake, kowacce acikinsu raba idanuwa takeyi kozataga mijinta shiru bbu MG bbu shahid basusan wanene acikin akwatinba.” gashi basuga d’ayaba balle su tabbatar.” ganin an nufosu ne yasa zuciyoyinsu karyewa, har gaban, farisa sukazo matar shahid suka ajiye gawar sannan kowa yacire hulansa Aikuwa nan danan ta zube kan gawar tana kuka kamar rqnda zai fita zuciyoyinsu duk yakarye.” anrasa wanda zaiyi kanta ya rarrasheta, yaranta k’ananune amma sun fahimta nan suka fara kuka Awanna lokacii *hanna* itama kukan takeyi natausayin fariisa dakuma nakanta narashin sanin halinda mijinta yake ciki.” da guduu ra’iisa matar abid tashige jikinsa tana kuka, na tausayin y’ar uwarta, ita kuwa *hanna* ganin sojojii sunfara k’arewa harsuka k’are, yasata farajaa dabaya, mai hakan yake nufii kenan? Badai wani abuu yasamii MG ba yana asibitii, rufe kunnenta tayi tafara kuka inaaaa hankainta bazai iya d’aukan wannan zance BA.”
Ficewa tayi tashige mota aguje, ta ce driver yatafii, suna isa bata barii yatsaida motarba tafice, aguje tashiga d’aki ta rufe kanta.” kuka takeyi kamar ranta zai fita.”

*NIGERIA*

karfe 1:00pm Dai-dai, jet yasauke MG A cikin gidan sarkii, jin jirgii ya tabbatarwa iyayensa shine ya iso.” yana futa bai 6ata lokacii ba yashige shahin ummii ganin yanda tarame, ya bashi tausayi dasaurii yak’arasa yazube akan guiwarsa, ya rungumeta tsam, fashewa tayi da kuka, tak’ara k’ank’ameshi, dakyar ya rarrasheta ya saketa sannan yace, ummii na nadawo lpy dan Allah kidaina kukannan, share hawayenta tayi tace nadainaa, d’ana, tashi yayi yace barin shiga gun abba, dasaurii yatashi yafice dan damuwarsa kawai yawuce shahinsa yaga *hanna* , mai martaba yayi murnar ganin d’annasa, damacan yana boye damuwarsa ne dan yanda ummii kesaka damuwa ranta.”
Baidade ba yafito ya nufii shahinsa ganin akulle abuu yabashi matukar mamaki juyawa yayi zuwa shashin ummii yasamu afeeyya har ta iso labarii ya isheta, ta guduu tatashi ta rumgumeshi tana cewa yaya ya baka fara zuwa wajan *hanna* ba?” dagota yayi yace dama *hanna* bata dawo ba?”
Gyada masa kai tayi tace yaya tak’ii dawowa, nan tafara bashi irin labarin damuwarda *hanna* tashiga, sannan tace masa har ciwo tayi, ai nanda nan idon MG yakad’a, son *hanna* yana k’aruwa azuciyarsa, jii yakeyi kamar amafarkii wai *hanna* ne take wanna abun kansa,” yawuce gidane domin ganin *hanna* dan yanada ya’inin bazata zauna zaman jiransaba, amma kuma yasamu sabanin hakan, juyawa yayi zai fice, ummii tace ina zakaje katsaya kacii abincii.” no ummii zan tafii wajan *hanna* bansan awani halii ta ke ba narashin ganina.” share hawaye ummii tayi sannan tatashi yariqo, hannunsa tad’auki wermer tadamka masa tace, kacii abincii ahanya Allah yamuku albarka, sumbatar goahinta yayi ya fice.”
Nan suka d’auki hanya dake jet ne k’arfe goma na dare suka isa, yana shiga alokacin *hanna* harta galabaita tsabar kuka.” yawuce sama yanda yaga wuta akunne alamu da mutum aciki.”
Dasaurii ya isa yana k’okarin bud’e kofar yajii akulle, da k’arfii yace, sweety am home, kamar amafarkii *hanna* tajii muryarsa aida gudu tatashi tabude, tana Kallon Sa atsaye da gudu tashige jikinsa, tana kuka sosai, har cikin jikinsa yakejin kukan, cikin kukan tafara inasonka wallhy inasonka idan kasake tafiyya kabarnii zanmutu.” runtse ido yayi yanajin maganganun ta har cikin zuciyarsa, ganin takii daina kukanne yad’ago kanta, yahad’e bakinsu waje d’aya, ga mamakinsa *hanna* batayi kok’arin kwace kantaba sqima biye masa datakeyi.”

To be continued

Ur’s
z33iiyyb3rw3r

*BIBIYATA AKEYI*

_Bismillahirrahmanirrahim_

Writing by
© _Zaynab Bawa_
( _z33iiyyb3rw3r_ )

_Like my page on Facebook :::Zaynab BAWA novels_

Followed me on instagram ::::mhiz_z33iiyyb3rw3r

“`Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un😭😭😭😭 Allah yajikanka Allah yarahamsheka Allah yasa aljannah ce makomarka😭😭😭😭😭 , dan Allah muna buk’atar addu’arku, Allah yayiwa lecturer d’inmu rasuwa, mal muhammad muhammad, addu’arku tafii komai mahimmancii“` 😭😭😭

*Manzon Allah tsirada amincin Allah su tabbata agareshi, yace,” ayatul munafiku na salatha, yace alamomin munafukai guda uku ne, izha hadatha kazaba, idan yayi magana yayi karya, wato mak’aryacii yana d’aya daga cikin alamun munafurcii, kuma yace,” wa”iza wa’ada aklafha, kuma idan yayi alk’awari yasa6a yanadakyau riqon alk’awari, domin mai karyashi Manzon SAW Allah yace mana munafiki ne, sannnan yace waizaa tu’umina kana, kuma idan aka yarda dakai kayi ka cii amana.” Allah katsaremu dacin amanar y’an uwanmu.”*

*Manzon Allah tsirada amincin Allah su tabbata agareshi yace,” da’a ma yuribuka ila mala yuribuka, kabar abunda kake kokonto akansa izuwa wanda bakada kokonto akansa, wallahu ta’ala a’alam, Allah shine mafii sanin gaskiya, Allah kasa mudace.”*

================

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply