Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 82


Bibiyata Akeyi 82
Viral

page 82

*
Cikin jirgii *hanna* nazaune kusada Marshall, ta kwantarda kanta akafad’ansa, tayi shiru alamun wani abun take tunanii.”
Shikuma marshall yak’ura mata idanuwa kawai ganin yanda tayi nisa Cikin tunani.”
Wata doguwar ajiyar zuciya tasauk’e, sannan ta lumhse idanuwanta, kallonta yakeyi ko kiftawa bbu, itakuma bata dad’e da rufe idanuwa ba bacci yad’auketa.”
Shima runtse idanuwansa yayi Cikin zuciyarsa yana addu’a ya Allah kada ka jarabceni da abunda bazan iyaba, ya Allah kada ka nunamin ranarda zan rasa *hanna* arayuwata, bansan wani halii zai shiga ba.” Ahaka har jirginsu yayi landing *hanna* tana bacci, baisan katseta daga baccinta data lula kuma alamun baccin yana mata dad’ii, hakanne yasa ya cewa su ummii su fara gaba, shi zai k’araso daga baya, akawai abunda zaiyine, su ummiii way’anda sukazo taryansu daga fadah sukabii,” shikuma yazauna jiran *hanna*, ga mutane dayawa dasuka zo taryansa, kama daga shugaban k’asa governor’s, ambasador’s ministers, Senate, dasauran su.”
Tafii 30 minute tana bacci, wata ajiyar zuciya tasaki, sannan tayi miqa ta had’a da addu’an farkawa daga bacci, ware idanuwanta tafarayi, akansa ta ware idanuwannata tass, murmushi yasakar mata, itama murmushin tamayar masa,” juyawa tayi da niyyar ganin su umma amma taga wayam dasauri tamiqe tazauna, zaro ido tayi tace ina ummii suke?”
Suntafii gida.” zaro ido tayi tace toh mu me muka tsaya yi?.” kajimun yarinya, me kike tunanin natsaya yii, kozan tasheki a bacci ne?” ehem, common tashi mutafii.” marairaice fuska tayi tace yi hak’uri dear, aida ka tasheni.” intasheki kuma?.” A’a kam gaskiya bazan iyaba.” yanzu kawai tashi muje, nasan ana jirana.” miqewa tayi tada’uko gyalenta ta yafa.” ya riqo hannunta suka futa.” ana bud’e door na flight d’in, flashes ne suka fara kashe musu ido, sa hannu *hanna* tayi ta k’are fuskanta, saida tad’an dad’e kafin tabud’e fuskan.” sojojine atsaye bakin jet d’in, alamu ya nuna sundad’e a tsaye awajen,” suna sauk’owa mutanen da sukazo taryansu, suma suka k’arasaso, hannu suka fara bashi kowannen su wasu na haugging d’in sa.” amma dukda haka hannunsa yana cikin na *hanna* gam yariqeta, dan yasan *hanna* yanzu saita rikice batason hayaniya sosai, barin yanda yalurada ita kwana kinnan.”
Ahaka har suka rakashi zuwa ga mota, duk yanda y’an jarida sukaso zantawa dashi bai tsayaaba, damuwarsa yakai *hanna* gida ta huta, dakansa ya bud’e wa *hanna* Mota tashiga yayinda mutanen wajan tsan-tsan mamaki ya tsaresu, lallai sun tabbatr duk Mulkin mutum sayya sauk’arda Kai a wajan mace, bud’e masa motan akayi sai shima ya shiga, haka suka tafii gayya guda zuwa fadah.”
Bayan sun isa ne aka bud’e k’ofan *hanna* tayi saurin fita tanufii shashin ummii.” su kuma dasauran jama’a aka wuce cikin fadah.”
A palour tasamu su ummii nan ta shiga tayi sallololinta tafito, tasamu abinciii tacii sannan tazauna A palour tarashe.”
Data gajii da zaman ne tashige d’akin labba takwanta dan batajin dad’in jikinta.” bacci tayi sosai sai Bayan sallan magrib tatashi.” tayi sallan ta sannan tak’ara dawowa palourn tasamii ummii, su afeeya sun tafii.”
Har kusan k’arfe 9 tana wajan ummii, sai lokacin marshall yazo suka wuce shashin su, komai agyare suka sameshi.” saboda gajiya wanka kawai sukayi sannan suka kwanta.”
Washe gari kuwa agida suka yini bawanda yafita, dan sun dad’e basu samii hutu irin hakaba.”
Suna zaune afalo hanna tad’aura k’afofinta kan cinyan marshall tana danne danne awayanta,” kallonta marshall yayi ya maido duk hamkalinsa gareta, yace, cutie, uhmm ta amsa, yakamata kije kingaida umma (kilishi) yau,” kinsan gobe bbu lokacii kina wajan zancen walimah, bata d’ago ta kalleshi ba tace, zuwa jimawa zanje.” tom kawai yace yacigaba da kallonsa dayakeyi.”

K’arfe takwas dai-dai *hanna* ta zumbula hijabinta tanufii shashin kilishii koda taje a palour tasameta, da fara’a, kilishii ta k’ar6eta sai riritata takeyii, itakuwa *hanna* taji dad’in hakan, kilishii ne tayi wata y’ar dariyar da kana kallonta kasan ta munafurcii ne tace, y’ata nashiga tashin hankali sosai, lokacin tafiyarsu yareema, gashi kuma kema kika shiga wani hali, ga baki d’aya hankalin mu atashe yake, mungaza sukunii, sunkuyarda kanta *hanna* tayi tace, ai gashi mundawo umma yanzu hankalin ku zai kwanta, wata dariyar kilishii tak’arayi tace ai kuwa y’arnan, yanzu munjii sanyii sosai.” aff kinga na sha’afah tun d’azu nahad’a miki zobo akan zan aika miki tunda kinzo aisai ki tafii dashi tafad’a tana miqewa, wani irin kwad’ayine yazowa *hanna* gabaki d’aya yawunta ya tsinke, Allah Allah takeyi akawo zo6on tasamu tasha, Har wani had’iye miyau takeyii.”
Da k’aton jug kilishii tadawo riqe ahannunta, ajiyewa tayi agaban *hanna*, cikin kunya *hanna* tace umma a’iina zan samu cup, inaso nasha ne,” dasaurii kilishii takwala wa wata kuyanga kira, umarnii tamata data d’auko cup, bata dad’e ba kuwa tadawo hannunta riqeda cup, ajiyewa tayi agaban *hanna* sannan tanemi izini ta zuba mata, k’ar6a *hanna* tayi takafa bakin ta tahausha zuciyarta d’aya, sanda tashanye sannan tatshi zata fita, umarnii kilishii tayi da a d’auki jug d’in abita dashi, godiya tayi sosai sannan tafice.”
Wata dariyar rainin hankali kilishii tayi tacce lallai wannan yarinya, shsshasha ce, kokad’an batasan mai sonta ba, inbanda abinki niceh zan miki zo6on? toko shi mijinnaki baikai wannan matsayinba, taja tsaki.”
Itakuwa *hanna* tana komawa sashenta, da kad’an kad’an taringa shan zo6on harta shanye tass, dan wani irin kwadayin zo6onne yakamata.”
Sanda tashanye kafin ta tuno bata ragewa Marshall ba, d’aga kafad’unta tayi🤷‍♀, sannan tace ohow, idan yazo zangaya masa.” dan tunda yafita d’azu haryanzu bataga idanuwansa ba, shirye shirye bikkunan da za’ayi yasa Marshall baidawo gidaba Sai kusan 10:15pm.” *hanna* na jiransa afalo dan yakanyii wuya ta iya bacci idan baikusada ita shiyasa take jiransa Yadawo.” da sallama yashigo ta amsa masa tana murmushi, yana zuwa ya zauna kusada ita.”
Sannu da dawowa yauwa cutie ya gidan?” Lafiya klau, ya ayyukan? klau cutie na, gaskiya yakamata abarmunkai ka huta haka, uhmm ainakusa fara hutuna, sai nayi months banfita ko nan da door ba, dariya *hanna* tayi sannan tace,” kahuta Sai kayi wanka naga Kamar agajiye kake, kaman kinsani nagaji dayawa.” yafii 30minute akwance a cinyanta, idanuwansa alumshe, amma Kuma ba bacci yakeyii ba.” *hanna* na wasa da gashin giransa dake had’e waje d’aya, bud’e idanuwansa yayi yace dear nagama hutun zanyi wanka.” ok tom tashi muje.”
Bayan yafito awankane Har yayi shirin kwanciya, *hanna* ta dubeshi, afff namanta honey, naje nagaida umma, harta bani zo6o.” gaban Marshall ne yayi mugun fad’uwa Jin ta ambacii zo6o, shikqnsa baisan dalilin fad’uwar gabanba.” shiru yayi baice komaiba, Sai Bayan *hanna* takwanta Har bacci nashirin ebanta, cutie yakira sunanata, uhmm ta amsa alamun bacci yafara kamata.” kinsha zo6onne?”
Uhmm nasha kayi hak’urii ban bar makaba amma gobe zanyi mana wani.” I LOVE YOU, yafad’a tana k’ara gyara kwanciyarta, uhmm kawaii yace baik’arayin maganaba.”
Kusan 3 nadare hanna ke kwance tana baccinta,
Shikuma Marshall Yana sallah, dan tunda *hanna* tafara way’annan irin abubuwan, bai iya bacci.”
Bayan ya idarda sallan yazauna Yana addu’oii wani irin ihuu *hanna* takwala, tatashi tana ihuu tana riqe kanta, tana cewa honey zasu kashenii, gasuncan, wayyo Allah tak’ara sake wani ihunn, tana shirin sauk’a daga gadon, da gudu Marshall yayi kanta.”

To be continued

Ur’s

z33iiyybawa

*BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL’S_

“`Wani sahabi yace, rana mun kasance muna Sallah a bayan Manzon Allah (S.A.W) da Annabi ya dakko daga ruku’u sai ya ce Sami’Allahu Liman Hamidahu sai wani mutum daga cikin sahabbai yace Rabbana Walakal Hamdu, Handan Kasiran Dayyiban Mubarakan Fihi da aka gama sai Manzon Allah ya waiwayo sai ya ce Wanene ya fadi wannan sai mutumin yace Ni ne ya Manzon Allah sai Manzon Allah ya ce Naga Malaika talatin da “yan kai suna rigagato wazai rubuta wannan aiki yaje ya gayawa Allah.“`

.
================

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply