Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 88


Bibiyata Akeyi 88
Viral

Page 88

*
*Hanna* harta fara sabawa da mutanen gidan dan da farko ko abincii suka bata, baxata ciba, yanzu hartakan zauna idan sunyii abun dariya tayi tayi nawuce hankali,”

Hussentu ne tadubi diddi tace, diddi wallhy kullum idan naga yarinyarnan tausayi take bani, bansan su inne da yasa ishaq idan kusa dawo wani irin kallo zasu mata ba, bansan da Wata manufa zasu d’auketa ba, su halinsu yafice daban, wallhy diddi kaman bakene kika haifii yaya ishaq ba, kamar innece ta haifeshi, diddi batace komai ba, tacigaba da cewa, wallhy inason yarinyarnan har cikin raina, jinakeyi kamar y’ar uwata, Allah idan sukace tabar gidan saidai inbita mutafii tare, diddi dai shiru tayi saican tace wallhy nima inason yarinyarnan, sosai, banjin zanrabu da ita idan bawai tadawo hankalinta bane tanemi komawa gun danginta ba, yanzu tashi kije kidubamin metakeyi, kotacii abincin, tashi tayi tace to, azaune tasamu *hanna* tace, kincii abincin?”
Juyowa *hanna* tayi amma batace komai ba,” ganin abincin tayi agabanta furr tak’ii cii, riqo hannunta tayi tace taho muje, tashi tayi tabita, dan yanzu komai nata da sauk’ii bandadai tayita dariya ba, bazaka ta6a ganewa da hauka ajikinta ba.”
Tana zuwa tace diddi kinga tak’icii furr, dubanta diddi tayi da kalar tausayii tace, kinsan tanada juna biyu bakowani irin abincin suke so ba, riqe hannunta taje store da frigde kinuna mata koda abunda zataso, idan tagani zata nuna, jan hannun nata tayi zuwa frigde.”

================

Da mamaki suka tsaya suna kallon sa, idanuwansa sunanan arufe kamar kullum, maganar ma bazakayi zaton daga bakinsa tafito ba,
Dama asali miskilancin sane yatashi, shiyasa yak’ii magana bawai dan bazai iyaba, bakuma dan maganar ta gagareshi ba.”

Mama ta amshi maganar bakaso akaika to wani dalili zaisa bazaka cire damuwa aranka ba kasamu lpy, abdallah kayi tawakalli ga ubangijinka, kasan cewa jarabawace yad’aura maka, nan tayita masa nasiha, mai martaba ne yace ka shirya gobe da tafiyar dan nan d’innan bawai naga wani cigaba bane, idanuwansa arufe yak’ara cewa, har indai sai nafita kafin nawarke tom bazan ta6a warkewa ba.”
Ummii ne takalli mai martaba tace dan Allah kabarshi anan d’in, tunda yayrada zaicire damuwa aransa.”
Mai martaba bai ce komai ba yafuce, office d’in likita yanufa, yana shiga litikan yatashi yana gaidashi, yana cewa ranka shi dad’e da kanka? Aida ka aika nazo, mai martaba bai kulashi ba yasamu waje yazauna sannan yadubeshi yace, nafasa fita dashi, Ina anan zaisamu kulawa sosai?’
Nisawa likita yayi yace zai samu amma saida taimaknku, dan mukad’ai abun yagagaremu, bazamu iya mukad’ai ba, dole aringa d’auke masa damuwa, sannan idan anan ne jinyan 2month zaidaukemu idan ak’asar wajan ne baifii 3weeks ba,
Mai martaba yace bbu komai, hakan kuwa akayi, anan aka fara jinyarsa, mama takanje bauchi tadawo,
Kuma kullum takansashi agaba da nasiha, harya fara cire damuwar,
Saidai abunda ba’a rasawa yanzu rashin magana harta nunka nada, dan saikayi sau 5baikulaba, watanshi 1yasamu lpy, amma sanda jinyarda suka yanke mata 2month dan yanda suka kalli yanayinsa mai karfin zuciyata, amma mafii akasarii akanyii 3-4month ana jinya, mai martaba ne yahana asallamesu har sanda yacika 3month cifff a hospital.”

===============

Cikin *hanna* yad’an tasa kad’an, amma kana ganinta zakaga alamun tanada ciki, gawani kyau da takara, abun mamaki harda k’iba, dan yanda take samun kula,

Yaune takasance ranarda su ishaq ta inne zasu dawo, maimakon murna sai suka shiga fargaba da zullumii,”
Wasu rantsattsun motocine suka fara shigowa gate d’in, diddi ta kalli Hussentu wanda lokacii d’aya duka gabansu yafad’i tace, yi maza kisakata ad’akinki ki kulle dasaurii tajata suka shiga d’akin.”

To be continued

Ur’s
Z33iiyyb3rw3r

*BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL’_

.

================

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply