Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 92


Bibiyata Akeyi 92
Viral

PAGE 92

*
Yau ma kamar wancan karon sassafe sadiq yatashi yatafi ruga d’an d’auko malam,
Dake malam baisanda zuwansa ba, kuma baishirya ba, sanda yajirashi ya shirya, sai 1:00.suka iso, yana zuwa yabaukaci ganin *hanna*, kawota akayi sai zazzare idanuwanta takeyi kamar wanda tayi k’arya, dasaurinta tak’arasa gefen inne tazauna.”
Cikin damuwa inne tafara yimasa magana, tace, malam duk randa nabata ruwan addu’oii nan, saitayi k’ok’arin halaka kanta kokuma abunda yake cikinta, kuma tanashan wuya sosai.”
Malam ayad’anyi shiru kafin yace, maganar gaskiya yarinyarnna turan aljanu aka mata, kuma ahalin yanzu idan aka matsa sai anciresu, kafin su fita zasu cutarda ita kokuma abunda yake cikin ta, zasu iyayin sqnadiyar cikin, idon inne ya cikciko tace yanzu wannan yarinya wani abu zatayi dahar za’a tura mata aljanu, mutane kokad’an bbu imani.”
Malam ne yadanyi jim kafin yace, Aibasai tayi musu wani abunba, yanzu d’an adam ake kiwo, ba dabba ba.”
Yanzu nakaoma zanyita yi mata addu’a da sauk’an qur’ani, yanzu zaikai kaman yaushe haihuwanta?”
Diddi ne tace, ba lallai ya k’arasa nanda wata biyu ba.”
Toh in sha Allah nan da wata biyu zata samu sauki, dan yanzu Allah kad’ai yasan halinda danginta suke ciki.”
Jijjiga kai inne tayi tace, hakane dole zuri’arta zasu kasance cikin tashin hankali da zullumii.”
Allah yabata lpy, dukansu suka amsa da amin, sai bayan la’asar, sadiq yamayar da malam.”

Marshall ne zaune da kayan soldier’s, ajikinsa rabonsa da saka kayan yakai 7month, yarame kam sosai, amma Sun masa kyau sosai, wayansa yad’auko yayi dialing numb d’in, captain Ahmad wanda ayanzu yadawo genaral Ahmad, yana shiga kuma aka d’auka, baijira wani sabon zance ba, yace kasameni a shahi na.”
Kusan 30minute kafin yak’araso sanda yakirashi yanemi izinin, shiga kafin yashigo, ganin agonnasa ayanayin daya dad’e bai ganshi ba yasa yak’araso dasaurii, yana fara’a, wajan zama yabashi, sannan yace magana nakeson muyida kai sannan kuma, ina neman alfarma, dasaurii, G Ahmad yace hava, yallabai yanzu har zaka nemi abuu awajena, sai ka kirashi da, taimako, kafadeshi kawai kai tsaye amtsayin umarni, Murmushi Marshall yayi sannan yace, yanzu zaka goyi bayan nayi aure?”
Aure kuma yallabai kokadan bazan goyi baya ba.”
B’atan madam ba hakan yana nufin bazata dawo bane, wallhy yallabai Ko 10yrs zatayi kajirata, dannasan idan itane awajanta, itama jiranka zatayi.”
Yak’e Marshall yayi akaro na biyu sannan yace, kuma er uwarta sukeso na aura, girgiza kai G Ahmad yayi yace, gaskiya hakan baidace ba,
Jijjiga kai Marshall yayi yace shiyasa nakeson kataimaka mun yau daddare kaje gidansu amatsayin, kana sonta, banso kab’oye mata komai, inason kaida ita, ku nunawa iyayenmu kun dad’e kuna soyyaya, dannasan nata wajanma bayarda zatayi ba, idan kaje mata da wannan maganar zatayi saurin amince wa.”
G Ahmad ne yace indai hakan zaitaimaka, to nayarda zan aureta, zanje yau nasameta, nagode Marshall yace, Ahmad ya girgiza kai yace bbu godiya atsakanina dakai.”
Ya tashi yafita.”
Dad’i ne yakama Marshall nafarko yarabu da aurenda akeso ayi masa, nabiyu kuma, na cikawa *hanna* burinta, dan bai manta lokacinda tace masa, inason kacikamun burina kasa, C. Ahmad ya auri hameeda.”
Tashi yayi fuskarsa ad’an sake yanufii sashin mahaifinsa.”
Su kansu sojojin sa sunyi mamaki, yanda yau suka ganshi, yana cikin kuzarinsa, da sallama yashiga, falon mahaifinnasa, amsawa mai martaba yayi dan ya dad’e baiji shi da irin wannan muryar ba.”
Koda zaiyi sallama saidai yayi ciki-ciki, kallonsa mai martaba yakeyi, har yak’arasa shigowa,
Yazauna yana gaidashi, shi kansa yaga fara’a kwance fuskar mahaifinsa, alamun yaji dad’in ganinsa ahaka.”
Mai martaba ne yacigaba da cewa, dama gashi inason muyi magana, sosa kai Marshall yayi yace to ai gani abba.”
Gyaran murya mai martaba yayi yace, dama inason na fad’a maka munyanke shawrar yimaka aurene, zaro ido yayi, sannan yayi kamar baisaniba yace, aure kuma abba, eh aure tunda kakasa daukan qaddara, kuma er uwar matarka zan aura maka, wacce kenan abba?, er gidan k’aninsa, kamar da gaske Marshall ya nuna firgici yace, abba budurwar Ahmad nefa, wani Ahmad? Dan gidan kanwan ummii mana, abba shine saurayinta, yaya za’ayi haka, k’anina nefa kamar yanda nakejin affan haka nake jinsa, kuma ku kad’ai yasani matsayin iyayensa, zai d’aukeku masu sonkai idan kukayi haka.”

Shiru mai martaba yayi duk jikinsa, yayi sanyii, yadubi Marshall yace tashi kaje, zankira Ahmad d’in zanji tabakinsa zansame ka.”

Tashi yayi yamiqe yafice murna aransa fall, yayi nasara danya fahimci jikin abba yayi sanyii.”

Abba ne yashigo afalo yasamu umma, badai yadda take walwala ada ba, zama yayi kusada ita yace khadija, juyowa tayi takalleshi, yace inaso muyi magana, amma kuma yakamata ki fahimceni, yakamata ki fahimci mezan fad’a miki, dan kada kiyi mana gurguwar fahimta, kisani komai mukaddarine daga Allah, nan yafara zayyano mata bayani, kallonsa kawai umma takeyi, ji takeyi, kamar tashaqe shi kokuma tarufeshi da duka, juyarda kai tayi gefe, har yagama bayanansa ya wuce, tabishi da kallon banza kawai dan wani haushi yabata.”

Tashi tayi tanufii d’akin hameeda, tana zuwa taganta kwance akan gado, duka ta d’aka mata, wanda yasa hameeda zabura tatashi, tana shirin kurma ihu.”
Umma tace da Allah rufamin baki, nasan abbanku zuwa jmawa zaizo miki da maganar wai zasu aura miki mijin er uwarki, idan kika kuskura kika amince nidake, zaro ido hameeda tayi, sannan tace umma er uwata kuma wacce?” mijin *hanna* zasu aure miki, wallhy idan kika amince saina kasheki, kuka hameeda tafashe dashi, tace haba umma yaya za’ayi na’amince, kamar uwa d’aya uba d’aya fa muke, kima amince dan wallhy zan iya kasheki, kokuma in tsine miki, kuka takeyi tana cewa wallhy bazan amince ba umma.”
Rufo mata k’ofar tayi da karfii, itakuma takoma takwanta tacigaba da kuka.” jitakeyi kamar amafarki wai mijin *hanna*,

K’arfe takwas dai-dai mai gadi yashigo afalo yasamu umma yagaidata, sannan yace, hajiya wani yana sallama da hajiya hameeda, ak’ofar gida, umma ne tace jeka kace tana zuwa, leqa d’akin hameeda tayi taganta tanata kuka kamar ranta zai fice, bak’in cikinta d’aya wai arasa wanda za’ace ta aura sai mijin er uwarta.”

Kitashi kije ana sallama dake awaje, mamakine yakama hameeda ganin, Ko ance ana sallama da ita umma sai tace ace batanan.”
Yau itada kanta take cemata tajeta ana kiran ta, harta juya zata fita sai tace, yauwa sannan ki gyara fuskarki, ki tareshi da tad’i, har babanku yazo yasameki.”
D’aga kanta kawai hameeda tayi, sannan tatashi tashafa powder, da turare tasaka hijabinta tafito fargabanta d’aya Ko waye yazo wajanta, itadai data aurii mijin *hanna* gwamma koma waye ta aura, afalo tahad’u ta umma, har tawuceta tajii umma nacewa, kuma kada kiga nace kifita kije kiyi rawar kai, ki kulada mtumcinki, kisan cewa Allah yana ganin ki, d’aga kanta kawai tayi tafice.”

Ajikin mota tasameshi yana jingineda mota, tun kafin tak’arasa tagane wanene.”
Tana isa tagaida shi, ya amsa, bai boye mata komai ba yafad’a mata yanda sukayi da Marshall, Jijjiga kai tayi tace wallhy hakan yafii, bansan wani irin abuu sukeson aikatawa ba.”
Kallon fuskarta yayi yace, kin amince dani kenan, kai kawai tad’aga masa, nan ya bata labarin sa, har tad’an saki jiki dashi suna hira.”
Motan abbane tadanno kai, tun daga nesa yahangeta tana hira, bai kulata ba yayi saurin parking Motan ya fito ya shigewa gida.”
Anan falon yasamu ummii, zama yayi cikin sanyin jiki yace wai baki fad’awa hameeda wannan maganar bane naganta atsaye tana hira, umma ne tace, banfad’a mata ba, tunda naga tanada wanda takeso, kulllum yana zuwa hira nayau d’aya ace anmata miji, dawuya ace na fad’a mata wannan zance lokaci d’aya sai dai idan kai zaka fad’a mata idanta shigo.”

Ganin lokaci yaja g Ahmad yace, barin tafii time yanaja sai gobe zanzo, kai tad’aga masa, sannan yace kuma kada kisake yin kuka anshawo kan matsalar dan fuskarki tanuna kinyi kuka, bazan sake ba tace sukayi exchange na number, sannan sukayi sallama.”

Afalo tasamu abba gabanta yayi mugun fad’uwa naganin sa, amma tadake tace sannu da dawowa abba, yawwa sannu yace, tana k’okarin wucewa, yace dawo nan zamuyi magana dake, dawowa tayi tazauna yadubeta yace, waye wannan wanda naganshi tareda ke yanzu, sunna kai tayi kamar maijin kunya tace, abba k’anin mijin *hanna* ne, shima sojane yanzu yakai matakin general, gaban abbane yafad’i, ya k’ara maimaita k’anin mijinta kuma, tace eh, yace Yau yafara zuwa kenan, girgiza kai tayi tace, A’a abba tun bikin *hanna* muka had’u baku ta6a had’uwa bane.”
Yadad’e ma yana cewa zai turo banbashi dama bane.”
Abba bai iya cewa komai ba yace tashi kitafii, tashi tayi tamiqe, dad’ii yacikata ganin yanda jikin abba yayi sanyii.”

To be continued

Ur’s
Z33iiyyb3rw3r

[8/14, 5:15 PM] Maryambawa: *BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL’S_

 

“`Hak’ika masoyinka shine wanda zai nemeka bayan bacewarka, hak’ika masoyinka shine Wanda zai damu bayan rashinka, hak’ika masoyinka shine Wanda zai soka bayan idonka.”
Nidai bbu abunda zance da irin yanda kuka nuna kulawa dakuma soyayya gareni.” Kudaina d’aga hankalinku ina cikin koshin lpy.” Am extremely ok, Nagode da kulaarku, Nagode way’anda Suka kiranki, da yawa naga sak’onnniku, da Kuma wanda nake ransu basu samu damaba.” Godiya da yawa ba adadi, soyayyarku gareni tasa naji dad’i tak’aramun karfin gwuiwa, kusani cewa Ina k’aunarku, Ina jinku har cikiin jikina.”“`

 

.

 

================

 

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply