Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 94


Bibiyata Akeyi 94
Viral

Page 94

*
Bakin labour room suke azazzaune, yayinda i’shaq ke zagaye, wajan yakasa zama, gabaki d’aya hankalinsa atashe yake, gani yakeyi kamar *hanna* zata mutu kamar yadda, maman ihsan tarasu wajan haihuwar ihsan d’in,
Mata uku ana kawowa, kusada d’akinda take suna haihuwa.” amma itakam shiru, ihunma takasayi, dan ita ba hankaline da itaba, kuma ba bakine da itaba balle tayi ihuu.”
Nan hankalinsu yak’ara tashi, barin i’shaq da jikinsa har 6ari yakeyi, idanuwansa sun kad’a sunyi jajjir.”
*Hanna* cikin labour room, abu yak’icii, gabaki d’aya, dan duk yadda sukeso *hanna* batayi, da azaba ta isheta tafara kai musu duka, nan suka fahimci hankalin ta ba k’alau ba, fitowa wata nurse tayi, dasaurii i’shaq ya nufeta, tambaya d’aya da yayi mata shine, ya take?”
Girgizakai nurse din tayi, sannna tace, bata sauk’a ba, amma tanada ta6in hankali ko?”
Wani irin bak’in ciki ne yatokare i’shaq yace, jin takirata da mai ta6in hankali nan danan ransa ya6aci, cikin zafin rai yace, ke wace irin wawiyace da bazaki duba file ba kafin kifara aiki, kisan awani yanayi zakiyi treating patient, wannan sakarci ne, ashe bakisan aikinki ba kenan, ko anfad’a miki bai rubuce cikin file d’inne, wallhy idan kika sake Wani abu yasameta, ki kuka da kanki.”
Ganin yana masifa kamar wanda ke shirin dukan nurse d’in, diddii ta fahimci halinda yake ciki, tasan abunda zaijii, awannan lokaci, mutuwar matarsa sabo fill zaidawo masa, gabaki d’aya ya rikice, kamoshi diddii tayi tace, zo kayi hak’urii, in sha Allah, zata sauk’a lpy.”
Sannnan tajuya takalli nurse d’in tace, kije kici gaba da aikinki.” juyawa nurse d’in tayi cikin k’unar rai.”
D’aure *hanna* sukayi yadda bazata 6ata musu aiki ba.”
Dan su kansu sun gaji, tun safe ake abu d’aya.”
Dan har ancanja wasu nurses d’in.”
Sosai haihuwar tazo gadan gadan.”
Wani irin ihuu *hanna* tasake, yace, “`yareeemahhhh“` da k’arfin gaske, wanda saida har wajen d’akin, ya amsa, dasaurii i’shaq ya miqe atsorace zai shige d’akin, kukan jaririn dayaji ne, yasashi tsayawa bbu k’akk’autawa, kuwa yaro yacigaba da tsala ihuu.”
Juyowa i’shaq yayi ya kalli diddii yace, diddii ta haihu fa, d’aga masa kai kawai tayi, dawowa yayi yatsaya, yana jiran fitowarsu.”
Wani k’atoton yaro *hanna* ta haiho, bbu yanda yabar mahaifinsa, sakk, gashi cikin k’oshin lpy, dansai kuka kawai yakeyi, itakuwa *hanna* tunda yaron yafito tajii kanta yafara juyawa, har aka mata stiching (dinki) batasan anyiba.”
Jini tafara zubdawa Sosai.”
Jinin yafita ajikinta wanda su kansu, doctor da nurses d’in abun yabasu tsoro.”
Nan suka rufu akanta Dan suga sun tsaida jinin amma abun ya faskara.”
Sunfii 30minute kafin yatsaya, nurse ce tashirya yaron, ta fiddashi su diddii suka ganshi, kar6an yaron inne tayi, tace masha Allah wannan d’a ai inaga ubansa balarabe ne, dan bbu yanda yabar larabawa, k’arasowa kusada ita sukayi suna kallon yaron, kyakkawan gaske.”
Sai mutsul-mutsul yakeyi, cikin k’aramin tissue towel.” nan dumfull d’insa ya bayyana, afili, subhanallh😍 mahaifinsa sakk, dasaurii hussentu takai hannunta wajan tana cewa, diddii kalli.”
Nurse d’indake bayansu ne wanda takawo yaron, tamiqo hannu tace ku bani shii.”
Yanzu za’a kaishi nursery, kar6an sa tayi sannan tajuya zata wuce, i’shaq yayi saurin tsareta, wanda shi duk rubibin kallon yaronda sukeyi hankalinsa yana wajan *hanna*, tsaida ita yayi yace, yajikin mahaifiyar yaron.”
Kallon sa nurse d’in tayi tace, tana buk’atar jinine, yanzu muje nakai yaron sai agwada naka dana wannan, tanuna sadik, ko akwai wanda zaizo dai-dai.”
Binta sukayi bayan ta ajiye yaron, taje gwada jinin, duk cikinsu bbu wanda jijinsa yazo d’aya da nata, dan jininta O+ ne, yana wahalan samu.”
Nan suka shiga neman jinin, har dare yatsala ba’a samu ba.”
Ahaka *hanna* takwana agalabaice, bbu yanda take, danko numfashima dakyar takeyi.”
Marshall shida yaransa, camroon suka wuce, dan anyii rikici, sosai.” Awani jiha, dake cikin camroon, yaje dubasune, amma daaa baiyii niya ba, zancan aurennnan ne yasa shi barin k’asar, yafake da zuwa nan, Awani hotel suka sauk’a.”
Yana zama tunaninsa d’aya wani hali *hanna* zata shiga, idan tajii wannan zancan auran, haka kawai yakejin yana, closed to *hanna* dan duk wani lokaci da zai had’u da ita tunkafin ya aureta, har indai zasu had’u saiya jishi awannan yanayi.”
Yana zaune afalon d’akin hotel d’in yaji ana knocking, idonsa arufe yace coming, shigowa soldier’s d’in sukayi, dake dama tundaga floor din k’asa da sama, sunkmashi da sojojinsa, saraa masa yayi yace, sir time yana wucewa,
Shiru yayi nay’an minute kafin yamiqe yayi hanyar waje, shima yabishi abaya, kai tsaye asibitin suka wuce, suna shiga gabansa ya tsananta fad’uwa, dafe zuciyarsa yayi sannan ya lumshe idanuwa, bayan sunshiga, doctor’s d’in dama sunsanda zuwansa, suka taryeshi, suna zagaya kowani sashi dashi, yagama duba patient d’in, wata nurse ce tashigo, takalli babban nurse dake bin marshall abaya tace, 6ta patient dinkinnan fa tanajin jiki, yanzu haka numfashinta yana sama-sama, d’ayan nurse dinne tace nikam narasa yadda zanyii, bayadda ban nemi jini kamar nata ba amma narasa,”
Marshall wanda yatsincii kansa da sauraren maganarsu, yajuyo yakallesu yace, kizo ki gwada nawa, idan yayi asaka mata.”
Duk doctor’s nawajan mamaki yakamasu, bai sake maganaba yanemi waje yazauna, babban doctor na hospital d’inda kansa yagwada, aikuwa yazo dai-dai, eban jinin suka farayi, laida biyu suka eba, ya tashi ya ja, hannun rigarsa, yasa bottle ya wuce zai fita, soldier’s dinsa suka rufa masa baya.”
Sanda yazo fita a hospital d’in gabansa ya tsananata faduwa fiyeda shigowarsa.”
Tsayawa yayi yajuya yakalli asibitin, yafii 3minute yana k’are masa kallo sannan aka bud’e masa k’ofa yashiga motar, sukaja, sukatafii.”

Batare da 6ata lokaci ba aka sakawa *hanna* jinin, laida d’aya kawai ta shanye, and’qura na biyun ta farfad’o.”

*Kuyi hak’uri wallhy ciwon, k’in typing yakamani, irin sosai d’innan fa, kuyimun addu’a nayi nagama nahuta.”*

To be continued

Ur’ s Z33iiyyb3rw3r*BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL’S_

“`Manzon Allah tsirada amincin Allah su tabbata agareshi yace, (man mata) Manzon Allah yace duk wanda yamutu, (wahuwa yad’uu ma’allahi iddan) alhali yana kirawa Allah kishiya, wato yanayin shirka, yana had’a Allah dawani, (dakalan nara) Manzon Allah yace zai shiga wuta.”
Allah karabamu da yin shirka, domin na d’aya daga cikin munanan ayyuka.”“`

Wannan shafin nakine *ZAYNAB UBA AHMAD (momyn yasmeen)* inasonki irin sosai d’innan Allah yaraya mana *yasmeen* musha biki, har shoki saina kwaso.”
Mummynta zeeyy na gaidata, yasmeen d’ina agaishemunda *baabaa(ameerah)*😜 ace mummy na gaidata, itada *iyah(ummii)*🙊🙊

“`Raheenat mahmoudouu, tunatarwane agareki, inasonki, irin bohut bohut d’innan, Allah yabarmu tare, ranar aurenki sai naje nijar fa.”😜
Niamey zatayi bak’i.”“`

.

==============

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply