Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 95


Bibiyata Akeyi 95
Viral

Page 95
*
Wajen amare yau akayi walima dake gobenne yakasance d’aurin auren, hafsat da hameeda duk a bauchi akeyin komai, yayinda itakuwa intisar tana kano event kuwa anyi sunfii kala shidda, bbu wanda ango ya halarta aciki, duk da tajii zafii bbu yanda ta iya, dan tasan burinta yana gabb da cikawa, gashi gobe d’aurin aure bbu ango bbu alamunsa, ita ba waya sukeyi ba, balle tatambayeshi yanda yashiga, tunda wannan abun yazoma, kotakirashi baya d’auka.”
Ta lula cikin tunani, kilishi dake k’are mata kallo, ta ta 6ata, dasauri tajuyo tana kallon ta, 6ata rai kilishi tayi sannan tace, mekike tunanine haka?” ko kinaso kiramene gobe d’aurin auren ki?” girgiza kai intisar tayi tace, Wallhy umma yaya yareema nake tunani, gobe ne d’aurin auren amma bbu shi bbu dalilinsa.” ta6e baki kilishi tayi tace, ai gwanda daya tafii d’in idan yananan zai iya jaaa mana matsalla, kar mahaifinsa yaga yashiga wani hali yafasa, kuma kinsan irin sonda fulani ke masa, zai iya zuwa yagaya mata, karki ga kina matsayin jikarta, Wallhy saitace afasa.” ajiyar zuciya intisar tasauke, kilishi tayi murmushi tace yawwa d’iyata, idan yaga dama kada yadawo sai aurenda wata d’aya mudai burinmu yacika ana d’aurawa zamusan yanda zamuyi dashi ya mance, wancan shashashar.”
Sai alokacin intisar hankakinta yakwanta, tashi tayi tanufii wajanda k’awayenta suke.”

Tunda aka fara zancen bikinnan afeeya ko leqo qafarta gidan batayi ba, su halima ma dan gudun 6acin ran kilishi ne, balle labba ta tabar k’asar gabaki d’aya.”
Ummii batada bakin magana, ido ne kawai nata.”

*Hanna* ta farfad’o, lokacin su diddi suna zazzaune ad’akin itada inne, da i’shaq, hussentu sadik yamayarda ita gida, dan zataje dabo abinci, dakuma kawo sauran kayanda ake buk’ata.”
Da kallo *hanna* tabisu alamun rashin sanii, atattare dasu, dasauri diddi tamiqe tana sannu bodd’i kada kiyi garaje mana, kinsan jikinki bbu k’arfii, bayanta *hanna* take leqawa ko zata gano marshall, saidai akasinsa, wanda i’shaq ne, dawowa da kallonta wajan diddi tayi tace, ina yareema?”
Diddi tarasa wanne zatayi dan da’almu *hanna* tadwo hankakinta, murnar dawowa hankakinta zatayi?” kokuma bak’in cikin mantasu da tayi?”
Tasowa inne tayi tace, ki kwantarda hankalinki, kinga bakida lpy yareema kuma bayanan, girgiza kai tafarayi tana cewa, Wallhy yana nan, ga jininsa ana k’aramun nan.”
Kallon juna sukayi, sannan i’shaq yace, ya’akayi kikasan jininsane? Bayan kina sume aka k’ara miki jinin.”
Harara ta wulla masa, sannan tace jinin abunda nakeso d’inne bazan iya ganewa ba.” bacin nasan duk duniya bbu wanda zai bani jininsa saishi.”
Maganar ta doki i’shaq sosai, shiyasa yayi Shiru baik’ara cewa komaiba, don shi ya tabbataa sonta yakeyi.”

Kuka *hanna* tafarayi tana cewa, dan Allah kuyiwa girman Allah kufad’amun yanda yake, rarrashinta sukeyi, sannan diddi tace wallhy bbu wani yareema Anan, dasauri *hanna* tad’ago tadubeta tace, tayaya zakice bayanan to a’iina aka samo jininsa?.”
Ku suwaye? Ni wallhy bansanku ba.”

Basukai ga bata amsa ba, nurse tashigo d’aukeda jaririn aciki bed nasu tana turashi, zagayanta uku kenan, tana samu *hanna* bata tashi ba.” k’arasawa tayi gaban gadon tace, kin farka, tafad’a tana ciro yaron, kar6eshi ki shayar dashi, kwanansa d’aya bai cii komaiba.”
Dakallo tabi mutanen d’akin, ita dai bata ta6a sanin tanada ciki ba balle kuma har yaro, d’aga mata kai inne tayi tace k’ar6eshi, yaronki ne, saka hannu *hanna* tayi tak’ar6i yaron Sanda gabanta ya buga, kamannin yaron d’aya sakk da ubansa.” kallon su tayi tace nashiga uku, dama inada ciki ne, yaushe?” k’arasawa kusada ita inne tayi, tace ki kar6i yaron ki shayardashi zanmiki bayani.” riqe yaron tayi dakyau,”
Futa i’shaq yayi yabarsu ad’akin.”
Tace wallhy bazan shayardashi ba harsai nasan ku su waye.” wannan yaronkam ko ba’a fad’aba nasan yaro nane, kama bazata nuna k’arya ba.”
Idankuma mafarki yakeyi plz kutasheni.”
Ba mafarki kikeyiba injii inne, watanki takwas awajanmu, zaro ido *hanna* tayi tace wata takwas, kwarai kuwa injii, diddi, tun lokacinda muka tsinceki, bamu sameki cikin hankalinki ba, munsameki baki da bakima balle kiyimana bayani.”
Kuka tasaka kawai tarungume yaron tsammm ajikinta, tana Kuka tace nagode muku, nagode sosai da kulawarku, samun mutane irinku sai an tona.”
Amma dan Allah kada kubarii yatafii agarinnan wallhy yananan, dan inada tabbacin wannan jininsane,” a lokacin i’shaq ya shigo da sallama yace.” hasashenki bai zama gaskiya ba.”
Wannan wani soldier ne yaji ana neman jini yabaki.”

Murmushin takaicii *hanna* tayi cikin babbar murya tace, field marshall Abdullahi abdulaziz lamid’o, zaro ido daga nurse d’in har i’shaq dayanzu yaje yatambaya yayi, dan sunanda aka gyamasa kenan.”
Takawarda kai gefe dan jikinta ciwo yake mata, k’arfin hali kawai takeyi.”
Zama i’shaq yayi baida bakin magana.”
Sai a lokacin hussentu ta dawo itada sadik, daukeda kayan tea ahannunta, had’a mata tea d’in akayi sannan aka miqa mata, wata iriyar yunwarda takeji tasakata shanyewa tass.”
Sannan tad’an koma ta kwanta.”
Diddi ne tace yaronnan yanajin yunwa, kibashi abinci.”
Shiru tayi kamar bataji ba, Sanda tad’auko yaron tasaka mata shii agabanta.”
Tashi *hanna* tayi tak’ar6i yaron, diddi tagwada mata yanda zatayi, kunya yasa ta sakashi cikin hijab, tafara bashi.” runtse idanuwanta tayi tanajin son yaron akowani ga6a na jikinta, yafiii 30 minute Sanda tajii alamun yayi bacci sannan tacireshi.”
I’shaq ne yashigo, yadubi *hanna* yace,” ganinsa zai mun wahala sosai, yanzu tunda an sallame muje gida kiyi wanka, sannan mutafii wajansa.”
Tattarawa sukayi suka koma gida, nan diddi ta wanketa itada yaron tass, cikin kayayyaki masu tsadar gaske, wanda i’shaq yasaya aka sakawa yaron.”
Sai yamma liqis suka nufii hotel d’inda yake, amma tundaga compund d’inda yake furr akaqi barii su shiga.”
Har magrib suna wajan, receptionist kuma sunki kiransa awaya, tundaga nan *hanna* tafara kuka.”
Dakyar suka lallasheta takoma gida.”

Washe gari kuwa, can nigeria sai shirye shiryen d’aurin aure sukeyi, kasancewar yanda abun zaifii sauk’ii yasaka, aka d’aura dukkanin auren akano.”
Ababban masallaci da farko aka fara d’aura auren *hameeda da Ahmad sannan bilal da hafsat.”
Ak’arshe aka d’aura auren marshall da intisar, bayan angama akayi reception.” kowa sai tambayar marshall yakeyi amma kuma bbu shii.”
Hakanne yasa mai martaba yad’aga waya, yakira shi, cikin zafii yace masa yanaso ayau d’innan yakwana agida, duk abunda yake yi, yabari yazoshi, and’aura aure, kashe wayar marshall yayi tsabar ba k’in ciki Sanda yayi kuka.”
Nan danan idanuwansa suka kad’a sukayi jawurr.”

Ba’adade dafad’a masa wannan maganarba, kawai saiga wani soldier yashigo sara masa yayi sannan yace, yalla6ai, tun Jiya wasu mutane sukazo wai sunason ganinka.” yauma gashi sundawo.”
Cikin zafii marshall yace, bazan samu damar ganin kowaba, yanzu haka and’aura aurena, kasanar nanda 30 minute zantashi zuwa nigeria.”
Da toh ya amsa yafita yana tausyin agonnasa duk dacewa bawai yadad’e dashi bane, amma anfad’a masa bacewar matarsa dayake bala’in so.”
Samun su *hanna* yayi yace, ku tafi oga, bazai saurareku ba, yana cikin wani yanayi, yanzu aka d’aura aurensa.”

*Hanna* dake zaune Sanda tazube k’asa, dan firgicii, zata sake magana yayi saurin katseta ya wuce abunsa.”

To be continued

Ur’s

Z33iiyyb3rw3r
[9/1, 6:27 PM] Maryambawa: *BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL’S_

 

_Your secound page, is here my *HAJJA CE* Allah yabarminke har abada, ke abun alfaharice ga al’umma.”_

 

*Idan kuka kalli, late reponds Kuyi hak’uri massage suna yawa wallhy har taraddadin bud’e data nakeyi dan nasan abunda zan tarar, Allah nafiku k’aguwa na gama na huta.” dan Allah idan kinyi magana banyi reponds ba amin uzurii.” kunsan d’an adam ajizi ne, nima inasonku danna tabbatar masoyinka shike nemanka.” ina sonku sosai.”*

 

*Y’an group dina kad’an yarage ayankani yau.” nadaiyi nahuta😒abarni nasha iska*

.

================

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply