Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 97


Bibiyata Akeyi 97
Viral

Page 97

*
Hafsat da hameeda, duk gidan mai martaba za’a fara kaisu, dake ita hafsat mijinta d’an libya ne, shikuma G. Ahmad gidan yatashi.” daga bauchi duka aka d’aukosu, sukayi kano.”

 

Kilishi atsorace tajuyo jin irin kiranda, k’awar intisar take mata.”
Tashi tayi dake tana cikin k’awayenta tana tambaya, manene yafqru haka aikin tsoratani.”
Agigice tace intisar tasume.” Saka hannu akayi, Kilishi tayi tace, wana irin tasume manene yasameta, ke kinada hankali kuwa.”
Yarinyar tafara wallhy umma ba k’arya nakeyi ba.”
Angonne yanzu yakirata waiya saketa saki uku shine……?” aibata k’ara saba, Kilishi ta danno wani ashar dan babban,,,,,,, ta mako shi, dan uwarsa k’arya yakeyi, ba’ahaifi kakar uwarsa bama.”
Tana danna ashar tawuce zuwa shashin mai martaba, danko takan intisar batabii ba.”
Yana tareda bak’ii amma taso shiga aka hanata.”
Zuciyarta tana zafii tawuce shashin ummii, wanda ke zaune batasan abunda ke faruwa bama.”
Tana shiga ko sallama batayiba, kuma gamutane ashashin y’an uwan ummii tasukazo, bikin ahmad, dake dan k’anwartane mamanshi da babanshi sunrasu tun yana yaro duka iyayensa larabawane, kasancewar and’auke marshall lokacin yatafii makarantar army, yasa tanemi abatashi, bawanda yamata gardama, aka batashi tagoyashi.”

Tana bankad’owa tasamu ummii acikin en uwanta, tatsaya tak’ara musu kallo, sannan tace matsiyata(😳😳kajimun mata, wai su ummii ne matsiyata 😂😂😂kishiii) shegu munafukai, tajuyo ga ummii tace, munafukar uwa kin zuga d’anki yasaketa ko?” To wallhy kijira kiga abunda zaibiyo baya.” idan wannan shrgiyar matar tasace, yarabu da ita har abada, yacire raii da ganin tama.”
Tabisu da kallo wanda suka tsaya suna kallon ta, batareda sunsan abunda take cewa ba, idan kacire ummii, itakuwa bata tanka mata ba, har tagama tafice.”
Har cikin ran ummii bawai tajii dad’iin sakinda marshall yayi bane, duk da cewa bason auren takeyi ba, amma kuma aitunda anrigada and’aura yakamata yayi hak’uri.” ba tasan lokacin da taja tsaki ba, en uwanta suka tsaya kallonta suna tambayarta menene yafaru?” nan tashaida musu abunda marshall yayi, masu yawan cikinsu sunyi murna wasu kuma suka jajanta abun.”

Bayan mai martaba ya sallami bak’insane zance yakai kunnensa, ransa ya bala’in baci, bai ta6a neman abu yarasa wajan yareema ba saiyau.”
Tunfarko dayace bazai iya aurenta ba, bai maida masa yarinya bazawara ba.”
Duk da cewa amatsayin budurwa take, bahakanne zai hana mutane ce mata bazawara ba.”
Yakira layin marshall yafii sau 80 amma baishiga ba.”

Intisar bata farfad’o ba sai da tayi 2hour’s, da kuka tatashi, takasa magana, babu abunda yake cimata raii kamar yadda ko 2hour’s ba’ayiba da d’aura auren yasaketa, dake ita kad’aine daga ita sai Kilishi yasa tace, Wallhy ummma gobe gobennen kije kiyi abunda za’akashe wannan yar banzan, Wallhy tamutu kawai, natsaneta, ta dalilinta yamun wannan cin mutumcin.” wallhy umma shima kada ki kyaleshi, duk sonda nake masa yanzu najii natsaneshi.”
Kawai kimin maganinsa, yadda bazai k’ara wulakanta wata mace ba.”
Kilishi tace haba y’ata aikema kinsan wannan zaunannan zance ne.”
Dole zan hukuntashi dai-dai da laifinsa, yanzu ki kwanta ki huta.” futa Kilishi tayi tabarta tana, jin zafii da yanzu tana shirin zuwa wajan diner.”

Ummii takira afeeya ta fad’a mana, afeeya harda ihu da tsallan murna.” tana cewa wallhy yaya yareema yabiyani arayuwa, tsaki ummii taja tace kyajida shirmanki, sannan takashe wayan.”
Da yamma aka kawo su hameeda da hafsat, nan shashin ummii aka saukesu, dan Kilishi bazata sauraresu bama.”

Harda mama akawo amare tadubii, ummii tace, amayar yarona tana inane, danni tawajnta zanii.”
Murmuahin k’arfin hali ummii tayi tace, kayya wana yaronki mai jawowa mutane abun fad’ah, kamar yaya mama ta tambaya.”
Ummii tace ana d’aura auren yakirata ya mata saki uku.”
Salatii mama tad’auka tama kasa magana, sukuwa y’an uwan *hanna* dake wajan dad’ii ne yakamasu.”
Mama takasa cewa komai kawai tayi Shiru, fahimtarda ummii tayi Jikin mama yayi sanyii yasa tace, kinsan Allah bazan masa fad’a ba.”
Lokacinda da suka yi shawarin auren bbu wanda ya shawarceni.” ballantana natausheshi, gabaki d’aya nunawa sukayi banda iko.” Sannan yanzuma daya gwada musu halinsa nima bazan tsawatar masa ba.”
Allah yakyauta mama tace, sannan tace amma yarima baikyautba gaskiya.”

 

Suna zaunane mai martaba ya aiko akirawo ummii, ummii tatashi tajeta.”
Tana zuwa tasamesu zaune shida Kilishi da intisar wanda take ta shar6an kuka.”
Da sallama tashiga, mai martaba ne kawai ya amsa bayan ta zauna yad’anyi y’an wasu, addu’oii kafin yafara magana, kinjii abunda yaronki ya aikata ko?” ya nuna mana mu bamu isada shiba, mu mahaifansa bazamu sakashi abuu yamana ba.”
Kilishi tace wallhy yaron baida tarbiya kokad’an, bai d’auki iyayensa da daraja ba.”
Murmuahin ummii tayi tace wallhy d’ana yanada tarbiya, bai ta6a gujewa umarnin d’aya daga cikinku ba.”
Tajuyo ga mai martaba tace, kai kanka kasani tunda kake baka ta6a haifan yaronda yake maka biyayya fiyeda shiba, cikin kissa Kilishi tace ki gyara harshenki sannan Kisan agaban waye kike da sarkii kike magana.”
K’arya kikeyi ummii tabata amsa tamijina nake magana, a waje yake sarki, tunda yarigada yshigo d’aki, nice sarauniyar, abunda bakisaniba shine, inada Lokacinda zanmasa magana amatsayin sa namijina ba sarkii ba.”
Sannan kada kace yaro yak’ii bin umarnin ka, ko sau d’aya baka zaunardashi kace na umarceka daka aurii intisar ba, A’a jin magana yayi awaje wanda hakan yanuna kunbi ra’ayin yarinyar kenan, shi kuma ba’a nemi tasa amincewar ba.”
Nina d’auki cikinsa wata tara nahaifeshi, kuma naraineshi, amma nima ba’anemi shawarata ba, duk wani d’a na halal yana kishin mahqifiyarsa, kuma d’ana maibin umarni nane, ko sau d’aya da annemi na zaunardshi na nusardashi da zai hakura, kai amatsayinka na mahaifinsa baka bashi umarni ba, nikuma matsayin mahaifiyarsa ba’a bani damata ba.”
Ai inaga bai kamata anemeni danya 6ata muku ba, kenan yanzu ansan amfanina kenan?”
Tajuya takalli Kilishi tace inaso kisani ba’a ta6a canjawa tuwo suna, ni mahifiyace, wanda y’ay’anta ke alfahari da ita.”
Sannan kijira agama bikinnan wallhy talllhy tunda kika furta cewa *hanna* bazata dawo ba har abada saikin fitoda ita, dan hakan yana nufiin da hannunki a6atanta.” zan lamunci komai, amma wannan kam bazan lamunta ba, dansai kin fitomin da d’iyata tana fad’in haka tatashi tafice.”
Mai martaba Shiru yayi yau yasan ankaita k’arshen makura, tunda ita bamai magana bace, jikinsa duk yabi yayi sanyii yasaka yashige d’aki, itakuwa Kilishi mutuwar tsaye tayi, tunda aka kawo ummii yau shekara 37 talatin da bakwai amma bata ta6ajin wata kalma mai k’arfi abakinta ba, sai su shari watanni bataji koda tarinta ba, amma yau wai itane ke irin wannan magan ganun?”
Kama hannun intisar tayi sukabar falon.”

7:30 suka tafiii diner, zuwa 9:30 kuwa sundawo dan ummii tace kada su dad’e, aikuwa hakan akayi amare sunyi kyau sosai, Saidai tunda aka fara bikin kullun sai sunyii kukan rashin *hanna* sunsan tabbas datana nan bakin saiyafii haka armashi.”

Afeeya wanda tahalarci diner duka sun tattaro sunyi gida.”
Amaren na daki asashin ummii, yayinda su kuma ummii da y’an uwanta had’eda mama wanda a gidan zata kwana suna falo suna hira.”

 

Tun 9:20.pm jirginsu su marshall yasauk’a, wani irin sanyin dad’i da ni’ima ne ke ziyartar *hanna* bayan wata takwas yau ita ce a k’asarta, gobenna saiya kaita wajan mamanta, ta fad’a cikin zuciyarta, dukansu sun lurada farin cikinda take ciki.”
kai tsaye, gida suka nufa, sunakai 20minute kafin su isa, mamakine yakama su diddi ganin sunnufii gidan sarauta, abun sai al’ajabi yanzu da mummunan riqo suka mata fa.”
suna zuwa marshall yadubii *hanna* yace cutie ki wuce shashin ummii, nasan yanzu mai martaba yana jirana, zanje najii yadda zata kaya.”
D’aga masa kai kawai tayi.”
Tanufii shashin ummii da zamud’in ta, suma suka rufa mata baya.”
Gani takeyi kamar bazata isaba.”
Tana zuwa da gudu tashige ko sallama bbu, su ummii mama da Anty Afeeya tagani wanda sauran bata tsaya dubawaba, dagudu ta fad’a kansu arzane suka d’ago suna dubanta, wani irin ihuu Afeeya tasaka ta rungumeta kamar zata tsagata, itama hannan ihuu tasaka, nan suka fasheda kuka, mama da ummii basuga fuskan ba, saida Afeeya tasaketa, da karfii ummii tace *hanna* d’iyata, aikaman akunnen mutanen gidan kowa yafito hadda amaren, ummii da mama lokacii d’aya suka rungumeta, suna kuka, su diddi suna gefe suna kallon abun al’ajabi, da wata irin soyayya wanda suka rasa afamily dinsu, wanda sai zuwan *hanna* tabasu shi.”

Ummii nasaketa da gudu tayi wajan hameeda ta rungumeta suka fasheda kuka.”
Tajuyo ga mama tashige jikinta, mama Shiru tayi tanajin d’umin y’arta ajikinta.”
Sunfii 15mimute ahaka ummii tace, dukanku ku tashi muje muyi alwala, mu nunawa Allah godiyar mu.”
Zuwa sukayi kowa yayi alwala suna nan aka gabatar da sallah raka’a biyu.”
Ummii tace *hanna* ke meyasa bazakiyi sallah dinva?”
Muryar inne dasuke can bakin k’ofarne takatsesu datace, kwananta biyu da haihuwa aii.”

Hamdala sukayi, sannan Afeeya tace ina d’annwa naganshi?” tana tare d’anta tana cewa narabu da d’an aro tunda nawa nakaina yazo, *hanna* nawasa da yatsunta tace, yana wajan yareema yayi shashin abba.”
Ummii ne Tajuyo gasu inne cikin fara’a tace dan Allah Kuyi hak’uri mun barku awajan bbu komai sukace, nan suka shigo aka basu wajan zama had’eda kayan motsa baki.”

 

Mama tace *hanna* ina kika shiga tsawon lokacii haka? Baki nemi gidaba, sunkuyarda kanta tayi tace mama bana hankalina, kwanana biy da dawowata hankalina, atare mutanen wajan sukace Allah yayaye.”
Ta nuna su diddi tace su suka riqeni tamkar y’arsu ko ince fiyeda y’arsu, ba abunda nanema narasa.”
Godiya aka shiga yi musu.”
Inne tace bbu komai aid’a nakowa ne, nan aka shiga labarai da surutai, wanda kowa kana kallonsa zaka ga farinciki kwance fuskarsa, mamane tafara bawa *hanna* labarin irin halinda marshall yashiga, *hanna* kuka takeyi kamar ranta zaifita, jitakeyi wani irin soyayyar marshall nabin duk wata ga6a na jikinta, ummii ne ke aikii rarrashi tace, haba *hanna* kuncinda rayuwarki take shiga tun kina yarjnyarki yayi, yawa haka, dan Allah daga yau ki kasance cikin farinciki, daga yau duk damuwarki takauce, jarabawa ce Allah yad’aura miki, kuma inada yaqinin kincii wannan jarabawar, yanzu lokacin kar6an sakamakonki yayi.”
*Hanna* na murmushi tana goge hawayenta tace, Wallhy ummii kukan tausayin marshall nakeyi, nikaina bansan wani irin so yakemunba, ina jiyewa randa akace bananan.”
Akullum nayi sallah zanyita roqon Allah yayita dad’a mun sonsa nima najin kwatan kwacin yanda yakejii.”
Murmushi ummii tayi tace, ai bbu wanda ya isa yafad’i iyakacin wannan soyayya, kokuma shi wanda take jikinsan, Allah ne yadorota shiyasan iyakacinta, godiya ga Allah daya dorata akanki daya dorata akan wanda tasan mahimmancinta, dan da wata ce zatayi amfani da ita, ta sashi yaguji danginsa tarabashi da kowa.”
Allah yabarku tare har iya tsawon rayuwarku, ameen suka amsa dukkaninsu, *hanna* tace nidai kumana addu’a Allah yasa mumutu tare dan bansan yanda d’aya zaiyii idan bbu d’an uwansa ba.”
Dariya duka d’akin aka saka, *hanna* tace mama kiramun babana naji muryarsa, dasauri mama tad’aga waya takirashi, baba hadda hawaye yana jiwa Allah godiya, amma nawajan itama takar6a suka gaisa.”

 

 

Moddibbo zauneda mai martaba, Moddibbo ne ke magana yana cewa abudulazizu kayi ganganici, tunfarko dama dazaka nemi shawarata zance maka kada kafara, bakasan irin soyayyar datake tsakaninsu da matarsa ba, Allah daya dasata shine kadai yasan iyakacinta, koksan cewa yarinyar nan matarsa data 6ata sihiri aka mata, kuma acikin gidannan, akansa dan mai yasa za’ayi mata abuu akansa, ace bazai yi hakuri yajirata ba, bashi yafad’a maka yanada sha’awar yin aure ba.”
Wata takwas da6atan matarsa.”
Kayi ganganci shima kuma yayi badai daiba, saidai kada akuma.”
Nasiha sosai yayiwa mai martaba yana ficewa marshall na shigowa.”

 

Mai martaba dakyar ya amsa gaisuwarsa.”
Nan yafara masa fad’a lallai yareema ka nuna ban isada kaiba ko.”
Girgiza marshall yayi yace a’a abba wallhy bahaka bane ina tsoron Allah yakamanine akan rashin adalci, Wallhy bazan ta6a iyayin adalci ba, abba da fannin yin adalci tsakanin *hanna* da wata mace inada raunii.”
Allah yace abba idan zaka iya adalci kayi mata biyu ko ko uku ko had’u,” idan kuma bazaka iyaba d’ayanma and’auke maka.”
Shiru abba yayi yace yanzu ka kyauta kenan? Saki uku ma er uwarka.”
Bai amsaba sai miqa masa jaririn hannunsa yayi yace, abba yasa hannu yakar6a yanabin jaririn da kallo yace, yareema wannan dai ko va’a fad’aba dankane.”
D’aga kai marshall yayi yace abba shekaran jiya aka haifeshi yaron *hanna* ne, dasauri mai martaba yad’ago yanacewa *hanna* cikin fara’a eh abba d’aza nasameta a camroon, Kilishi dake la6e tayi wufff tafito tana cewa k’aryane, yawan karuwancinta tatafi taje tahaifo d’a zata kawo ta liqa maka shii.”

_Kuyi hak’uri banyi editing ba akaranta da hak’urii dare yayi sosai_

To be continued

 

Ur’s
Z33iiyyb3rw3r
[9/1, 6:30 PM] Maryambawa: *BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL’S_

_Here is your fourth Page my *HAJJA CE* ILYSM_
=====================================

_Godiya gareku masu kirana masuyimun text dama wanda baku samu dama ba, nasan ina cikin ranku sosai, nagode sosai moayan littafin in ataredaku aduk yadda kuke, yau zaynab bawanku tadawo in sha Allh bazata tasayba saita k’arasa muku wannan labarin.”_

*Nasadaukar da wannan shaafi gareku an2y rashida an2y nafii I LOVE YOU SMCH*❤❤
*

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply