Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 98


Bibiyata Akeyi 98
Viral

page 98

Suna zaunane mai martaba ya aiko akirawo ummii, ummii tatashi tajeta.”
Tana zuwa tasamesu zaune shida Kilishi da intisar wanda take ta shar6an kuka.”
Da sallama tashiga, mai martaba ne kawai ya amsa bayan ta zauna yad’anyi y’an wasu, addu’oii kafin yafara magana, kinjii abunda yaronki ya aikata ko?” ya nuna mana mu bamu isada shiba, mu mahaifansa bazamu sakashi abuu yamana ba.”
Kilishi cikin tsafii tace wallhy yaron baida tarbiya kokad’an, bai d’auki iyayensa da daraja ba.”
Murmushin ummii tayi tace wallhy d’ana yanada tarbiya, bai ta6a gujewa umarnin d’aya daga cikinku ba.”
Tajuyo ga mai martaba tace, kai kanka kasani tunda kake baka ta6a haifan yaronda yake maka biyayya fiyeda shiba, cikin kissa Kilishi tace ki gyara harshenki sannan Kisan agaban waye kike da sarkii kike magana.”
K’arya kikeyi ummii tabata amsa damijina nake magana, a waje yake sarki, tunda yarigada yshigo d’aki, nice sarauniyar, abunda bakisaniba shine, inada Lokacinda zanmasa magana amatsayin sa namijina ba sarkii ba.”
Sannan kada kace yaro yak’ii bin umarnin ka, ko sau d’aya baka zaunardashi kace na umarceka daka aurii intisar ba, A’a jin magana yayi awaje wanda hakan yanuna kunbi ra’ayin yarinyar kenan, shi kuma ba’a nemi tasa amincewar ba.”
Nina d’auki cikinsa wata tara nahaifeshi, kuma naraineshi, amma nima ba’anemi shawarata ba, duk wani d’a na halal yana kishin mahqifiyarsa, kuma d’ana maibin umarni nane, ko sau d’aya da annemi na zaunardshi na nusardashi da zai hakura, kai amatsayinka na mahaifinsa baka bashi umarni ba, nikuma matsayin mahaifiyarsa ba’a bani damata ba.”
Ai inaga bai kamata anemeni danya 6ata muku ba, kenan yanzu ansan amfanina kenan?”
Tajuya takalli Kilishi tace inaso kisani ba’a ta6a canjawa tuwo suna, ni mahifiyace, wanda y’ay’anta ke alfahari da ita.”
Sannan kijira agama bikinnan wallhy talllhy tunda kika furta cewa *hanna* bazata dawo ba har abada saikin fitoda ita, dan hakan yana nufiin da hannunki a6atanta.” zan lamunci komai, amma wannan kam bazan lamunta ba, dansai kin fitomin da d’iyata tana fad’in haka tatashi tafice.”
Mai martaba Shiru yayi yau yasan ankaita k’arshen makura, tunda ita bamai magana bace, jikinsa duk yabi yayi sanyii yasaka yashige d’aki, itakuwa Kilishi mutuwar tsaye tayi, tunda aka kawo ummii yau shekara 37 talatin da bakwai amma bata ta6ajin wata kalma mai k’arfi abakinta ba, sai su shari watanni bataji koda tarinta ba, amma yau wai itane ke irin wannan magan ganun?”
Kama hannun intisar tayi sukabar falon.”

7:30 suka tafiii diner, zuwa 9:30 kuwa sundawo dan ummii tace kada su dad’e, aikuwa hakan akayi amare sunyi kyau sosai, Saidai tunda aka fara bikin kullun sai sunyii kukan rashin *hanna* sunsan tabbas datana nan bakin saiyafii haka armashi.”

Afeeya wanda tahalarci diner duka sun tattaro sunyi gida.”
Amaren na daki asashin ummii, yayinda su kuma ummii da y’an uwanta had’eda mama wanda a gidan zata kwana suna falo suna hira.”

Tun 9:20.pm jirginsu su marshall yasauk’a, wani irin sanyin dad’i da ni’ima ne ke ziyartar *hanna* bayan wata takwas yau ita ce a k’asarta, gobenna saiya kaita wajan mamanta, ta fad’a cikin zuciyarta, dukansu sun lurada farin cikinda take ciki.”
kai tsaye, gida suka nufa, sunakai 20minute kafin su isa, mamakine yakama su diddi ganin sunnufii gidan sarauta, abun sai al’ajabi yanzu da mummunan riqo suka mata fa.”
suna zuwa marshall yadubii *hanna* yace cutie ki wuce shashin ummii, nasan yanzu mai martaba yana jirana, zanje najii yadda zata kaya.”
D’aga masa kai kawai tayi.”
Tanufii shashin ummii da zamud’in ta, suma suka rufa mata baya.”
Gani takeyi kamar bazata isaba.”
Tana zuwa da gudu tashige ko sallama bbu, su ummii mama da Anty Afeeya tagani wanda sauran bata tsaya dubawaba, dagudu ta fad’a kansu arzane suka d’ago suna dubanta, wani irin ihuu Afeeya tasaka ta rungumeta kamar zata tsagata, itama hannan ihuu tasaka, nan suka fasheda kuka, mama da ummii basuga fuskan ba, saida Afeeya tasaketa, da karfii ummii tace *hanna* d’iyata, aikaman akunnen mutanen gidan kowa yafito hadda amaren, ummii da mama lokacii d’aya suka rungumeta, suna kuka, su diddi suna gefe suna kallon abun al’ajabi, da wata irin soyayya wanda suka rasa afamily dinsu, wanda sai zuwan *hanna* tabasu shi.”

Ummii nasaketa da gudu tayi wajan hameeda ta rungumeta suka fasheda kuka.”
Tajuyo ga mama tashige jikinta, mama Shiru tayi tanajin d’umin y’arta ajikinta.”
Sunfii 15mimute ahaka ummii tace, dukanku ku tashi muje muyi alwala, mu nunawa Allah godiyar mu.”
Zuwa sukayi kowa yayi alwala suna nan aka gabatar da sallah raka’a biyu.”
Ummii tace *hanna* ke meyasa bazakiyi sallah dinva?”
Muryar inne dasuke can bakin k’ofarne takatsesu datace, kwananta biyu da haihuwa aii.”

Hamdala sukayi, sannan Afeeya tace ina d’annwa naganshi?” tana tare d’anta tana cewa narabu da d’an aro tunda nawa nakaina yazo, *hanna* nawasa da yatsunta tace, yana wajan yareema yayi shashin abba.”
Ummii ne Tajuyo gasu inne cikin fara’a tace dan Allah Kuyi hak’uri mun barku awajan bbu komai sukace, nan suka shigo aka basu wajan zama had’eda kayan motsa baki.”

Mama tace *hanna* ina kika shiga tsawon lokacii haka? Baki nemi gidaba, sunkuyarda kanta tayi tace mama bana hankalina, kwanana biy da dawowata hankalina, atare mutanen wajan sukace Allah yayaye.”
Ta nuna su diddi tace su suka riqeni tamkar y’arsu ko ince fiyeda y’arsu, ba abunda nanema narasa.”
Godiya aka shiga yi musu.”
Inne tace bbu komai aid’a nakowa ne, nan aka shiga labarai da surutai, wanda kowa kana kallonsa zaka ga farinciki kwance fuskarsa, mamane tafara bawa *hanna* labarin irin halinda marshall yashiga, *hanna* kuka takeyi kamar ranta zaifita, jitakeyi wani irin soyayyar marshall nabin duk wata ga6a na jikinta, ummii ne ke aikii rarrashi tace, haba *hanna* kuncinda rayuwarki take shiga tun kina yarjnyarki yayi, yawa haka, dan Allah daga yau ki kasance cikin farinciki, daga yau duk damuwarki takauce, jarabawa ce Allah yad’aura miki, kuma inada yaqinin kincii wannan jarabawar, yanzu lokacin kar6an sakamakonki yayi.”
*Hanna* na murmushi tana goge hawayenta tace, Wallhy ummii kukan tausayin marshall nakeyi, nikaina bansan wani irin so yakemunba, ina jiyewa randa akace bananan.”
Akullum nayi sallah zanyita roqon Allah yayita dad’a mun sonsa nima najin kwatan kwacin yanda yakejii.”
Murmushi ummii tayi tace, ai bbu wanda ya isa yafad’i iyakacin wannan soyayya, kokuma shi wanda take jikinsan, Allah ne yadorota shiyasan iyakacinta, godiya ga Allah daya dorata akanki daya dorata akan wanda tasan mahimmancinta, dan da wata ce zatayi amfani da ita, ta sashi yaguji danginsa tarabashi da kowa.”
Allah yabarku tare har iya tsawon rayuwarku, ameen suka amsa dukkaninsu, *hanna* tace nidai kumana addu’a Allah yasa mumutu tare dan bansan yanda d’aya zaiyii idan bbu d’an uwansa ba.”
Dariya duka d’akin aka saka, *hanna* tace mama kiramun babana naji muryarsa, dasauri mama tad’aga waya takirashi, baba hadda hawaye yana jiwa Allah godiya, amma nawajan itama takar6a suka gaisa.”

Moddibbo zauneda mai martaba, Moddibbo ne ke magana yana cewa abudulazizu kayi ganganici, tunfarko dama dazaka nemi shawarata zance maka kada kafara, bakasan irin soyayyar datake tsakaninsu da matarsa ba, Allah daya dasata shine kadai yasan iyakacinta, koksan cewa yarinyar nan matarsa data 6ata sihiri aka mata, kuma acikin gidannan, akansa dan mai yasa za’ayi mata abuu akansa, ace bazai yi hakuri yajirata ba, bashi yafad’a maka yanada sha’awar yin aure ba.”
Wata takwas da6atan matarsa.”
Kayi ganganci shima kuma yayi badai daiba, saidai kada akuma.”
Nasiha sosai yayiwa mai martaba yana ficewa marshall na shigowa.”

Mai martaba dakyar ya amsa gaisuwarsa.”
Nan yafara masa fad’a lallai yareema ka nuna ban isada kaiba ko.”
Girgiza marshall yayi yace a’a abba wallhy bahaka bane ina tsoron Allah yakamanine akan rashin adalci, Wallhy bazan ta6a iyayin adalci ba, abba da fannin yin adalci tsakanin *hanna* da wata mace inada raunii.”
Allah yace abba idan zaka iya adalci kayi mata biyu ko ko uku ko had’u,” idan kuma bazaka iyaba d’ayanma and’auke maka.”
Shiru abba yayi yace yanzu ka kyauta kenan? Saki uku ma er uwarka.”
Bai amsaba sai miqa masa jaririn hannunsa yayi yace, abba yasa hannu yakar6a yanabin jaririn da kallo yace, yareema wannan dai ko va’a fad’aba dankane.”
D’aga kai marshall yayi yace abba shekaran jiya aka haifeshi yaron *hanna* ne, dasauri mai martaba yad’ago yanacewa *hanna* cikin fara’a eh abba d’aza nasameta a camroon, Kilishi dake la6e tayi wufff tafito tana cewa k’aryane, yawan karuwancinta tatafi taje tahaifo d’a zata kawo ta liqa maka shii.”

Wata irin fad’u Waar gaba Marshall yajii,yayainda kilishi ke Kira masa yaro da shege, jiyake Jamar yatashi ya shake ta, na shegnta masa yaro da tayi, amma Kuma bazai iya aikata hakan Ba hasalima ko iya buda baki ya fad’a Mata Wata magana bazai iya ba, kasancewar yadda yake daukanta matsayin mahaifiya, take yajii wani irin zafii cikin ransa, nan da nan idanuwansa suka kada sukayi jajir, ganin haka yasa Mai martaba yayi saurin katseta da tsawa yana Fadin kada ki kuskura nakara jin haka abakinki kilishi, ranki zai mummunan bacii, zan dauki mataki Akan hakan idan kika kara” kuka tasaka, tana fad’in aii wato nii duk abunda, akamun, sai nayi shiru nakasa daukan mataki kenan?” ayau ko wace uwa akayiwa abunda akamun dole ranta ya6aci, amma ni kenan bazanyii magana ba, kasancewar d’an soo ne ya aikata laipy, nikuma nawa ko ohow, har indai kaga abunda yayi yayi dai-dai shikenan, muje zuwa dani kuke zancen” tasaka Kai tafuce batare da wani yak’ara tanka mata ba, Mai martaba yabita da kallon Al’ajabi jikinsa duk yabii, yayi sanyii, shakku bbu kilishi anyi mata ba dai-dai ba,amma wasu maganganun da take fad’i suna wuce mizani, sukansa mutum shakku akanta, wata zuciyar ne tace masa hava Kai kuwa bawan Allah kokaine aka maka abunda aka mata ranka zai 6aci, dole wasu irin magan ganu zasuyita futowa abakinta sakamokon bacin raii, ranarda ta aurar da d’iya amata Saki uku, girgiza Kai yayi yana nanata inna lillahi wa’inna ilaihii raj’un acikin zuciyarsa, afili kuma yace Allah yakyauta yakare nagaba, da Dakyar Marshall ya amsa da amin dan duk yajii Ransa yabi ya6aci” mai martaba ne yamaida kallonsa kan jaririn dake hannunsa da murmushi dauke afuskarsa yace, ma sha Allah, Abdallah yaron nan du-du Kama dakai yakeyi, murmushin shima Marshall yayi najin dadin ance yaronsa yana kamadashi, Allah yaraya mai martaba yace, Marshall ya amsa da amin.”Mai martaba ya miqa masa yaron sannan yace maza kaishi wajen mahaifiyarsa Dan naga yaron yanada bukatar hakan, sannnan kasanrda su cewa inason magana dasu gobe da hantsi kowa ya hallaro shahina, bbu musu marshall yakarbi yaron daga wajen mai martaba sannan ya amsa da toh Abba, sannan yayiwa mai martaba sallama yafice, bin bayansa Mai martaba yayi da kallo sannan yace Allah yatashemu” ahankali yafad’i hakan bawai dan yayi zaton zaijishiba, ajiyar zuciya yasauke bayan yasauke idonsa daga kan kofa, yanason yaronsa gabaki daya, baison yimasa fada, amma kuma ayau dolece tasa yamasa dan yayi masa abunda baijii dad’ii ba, dole ne tasa ya nuna masa bacin ransa, d’an tsaki yaja sannan yace yarima baka kyauta munba” yanzu da d’an uwana yanada raii, kai wannan abun ad’iyarsa, Allah kadai yasan abunda haakan zai haifar.”.

Marshall shahinsa yawuce ra yaron don bayajin zai iya kai yaron wajen mahaifiyarsa, awannan lokacin, kai tsaye shsahin sa ya wuce,” ajiye yaron yayi kan gado,bai barshi ba sanda ya tabbatar ya shafeshi da addu’oii , sannan yatashi, wanka yafarayii, yanajin wani irin farinciki, jiyakeyi kamar mafarki gashi ga *hanna*, duk da cewa halin yanzu ba’a tare suke ba, amma yasan aduk lokacin da yake bukatar ganinta sai samu, sauri-sauri yayi ya fito daga wankan kaasancewa yabar yaron shii kadaii, yaron yana kwance kan, gadon bacci yakeyi, matsawa yayi gabb yaron yana kare masa kallo, yadda yaron ke bacci cikin kwanciyar hankalin, tashi yayi ya isa gaban mirror ya shafa mai da turarurruka, sannan yanufii, wadrop ya6are sabuwar jallabiya ,da gudu-gudu yai ya zura jallabiyan kasancewar ya hango yaron yafara motsi, jin yadda yaron yafara kuka kadan-kadan, dasaurii ya karasa kusa dashi sannan yasaka hannu yadauko yaron, lallashin sa yafara yii amma kukan yanad’an k’aruwa kadan-kadan, totsan bakinsa yaron yakeyi alamun yunwa yakeji, tausayin yaronne duk yabii yakamashi, daukan waya yayi da niyyar yakira *Hanna* tafito takarbeshi, tsaki yaja, tunowa da yayi cewa bbu waya ahannunta,” tsakin yakaraja akaro nabiyu, tunani yakeyi baisan wazai kiraba, idan yakira ummi yasan zata nemi ganinsa shikuma a halin yanzu baison suhad’u, baison duk wata magana daza’ayi wacce zata 6ata masa raii, yau soyakeyi yakwanta yayi bacci cikin farincikin daya dad’e bai tsinci kansa cikiba, komadai menene abarii sai sun had’u gobe da safe dan ashirye yake yadauki hakan.”

Ganin bbu yadda zaiyi ne yasashi danna number ummi da tunanin mai zai biyo baya, wayar tayi ringing har takusan tsiniewa kafin aka dauka, shirune yaziyarcii cikin wayon nadan wasu dakiku, daurewa yayi, yayi sallama, amsawa tayi batareda ta nuna masa wani abuu amuryarta ba,cikin kame kamen murya yace ammm ummi *hanna* na kusane tafito ta karfin yaron yafara kukkk, katseshi tayi da ,auu da nadauka ai tare zaka kwana dashi tunda kana da abincinsa wajenka, d’an sosakai yayi yana murmushi kaman tana kallonsa yace,” ummi ina wajen mai martaba ne fa shiyasa kika kalli na dad’e, ummi kiturota plz yana kuka, ummi ne tace *hanna* kam bata zuwa zan turo maka afeeya kabata yaron. Zai kara yin magana tayi saurin katse wayan, dago wayan yayi daga kunnensa yaba binta da kallo,” rungume yaron yayi ajikinsa sannan yasauko, yanufii hanyar waje, dake k’ofanna glass ne soldier’s dinsa suna hangoshi da gudu sukazo suka bud’e mar kopa, fita yqyi 2aje ea fara’a afuskarsa, mafii yawancin soldier’s din basu ta6a ganinsa cikin farinciki irinna yauba, sa6anin kullum da yake cikin murtuke, d’aya daga ciki ne yayi karfin halin tambayarsa, yanayi yanajin tsoro yace,” sir babyn kane wannan tun d’azu munganka taredashi, ga mamakinsu murmushi yayi ,sannan yace yarona ne, 2days Kennan da haihuwarsa, mamakine yakama wasu daga cikinsu, kasancewar Sunsan yau aka d’aura auransa, kuma suna da shaida kan mai gidannasu, bai kasance fasikiba, dukiyarsa mulkinsa, baisa yakasance mai wata mummunar dabia ba, hasalima halinsa kowa zaiso yayi koyi dashi, yayinda wasu daga cikinsu sunsan da bacewar matarsa, eukuwa sauran tambayoyi fall cikin ransu, yayinda sauran suka farayii masa addu’ar Allah yaraya, tsayawa yayi yana amsawa cikin farinciki, alokacin cpatain Ahmad dakuma captain bala suka k’araso, cikin farinciki atare suka rungumeshi, yaronda yake hannunsane yasa sukayi saurin sakeshi, dariya kawai yayi, c. Ahmad yasaka hannu ya karbi yaron, sake masa shi marshall yayi, sai yaba kywaun yaron sukeyi, alokacin kuma suka fara labarin dawowar *hannna* anan ne soldier’s dnsa da basu saniba suka fahimci cewa yanada mata, kukanda yaron yafarane yasakashi saurin karbansa, yafara tafiya zuwa shahen ummi, rufa masa baya sukayi nan yatsayar dasu, da saurii-sauri yake tafiyan, bai dad’e ba kuwa Ya’isa afeeya yasamu awajen tad’ade tana jiransa, wani ean karamin tsaki yaja sannan yace mata ina *hanna*?”
*Hanna* Ummi tahanata fitowa ya yareema bani yaron nakaishi kaga kuka yakeyi, harrara ya dallah mata sannan yace,” bazan badashiba ki koma kituromin *hanna* Nidai ya yareema kabani naganshi sannan naturo maka ita, bbu musu yamiqa mata yaron cikin zumud’i takar6eshi tana cewa, ya Yareema wannan yaron sakkk dani yake kama, murmushi yayi sannan yace, aidolensa ma yayi kama dake, cikin farinciki ta miqa masa yaron tana cewa yaya yareema, barinyii saurii nakirata Dasaurii tajuya, shikuma yatsaya wajan yana jira, kusan10minute baiga kowa yafito ba, gashi yaron yafara kuka sosai wani irin zafii yakejii cikin ransa nakukan da yaron yakeyi, ciki kuwa sunjirane ko zaigaji ya kawo yaron ammma shiru, dan ummi tasan sarai idan tababarii *hanna* tafita itada yaron duka zaibii yariqe mura taje takama yaro.”
Ganin shiru yasa mama takalli *hannaa* sanan tace, tashii kije kinbarshi waje asanyinnnan, dama itama *hanna* kamar jira take tamiqe zumbur har dukansu suna mata dariya dasaurii tafice cann ta hangoshi zaune kan wata resting chair tareda yaron rugume a jikinsa, yadda sanyi bazai ratsashi ba, da sassarfa taqarasa wajansa sannan tasaka hannu tabaya tarufo masa Idanuwa alokacii d’aya dagashii har ita suka sauKe ajiyar zuciya, sako hannu yayi yajawota tabaya sannann ya hada yarungumeta ita da yaron sun ebi tsawon lokuta ahaka sannann yasaketa tazauna kan kujera, amma hannwansuna makale ciki najuna,ta kwantarda kanta akafadarsa sannan ahankali tafurta i miss u habibii, batareda yace komaiba yamiqa mata yaron sannan yace cutie babyn sai kuka yakeyi tun d’azufahh, karbansa tayi sannnan ta shimfidashi akafadunta tana rarrshin sa, kallonta yakeyi baki sake yana cewa, cutie yunwafa ayakeji, ai nasani tabashi amsa atakaice, to tunda kinsani aisaiki bashi abincii kibar wani rarrashinsa, toh kawai sannnan tacii gaba da rarrashinsa, d’an 6ata fuska yyi sannnan yace cutie kinaso muyi fad’a girgiza masa kai tayi ahankali, yace toh idan bqkiso muyi fad’a kibawa yaronnan abincinsa narai-narai tayi da ido kaman mai shirin yin kuka tace, Allah tsoro nakeji, d’an k’aramar tsaki yaja sannan yace kika haifeshi ma, aiduk wani abunda zai biyo baya mai sauki ne, me sauk’i? Tanana ta, sannna takaracewa saukifa kace, lallai dan baka sani bane shiyasa,” gyra zamansa yayi gabaki da yajuya yana kallonta, sannnan yace” cutie bawai kinaso kicemun tunda yaronnan yazo duniya bai cii komai ba?” Turo baki tayi sannan tace aibangaya maka hakaba,” kuma aii dan bakasan ciwonda akejii bane shiyasa, uhmmm kawai yace sannan yaja bakinsa yayi shuru dan yaga abun *_hanna_* yayi tsaurii, da alamu nan bada dad’ewa zatace masa ma dan baison zafin haihuwan bane, d’an murmushi yayi kawai da yatuno irin tsaurin bakinta abaya, aransa yace” wai dan taragema da abunma saiyafii haka, ganin yayi shiru ne yasaka ta tunanin ko ransa ya6aci, ne, ta6oshi tayi yajuyo ya kalleta sannnan tace, honey kayi fushi ne, girgiza kaii yayi sannan yace, kindai 6atamun raine ammma aii kinsan bazan iya fushi dakeba, kaman zatayi kuka tace kayi hakurii plz, bazan karaba, nima banaso kirara yafad’a *hanna* plz komai zakiyii kigujii batawa yaronnan dan kinsan akansane kawai zan iya 6qtarai dake, wasu hawayene suka gangaro mata, cikin kidimewa yariqe hannunta yana cewa subhanallahi cutie menene yafaruu?” cikin kuka tace wato yaronda kwanansa biyu aduniya, few hour’s kqyi atare dashi amma ka nuna kafisonsa akaina koh? Subhannallahi, hava cutie nifa bahaka nake nufii ba haka kake nufii mana tunda gashinan kawani zage sai fad’a kakemun akansa, shid’ai baiga loacin da ya zage yana mata fad’afa aamma sanin halin rikicinta yasashi cewa” kiyi hakurii hakan bazata kara faruwa, ke kanki kinsan bbu yadda za’ayi ace naifisonsa aknki yana karaea fad’in hak yana share mata hawayen fuskarta.”

Plz cutie kibar kukannan haka kukanki ya isheni da jii bansan sake ganin hawayenki, hava-hava, murmushi tayi sannnan tace nadaina, yawwa cutie toh bashi abincii, bbu musu tafara shayarda yaron, har sanda ya koshi, haka sukayita zama wajen su kansu basusan lokacii yatafii ba dare yatsala sosai, kallonsa tayi sannan tace honey darefa yayi sosai, ah havadai yaushe kika futoma cewar marshall miqewa tayi tana cewa, nikam miqominshi mutafii, A’a dare yayi muwuce shashinmu kawai, nikam bazanjeba tabshi amsa, yanzuma dai nikam bansan da wani ido zan shiga ciki ba, dariya yayi sosai yace da idonki mana cutie, konawa kikeso nabaki aro?” aida zaifiikam danna gansu asoye tafad’a tana kokarin karbe yaron, riqeta yayi yana kokarin kissng dinta yana cewa barina gwada miki yadda suke asoye, samu tayi takar6e yaron, tana masa dariya, tashige shashin ummii, shafa sumar kansa yayi yanajin wani nishadi, ya dad’e kafin ya samu yatashi yanufii shshinsa.”

Koda tashiga tasamu wasu daga cikinsu basuyi bacci ba, dan sunajiran kallon yaron kamar muna fuka ta miqashi awajen ummii bbu wanda yauna yasan tana sunne sunnenta ma, ganin hankalinsu yayi kan yaronne yasa tashige tayi kwanciyarta.”

Washe garii da safe misalin karfe sha d’aya 11 kowa ya hallara a falon mai martaba, hadda momy wacce sassafe ta iso, mai martaba ya nuna farin cikinsa sosai naa ganin *hanna* kowa ya hallara kilishi da intisar ne kawai basanan, mai martaba ya aika akirasu, amma shiru jakadiyane, tashigo tadurkusa gaban mai martaba sannan tace, ranka shi dad’e, mai kulada shashin ta sanardani tun sassafe suka fice haryanzu basu dawo ba, daga nata kai kawai yayai tatashi tafice cikin ransa yanajin zafin yanda tafita batareda ta tambayeshi ba, amma bai nuna ba, ahaka akayi zama sosai aka nunawa marshall laipinsa, su inne kuwa sunsha godiya yayinda mai martaba buk’acesu akan su zauna sai bayan suna su tafii, basuyi musu ba, dan su kansu suna bukatar hakan.”

Alokacinda affan yasamu labarin abunda marshall yayiwa intisar har cikin ransa bayai yaji dad’ii ba.”
Ransa yabaci sosai kuma yasan umma(kilishine) tajawo mata, bai sake tsinkewaba da tausayinta ba saida yaga yadda intisar tarema lokacii d’aya tausayinta yakamashi, aikuwa dabad’an dan uwansa vane yayi mata wannan wulakancii da’anga yadda zasu kwashe, wasu kuma daga cikinr y’ay’an kilshi cewa sukai aidama namiji ba’ayimasa auran dole, Allah yasa hakanne yafii mata saukii agareta,

Kilishine gaban bokanta tana zaune dirshan daka ganta kasan magan ganun dayake fad’a mata ranta baiyi mata dad’i dasuba.”

To be continued

Ur’s
zaynab bawa
[9/1, 6:35 PM] Maryambawa: [8/14, 10:26 PM] 6ta Abuh: *BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL’S_

 

_Your fifth page, is here my *HAJJA CE* Allah yabarminke har abada, ke abun alfaharice ga al’umma.”_
_Allah yaraya mana ihsan musha biki.”_

====================

Tabbas ke k’awar arziki ce *ASMY B ALIYU* godiya da mai yawa ga dumbin soyyayarki gareni Allah yabar zumunci.”

 

*

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply