Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 99


Bibiyata Akeyi 99
Viral

page 99

Bayan sunbar shashin mai martaba, kusan gabaki d’aya shashin ummii aka nufa, alokacin harsu yaya hindu duk sunzo, murna dai ranar acikin wannnan dangii ba’acewa komai, hanna ne zaune da su anty afeeya, dakuma sauran yayaunta, kallon anty afeeya tayi sannan tace nifa bqnga labba ba, dafqrko nadauka tana gidaki kuma naga haryanzu bata iso ba, murmushi anty tayi sannan tace labba kam tana nan tana tayqki kishi tama tattare kayanta gabaki daya takaoma wajen dangin ummii, tun jiya nake kiranta taki dauka tunani takeyi dan fad’a mata zancen and’aura aurenne ne, anty *hanna* labba tashiga tashin hankali, kowa yashiga tashin hankalin rashinki, yaya hindu ce ta kar6e maganar da cewa *hanna* ki gode Allah kina tare da masu k’aunarki dayawa, hakan yakasance abun dubawa dukda bazai kasance kowa yasoka ba arayuwa, idan kaga mai k’iinka saika tuna da dumbin masoyanka, mungode Allah daya dawo mana dake cikin koshin lpy, wannan kad’ai ya ishemu farinciki, kuka *hanna* tafara tana cewa kuyafeni en uwana, bason raina bane na 6ace nabarku cikin tashin hankali, nima nayi missing dinku sosai fiyeda yadda baki zai iyq furtwa, nayi missing dinku fiyeda yadda hankali zai d’auka, fiyeda tunanin yadda tunani zai dauka, inasonku sosai, inasonku tafad’a had’eda share hawayen fuskarta.” kar6an wayar hameeda tayi sannan Tad’auki number din labba awayqr afeeya, dialing tayi, harta kusan katsewa ba’a daukaba,”
Labba dake kwance kan gado hankalinta duk yana gida amma batason komawa ne dan bataso takoma tajii and’aura quran yaya yareema ta intisar, intisar er uwartace bawai batason auran bane dan batason intisar ba, a’a saidan ganin rashin dacewar hakan, hakan yakasance butulci da’ace *hanna* tana nan yaya yareema zaiyi aure abun bazaiyi mata ciwo ba, kamar yadda ace batanan ta 6ace, yanzu wayanasan ma, kodan yaya yareeman akayi mata wannan abun ta6ace, yanzu rana d’aya ace *hanna* tadawo tasamu wannan labari wani irin hali zata shiga?”
D’an tsaki taja yayinda wayarta ta dameta da ringing kamar bazata d’aukaba harya kusan tsinkewa tak’arajan tsaki akaro nabiyu sannan tayi picking, shiru tayi batace komaiba, daga d’aya bangaren kuma *hanna* dataji and’auka, dasaurii ta ambacii *habibtiii* aikuwa labba ko bacci tatashi dashi bazata mance wannan murya ba, Batason lokacin da tafad’o daga kan gado ba, ita tayi gefe wayar tayi gefe, k’arar fad’uwar wayanne yacikawa *hanna* kunne yasa tayi saurin d’agawa daga kunnenta tana kallon wayar, sauri labba tayi ta nemo wayar, hango waya tayi agefe, daukan wayar tayi sa’arta d’aya wayar bata mutu ba, saurin karawa tayi akunnenta tana cewa, habibty habibty, dai-dai lokacin *hanna* tamayar da wayar akunnenta, na’am *hanna* ta amsa had’eda farfara ido kamar tana kallonta, jiki na 6ari labba tace sis ta gaske kece, gashi kuwa kinjin hanna tabata amsa atakaice, sannan tad’aura dacewa saura 4days suna yqronki, kiyi kizo idan ba haka ba baby yayi fushi dake, zqtayi magana *hanna* tayi saurin katse wayar ta kasheta gabaki d’aya, dariya afeeya tasaka sannnan tace aikuwa kin iya maganainta, yanzu zata fara shiri sannnan tatashi hankakli anem mata visa, aikuwa baku kyauta mataba, cewar yaya hindu yanzu haka zakusa hankalinta yatashi, dariya kawai *hanna* sukayi.”

Palour suka koma waJen mama momy dakuma ummiii da inne da kakarsu, ita kuma hussentu tana taredasu *hanna* da yarinyar isshaq, sukuma Sadiq da isshaq suna masaukinsu, basu dad’e da zama afaon fa marshall yashigo d’aukeda sallama, mafii yawanci d’akinne suka amsa, sannan yakarasa shigowa kayan sodier’s ne ajikinsa yayi masifar kyau, fuskarsa d’aukeda murmushi, da annurii, tsugunnawa yayi yagaida manyan dake wajen sannan yadubi mama yace,” mama akwai wayanda zasuzo daga bauchii ne? Eh akwai tabashi amsa atakaice, sannan tadaura da cewa inaga kaman Aisha da rabi’atuh da ammansu zasuzo nikuma zankoma saboda su karima akwai hassana da husaaaina d’azu karima takirani sunata kuka, babuk’atqr komwarki marsall yafad’a sannan yad’aura da cewa inaso na aika soldier’s yau za’a taho dasu, sannan masu zuwan su jira soldoer’s su isa sannan su taho tare sabilida hatsarin dake cikin tafiyarsu su kad’aii,” jirgi zasu tafii dan haka ba wani jimawa zasuyiba.” d’aga kaii kawai mama tayi jikinta duk yabi yayi sanyi tasan lokacin rabata da yaran dasuka riga sukabi jinin jikinta yazo, ahanakali ta furta Allah yayi taimako yabaku sa’a abdallah kakula sosai kasan hatsari irin na way’annan mutanen.” squran dake d’akinma addu’ar suka yi masa, juyawa yayi zai fita *Hanna* Wanda tun shigowarsa idanuwanta yake kansa sakamakon wani irin kyau da yayi, har zuwa lokacinda yayi gaisuwa idanuwanta yana kansa, alokacin da yafara magana kansu karima ne tunaninta yafara canjawa abubuwa dayawa sukayita dawo mata way’anda suka faru abaya.” kukanda *hanna* tasakane yasashi juyowa tsayawa yayi kawai yana kallonta, maamakine yakamashi menene kuma nakukan?” ohow, yabawq kansa amsa, *hanna* akan gwuiwowinta, ta tsugunna agaban ummii tana kukaa tana cewa ummii dan Allah kihanashi zuwa wallhy akwai abunda zai faruu, marshall ne yace shhhhhhhhhhhh *hanna* bbu abunda zai faru, akwai tafad’a kayi shiru kawai kai baka sani ba, kabarsu da Allansu kawai plz karkje wani abuu yafaru dakai way’ananna mutane hatsabiban mutane ne.”
Tsayawa kallonta yayi kawai dan baisan mai takeson cewa ba, sqka bayan hannunta tayi ta share hawayen fuskarta, taja majinar dake hancinta sannan tace ummiii sune way’anta suka sa aka harbeshi adubai gaban ummii ne yafadi daran tace hanna me kike shirin cewa ne??, hard’e hannayensa a k’irji marshall yayi, a iya saninsa yasan bai ta6a furtawa *hanna* cewa anharbeshi ba, sannan yasan bawai tasanda hakan bane, a hankali yafurta tayaaya akayi kikasan hakan *hanna*, nan da nan tashiga basu labarin abunra yafaru a highcourt lokacin zuwansu da amira wajan babanta, takara da cewa alokacin naso nasanar dakai toh idan zanyi hakan bansanka ba bqnkuma san a’ina zan sameka ba, amira ce ta hanani sanrada wani sabilida akwai hannun manyan mutane aciki bakasan wa zaka fad’awa ba dakuma mai hakan zai janyo Ba, labari taci gaba da basu, har izuwa lokacinda taji sanarwa a tv akan cewa an harbeshi bbu tabbacin yanada raii kokuma yamutu, dakuma mafarki da takeyi dashi, hanakalin ummiii yatashi sosai jin irin wannan labari, mama girgiza kai tayi sannan tace assha asssha *hanna* meyasq kika kasance mai zurfin ciki haka?” ni mahqifiyarki ace munkwana daki daya muntashi d’aki daya kikasa fad’amun wannan?” kuka kawai *hanna* takeyi takaea cewa komai, marshall wanda kukan *hanna* yafii d’aga masa hankali fiyeda maganganun da tafad’a masa yace shhhh *hanna* taso kizo nan, bbu musu tatashi tanufeshi, kama hannunta yayi suka fice waje sukabar mutanen ciiin wajen da zullumi, ummii idan tace bata shiga mummunan tashin hankali bama toh wannan ta yaudari kanta ne , tunowa da tayi irin tashin hankalin da tashiga lokacinda akasabarda ita cewa an harbeshi ahalin yanzu da sukasan cewa rayuwarsu tana cikin hadari dole zasu nemi yadda zasuyi kuga bayansa,”
Ayanzu kam bataga na zama ba dole dukansu sutashi da addu’a.”
Lokacii d’aya suka miqe da mama kamar wanda ko wacce tasan abunda d’an uwanta yake sakwa acikin zuciya, alola sukayi sukai nafiloli sannan suka runga roqan Allah yarabasu da matsalolinsu sannan yarabu daga sharrin duk wani mai sharri.”

Marsahall har shashinsu ya zarce da hannunsa riqeda na *hanna*,” zaunarda ita yayi bakin gado sannan ya canja kayansa daga na sojiji zuwa, ainihin shadda geznah, jamfanne amma batayi girma sosai ba, links yad’auko yana k’okarin sakawa *hanna* tataso takar6a sannan taaaka masa, bud’e wadrop d’in tayi tad’auko hula tasaka masa, juyawa yayi yakoma kan gado yakwanta, kallonsa tayi tace ba futa zakayi ba, girgiza kai yayi sannan yace,” nikam bbu yanda zanje, ina zaune dake agida, karasowa tayi sannan ta kwanta agefensa tace,” duk wannan kwalliyar tawace kenan?” ke kad’anki ma kuwa yataba amsa.” murmushi tayi, ba’a dad’eba kiran labba yashigo wayan marshall yana d’auka ko sallama batayiba tace ya yareema plz kafad’am sis tadawo, dariya tabashi yace labba ko gaisuwa bbu rabonki raki nemeni tun yaushe, fushi kikeyi dani kenan?” toh bazan fad’a ba, tunda yaune kikasan amfanina, dariya tayi sannan tace aii bama saika fad’aba yanayin yadda kake magana yanunamin, tana fad’in haka takashe wayarta tafita neman visa.”
Karima ne zaune awani garden, tun d’azu take jiransa, bai isoba gashi yanzu bataso sutafii batareda tatafi tasanar dashi yadda zaai sameta, ba gashi ta tabbata yanzukam anata jiranta, ranta bbu dad’i tatashi zata tafii,” hango motarsa tayi yayi parking nufota yayi tayi, bata tsaya ya k’araso wajanta ba tayi saurin ajiye masa wata farar takarda, tashige adai-daita dinda yake jiranta.” bai bitaba dan yasan ba tsayawa zatayi ba, k’arasawa yayi yad’auki takardan data ajiye, d’in sannan yajuya tana zuwa kuwa tasamuu ita kad’ai ake jira dasaurii tashiga, taduko abunda zata buk’ata tafito abida kam ta dad’e da shiga mota itada twins, da kabir, karima itama tashiga motar suka, nufiii airport, duk saita kejin bbu dad’i, batajin zata iya rabuwa da mama, jitakeyi yanzu basuda mahaifanda suka fisu ita kanta tasan cewa bbu wanda, zairiqesu kwatankwacin yadda mama ea sauran mutanen gidan suka riqesu, ashe ba ita kad’ai take wannan zullumin ba, su kansu y’an uwanta Abunda ke cinsu arai kenan,” haka suka isa airport, ran karima cike fall da tunanin mutumin da batasan koshi wayeba, bata ta6a bashi damarda ko sau d’aya zaiyi magana da itaba,”
Amma wannan sak’onda tabar masa ta tabbata, har indai dagaske yadda yake fad’in yansonta akullum saidai bata fitaba yana bibiyar rayuwarta, to tabbas idon son gaskiyane zai nemeta.”
Daganan jirginsu yad’aga zuwa kano.”

 

Kilishi ta firgici tadawo gida, ad’aki tasamu intisar ta kulle k’ofa, bugawa tahauyi kamar zata 6alla kofar, dasaurii intisar tataso ta bud’e kofar, ganin kilishi ahaka yasata tsorata tun daga kofa tafara tambayarta kan cewa lpy kuwa taganta haka, kilishi tace ina kuwa lpy er nan zama tayi bakin gado ta lalu6o number din hajiya hadiza takira, tana d’auko ko sallama bbu tace hajiya komai ya6aci, kinaji sharad’in daya bani cewa idan yayi aiiki har indai aikin bai tafii dai-dai ba to tabbas zanmutu, idan kuma ba’ayi aikin ba to tabbas zan haukace, nikuma bazan iya daukab risking haukacewa ba,” ya tabbata har indai banaso nayi hauka sainaje nafad’a musu duk wani abunda na aikata kafinnan da gobe,” ta cikin wayar hajiya hadiza tace toh nikuma meye nawa aciki kafin ayi aikin ainafad’a miki cewa akwai sharad’i kikace kinji kin dauka dan haka zaiki za6a acikin uku diff takashe wayanta.”
Cire kwalin kanta tayi, intisar dake gefenta tace na shiga uku umma yaya zamuyi nimaa bansaniba, tabata amsa atakaice,”

Wajen k’arfe uku su ammah dasu karima suka iso, kai tsaye shashin ummii aka wuce dasu, zuba idanuwa sukeyi kawai koda cewa zasuga *hanna* amma shiru sai jaririn dake hannun afeeya, amma ne bakinta yakayin shiru tace, nikam ina d’iyata, idanuwana suna bidar ganinta, bakina yakasayin shiru karimace tace wallhy nima tun d’azu nake zuba idon ganinta, murmushi ummii tayi sannan tace, barina kirata d’aga wayanata tayi takira layin marshall,” karar wayane tatashesu daga bacci mqi.nauyi daya daukesu, daukan wayan yayi ganin ummi yasashi saurin miqewa ya amsa,” katuro *hanna* yanzu ammanta tazota.” dama wayar a speaker take hanna tanaji da gudu tamiqe tayi waje, girgizakai marshall kawai yayi yana murmushi,”
*Hanna* tana isa da gudu tafad’a jikin ammma murna kamar tayi yaya, haka tayi farin cikin ganinsu karima sosai.”
Nan aka shiga jajanta maiyafaru, kowa sai alhini yakeyi, kowannen cikinsu yakwana da zullumin abunda zai faruu gobe mafii yawancinsu basuyi bacci ba, sun kwana sunakai kukansu wajan ubangijinsu,”

Washe gari da sassafe *hanna* dasu karima suka wuce court tareda marshalll” anan sukarima suka kalli yayarsu rauda wacce take kasar waje tana aure,” marshall ne yasanarda itaa cewa k’annenta suna raye.”
Sosai tayi murnar ganin k’annenta hadda kukan murna.”
Bawata shari’a mai tsayi akayiba kasancewar marshall yad’ade da gabatarda shaida, basuda wani abunda zasu kare kansu,” Mafii ywancinsu an yanke musu hukuncin kisa yayinda wasu daga ciki aka d’auresu rai da raii, ayau su karima sunyi farin ciki duk da kasancewar bawai angabatarda sharia akan mahaifansu da aka kashe bane tunda bawai sunada wat kwararriyar shaida bane, amma hakan yayi mata dad’ii tunda sunga, wanda sukeson gani awulakance.”
Haka suka tattaro suka dawo gida kowannensu cikeda farinciki.”

 

Kilishi ce zaune ad’aki tarasa wacce shawara zatabi, tarasa mekeyi mata dad’ii.” shin tatashi taje tasanar dasune komai zai biyo baya ya biyo kokuma tajira tagani koda gaske boka yakeyi mata.”

 

To be continued

 

Ur’s
Z33iiyyb3rw3r
[8/16, 4:07 PM] 6ta Abuh: *BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL’S_

“`Wannan shafin sadaukarwane ga duk wani mai karanta BIBIYATA AKEYI dakuma fan d’in buk d’in kai koda ace baka karantawa ko sunan littafinne yayi maka dad’i nasadaukar da wannan littafi gareka.” kusani kune abun alfaharina.”“`

*
*continuation of page 99*

Bacin raii sosai labba tashiga, dan rashin samun visa da batayi ba, har sai nanda kwanan biyu,” gashi tayi fushi bazata k’ara kiran kowa ba, saidai kawai su ganta.” haka kuwa akayi dan share kowanne daga cikinsu tayi bata k’ara kiransu ba, tazauna zaman jiran visa.”
Bayan su *hanna* karima da labba sun koma gidane aka shiga jajjaba abubuwanda suka faru, sukuwa karima abida rauda twince da kabir, ransu yayi dad’i kasancewar, ayau an hukunta masu laipy, iyayenta kuwa sai dai suyita binsu da addu’a sannan suroqa musu gafara awajan ubangijinsu.”
Ranarda yamma danginsu karima suka iso kar6ansu, dan dama ansanarda su cewa yaarn suna raye.”
Koda sukazo kamar yadda akayi zato sun bukaci da abasu yaran,” bbu wanda yak’i musu hakan dan dama sukeda ikon riqesu, sai dai ran mama kamar wuta takejin sa, tarigada tasaba, da yaran jitakeyi kamar ita ta haifesu,”
Hakanne tafaru wajen yaran, sa6anin karima, da abun bai mata ciwo sosai, tunda ta tabbata ba dad’ewa zata k’arayi agabansu ba, hasalima ita tafiso daga anzo tambayar auranta abayar, mahaifanta ba’araye suke ba, tasan bawani dad’in zaman gaban dangin nata zatayi ba, kasancewar ba shakuwa sosai sukayiba.”
Abin tausayin kannenta tafiji suna wanda dole sai sunzo sunkoyi saboda su.”
Godiya sukayiwa su mama sosai ta fatan k’ulla zumuncin da bazai rabu ba.” suna kuka haka aka tatttarasu aka tafii dasu.”
Najeeb ne zaune da takarda a hannunsa yarasa farin ciki zaiyi kokuma akasin haka, da farko dai farin ciki ne, na abunda yakeso zai samu, amma kuma damuwarsq d’aya itace, bai santaba baikuma san wacece itaba, ko sau d’aya bata ta6a tsayawa ta saurareshi ba.”
Amma kuma yanada yak’inin yarinya ce mai tarbiyya, kuma yanada tabbacin tanada alaqa da *hanna* dan haka kawai bazata zo gidansu tazauna ba.”
Kumada tatashi bashi adreshi akano ne, kuma bataso yawuce nan da kwana biyu.” miqewa yayi sannna yace da zafi-zafi ake dukan karfe.” shashin mahaifinsa yanufa koda ya shiga da sallam akishin gide yasameshi.”
Bayan ya gaidashi kai tsaye yasanr da mahaifinsa abunda ke tafe dashi, dan shi yanzu gaskiya baya shakkan akan abunda yakeso, rasa *hanna* dayayi yatabbat yayi asara babba yanzu kuma gashi Allah yacanja masa da alhairii, bazaiyi sake yarasa wannan bama,”
Ga mamakinsa murmushi mahaifinsa yayi sannan yace,”
Yanzu barina sanarda en uwana in sha Allah zuwa gobe za’aje kajii.” d’aga kai yayi sannan yafita yana godiya, dakin mahaifiyarsa yaje yasanarda ita, itama tayi murna sosai.”
Washe gari kuwa iyayen najeeb suka d’auki Hanyar kano,” dafarko gidan mai martaba suka fara sauka, dan nan takwatanta masa, hannu bibbiyu mai martaba yakar6esu, nan yasa akayi musu jagora har Zuwa danginta, anan aka dai-dai ta komai dake sukkaninsu y’ay’an mutuncine aka bada sadaki awajen dama da goron tambayarsu sukazo, da kayan nagani inaso, ran ne kawai ba’a tsayarba sai daga baya.”
Jin haka washe garii najeeb yataso yazoshi tad’an sake masa alokacin sabo yad’an shiga tsakaninsu.”
Bai boye mata komaiba gameda soyayyarsa da *hanna* , eyeyer tausyi yabata ta jajanta masa, murmushi yayi Sannan yace, yanzukam bagashi Allah yacanjamun dakeba,” kuma duk tq dalilinta Allah yabiyata, dole mugode mata.” alokacinne takeasanar dashi cewa ai ta haihu sannan kuma tadwo, kafin najeeb yatafii sanda yaje yaga *hanna* da baby, gafararta ya nema akan magan ganunda yayi mata, bata nuna damuwa ba tace masa bbu komai, nan yasanr da ita tsakaninsa da karima, fatan alkhairii tamasu, sannan marshall yazo shima suka gaisa, sannan yatafii.”

Yaya jalal ne ya iso dan dawowarsa kenan daga tafiya aikuwa bai zarce ko inaba sai gidan *hanna*

Sosqi *hanna* tayi murnar ganinsa, nan yake sanarda ita cewa, aii yakira amaiira yafad’a mata tananan zuwa gobe, kuma goben yakasance suna.”
Murna tayi kasancewar ta dad’e bata gantaba, dawowarta kuma takirata baishiga ba.”

Sai ranara suna kafinnna labba ta iso da sassafe su yaya hajjah ma duk sunzo, amira itama ta iso, lallai wannan suna yaga dangii dayawa,” kasancwar an had’a sunan da walimar dawowar *hanna*
Ba’ayi almu bazzarancii ba, hasalima masu karamin karfi akabi anata bawa sadakaa dakuma mabuk’ata yaro yaga gata sosai yayinda yacii sunan maddiibo.”
Su hafsa da hameeda kasancewar kowa ankaita gidan mijinta suma duk sunzo.” akwati biyu najeeb ya aiko karima dashi d’aya na baby d’aya na mamansa.” yaya jalal ma ba’a barshi abaya ba, shima haka yajido kaya, shikam marshall ba’a zancensa, kasancewar irin kayan dayayi idan yafitar dashi adangi zai zama abun magana shiyasa ya ajiyeshi agidansu, duk ranarda tadwo shashinsa saita samesu.” ummii kuwa da mai martaba idan kagansu kamar alokacinne aka farayi musu jika,” koda yake aii wannan ne nasu shine suekda iko dashi sauran duka na arone😜.”
Kaii tun ina irga kayanda y’an “ *`BIBIYATA AKEYI FAN“`* sukayi har nagagara nadaina, dan sunyii kokari, haka *ZAINAB BAWA NOVELS* ma dana facebook dana whataapp duk sunyii bajinta Dan ba’a barsu abaya ba.”
Duk wannan biki da akeyi kilishi ko sau d’aya bata leqo ba, kuma bbu wanda yadamuu da hakan y’ay’anta kam komai dasu akeyi awajan.”

Washe garin suna da sassafe saiga danginsu karima nan, hassana da husaina sunki zama duk yadda akayi sunqi bbu irin lallashin da ba’ayi musu ba dakuma gatan da ba’a nuna musu ba.” amma abun yacii tura.”
Daga bayama sai d’aya tadauki zazza6i sannan itama d’ayar takama ala dole aka dawo dasu wajan mama, hakan kuwa yayi mata dad’i.”
Dan itama washe garin suna tatafi itada hassana da husaina taso abata *hanna* sutafii amma kunya tahanata tambaya haka tatafi batareda tatambaya ba.”

Aikuwa kilishi ganin har kwana uku da fad’in boka bbu abunda yasameta yasakata, ishishishrewa tace dama karya yakeyi.”
takira hajiya hadiza tamata tastas.”

*BAYAN KWANA BIYU*

Kilishi na zaune ad’aki jitakeyi gabaki d’aya d’akin yafara juya mata.”
Rasa yadda zata saka kanta tayi nan danan ta yanki jiki tafad’i bayan ta farfad’o bata sake sanin yadda kanta yake ba,” ssai wani irin surutai da takeyi, wanda bazaka fahinmci nai take fad’i ba, ahaka y’ay’anta sukazo suka sameta, mai martaba suka aika aka kira, koda yazo sai bakinta ya bud’e duk wani abunda tayiwa *hanna* sanda tafad’a ran mai martaba abace yafice yabar da’in batareda ya furta ko kalma d’aya ba.”

 

To be continued

Ur’s z33iiyyb3rw3r
[8/27, 6:35 PM] 6ta Abuh: *BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

الحمدالله

*Alhamdulillah en uwa barkanmu da sallah, Allah ya mai-maita mana* عيد مبارك

 

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply