Dare Daya Hausa Novel Hausa Novels

Dare Daya 27-28


Dare Daya 27-28
Viral

PAGES 27&29

Daƙyar yasamo rance dubu hudu da yake tunanin zasu kaita Zamfara ya siyo mata biredi, koda ya dawo gida har duhu yayi sbd an gama sallar magrif INNA najin sallamar ta fito daga ɗakinda hafsa take ta faɗa ɗakin ta girgiza kai yayi ya shiga ɗakin Hafsa din ya tadda ita a duƙe idonta sunyi jajajir fuskar ma ta danyi ja amma ba sosai bah tun kafin yayi magana ta bude baki ta fara magana Abba na fasa tafiya na yarda zan auri Dan Asabe wani murmushin manya yayi, kafin ya fara magana Hafsa miyasa zaki auri wanda bakyaso miyasa zaki ciuci kanki miyasa zaki ƙaryata zuciyar ki, bazaki taɓa auren ɗan Asabe bah tashi maza ki fara haɗa kayanki babu abunda Zuwaira ta isa tayi miki saida izinin ubangiji, idanma itace tazo tace miki wani abu to ki kwantar da hankalil ki kinji gyaɗa masa kai tayi alamar to yayi murmushi ya shafa fuskar ta, Tashi tayi ta haɗa kayan ta gaba ɗaya a cikin wata yar ƙaramar jaka, kayan dudu du basu fici kala goma bah, hijab tasa ya kama hannunta yaja zasu fita Zuwaira tasha gaban su bura ubancan ni zaku tonawa asiri bayan na karɓi sadakin yarinya zaka gudu da ita toh wlh baka isa bah, sai zazzagar jiki take tana kumfar baki hannu kamalu yasa ya tureta aekuwa ta baɗi timmm a ƙasa ihu ta saki ta tashi ta shiga kitchen ta dauko wata sharɓeɓeyar wuta sai ƙalli bakinta keyi tace kamalu inka fasa fita da yarinyar nan ubanka yaci uwatai na fika zama yar tasha wlh koda ka aureni na auri yan tasha har guda biyu nufosa tayi da wuƙar aekuwa da sauri ya koma baya ya tura hafsa cikin ɗaki suka shiga dambe harta samu sa’ar sa ta yanka masa wuƙa a hannu nan take jini ya ɓalle ta ƙwasha aguje ta shige ɗakinta ta mayar da ƙofa ta rufe kar ya biyota sai jikinta ke rawa yana kyarma, fita yayi sbd ya nemi taimakon jama’a yaga jinin yaƙi tsayawa aekuwa yana fita ya samu maƙwafcinsa ya tauna BAGARUWA ya zuba masa nan take jini ya tsaya. BAGARUWA tana tsayar da jini kuma cikin gaggawa kafin aje asibiti, ki tabbata kin tanaɗi BAGARUWA a gidanki koba danke bah. Bai dawo gidan ba daga can masallacin ya wuce a acan ya kwana sai 4:30 ya fito bayan yayi kiran sallah cikin sanɗa ya shiga gidan cikin ikon Allah kuwa harya fita da Hafsa gidan Zuwaira bata tashi bah bai dawo ba sai ya tsaya masallacin saida yayi asuba suka kama hanya zuwa tasha ya hannun tawa wani driver ita sannan ya jiuya ta nan zaune har 12 driver bai tashi bah ashe masu zaman tasha ne Kamalu ya ba kuɗi ba driver mota ba shikuwa ana bashi kuɗi ya fece dama ya tashi Bako sisi. Hafsa na nan zaune aka tayar da haya niya a tashar ashe yaran Dan Asabe dashi kansa sunzo da wuƙake sai zage zage suke suna tambayar wace mota ce ta dauki yar gidan malam Kamalu wani tsoho dake zaune a gefe ya tashi ya sulale yaje gurin hafsa dake zaune a bayan wata mota tana gengeɗi yace yarinya kece hafsa yar gidan malam Kamalu jiki na rawa tace Ehhh ya zaro ido yace toh wlh wannan haya niyar da kike ji sbd ke ake yinta samarine sunkai su biyar suka zo neman ki ki tashi kinga hanya nan zo ta tashi jiki na rawa tabi bayansa ya fitar da ita ta bayan tashar yace kiyi ta gudu zaki iya samun motoci da basu cika ba saiki tara ki shiga fashe tayi da kuka tana cewa wlh Baba banda kuɗi Abba ya bawa wani driver kudin mota na murmushi tsohon yayi ya ciro wasu tarkacen yan Naira ishirin ishirin yace kin gansu dubu ɗaya ce karɓa tayi ta kama hanya ta fara gudu saida ta ƙwashi awa uku tana gudu a hanya har takalmin ƙafarta sun cire amma bata dena gudu bah, Sharara gudu kawai yake kamar zai tashi sama sbd ba haka yaso bah, wani uban burƙi ya taƙa ƙiiiiiiiiiiiiiiii sbd mutun daya gani kwance a tsakiyar titi kuma daga gani mace ce shiyasa ma ya tsaya gefe ya koma yayi packing ya kuma dawo baya kaɗan sai addu’o’i yake a zuciyar sa kar ace ba mutun bace yana ƙara sowa daf da ita yaja baya bakinsa na rawa yace MAHELET??????
Wata wahalalliyar ajiyar zuciya ta sauke tana faɗi ruwa ruwa cikin sassarfa ya koma mota ya dauko bottle water ya buɗe duƙawa yayi ya ɗago kanta ya dauke ta cak ya mayar a gefen titi ya buɗe bottle din ya kafa mata a baki ta fara sha saida ta shanye ruwan tass kafin ta fashe da kuka tana cewa mutuwa zanyi, ganin gaba ɗaya bata cikin hayyacin ta yasa ya dauke ta ya nufi mota da ita yana sata ya koma mazaunin driver ya jasu a tsiyace Zamfara ya koma yana cikin mota ya kira Dr Jameel hlo! Hello Abbas baka isa bane haryanzu Hmmm Dr MAHELET na tsinta a hanya a sume sai numfashin wahala take sauke wa sora kaɗan na ƙaraso cikin Zamfara MAHELET?? Ehh Aa ba MAHELET bace sbd yamma nayi waya da ita wlh Dr itace yana magana yana ƙara jiuyawa yana kallon Hafsa dake kwance rai a hannun Allah, cike da tashin hankali da ruɗewa Dr Jameel ya kashe waya ya kira MAHELET ringing ɗaya gana biyu ta dauka cikin muryar bacci ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa alhamdulillahi a hankali yace bacci kike uhhumm tace sbd idonta cike suke da bacci, kashe wayar yayi ya ƙara kiran Abbas yace Abbas bafa MAHELET bace MAHELET na gida tana bacci ƙara jiuyawa Abbas yayi ya kalli hafsa yayi tsaki yace wlh yaya wannan MAHELET ce gamu nan ƙara sowa murmushi Dr Jameel yayi jin Abbas ya kashe masa waya yayi zaune yana jiran ƙara sowar su yasan bazai kaita general hospital ba doli clinick din nan zai kawo ta..
Komawa yayi office dinsa ya zauna ya cire lapcord yayi hanging dinta jikin hanger Abbas kuwa gudu yake baji ba gani sbd ganin yake kamar mutuwa zatayi kamar yanda take cewa mutuwa zanyi! Cikin ƙanƙanan lokaci ya shigo cikin garin Zamfara direct clinick din Dr Jameel ya nufo da ita nurses biyu suka sa ta a chair aka turata baibi ta kan Dr Jameel ba sbd yasan komi na clinick din da taimakon nurses ya samu ta dawo daidai ya daura mata drip, fitowa yayi daidai Dr Jameel ya fito daga office dinsa sbd ya gaji da jiran Abbas , da sauri Abbas ya ƙaraso gun sa yana cewa yaya wai Kaga yadda ƙafafunwanta suka farfashe kuma me tajeyi *Bungudu* shiru Dr Jameel yayi yana kallon Abbas nifa Abbas na gaya maka MAHELET na gida koda na kirata bacci ma takeyi okay zo muje ka gani yaja hannun Dr Jameel din suka shiga dakinta Hafsa ke kwance tana baccin halawa, waroo ido Dr Jameel yayi 😳yana tsarki ya tabbata ga Allah madaukaki ya Allah wannan wace irin kama ce wannan kamar tayi yawa ƙara sawa yayi yasa hannu ya shafa fuskar hafsa yasa hannu ya yaye blanket din da aka rufe mata ƙafafun yace wallahi Abbas mutunce ka gani ka gani kalli ƙafafun Kaga Hmmm Yaya ni nasan mutunce yanzu janje gida sbd dama Abba ne yace naje bungudu na kaiwa wani mutume saƙo to sauran kadan na ƙarasa garin na tsince ta a tsakiyar titi kwance kamar gawa, Okay yanzu kaje ka yiwa Abba bayani, ni zanje gidansu MAHELET to wa zamu barwa wannan baiwar Allah fah banaso ta farka babu kowa gunta sosai Dr Jameel yayi ƙuri yana kallon idon Abbas ganin tsantsar tausayi mai kama da ƙauna kwance a fuskar Abbas dafa kafaɗarsa Dr Jameel yayi yace Come down bros zansa Nurse Aysha ta kula da ita a tare suka bar clinick din Dr Jameel ya nufi gidan su MAHELET shi kuma Abbas ya nufi gida…….
[7/16, 9:26 AM] Typing….✍🏻: https://chat.whatsapp.com/IduG4o88ZqIHmN1bZ7UDpi

 

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply