Dare Daya Hausa Novel Hausa Novels

Dare Daya 31-32


Dare Daya 31-32
Viral

PAGE 31&32

 

Mannal ce ta katse shiru ta hanyar cewa Daddy are they identical twins? Best-loved uncle kamarsu ɗaya tana magana tana ƙarasawa Abbas sbd bata ganin MAHELET sosai ɗaga mata kai Abbas yayi yanaji a zuciyar sa MAHELET da HAFSAT kamar sunada special bone, kasa haƙuri MAHELET tayi ta ƙarasa ta shafa fuskar HAFSAT harda kama hannunta tana kallo har yatsun hannunsu kala ɗaya ƙara dago wa tayi ta kalli HAFSAT suka kuwa yi 4eyes saida MAHELET taji tsoro sbd har eye ball dinsu kala ɗaya ba baƙi bane maroon ne murya na rawa tace ya su nanki Kallonta hafsa taci gaba dayi kamar ba zatayi magana ba sai kuma tace HAFSAT KAMALU IMAM murmushi MAHELET tayi kafin tace sunana MAHELET IBRAHIM itama murmushi ta mayar mata tana ƙara binsu ɗaya bayan ɗaya da kallo zuciyar ta cike da tambayoyi Mannal ce ta katse musu shiru da cewa Aunty kin samu yar uwa wlh kamarku ɗaya duka murmushi suka sakar mata aekuwa ta washe baki tana cewa Daddy kalla Kaga wallahi har murmushin su kala ɗaya aekuwa Abbas da Jameel me zasu yi inba dariya bah. Sosai jikin hafsa ya warware taji tanajin ƙarfin jikinta saidai ƙafafunta dake yi mata zafi kamar ansa wuƙa an yanyanka mata su,Sai bayan magrif suka watse sosai Abbas kejan HAFSAT da fira da kuma son jin meya fito da ita daga gida take gudu amma taƙi gaya masa haka ma bayan yayo sallar isha yazo su tafi gidansu amma fir taƙi saida Jameel yazo yayi mata jan ido kafin ta yarda ta bi Abbas gida haka a mota yayi ta yi mata fira amma bata basa amsa har suka isa gida sosai Umma ta tarɓesu cike da fara’a, Abbas ya shige ciki ya barsu itada Umma a falo kasa ƙarasawa tayi cikin falon sbd tsoro tunda take a rayuwar ta bata taɓa ganin falo mai girma kalar wannan bah umma tasa hannu ta riƙota tana kallon fuskarta Ya su nan ki a hankali tace Hafsa okay hafsa karkiji tsoro kinji bazamu taɓa ciutar dakeba kinji gyaɗa mata kai tayi, haka umma ta jata suka shiga daga ciki har ɗakinta tunda umma take a rayuwar ta bata taɓa kai wani baƙo ɗakinta bah sai yau ko waye shi kuwa saidai su shiga ɗaya daga cikin ɗakunan gidan amma lokaci ɗaya taji yarinyar ta kwanta bata kuma taji ta bata tausayi ga tsoro kwance a fuskar ta kuma, zaunar da ita tayi gefen gado itama ta zauna zame jiki MAHELET tayi ta zauna akan carpet din dakin dake shinfiɗe mai shegen laushi sai sheƙi take murmushi umma tayi ganin taƙi yarda su zauna gu ɗaya, tashi ki shiga kiyi wanka kinji bara na duba miki wasu kaya kinji tashi tayi ta shiga duba wadrobe dinta ko zata samu wasu kaya wadan da zasu yi mata sbd taga tanada dan girman jiki aekuwa taci sa’a ta samu wata gawn mai kyau milk colour jiuyowa tayi amma saita ganta a zaune bata ko motsa ba a inda take murmushi tayi ta ƙaraso tana cewa Hafsa na’am Umma aekuwa umma tayi wani ƙayataccen murmushi sbd jin yanda Ta kirata da umma gaba ɗaya saita tuna mata da marganya Khadeeja babbar Yarta kawai ta tunanin tayi tare dayi mata addu’a hannu tasa ta ɗago ta tajata zuwa toilet ta haɗa mata ruwan wanka ta nuna mata yanda zatayi amfani da komi dake cikin toilet din. Bata wani tsima ba ta fito sbd tsoro saidai tayi tsaye ganin babu umma a ɗakin taji wani tsoro ya rufeta nan take jikinta ya fara rawa ASSALAMU’ALAIKUM da sauri ta ɗago kanta jikinta sai rawa yake hafsa kin fito to zokisa kaya kinji saiki fita muci abinci kona kawo miki anan kici da sauri da ɗaga mata kai alamar Ehh hijab umma ta miƙa mata ta saka ita kuma ta fita ta haɗo mata abinci tuwon ɗawa ne da yaji miyar bushasshiyar kuɓewa sai kamshin man shanu da tashi, kaya ta bata ta saka ta gabatar da sallar isha’i ta zauna ta fara cin abinci saida taci nayi nak abunta ta tashi da plate a hannu umma tace Aa ta kawo badan taso bah haka tabawa umma plate ita kuma ta koma ta zauna umma ta dan jima bata dawo ɗakin bah tana palo ita dasu Abbas suna fira, waii Abbas yarinyar nan ta gaya maka daga wane gari take Aa umma haryanzu bata magana amma kuma bara kiji wani abun mamaki kamar su ɗaya da MAHELET yar Alhaji Ibrahim da hajiya Asiya wlh umma kamar su ta ɓace kamar identical twins bara kiga hoton MAHELET din nan take ya shiga gallery din wayar sa ya kamo hoton MAHELET Banason rainin hankali Abbas ae wannan duka mutun ɗaya ce wlh umma ba mutun ɗaya bace yauma muka yi hoton wlh ba haɗa su muka yi bah Abb dake darning yana cin abinci yace Abbas zo muga nan take Abbas ya tashi ya kai masa Abba na gani ya shiga tari zuciyar sa na bugawa da ƙarfin tsiya nan take Umma taga tsoro kwance a fuskar Abba murya na rawa yace ina ita wannan yarinyar take daka tsinta a hanyya ki ramun ita ya ture abincinda yake ci a gefe Umma ta tashi taje ta janyo hannun Hafsa saida Abba yaji tsoro ganin kamar su ɗaya da MAHELET babu makawa watan tonon asirin sa ya kama innalillahi wa’inna ilaihi raji’un ya ringa furtawa a zuciyar sa yana jin ya tsani kansa Sam bansan kalar wannan ranar zata zo ba da wlh bazai rabasu da mahaifiyar su bah, Gaisuwan da tayi masa ne ya dawo dashi cikin duniyar mutane domin tune ya haura wata duniyar tunanin nan take Umma ta ƙara fahimtar wani abu, cikin e’ena ya amsa da lafiya qlau ya jikin naki cikin sanyin murya tace alhamdulillah ƙuri abba yayi yana kallon ta kafin yaci gaba da magana, ke yar wane gari ce? Shiru hafsa tayi saida ya ƙara maimaita mata abinda yace kafin tace ni haifaffiyar yar garin nan ce Zamfara amma muna zama a Bungudu nida mahaifina sai kuma tayi shiru, duka tsaya suka yi suna kallon ta amma tayi shiru bata ƙara cewa komi bah cikin sanyin murya umma tace Allah sarki toh meya faru kika baro mahaifinki da kuma mahaifiyarki, cikin kuka tace ni bansan mahaifiya ta sai a hoto mahaifinmu yace ta rasu ne tun bayan data haifemu? Ta haife ku kenan kinada ƙannai girgiza musu kai tayi, kowa shiru yayi sai Dr Jameel da yace ya sunan mahaifinki da mahaifiyar ki saida ta danyi shiru na ɗan wasu daƙiƙu kafin ta fara magana sunan mahaifiyata Rukkayya sunan mahaifina kuma Malam Kamalu waro ido Abbas da Abba suka yi har suna haɗa baki gurin cewa ke yar malam Kamalu ce itama saida taji tsoro jiki na rawa tace Ehh shi yace na gudo zasu yimin Auren doline yace nazo Zamfara ya bani number wani mutume amma kayana bansan inda suke bah harda Adress ya bani yace mutumen likita ne ta share wasu hawaye da suka zubo mata murmushi Abbas yayi yace to ke bakisan sunan mutumen bah duk ya gane nan gidan ne sbd tune yaga paper din da malam Kamalu ya bata harda hoton mahaifiyar ta da mahaifin ta duk ya gani suna nan ya ɓoye a ɗakin sa, cikin rawar murya tace cemun yayi DR AHMAD JAMEEL wani ƙayatatcen murmushi Abbas ya saki sbd yafi kowa farin ciki da wannan zancen cikin e’ena Abba yace to miyasa bana samun mahaifinki idan na kira sa an sace wayar sa ne shiyasa kuma baya wuni a gida girgiza kai Abba yayi ya tashi babu wata walwala a fuskar sa. Umma ta bisa da ido harya ɓacewa ganin ta, tashi tayi ta shiga kitchen ta tafasa madara ta zuba a cup ta rufe ta fito ta nufi ɗakin da abba ya shiga yana zaune ya rafka uban tagumi ya lula duniyar tunani a hankali yaji ta dafasa cikin sanyi murya tace Abban Jameel dan Allah me kake ɓoyemun dan Allah ka gayamun ni matar kace saina taya ka da addu’a Allah ya yaye maka damuwarka wlh Abban Jameel ka canza sosai gaba ɗaya baka samun bacci jiuyo da fuskar sa tayi daidai mirro tace kalli kanka ka gani duk ya wani rame har duhu fatarsa tayi ga wata furfura data fito masa lokaci ɗaya, cikin sanyin murya yace san gaya miki ya zame jikinsa ya shige toilet bata takurasa ba itama ta tashi ta fita……..✍🏻
[7/19, 11:23 PM] Typing….✍🏻: *DARE ƊAYA*

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply