Dare Daya Hausa Novel Hausa Novels

Dare Daya 37-38


Dare Daya 37-38
Viral

PAGE 37&38

idanun Dr Jameel nakan MAHELET da yaga fuskanta yadan kumbura kaɗan, murmushi ya sakar mata itama ta mayar masa ta nemi guri ta zauna, Gaisawa sukayi kafin yace Abbas je Kaga Idan an dauko malam Kamalu fita yayi bai wani jima bah sai gashi yana gaba malam Kamalu na binsa a bayan jikinsa duk a kumbure harda ɗinki aka yi masa a hannu, da gudu hafsa ta miƙe ta faɗa jikinsa tana cewa Abba sai kuka shafa fuskanta yayi yana girgiza mata kai karkiyi kuka Hafsa kinji, gyaɗa masa kai tayi suka koma suka zauna amma yanzu akan kujera sbd bazai iya zama a ƙasa bah Abba yace ya jiki Malam Kamalu Alhamdulillahi ngd sosai Allah ya saka da alkhairi ya biya ka da gidan aljanna ka taimake ni kuma ka taimaki rayuwar ‘yata bakomi dama na tarasu nan ne domin na gaya musu gaskiya abunda na ɓoye shekeru da dama girgiza kai malam Kamalu ya shiga yi wasu hawaye masu zafi suna zubo masa hannu hafsa tasa tana share masa hawaye riƙe mata hannu yayi yana cewa Hafsa karki tsaneni kinji nayi haka ne domin kagin kin samu farin ciki a rayuwa fashewa yayi da kuka gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi sai Abba suke kallo domin jin me zai ce, Haƙiƙa MAHELET da HAFSAT yan biyu ne kuma ba kowane mahaifin su ba face wannan mutumen yana nuna malam Kamalu gaba ɗaya suka jiuyo suna kallon malam Kamalu da kuka ya fara cin ƙarfinsa, Momma kuwa zuciyarta sai luguɗe take sai zufa take domin batason a ƙwace mata MAHELET daga hannunta, shafe gumi Abba yayi kafin yaci gaba da cewa wata rana na fita aeki na haɗu da wannan bawa shida matarsa ya kawota haihuwa, matar ta wahala sosai ya nemi na taimaka masa nayi mata aeki bashi zai biya ni ko yayimin gaɗi har sai ya biyani kuɗin da nayi mata aeki sharce gumi Abba yayi kafin yaci gaba da cewa Nikuma saboda son zuciya da ƙwaɗayin abun duniya kalar nawa yasa nace masa ba haka ba saidai ya sayar min da jariri ɗaya dake cikin matarsa, gaba ɗaya suka ɗago suna kallon Abba da yayinda MAHELET kebin malam Kamalu da wani kallo, nisawa Abba yayi kafin yace Nikuma na kira wannan matar Hajiya Asiya da Mijinta Alhaji Ibrahim domin sune suka sani na nemo masu jariri sabuwar haihuwa zasu bani kudin Naira Billion 10, kafin mu shiga aeki na kira su suka zo kawa kwantar da ita a asibiti tayo cikin ƙarya bayan mun fito daga gurin aeki na saci jaririya ɗaya wacce naga tafi zama ƙarama nacewa Nurses wannan jaririyan batada lafiya zanje na dubata bayan wasu yan mintuna na dawo nace musu ta rasu fashewa yayi da kuka gaba ɗaya falon yayi shiru, Dr Jameel sai zuciyarsa ke tafarfasa yana jin tsanar mahaifin nasa,😓 sai da safe Matar malam Kamalu ta dawo daidai kuma alhamdulillah jikinta yayi kyau sosai sbd ba wani aeki bane nayi mata, nayi mata ƙari ne sai kuma yaran a jiuye suke saida na gyarasu sannan nayi mata ƙari, nan ta tayar da hankali ta tana cewa yara biyu ta haifa kuma lafiyar su qlau sosai naji tsoro kada ta tona mana asiri bayan harna sayar da jaririyan ɗaya kuma na bawa malam Kamalu dubu dari biyu, jin tsoro kada ta tona mana asiri yasa nayi mata wata allura mai gusar da hankali nan take tafita daga hayyacin ta kwanansu biyu a asibiti na basu sallama suka tattara suka koma Bungudu, satin su ɗaya da komawa malam Kamalu ya kirani ya gayamin Matarsa ta rasu 😭tabbas wannan allurar ce ta zama ajalinta domin tun lokacin da nayi mata allurar bata ƙara lafiya bah, shiru falon yayi sai sautin kukan MAHELET dake tashi HAFSAT kuwa kanta ne taji yana mata wani kalar ciwo kamar zai fashe idonta zun bushe babu ko alamun kuka akansu sai kallon mahaifin nata take yi a hankali MAHELET ta tashi ta matsa gefen da malam Kamalu ke zaune ta dafa kafarsa ta ƙara sautin kukanta rungume ƙafafun sa tayi tana wani kuka mai karya zuciyar mai sauraro rufe idonsa yayi gam yana jin kukan MAHELET har cikin zuciyarsa, a hankali ta fara magana Tace Baba Meyasa ka siyar dani me kayi da kuɗin? Sai kuma ta fashe da kuka kafin taci gaba da cewa da gaske mahaifiyar mu ta rasu? Miyasa ka bari aka yi mata allura? Miyasa ka zaɓi abun duniya akanmu BaBa gaba ɗaya falon yayi shiru sai sautin kukanta ke tashi da maganganun ta, a hankali ya shafa bayan ta yana girgiza mata kai mitsewa tsaye HAFSAT tayi zata fita a falon gaba ɗaya bata ganin kowa duhu take gani MAHELET ta tashi ta rumgume tsam tana fashewa da wani sabon kuka tana cewa ashe ke yar uwa tace? Tun ranar dana fara ganin ki naji inason ki. Naji cewa ke jini nace ashe dama mafirkin da nake yi gaskiya ne, zame jikinta tayi tana kallo HAFSAT shafa fuskar tayi tayi mata kisa a forehead tayi mata a kumatu luuuuuu HAFSAT tayi ta faɗi sumammiya ihu Abbas yayi yayo kanta yana kiran sunanta Malam Kamalu kuwa mutuwar tsaye yayi kar ace itama mutuwa zatayi MAHELET ta ƙara fashewa da wani kuka tana cewa wayoo Allah hafsa karki mutu ki barni nima mutuwa zanyi komawa tayi gurin Momma ta riƙo hannunta tana cewa momma muje asibiti tashi muje gaba ɗaya ta ruɗe sai surutai take Umma ta tashi ta fito da ruwa masu sanyi ta miƙara Dr Jameel sbd Sam Abbas baya cikin hayyacin sa sai bubbuga kumatun Hafsa yake yana kiran sunanta yana ta tashi karta tafi ta barsa, bude ruwan Jameel yayi ya iba a hannu ya shafa mata a fuska saida yayi haka har sau biyu kafin ta sauke ajiyar zuciya tana bin mutanen gurin da kallo idonta ya sauka akan BaBa murya na rawa tace BaBa mafarki ne nake ko kar kace da gaske ne, girgiza mata kai yayi yana cewa Hafsa ba mafarki bane yana magana yana shafe hawayen da ke zubo masa masu mugun zafi da yake jin zafin su har cikin zuciyar sa, Kuyimin rai ku gafarce ni yarana wlh inason ku ƙwaɗayin abun duniya ne ya jefani a halaka, badan banason ku ba, wlh inason ku ya haɗa hannayen sa duka biyu yana roƙon MAHELET da HAFSAT nasan na ciutar daku nayi sanadiryar rabaku da mahaifiyar kuh dan Allah ku yimin afuwa, Faɗawa jikinsa MAHELET tayi saɓanin HAFSAT take binsa da eyes, HAFSAT MAHELET Abba ya kira sunan su dan Allah ku yafe min kuyimin afuwa wlh banyiwa mahaifiyar kuh allura da niyar ta mutu bah ko ta ciutar da ita nayi ne sbd kada asirina ya tonu 🙏🏻ya haɗa hannayen sa duka biyu yana roƙon su, murmushi ƙarfin hali MAHELET tayi tana share hawaye tana cewa Abba babu wanda ya isa ya canzawa mutun qaddararsa sai Allah, koda baka yi mata allura bah haka Allah ya rubuto bazamu rayu tare da ita bah, roƙon hannun HAFSAT tayi tana cewa Hafsa kiyi haƙuri wannan ce qaddararmu dan haka mu karɓeta hannu biyu-biyu kiyi haƙuri kinji nasan kinsha wahala a rayuwa ba kamar ni bah dana taso cikin daula cikin jindaɗi fisge hannunta tayi tafita daga falon sosai hankalin malam Kamalu ya tashi ya miƙe zai bita Umma ce tace A’a karka bita, tana buƙatar tayi kuka duk wannan abun da kuka ga tanayi sbd batayi kuka bane……. ✍🏻
[7/25, 8:52 AM] Typing….✍🏻: *DARE ƊAYA*

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply