Dare Daya Hausa Novel Hausa Novels

Dare Daya 45-46


Dare Daya 45-46
Viral

PAGE 45&46

 

Shiru Jameel yayi yanajin zafin kukan da Momma keyi a hankali ya kama hannunta yana miƙar da ita jan hannunta yayi yana cewa muje gida, Direct gidansu ya nufa da momma har lokacin kuka take suka shiga gaba ɗayansu suna zaune gaba ɗaya a falo suna breakfast, ɗagowa umma tayi ta miƙe tana cewa Jameel lafiya zuciyarta na bugawa kardai ace wani ne ya rasu daƙyar ta samu ta tattaro natsuwar ta tana cewa Jameel lafiya a hankali yace umma MAHELET ce bah lafiya Hafsa dake cin abinci ta ƙware Abbas dake gefenta ya miƙa mata ruwa ta ƙarɓa ta fara sha umma ta ƙarasa gunsu ta kama hannun umma suka shiga ciki suna shiga ta fashe da kuka tana cewa Khadeeja na shiga uku na lalace zuciyata ciwo takeyi a hankali tace kici gaba da faɗi Hasnunallahu wani’imal wakeel ɗaga mata kai tayi, yauwa tashi ki gyara jikin ki ga toilet nan bara na kawo miki abinci bata jira me zatace bah ta tashi ta fita falo ta koma nan kunna ta suka jiye mata abunda ke samun MAHELET ita kanta saida taji tausayin momma shekaru sama da talatin tana zaune tare da Alhaji Ibrahim,Ƙara sawa tayi tana cewa yanzu ya jikinta ta farfaɗo? ehh Dr Jameel yace yana cewa yanzu zanje nasa ayi mata tranfer zuwa hospital dinmu idan jinin da aka daura mata ya ƙare dan Allah umma ki kula da momma karku bari ta fita ko inna Abbas ka bata magani tasha harda na bacci kaji okay yace shima yana tashi Baba kuwa mutuwar tsaye yayi jin Alhaji Ibrahim na ƙokarin yinwa MAHELET fyaɗe Hafsat kuwa kuka kawai take Jameel zai fita tace Yya Jameel zan bika girgiza mata kai yayi yana cewa Ehh sai zuwa anjima, haka ya fita yaje yayi clearing komi aka mayar da ita hospital dinsu domin ganin yake a gunsa zatafi samun kulawa aekuwa suna zuwa ya fara bincike harda virgin dinta saida ya duba yaga minor injury ne kawai amma babu abunda yayi mata saidai yayi ƙokarin sawa sa, shiyasa gabanta yayi jajajir, ajiyar zuciya ya sauke ya gyara mata riga jikinta yabi da kallo yaga yanda fuskanta ya kumbura saida ya runtse idonsa yana ƙara jin tsanar Abbi wannan shine na biyu aekuwa bara kayi na uku ba ko gidan naka ma bara ta koma bah tsohon dan iska, fita yayi gaba ɗaya daga hospital din ya nufi gida nan ya tadda hafsa tasa rigama kamar wata ƙaramar yarinya sai kuka take akaita gun MAHELET dan ƙaramin tsaki yayi ya shigo nan yashiga ƙwantarwa da momma hankali harya samu taci abinci ta shirya ya dauketa ya kaita asibiti Alhamdulillah taji sanyi a ranta ganin yanzu an cire mata oxygen dinda aka saka mata sai bacci take, harda murmushi ta saki tana yiwa Jameel godiya sai lokacin tace ina key din mota na zanje gida okay baice komi ba ya miƙa mata key dinta ta fita saida ya bata almost 20 minute kafin yabi bayan ta, aekuwa abunda yake tunani shi ke faru sosai suke dambe har. Abbi ya fasawa momma baki sai cewa yake ya saketa saki ihu kuma ta fito masa da MAHELET dinsa su Adamu duk sun fito sunyi tsaye suna kallon ikon Allah abunda basu taɓa gani bah momma ta shiga cikin gida ta fara watso maza kayansa tana cewa dama gida nane dan haka yau bazai gobe ba saika barmun gidana tsohon banza ƙwarto!!! Ƙwatooo!!! Kuyi masa ihu yana ƙwartanci ya rasa dawa zai yi saida yar cikin sa Jameel kuwa ganin faɗa bamai ƙarewa bane yasa ya kira Police duk aka tattara su aka yi Police station dasu hardasu Adamu sbd anaso subada statement. Ranar dai gaba ɗaya saida yan area’s din Gidan momma sukaji meya faru suna ta alhini da wannan al’amari wasu kuma na Allah wadai da masu hali kalar na Abbi. Satin su ɗaya a hospital jikin MAHELET ya warware sosai taji sauƙi sai ƙafarta dake yi mata ciwo idan ta taƙa
Sam bata bari su haɗa ido da Dr Jameel data gansa zata mayar da idanunta ta rufe, wani lokacin ƙamshin sa ma kawai Zataji ta rufe idonta, momma ce zaune tana bata tae a baki tashin ta kenan daga bacci kwana biyu Alhamdulillah ana samu tanacin abinci kuma ta dena kukan da take yawan yi, a hankali momma tace MAHELET Dan Allah ki saki jikinki kinji komi ya wuce idan ba sakin jikinki kika yi ba Jameel bazai bari mu koma gida bah kuma kinga gwara mu koma na fara shirye shiryen bikin aure autana kuma my one and only daughter, shiru MAHELET bata yi magana bah hannu tasa ta ɗago haɓarta hawaye ta gani kwance a kumatun ta girgiza mata kai tayi tana ƙokarin haɗiye nata hawaye noo MAHELET Meyasa kika kasa mantawa ki manta mana kinji banaso ki ringa sa abun a ranki kinji ɗaga mata kai tayi tanasa bayan hannu tana share hawayen ta, Oya karɓa ki shanye tea din karya huce kuma kice bazaki sha ba, tana karɓar cup din Dr Jameel na turo ƙofa dagowar da zatayi sukayi 4 eyes zakin cup din tayi gaba ɗaya ya zube mata a Jiki tayi saurin rintse idanunta tanajin yanda zafin tea din ke bin jikinta, subhanallah MAHELET momma ta faɗa amma sai taga Dr Jameel a tsaye nan take ta gano dalilin rufe idanun da kuma sakin cup din tea,Girgiza kai tayi kafin tace Jameel ƙaraso mana, momma ina kwana an tashi lafiya? Lfy qlw Alhamdulillah Jameel ygd yasu umma? lfy qlw ya mai jiki Insha Allah yau gida zata wuni murmushi momma ta saki saida haƙoranta na Makka suka baiyana guda biyu sosai taji daɗi har cikin ranta dama ta gaji da zaman asibitin nan, ƙara sowa yayi amma sai yayi tsaye sbd momma dake gun, ganin yanda yake kallon MAHELET yasa momma tace ina zuwa, ta tashi ta fita gaba ɗaya tabar musu room din, mugun daɗi Dr Jameel yaji, ƙara sawa yayi yana kiran sunanta a hankali ƙara runtse idonta tayi girgiza kai yayi ya janyo kujera ya zauna hannu yasa yana ƙokarin yaye blanket dinda ke jikinta aekuwa ta riƙe blanket din gam, Murmushi yayi yana cije lips din sa kafin yace Oya open your eyes!! Idan ba haka ba saina yaye blanket din nan bata buɗe ba tashiga girgiza masa kai, cikin ɗaga murya yace nace ki buɗe idannunki fashewa tayi da kuka still tana girgiza masa kai, mamakin abun ya fara bawa Jameel ganin da gaske bazata buɗe idanunta ba ta kallesa
Hannu yasa ya kamo hannunta na dama ya riƙe cikin nasa a hankali ya fara magana MAHELET ki taimakawa rayuwa ke buɗe idannunki ko sau ɗaya ne na kalle ki, MAHELET meyasa kikeson hukunta ni akan laifin da bani na aekata bah do you want me to die girgiza masa kai tayi amma still bata buɗe idanun ta bah, okay toh ki buɗe idannunki MAHELET nasan kinji sauki amma sbd bakya buɗe idannunki idan nazo dubaki shiyasa naƙi sallamar ki ku koma gida, kuma ya kamata ace kina gida sbd shirye shiryen bukin mu, ko bakyaso nane da sauri ta girgiza masa kai, to ki taimakawa son da kike mun ki buɗe idannunki ko sau ɗaya ne na ganki MAHELET so aljannar duniya ne amma ban fahimci hakaba sai da na kurɓi ɗanɗanon zumar soyayyarki, MAHELET bazan taɓa dana sanin zaɓen ki da nayi ba a matsayin masoyiyata ba, kuma matar da zan aura saboda kece zuciyata ta zaɓa kece wacce raina ya aminta da ita, kece zuciyata ta zaɓa ki zamo uwar ‘ya’ yana mukasance tare har fitar numfashina na ƙarshe yana kaiwa nan ya matse mata hannu aekuwa ta buɗe idanunta da sauri Jameel ya ɗago yana ƙare mata kallo sai yanzu yaga yanda ta canza tayi kyau tayi wani haske fuskarta sai shaning take ajiyar zuciya ya sauke yasa hannu ya shafi fuskarta yana cewa Inason ki mata na murmushi tayi tasa hannu ta ɗaya tana rufe fuskarta shima murmushi yayi yaci gaba da murza yatsun hannunta….. ✍🏻
[7/30, 11:35 PM] Typing….✍🏻: *DARE ƊAYA*

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply