Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 32


Farhatal Qalb 32
Viral

PG:32_

===

Gaba daya ji Zayn yake yi tamkar babu laka ajikin sa. Saboda yanayin yadda jikin nasa yayi laushi ya kasa zare zaren. Jikin sam ba karfi.

“Sorry….” Ya sake maimaitawa yanata kiciniya.

Nadra dake jiran Waheedah ta karasa . Hannu daya ta saka ta yage awawwaron zaren ya fita daga ciki.

“Ya Zayn . Ahlam na jira fa…”

“Gani nan… ” Ya amsa ta yana sauke kai.

Wasu masu serving abinci zasu shige ciki ya dauki ruwan roba daya daga cikin ledar sa. Nan da nan ya shiga kwankwada. Sakamakon wani zafi dayaji yana taso masa.

Abokan suka karasar da shi wajen Ahlam. Ta kama hannuwan sa acikin nata. Yayinda kafadun su ke gugar na juna. Ya juya ya kalleta. Ta dan daga tsayinta zuwa kunnen sa ta rada masa,

“I’ve the right hubby …… An daura ai ko?” Ta karasa ce masa tana murmushi.

A haka suka shiga cikin marque din ango Zaid da amaryar sa Jannat sune a farko. Sunyi matukar kyawu ta saka wata riga baka gown me flowing da wasu stones masu glittering farare tas.

Sai shi ango Zaid da yayi shigar alfarma shima cikin wagambari fara data sha aikin baki. Yayi bala’in kyau ba kadan ba. Shi da amaryar tasa sun bada color .

Sai couple na biyu. Ango Zayn dayayi shigar wagambari baka data sha aikin kala fara. Sai amaryar sa Ahlam data sha kyau itama cikin farar gown mai glittering (kyalkyali) na stones baki.

Ba kadan ba sunyi kyau. Kyawu irin wanda alkalami yayi kadan wajen fassara shi. . ..

Gaba daya kowa sai da ya miqe a cikin marque dinnan in honor of the couples. Har sai da suka zazzauna awajen zaman su. Tukun sannan kawayen amare da abokan angwaye suma aka sakar musu speaker rawa suka dan tattaka. Kafin su koma wajen zaman da akayi musu na musanman suka zazzauna.

Daga nan aka kira wata babbar malama. Ta bude taro da addua. Sannan gayshe gayshen yan uwa da abokan arziki. Sanarwar zuwan manyan baki na musanman. Bada tarihin amare da angwaye daga abokanai da kawaye. Sai kuma refreshments.

Abinci ne kala kala babu irin wanda babu. Menu aka bawa kowanne yayi ticking abincin da yake so. Dik wanda ka zaba shi din ake kawo maka. Nadra da kanta ta zabarwa Umma Hadiza. Aka kai mata. Yayinda Waheedah ta zabi wanda take so.

Karar kwanuka da cokula kawai kakeji sai slow music da ke tashi. Amare da angwaye ma an saka su dole su ci. Bisaga jagorancin Ummimi da tace jikokinta ba zasuyi jidalin yunwa ba. Bayan kowa ya take ciki yana cika cikin sa.

Aka saka dariya baki daya. Ahlam ta juya ta dubi Zayn da ke danna wayar sa.

“Hubby .. abincin fa?”

“Na koshi…” Ya amsa yana kallonta

“Ya zaka ce ba zaka ci ba…? Bayan Ummimi tace duk mu ci. ”

“Banacin abincin wadanda bansani ba gaskia. Wanda na sani dinma rarely nake ci.”Ya karasa yana cigaba da danna wayar sa.

Ahlam ta juya ta kalli su Zaid da Jannat. Suna feeding junan su suna hirar su kasa kasa. Wani tuququn bakin ciki ya tsaya mata a makoshi. Ganin ita natan yayi biris da ita waya ce ma agaban sa. Ko irin lallashin nan nata baya yi.

“Zayn….”

“Naam .. Ahlam”

“Ba zaka ce naci abincin ba?”

“Tohm Waheedah ki ci abincin .”

“Waheedah Kuma?” Ta tambaye shi cikin tsantsar kulawa.

Sai a sannan Zayn ya gano baranbaramar da yayi. Yayi saurin fuskewa hadi da mayar da wayar sa aljihu. Kasan zuciyar sa tunanin Waheedah yake tabbas. Amman harshen sa daya ambata sam baisan dalili ba .

“Look Ahlam….”

Ta katse shi.

“Babu zancen look … Zayn I’m i that unimportant? ”

“Noo . .. Kinaji Dawud ne ba kinga dazu na je wajen sa ba…!”

“Eh….”

“Toh maganar Waheedah din yake mun . Yana son ta ”

Ahlam ta sauke gauruwar ajiyar zuciya. Amman duk da haka ta sake tambayar shi da,

“To meyasa zaka kira ni da Waheedah? Tun da ai ba awajen bane. Yanzu ni da kai ne a zaune ”

Ya sosa keyar sa yana murmushi.

“Yes I’m all ears Zayn .. saboda me zaka kira sunana da Waheedah?? Sunana bashida matsayi a zuciar ka ne ko kuwa?”

“Da shi muke magana ta WhatsApp … Kingan shi da can wayar sa a hannu.”

Ya nuna mata Dawud da yatsa. Nan taga Dawud din wayar sa a hannu yana dannawa. Hankalinta sai ya kwanta. Ta danyi murmushi lallausa

“Na yadda ..”

“Yauwa…. ” Ya amsata yana murmushi

“Abincin fa?”

“Ki ci….”

“Ka bani…. Feed me pls”

Ba yadda ya iya. Ya debo fried rice da patoosh salad a spoon ya saka mata a baki. Ya zuba ruwa a cup ya bata.

Kawayen amarya na ta awwwwn.. Waheedah ta dube su cikin kulawa. Suna birgeta kwarai matuka da ka gansu kasan su din suna kaunar junan su .

Ya dakko tissue ya goge mata baki.

“Thank you hubby….”

“Anytime….”

Yana daga kai suka hada idanu da Waheedah . Ya janye idanun sa da sauri yana saisai ta kan sa.

Haka aka cigaba da gudanar da shagalin bakin ranar. Yan uwan juna gaba da baya. Kamar ko da yaushe. Babu wasu bare sai yan gayyata da wasu tsirarru na daga kawaye ko abokai dama makota da sauran su

Anyi ‘barin kudi ranar tamkar bishiyun kudi ne da su suke zazzaga su.

Dukkanin iyalan Ummimi matan su 3 anko sukayi gwanin shaawa. Cikin wani dandatsetsen lace mai dan karen kyau da kyalkyali. Yayin da mazan suma sun zuba wata gezna shadda mai madaukakin tsada da kyau

Lamarin sai wanda ya gani ya kuma halarci taron kawai. Anci an sha anyi hani’an.

Zayn yayi excusing kan sa ya fita daga cikin marque din. Ya tsaya a tsaye yana mai furzar da iskar bakin sa.
Kansa sai wani sara masa yake yi .

Yanayin jikin sa baki daya ba dadi. Ya kuma tabbatar da hakan nada nasaba da wannan bikin. Gaba daya ya rasa wane tunani ma zai kama da zai fitar masa da mafita.

“Zayn… Ka dawo ciki zaa dauki pictures.” Cewar Awais abokin sa.

Gyada kai kawai yayi alamun toh. Ya koma ciki. Aka shiga daukar hotuna ta ko’ina photographers nata haskakawa da aiyukan su.

Sannu ahankali wadanda aka gayyato suka fara tafiya inda suka fito. Ciki har da Waheedah da Umma Hadiza. Daga karshe kuma bayan yan uwan sun gama warkajami. Aka tashi daga taron sai kuma na washegari idan Allah yayi da rabon ga ni….

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al’amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K’ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K’ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰_*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

 

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply