PG:33_
=====
*GIDAN MALAM NALADO*
*DA* sallama a bakunan su, Suka shiga cikin gidan na su. Marka na kwance akan shimfidar tabarmar ta. Saitin gefenta daga dama kuwa fitila ce ta wuta mai lagwani.
Bata amsa sallamar ba. Sai ma dago fitilar da tayi don ganewa idanun ta.
“Wohoho. Fito nan mai sunan malam. Ai na gayan ka.”
Nan da nan Malam Nalado ya fito daga cikin daki. Ya tsugunna agaban mahaifiyar ta sa.
“Kaga ni ko …..? Wane tsinannen biki ne za’a tafi tun rana tsaka sai dare zaa dawo?”
Umma Hadiza ta fara girgiza kai zata yi bayani. Marka ta hanata. Ta hanyar mikewa jikinta har kakkarwa yake saboda bala’i.
“Dube su … Dubi kayan jikin Wahidin fisabilillahi… Wannan shiga ta dace? Dubi fatar jikin ta da fuskar ta. Tayi kwailin.. kalli yadda ta kode tsabar bilicin.”
“Wallahi Allah bana bleaching Marka .. Mai ne da sabulu Nadra ta bani. Wadda Umma ke yiwa mahaifiyar ta ai…”
“Zaki rufe mun baki ko sai na zo na gabje ki anan?”
“Allah yabaki hakuri ….” Ta fada hawaye sirara na zuba a kyakkyawar fuskar ta…
“Na gaji….. Mai sunan Malam. Yau dai kagani da idanun ka. Ire iren rashin tarbiyyar da suke gudanarwa acikin gidan nan..”
“Wallahi Malam… Ko tashi ba’ayi ba awajen taron muka taho.”
“Bikin gidan na uban ku ne dama da zaku zauna?. Ai malam na dauka abun na mutunci ne da arziki da mu ma za’a gayyace mu. Muje mu kashe kwarkatar idanun mu. Amman saboda tsabar akwai kaucewar hanya ai kaga su kadai suka tafi. Sai cikin dare. Kowane gidah sun kulle gidajen su banda mu. Su sun tafi regargadin biki gidan mu a yashare. ”
Umma Hadiza ta tsugunna tana jujjuya kai. Idanunta sun kawo ruwa sosai. Cikin muryar ban hakuri da sanyin jiki tace,
“Dan Allah Marka kiyi hakuri …. Wallahi wallahi babu inda mukaje sai wajen taron bikin nan. Kuma acikin gidan yake daga wani bangaren. Kayi hakuri Malam. Dan Allah ku yafe ni.”
“Hakuri … Wohoho ko ba hakuri ba? ”
“Eh dan Allah Marka ”
“Mai sunan Malam..”
“Na’am Marka .”
“Kace Hadiza ta bar maka gidan ka. ”
“Kiyi hakuri Marka ..” ya fada a hankali yana kallon Hadiza ta gefen idanu
“Nayi hakuri ?” Ta tambaye shi. Tana binsa da kallo sheqeqe.
“Ehh .”
“Matsa can. Sahoro mijin sahorama. Gidah na waye?”
“Na ki ne Marka.”
“Toh wabillahil lazi zaman Hadiza ya kare a gidan nan.”
“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun!!!” Kamal ya shiga furtawa. Yana takawa dakyar hannun sa dafe da bango
“Matsa can. Gawa taki rami kawai ”
“Haba Marka .. Haba Marka.” Umma Hadiza ta fada . Hawaye na kwarara a fuskarta sosai jin yadda Markan ke aibata Kamal jikan ta.
“Karya nayi? Ba ragowa bane shi? Kullum akan magani. Nakasasshe, Bushassshe. Kanjamamme. Ai kuwa gawa ce shi din da taki rami ”
Kamal yayi murmushi. Ya dafa bango ya zauna yana sauke numfarfashi
“Marka… Ki dena cewa haka … Tamu kaddarar kenan. Lapiyayyun ma basu da tsimi bare dabara. Kowanne rai Allah ya halicce da dukkanin dik wasu abubuwan da zasu faru agare shi. Don haka wannan cuta da muke fama da ita kankarar zunubai ake mana…Marka mu fa jikokin k ..”
“Karka karasa… Kar ka soma karasawa. Bani da tabbacin kudin jikoki na ne ko akasin haka. Mai sunan malam babu yadda banyi ba kar ya auro Hadiza. Amman ya toshe kunnen sa. Yayi kunnen uwar shegu. Hadi da badawa idanun sa kasa. Ya kafe ya nace ya cije kan dole sai ya aurota. Gashi nan ai baki dayan tattalin arzikin sa ya kare akan ku da uwar ku. Dukkanin ku ku ukun ba mai lapia ingatacciya. Ita wannan baki daya ma makanta ce da ita. Sai da temakon gilashi take gani. …” Ta karasa tana mai sakarwa Waheedah rankwashi .
Waheedah bata ce komai ba. Yayinda kanta ke a kàsa kawai.
“Kai maganganun menene haka ne..? Cikin bacci na ke jiyowa.” Cewar Inna Sa’adatu . Ta gantsare tana miqa hade da yin hamma.
“Su wa kika sani? Hadiza da iyalanta ne. Ina magana suna mayar mun. Munata musayar yawu da ni da uwar tasu. .”
“Au wai sai yanzu kuka dawo…? ” Inna saadatu ta tambaya tana mai sauke kallon ta bisa fuskar Umma Hadiza .
“Eh yanzu muka dawo Sa’adatu ” Umma Hadiza ta amsa ta.
Inna Sa’adatu cikin makirci ta sake cewa,
“Yanzu ku kuna mata ku ka kai wannan tsakar daren awaje? Fisabilillahi biki bana dangin iya ba bana baba ba ? Meyakwan ke Hadiza ki taso keyar ta ku dawo tun tuni.”
“Wacce hadizan ce zata ce wa yarta su dawo da wuri? Bayan watsewar ita ke koya mata ..”
“Allah ya baku hakuri Marka..”
“Ni fa idan kina gayamun Kalmar hakurin nan ji nake tamkar wuqa kika dabamun a zuciya. Hakurin ubanme zanyi? Kama ki zan na saka a garke na daure ko kuwa? Ai babu abunda ke tsakani na da ke Hadiza. Ba auren ‘da na kike ba …. Shekaru masu dadewa.”
Umma Hadiza ta tamke idanunta tana dartse bakinta. Baki daya kanta ya mata nauyi. Duk tarin shekarun nan da aka dauka. Bata taba buda baki tacewa yaranta basa tare da mahaifin su ba. So take akwai lokaci da ta ware zata sanar musu idan Allah ya so. Amman baki daya Marka ta tarwatsa mata lissafi. Kusan kullum seta goranta mata. Tayi ta shelan ba aure tsakanin ta da dan ta. Tamkar wani lefi tayi babba da yasa ya saketa. Bayan Markan ce ta saka dole ya saketa babu wata kwakkwarar hujja.
Hawaye sirara suka shiga zuba a idanun Umma Hadiza. Marka ta kalleta tana yamutsa baki.
“Ni fa kukan munafurci ne banaso. Uban me na miki iyye?”
Umma hadiza ta girgiza kai kawai. Hade da saka hannu ta share hawayen ta.
“Babu komai ..”
“Toh mai sunan Malam… Yau magana ta kare. Idan Allah ya kai mu wayewar gari. Inason Hadiza ta tattare nata ya nata ta bar mun cikin gida. Kar kuma ta sake tako kafarta kofar gidan nan idan ba da wani dalili ba kwakkwara. Wannan shine zancen da na yanke. ”
“Tohm Marka.. Allah ya tashe mu lapia ” Umma Hadiza ta fada hade da miqewa tsaye. Ta kamo Kamal ta temaka masa ya shiga daki.
Dan sauran kayan kwalam da suka samu awajen bikin ta juye musu akan faranti ta raba musu shi da Najib.
Sannan ta kunna musu maganin sauro tasa daga bakin kofar daki. Tayi sai da safe ta koma daki.
Waheedah ta cire kayanta ta mayar da na gidah. Wata riga da ta mayar da ita ta bacci. Sai hula da ke kanta
“Baki kwanta ba….? Tara da kwata fa ”
“Zan kwanta Ummaa. Yanzun dai bana jin bacci ”
Umma Hadiza ta sauke nannauyar ajiyar zuciya. Hawayen da ta ke kokarin zubowa ya shiga tsiyaya . Tayi sauri ta goge . Nan ta fara jiyo sautin na waheedah har da shessheka. Tayi saurin janyo ta jikinta tana lallashinta.
“Bar kuka Waheedah … Kowane dan adam da tasa kaddarar., Mu ta mu …..
❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥
*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al’amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*
*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*
*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K’ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*
😄😄😄😄😄😄😄
*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*
*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*
INAYA(riba biyu)___mamughee
SANADIN LABARINA___Rano
BABU SO___Billynabdul
FARHATUL K’ALB___Miss xoxo
GURBIN IDO____Huguma
*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*
*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*
Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300
*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank
*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902
*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107
*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰*_RANO SCRUMPTIOUS MEAL_*
_(Where every flavour tells a story …..)_
*_By HAFSAT RANO_*
_(Mother/wife/writer)_
_08030811300_
_IG:Rano_scrumptious_meal_
_INA MA’ABOTA ABINCI? WATO *TRADITIONAL FOOD IN KANO*? GANGARIYAR ABINCI NA AL’ADUN HAUSA DA NAHIYAR KETARE? BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA. MUNA DA LEMUKA WATO *LOCAL DRINKS*. ZAKU IYA KAWO NA HIDIMOMIN LIYAAFA MUYI MUKU_
_MU NA YIN:_
*_FUNKASO_*
*_ALKUBUS_*
*_SINASIR_*
*_WAINA_*
*_ASSORTED MEAT (KAYAN CIKI)_*
*_COW TAIL/COW LEG (DAB’URI)_*
*_CHICKEN AND FISH PEPPER SOUP_*
*_LOCAL DRINKS:_*
_HIBISCUS (ZOBO)_
_GINGER_
_AMAANI FRUITY SHAKE_
_MUN TANADAR MUKU MOUTHWATERING ABINCI KALA KALA WADANDA KE GINA JIKI DA KARA LAPIA. ABINCIN MU A TSAFTACE YAKE. KUMA MUNA YIN SU NE AKAN YADDA KOWANNE MUTUM ZAI IYA CI . AKWAI SPECIAL SOUPS NA MASU ULCER WADANDA BABU YAJI. AKWAI KUMA NA PEPPER DEM GANG GA MASU SON HOT AND SPICY…._
_KADA KU MANTA MUNA YIN NA TAKEAWAY/ORDER . MUNA KUMA YIN NA BIKI (WE CARTER TO SMALL/LARGE EVENT…._
_FUNKASO TO PAIR WITH COW TAIL:2K_ _WITHOUT COW TAIL:1K_
_ALKUBUS TO PAIR WITH ASSORTED MEAT (KAYAN CIKI) 2K. WITHOUT ASSORTED MEAT :1K_
_PLS NB: PAYMENT VALIDATES INTEREST….. DELIVERY WITHIN KANO:500 NAIRA_
________
*_FARHATAL-QALB_*
_(FARIN CIKIN ZUCIYA)_
_NA_
_NANA HAFSATU_
No one has commented yet. Be the first!