Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 60


Farhatal Qalb 60
Viral

PG:60_

“Kinyi shiru Waheedah…. ” Cewar Haj Hameedah. Ta dan jijjiga waheedan.

Umma Hadiza ta sake dukar da kanta a kàsa. Tausayin tilon yar ta ta mace ya kamata kwarai matuka

“Waheedah… Diyar albarka.” Gwaggo haule ta fada itama gabanta na harbawa.

Waheedah ta daga kai. Ta sauke numfashi da kyar tana jijjiga kanta da sauri

“Menene Waheedah?” Maa ta sake tambayar ta cikin kulawa.

“Maa, Umma, Gwaggo. Kuyi hakuri amman ba zan iya zaman aure da Ya Zayn ba.”

“Meyasa Waheedah… Why?” Maa ta tambaye ta cikin fargaba.

“Bar cewa haka Waheedah…. Kinji?” Cewar Gwaggo haule.

“Ya Zayn tamkar marigayi Ya Kamal na dauke shi. Na dauke shi tamkar wanda muka fito ciki daya. Yaya Ahlam itama tamkar Yaya ce awaje na. Ta dauke ni kamar kanwar ta da suka fito ciki daya…. Ya zata ji idan har taji ni da ya Zayn an daura mana aure? Zata dauka naci amanar ta ne. Dan Allah kuyi hakuri amman ba zan iya zaman aure da ya Zayn ba. Na amince a auramun koma wanene amman banda ya Zayn.. Dan Allah…Zuciyata zugi ta ke Maa. Kasan zuciya ta tamkar zai ballo saboda radadi..”

“Dan Allah Waheedah ki bar cewa haka kinji? Wannan aure Allah ne ya hada. Da kuma rokon da Zayn ya dukufa yanayi a sujjada har Allah ya karbi adduoin sa. Zayn ya dade yana dauke da kaunar ki a zuciyar sa Waheedah. Ke ce FARIN CIKIN ZUCIYAr Zayn … Yana kaunar ki tun kafin a daura auren su da Ahlam Waheedah. Zan iya tabbatar miki cewar kece first love din Zayn kamar yarda ya sanar da mu. Ya fara kaunar ki tun kafin ki zama yadda kike a yanzu. Maana tun kina karama… Ki sani auren ku da Zayn ba kici amanar Ahlam ba. Hakama Zayn bai ci amanar Ahlam ba. Zaki fi dukkanin mu masaniyar komai saboda kece kike zaune a tare dasu… Kinsan irin zaman da suke yi. Wanda maslahar sa aure ce. Na karkare miki zance har satin bikin Zayn bai dai na roko na a fasa auren nan ba don yanada wacce zuciyar sa ke muradin kauna., Bamu amince da auren ki da Zayn ba don mu muzanta miki. ko dan muci amanar ki mu kuma tauye miki hakki.. No! Auren ki da Zayn alheri ne. Auren ki da Zayn zukata da yawa sunyi farin ciki. Auren ki da Zayn abubuwa da yawa zasu gyaru. Domin ke din wani haske ce a tattare da rayuwar mu baki daya Waheedah. Kaunar da na ke miki ta sa na amince da auren ku. Na kuma yi farin ciki marar misaltuwa da kasancewar hakan Waheedah.. Ki dau wannan auren a matsayin taki kaddarar. Ki kuma yafe mana da zartar da hukuncin auren ku batare da an shawarce ki ba. Kauna ce ta kawo hakan.., Idan kuma kina kan bakan ki na rabuwar ku… Ba zan shiga hakkin ki ba. Zan samu Zayn ya sawwake miki a yau ba sai an ja da nisa ba. Kinji Waheedah? Kiyi hakuri bazan takura ki ba wallahi. Wannan auren ba zai ruguza zumuncin mu da ke ba. Zaa warware shi da yardar Allah…. Bar kuka.”

Haj Hameedah ta karasa fada muryarta na rawa. Yayin da itama hawayen ke tsiyaya a fuskar ta.

Gwaggo haule da Umma Hadiza suka shiga basu hakuri duka. Haj Hameedah ta zame jikin ta daga na waheedah ahankali ta mike. Soro ta nufa ta kira Zayn a waya. Ta sheda masa dukkanin yadda sukayi da Waheedah. Don shi ma sai a satin daurin auren ake sanar masa da na su zaa hada. Ya yita FARIN CIKI yana azumin godia ga Allah na gwarzon sa’ar samun mallakar Waheedan .

Maa ta tilasta masa da lallai yazo wajen waheedan ya sawwake mata tunda dai ta tsaya akan bakan ta. Idan kuma ta amince to yasanar da ita yadda suka tsayar da matsaya.

Ko da Haj Hameedah ta fita daga dakin. Gwaggo haule ta shiga tausasar Waheedah. Amman sam waheedan ta ki bada kai sai ma ambaliyar hawaye da ta ke ta zubarwa. Fuskar Ahlam kawai take hangowa .. Gefe daya kuma ta Zayn da ko a baya ranar bikin sa yake sanarwa Dawood kan meze yi da Waheedah yar ficika da ba budurwa ba ce bata isa aure ba. Kuma a yanzu shi aka bata a matsayin miji? Ta girgiza kai kawai tana cije lebe tare da sake kyakkyabewa da wani sabon kukan.

Nadra ta shiga dakin. Su gwaggo haule suka basu waje. Nadran ta shiga bawa waheedan shawarwari duk kuwa da ba sauraron ta take ba kuka take mai fitar da sauti ahankali. Duk da haka Nadra bata fasa ba sai da ta karasa maganganun ta tukun sannan ta shiga tsokanar waheedan har tana mintsinin ta.

“Bakiga customized boxes dinki ba. Harda hashtag na #ItWasAlwaysYou:W💕? Ni dai daman na san dan kumbure kumburen da Akiey yakeyi idan ya ganki duk kauna ce. Ya yita saki aiki duk wayon ya kare miki kallo ne. Shi kadai yasan labarin da ke cikin zuciyar sa . Ashe dai Waheedah itace FATHATAL-QALBin Ya Zayn.. Sai yanzu na kara amincewa da hashtag dinnan na It was always you Waheedah… Kaunar ki a zuciyar sa ta dade tana tsumuwa ke din ce always and forever dinsa. Bai taba soyayya ba sai akan ki. Ashe yar mutan shurah ce ta sace zuciyar Yayan mu har ya kasa hakuri sai da ya mallaketa? Ina muku fatan alkhairi. our newest sister in-law… Aunty Waheedah…. Mrs Zayn Adams Nasser. U r highly welcome to the Adams family… Allahumma bareek ” Tana karasa fada ta sumbaci kan waheedan ta mike bayan ta mata sallama ta fice daga dakin

Tunda ta fara magana har ta karasa Waheedah bata kulata ba. Tana dai sauraron duk wata kalma data ambata.

Tana jiyo sanda suka karasa wasa da dariyar su. Kafin daga bisani su tashi su tafi . Fannah da Basira suka bi su da kayan makulashen da suka tanadar musu. Da dan tukwicin da suka bayar a matsayin su na marasa shi.

Ko bayan sun musu rakiya sun dawo. Akan Waheedah suka taru suna bata baki. Banda Umma Hadiza da ta zauna agefe kawai tana canza channel din yar rediyon da ke hannun ta.

Da suka takura mata da magana kuka ta fashe da shi. Daga karshe ma ta bi su fannah da Basira gidan su wajen Deluwa dubo yaran kamar yadda Gwaggo haule tace. Suna zuwa kuwa Waheedah adan guntun ilimin ta take sanar da su Basira ko ciwon idanun jaririyar dayar anophthalmia/microphthalmia ne?

Daga baya kuma su Gwaggon suka kai kayan lefen gidan wajen Marka. Inna Sa’adatu na asibiti bata farfado ba Ya yin da zainabu ke gadon asibiti itama batasan wanda ke kanta ba. Marka kuwa tamkar sabuwar tabi. Don kayan lefen da aka kawo mata tagani ma zugii su ka karawa zuciyar ta. Ta shiga kokawa tana bubbuga kirji. Sai hararar kayan take.

Ya yin da makota na kusa da na nesa suka debo kafafuwa don ganewa idanun su akwatunan shake da lefen Waheedah. Kaf ko a tarihi babu wanda aka taba kawowa kaya himili guda irin Waheedah. Lalle duk mai hakuri zai ci riba watan watarana.

Saboda tsabar bakin mutane. Kit da gwalagwalen ke ciki Najan Isubu kasa fitowa tayi da su. Kar abi dare a sace su tas. Ko bakuna su tsige auren . Masoya sun sanya albarka da fatan zaman lapia tsakanin Waheedah da mijin nata.

Sam marka batasan dan masu kudi Waheedah zata aura ba. Da bata amince da auren su ba. Ta hararo lefen da wutsiyar idanun ta . Hade da saka yatsanta a baka ta gartsana shi cikin tsantsar hassada da bakin ciki. Kasa jurewa tayi ta koma cikin dakin ta.

Ko da yan kallon kayan suka kammala gani. Aka mayar da su gidan gwaggo haule. Kafin washegari a mayar da su gidan na The Adams Family don gudun barayin dare masu bin lefunan mutane su sace su.

*******

Kallon kansa ya tsaya yi a gaban mirror. Yana sanye cikin dakakkiyar wagambari da ta sha aikin hannu. Da hular data dace da aikin kayan . Sai hula data sha kari ta zanna bukar. Agogon sa ya hau da kayan jikin sa. Hakama takalman da ke sanye cikin kafafun sa.

Ya yi matukar kyau. Ya dakko turaruka ya shiga feshe dukkanin lungu da sako na jikin sa. Ya goga chappete a bakin sa. Ya gyara zaman zobunan azurfar da ke yatsan sa.

Sannan ya dau wayar sa ya zura a aljihun gaban rigar sa ya fuce daga dakin nasa cikin takun kasaita irin ta angwaye. Dake tattare da farin ciki da annushuwa.

Kamshi ne kawai ke tashi daga jikin sa. Ga wani kyawu daya kara haskaka shi. Yana sauka daga mattakalar bene ya na mai bare ledar chewing gum din hannun sa. Me mint flavour ya jefe a baka yana taunawa ahankali.

Ahlam na zaune a doguwar kujera da wayarta a hannu. Ta dube shi ta watsar. Tun da Ummimi ta zo da kanta gidan ta sanar mata rana i ta yau daurin auren Zayn.. Amman bata gaya mata wadda zai aura ba. Ta ja mata kunne sosai tare da mata nasiha akan zamantakewar aure da hakkokin sa…..

Da harara tabi shi. Yayi murmushin gefen fuska kawai. Ya zauna akan hannun kujera yana kare mata kallo. Ya kasa gane muhimmancin da ta bawa zama da kayan bacci. Ta kwanta ta tashi da su. Da rana ma tayi wanka ta mayar da su.

Ya dan lekar da fuskar sa ga wayar da ke hannun ta hausa novel take karantawa na: zafafa biyar

“Meye zafafa biyar kuma?”

“Ina ruwan ka? Littattafan hausa ne mana..”

“Amma…I’m very sure. Inde littattafan hausa ne suna muku koyi ta yadda zaku dinga kula da tarairayar mazajen ku. Kula da tsaftar jikin ku.. da sauran su. Su kan su ba zasu baku gurbatacciyar shawara ta fatali da ayyukan gidajen auren ku ba .”

Bata bashi amsa ba ta juyar da kanta gefe tana turo baki gaba. Gyara zaman sa yayi ya shiga yi mata nasiha mai ratsa jiki tare da bata hakuri akan dukkanin wasu lefukan da yayi mata a bisa rashin sani. Da kuma wanda yayi da sanin, Ya kuma karkare da batun,

“Game da wacce na auro kuma…. Bata da masaniyar neman auren ta ma ballanta na batun daurin auren mu da ita. Kuma ko da aka sanar mata tanacan tace dole awarware auren nan… Badan komai ba saboda tamkar cin amana ne awajen ki. Duk kuwa da bata kauna ta. Tana mai jin kunyar kasancewar abokiyar zaman ki .. Ahlam!! Wannan ba kowa bace fyace…”

Ahlam ta daga kai da sauri ta dube shi. Gabanta na tsananta bugawa.

Zayn ya kada kai alamun tabbatarwa da zancen sa kafin ya ce,

“Waheedah itace wadda na aura ba tare da masaniyar neman auren ta da nayi ba. Ballanta na kuma daurin auren mu da aka daura yau ..”

Kasa magana Ahlam tayi. Idanuwan ta suka shiga kiftawa. Hawaye sirara suka shiga reto a kyakkyawar fuskar ta. Ta mike da sauri tayi sama tana mai fashewa da wani sabon kuka..

Ya dan jima yana sake sake a zuciyar sa. Ya bita saman yana ta roko ta bude dakin taki. Ya sauka fice daga gidan. Kai tsaye ya nufi gidan Gwaggo haule.

*WAHEEDAH….*

Suna tsakar gidah baki dayan su. Ciki harda Waheedah data rufe kafarta saboda soro. Tana mai karanta sakon da ya shigo wayar ta ta lambar Dawood,

“Nikah Mubarak my wife, You are a missing ingredient of my life that has everything..D has now been completed. For me it’s not just about showering you respect, you are and always will be my respect, My queen and I honour and respect your family at all times .May Allah give me ability, power and strength to make you happy, for the rest of your life… I love soo much… With every fiber of my being darling…💕” Tana karasa karanta sakon,

Zayn yayi sallama. Sai da aka bashi iso ya shiga. Ya gayshe da su cikin girmamawa. Waheedah ta gayshe shi fuskar ta a kumbure.

Ya karaci zaman sa. Suna hira da gwaggo da yake jefa kalamai daya biyu. Ya musu sallama yana sosa keya ya fuce. Gwaggo tasa Waheedah ta raka shi.

Har waje ta raka shi. Yana gaba tana biye masa a baya. Sun danyi tazarar har zuwa wajen motar sa. Dake ba mutane awajen layin shiru. Hakan ya sanya Zayn rarumo Waheedah tanata ture shi amman yaki sakinta. Ya rungume ta tsam a faffadan kirjin sa. Yana sinsinar wuyan ta dake tashin kamshin da kofofin hancin sa basa mantawa.

“Please Waheedah .. Kyale ni naji dumin jikin ki . Ko kinsan wata rana da muka fara haduwa da ke? A gate din gidan mu. Wanda muka bigi juna har glasses dinki suka cire?” Yana mai goga karan hancin sa akan nata karan hancin ya cigaba da cewa,

“Tun ranar na tsinci kai na da kaunar ki. Kamshin turaren ki. Idanun ki, kyawun ki, nutsuwar ki, kyakkyawar halayyar ki da ma sauran dimbin ladubban ki suka kara ingiza zuciyata da kaunar ki .. Waheedah ke ce FARHATAL QALB na..I remember every second, Your magnificent smell, Your incredible eyes, I remember everything… You are my best present and future Waheedah.. Tun kallon farko ..I always liked you at first glance… Ki sake bamu dama Waheedah. Karki bari a raba auren mu..If only you could give us one more chance”

Kiciniyar kwace kanta take son yi. Zayn yayi nasarar saka bakin sa ya sumbaci gefen wuyan ta. Ta rufe idanunta da sauri jikin ta na ta rawa. Ya busa mata iskar bakin sa a kunnen ta ahankali cikin wata iriyar murya ya shiga rada mata,

“If only you could give us one more chance…. ” Yana karasa fada ya samu kansa da saka hannu ya tallabo fuskar ta,

Ya sanya labban sa akan nata. Cikin wani irin yanayi ya shiga sumbatar Waheedah. A hankali kuma cikin nutsuwa,

“What did you hear…..uhm… Me kika ji, ?”

Ta sauke numfashi tana kauda fuska. Ashe dan iska ne? Saboda ya kyaleta tace,

“Naji….”

“No… in english please …”

“I hear voices of children ….” Ta amsa shi hade da juyawa kadan ta kalli yaran da ke gara taya a tsallaken kwata suna musu …

“And then….?”

“Kukan dabbobi da tururin numfashin…..

“In English …. Kinji?” Ya karasa fada yana sinsinar bayan kunnenta..

“Crying of animals…And the hint of your breath….”

Rarumota yayi ya rungumeta tsam a jikin sa.

“Ina kaunar ki Waheedah.. I’m in love with you..I love you more than anyone, Fiye da kowa da komai… Meyasa kike son a raba auren mu? Meyasa kike tsane ni haka?…”

“Ka bari … Ya Ahlam…” Ta shiga zame jikin ta. Tunowa da Ahlam da tayi,

“U’re worried about Ahlam… Yeah I knw..But what about us?what about my love for you? Kinsan irin kaunar da na ke miki Waheedah? Bansan so ba sai akan ki. Bansan tacacciyar kauna ba sai da na fara dakon soyayyar ki Waheedah.. ” Yana magana yana sake matseta a jikin sa.

Ganin zai iya nasara akanta. Hakan ya sa da sauri ta yage jikin ta daga nasa ta shige gidah. Sun bar tsakar gidan suna dakin gwaggo haule. Don haka fitsari tayi kawai da alwala ta kwanta tana tunano Zayn da ajiye kunyar da yayi a gefe yau. Ta dora hannunta daya akan lebenta tana zagaye su. A haka bacci ya kwashe ta…

×××××

Wasa wasa sai da Waheedah ta kara kwana biyar agidan su kafin Haj Hameedah ta turo a dauketa da kayanta.

Daki wadatacce aka bata asaman gidan na Haj Hameedah kafin komai ya sake sararawa Waheedah ta koma gidan Zayn.

Duk sanda zai zo wasan buya suke. Bata bari su hadu. Ranar daya gaji ya kirata a waya taki dagawa.

Ya tura mata sako da,

“I’m in the car…”

Ta karanta tayi shiru. Ya sake tura mata da,

“Come down! I won’t accept no.or I will alert the whole neighborhood ..”

Tana karasa karantawa ta kashe wayar baki daya. Zayn ya shiga gidan kan sa tsaye. Yayi hamdala Maa bata nan tana sashen Abiey din su. Da sauri ya haye saman dakin da Waheedah take ya tura kofar ya shiga ya murza mata mukulli. Nufar ta yayi gadan gadan ta gudu bayan kofa ta tokare tana rau rau da idanu, Yayi murmushin gefen fuska kafin yace,

“Waheedah you made a
big impression on me ..”

“Ya a Zayn…, Dan Allah ka bari..”

Girgiza kai yayi. Tana baya baya yana kara matsawa kusa da ita. Ta rakube a karshen kofar tamkar zata shige cikinta baki daya. Tana mai rufe bakinta da tafukan hannayenta. Cikin rawar baki ta shiga cewa,

“Sis Ahlam……”

“Shhhhhh!!! I love you more than anyone….. Enta FARHATAL -QALB.…. yes Waheedah ke ce FARIN CIKIN ZUCIYA tahhh..#ItWasAlwaysYouW💕…” Yana karasa fada ya saka hannun sa yana sharce mata hawayen da ke tsiyaya a fuskar ta…

Kafin ya samu kansa da tallabo bakin nata. Ya shiga bata deep and passionate sumba mai ratsa mugudanar jini da bargo..

Yayi nasarar kashe mata lakar jikin ta. Daga shi har ita sun shagala sai bugun kofa suka ji.

“Waheedah kinyi bacci ne?” Suka jiyo muryar Maa.

Waheedah ta tattake iya karfin ta ta ja hannun Zayn ta tura shi abandaki. Ta rufe bandakin da mukulli gabanta na tsananta bugawa. Kunya duk ta dubibiyeta tamkar Maa din na ganin su.

Ta kalli kanta a mudubi gaba daya ko ina a hautsine. Ta juya ta dankarawa kofar bandakin harara sai kace Zayn din yana gani.

Tayi sauri ta gyara ko’ina sannan ta bude kofar. Maa ta shigo tayi hanyar bandakin tana,

“Ashe shower ta lalace sai Nadra ke fada. Haka kiketa wanka da sanyin nan Waheedah? Bari na dau hotan wajen na turawa me gyara sai ya sayo abunda babu…”

Tamkar mota haka Waheedah taja kafafuwa a guje sai gata agaban Maa.

“Ki..ki..ki barshi Maa.”

Maa din ta kalleta tayi murmushi,

“Haba Waheedah? Dan Allah ki cire wannan kunyar ai an riga da an zama daya..”

Waheedah ta shiga girgiza kai. Tamkar zata fashe da kuka. Yayin da Zayn dake ciki yanata murmushi da adduar Allah yasa Maa ta bude ta ganshi ta bashi matar sa. 🤣

“Akwai … Shan…” Ta kasa karasawa tanata rawar murya.

Maa ta yi murmushi kafin cikin kulawa tace,

“Okay ko kin wanke undies ne bakyaso agani? Well kina da gaskia. Ba damuwa zuwa da safe sai ya zo kawai ya gyara. Idan zaki wankan to dan Allah ki fada a kawo miki ruwan zafi ko ki shiga bandakin Nadra . Kinji?”

“Insha Allah Maa. Nagode kwarai.”

“Yauwa… Sai da safe.”

Tana fita Waheedah ta sauke zuciya. Hannunta akan kirjinta. Yau da Maa ta yi ido biyu da Zayn batasan wacce iriyar kalar kunya ce zata shiga tsakanin su da Maa din ba….

#DESTINED LOVE… #ZAYNUL-WAHEEDAH..
#ITWASALWAYSYOU:W💕

_WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA…_
[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

 

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply