Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 14


Gurbin Ido 14
Viral

14

Sanda aka gama musabaqar suna tsaye a jikin motar dr marwan(abbi) suna jiransa yayi kiransu,ya hadasu da mahaifin shaheeda da ita kanta shahidar suka gaisa,irin dadin da shaheeda taji ba qarami bane ganin cewa akwai sanayya tsakanin mahaifinta da nashi,ko meye zai dan zo mata da sauqi,ba kamar ace babu komai tsakaninsu ba,kwata kwata bata nuna wannan farincikin a fili ba saboda kamun kai da kuma tsira da mutunci.

Babu jimawa shaheeda ta ziyarci gidan dr marwan,nan da nan ta saba da mafi yawa na jama’ar gidan,tayi amfani da hikima da kuma hankalinta da wayo ta shiga jikin anni da amma mahaifiyar ja’afar sosai,a lokacin jaafar tuni sun koma hutunsu,bata damu ba tasan tana da target a kansa komai dadewa,baka isa kace son ja’afar take ba,don ko zancansa bata taba yi ba bare ka kawo hakan cikin ranka,saidai a hikimace ta gama karantar dabi’unsa daga hirarsa dake bakin ‘yan uwansa,da kuma yawan ambatonsa da anni takeyi,ta gama gane abinda yakeso da wanda bayaso,ta haddacesu tsaf bisa kanta.

Sanda suka dawo hutu sun samu shaheeda a gidan,don tuni ta maida gidan wajen zuwanta,sun kuma saba sosai ta zama kamar ‘yar gida,da yawa suna cewa saboda gidansu duka maza ne shi yasa tafison gidan baba dr kamar yadda take kiransa,don nata ‘yan uwan duka maza ne,ita daya ce mace.

Eh tabbas,zamanta a gidan na mata dadi,saboda tana da abokan hira sosai ba kamar gidansu ba,saidai nata plan din ja’afar ne,boyayyen sirrinta da babu wanda ya sani,tayi qoqari matuqa wajen ganin ta janyo hankalinsa kanta cikin hikima da basira,ba tare da shi kansa ta bari ya fahimci komai ba,komai na ja’afar din dabanne,ita ke kula da wasu abubuwa nasa.

Da farko bai farga ba,saboda sam hankalinsa bashi a wajen,mma daga bisani ya soma fahimtarta,ya kira qanwarsa nadiya,ita yake nema idan yana buqatar wani abu da anni ko su amma basu iya ba ko ba zasu iya ba,wadda tasu tafi zuwa daya saboda kamanceceniyar da kuma nutsuwarta,ya yanka mata warning akan ta cire shaheeda akan duka sabgarsa sai idan shine ya buqata.

Farko nadiya ta kasa gayawa shaheeda,sai ita da kanta ta fahimta,ta kuma yiwa nadiya maganar,bata boye mata ba ta gaya mata,tun daga ranar shaheeda ta fita a sabgarsa gaba daya,duk wani abu da ya shafeshi ta fita a ciki,koda zaune take a wajen yazo zata tattara tabar wajen,hakanan abu idan ya dangaceshi komai yadda ta iya babu ita a ciki,abun yana cinta a rai,tana jin ciwo amma ta danne zuciyar tata,mutum ce mai yawan addu’a,maimakon damuwa ta rinjayeta,saita rinjayar da addu’a,takan hana idanunta barci ta tashi cikin dare ta gayawa Allah damuwarta.

Sannu a hankali shima ya fara noticing canzawarta,sai ya fara jin damuwa a kanta cikin zuciyarsa,shi da kansa ya dinga mamakin kansa,damuwa for what?,akan wata mace?,sannu sannu Allah ya fara matsa zuciyarsa,sai ga ja’afar da kansa ya fara nema shaheeda tayi masa wasu abubuwan,kamar kalolin girke girken da take masa a baya,amma fur sai ta murje idonta taqiyi,duk da yadda zuciyarta kan buga,taji babu dadi amma haka take mazewa.

Rana ta uku daya aika tace ace bata da lpy taqiyi zuciya tazo masa iya wuya,yana zaune a sannan yana duba saqonnin da yake samu daga companies na jiragen sama dakeson yin aiki tare dashi,zare laptop din yayi daga saman qafarsa ya ajjiyeta gefe ya miqe ya fice.

A dakinsu nadeeya ya samesu zaune an kafa majalisar hira,tana ta dariya tana dariya harda riqe ciki,Har kowa yayi shuru bata ankara ba,sai da taga hankalin kowa ya karkata ga qofa,sun kuma saka nutsuwa a jikinsu sannan ta ankara,tayi hanzarin jawo dankwalinta ta rufe lallausar sumarta ta fulani,gabanta na wani irin faduwa saboda zallar kwarjinin da yayi mata,tana jin kamar zaman ma ba zata iya ba.

Bata ji yace musu komai ba amma sai taga kowace ta fara miqewa tana fita a dakin,ganin sunata ficewa ba tare da tasan dalili ba sai itama ta miqe tayi joining dinsu.

Nadeeya ce qarshe sai ita,nadiya na fita ya matsa yayi blocking qofar gaba daya da jikinsa yana kallonta da idanunsa da suke fasa mata zuciya,tayi baya kadan ta kuma sauke kanta qas,don ba zata iya jurewa kallonsa ba,ta fara lanqwasa yatsunta,tana son tace ya matsa mata itama ta fita amma kuma tasan cewa tayi kadan ta iya fadin hakan.

“Baki da kunya ko?” Ya fada a taqaice kamar me ciwon baki,abinda yasa babu shiri ta daga kanta ta kalleshi,sai kuma ta sake saukarwa saboda idonsa yana kanta

“Ni sa’anki ne da zan dinga aikowa kiyimin abu kina rejecting,bakisan ba kowa nake sawa yayi mun abu ba?” Sosai maganar tasa tayi mata dadi,wani abu ya tsarga mata,gefe daya kuma rauni ya kama zuciyarta har ya sanya qwalla silalowa daga idanun nata tare da kalmar

“Kayi haquri” shuru na sakanni yayi kafin ya sauke hannayensa ya juya ya fara ficewa daga dakin,sai ta bishi da kallo har yabar wajen.

Kwata kwata ji tayi bataji dadi ba,cikin ranta kuma tana tsoron kada fa ta barar da damarta,a sukwane tayi kitchen ta fara hada masa abinda ya buqata a daxun,tana tsaka da aikin su safina suka shigo

“Me yayi miki?,me ya faru?” Tambayar da suka dinga mata kenan

“Ba abinda yayimin” ta amsa musu hankalinta na ga girkinta

“To wannan abincin fa?,naga bamu jima da gama cin abinci ba” safina ta fada tana bude tukunyar

“Na yaa ja’afar ne” amsar daya sanyasu kallon kallo a junansu,suka fara kuma tsegumin anya kuwa?,bata bi ta kansu ba,itadai burinta ta gama ta kai masa.

Sanda khadim yakai masa dawowa dashi akayi,yace bayaso,abinda yasa hankalinta ya tashi sosai,ta kuma boye ta dinga kuka,washegari ta hada kayanta tace zataje,duk da kwanakin da takeyi basu cika ba.

Kwana biyu rak a tsakani ya karanci bata gidan,yayi kaman ya share amma sai yaji ya kasa,ya kira nadeeya ta tambayeta,bata boye masa ba ta gaya masa duk abinda ta sani,ya sallameta,sannan yayi shuru shi daya yana tunani,rashin cin abinda ta aiko masa ne ya kawo faruwar hakan?,washegari sai ya tsinci kansa da shiryawa ya tafi gidan daukota,babu ko rakiyar jabir.

Suman zaune tayi sanda akace mata ja’afar ne na gidan baaba dr,bai shigo ba ya dai aiko da gaisuwa wajen ummanta,sannan yace a gaya mata ta fito su tafi,saqon da ya bata mamaki,haka ta shirya kayanta ta biyoshi.

Cikin motar kamar bashi ba,har ta fara cire hope,saboda ko uffan bata hadasu ba,sai da suka kusa gida sannan ya magantu

“Idan kika sake wannan kuskurem sai na hukuntaki” ta fahimci da qaramar magana yake isar da saqo me yawa,maganarsa guda daya idan ka fassarata taka dauki.ma’anoni.masu yawa

“Kayi haquri” tace dashi,yaji dadi cikin ransa na yadda take da sauqin kai,saidai ko ka fuskarsa haka bai nuna ba.

Wasa wasa sai shaheeda ta karbe komai nasa cikin gidan,nan da nan kowa ya fara daukan haske,duk da cewa shi gogan yana jin dadin hidimarta sosai saboda ya yadda da tsaftar ta da qwarewarta wajen girki,sannan yana jinta a ransa wanda yafi ta’allaqa hakan da sabo,amma babu wata maganar soyayya data taba gittawa tsakaninsu.

Tsarin gidansu shaheeda daga candy mahaifinta bashi da ra’ayi barin diyarsa mace ta qara gaba,sai kuma gashi guda daya ce macen da Allah ya bashi,a lokacin shaheeda tayi candy,mahaifinta ya tasamma aurar da ita,dr marwan na samun labari ya nemawa ja’afar bisa shawarar anni,saboda qoqarin da taga shaheeda nayi a kansa,da kuma yadda ta karabceshi tsaf,tamkar ita ta haifeshi.

Kowa yayi tunanin za’a samu matsala sanda ja’afar yaji an nema masa auren shaheeda,sai gashi bai wani damu ba,hasalima kusancin dake tsakaninsu ne ya sake daduwa,hakanan itama ta sake qara qaimi wajen kula dashi,abinda yake matuqar yi masa dadi a rai,duk da dan uban miskilancinsa.

Wata iriyar zazzafar soyayya yake mata silently,mutum ne shi da bai iya so ko qi ba,shi daya yasan girma da kimarta cikin ransa,ta kula da komai nasa,dai dai da lokacin sallah ta dauki wayarsa ta saita masa,hakanan duk sanda ta tashi sallar dare dai tasan yadda tayi ta tasheshi,ko.ta tura masa tex ko tayi masa flash call,duk sanda tayin kuwa sai ya gani,kasancewarsa mutum da baya bacci da wuri,ita ta koya masa sallar dare,ta kuma koya masa abubuwa da yawa wadanda daa basa cikin habit dinsa,ta samu gurabe sosai cikin rayuwarsa,wanda hakan ya qara soyayyarta da qaunarta cikin ransa ba tare da ya ankara ba.

Sanda sukayi aure da shaheeda lokacin ya zaba kamfanin da zaiyi aiki,saidai ba anan nigeria yake ba,anni ta dinga fada,akanme zai zaba kamfani a wata qasar bayan yanzun yana da iyali,Allah sarki shaheeda ba haka taso ba,amma ita ta haqiqancw kan cewa babu komai,saboda fa fahimci burinsa kenan,yana matuqar qaunar piloting,tana bala’in girmama buqatarsa da burinsa saman nata,tayi kwance kwance ta dinga bawa anni haquri gami da kareshi.

Suna kan hanyarsu ta komawa sashensu ya kama hannunta ya saka cikin nasa

“Me yasa kike bani kariya?,bayan kema nasan ba haka kikeso ba?”
Murmushi tayi sannan ta dora kanta a jikin kafadarsa

“Bani da wani zabi bayan naka,bani da wani abu da zanso sama da abinda kai kake sonshi,bazan taba son wani abu sama da wanda ka zaba ba,dukka zabina dama rayuwata ta narke cikin taka,taka ce” wani abu ne ya dunga tsarga masa,baisan wanne irin so shaheeda ke masa haka ba,kasa magana yayi,sai kawai yasa hannu ya dauketa cak yaci gaba da takawa da ita zuwa sashensu,abinda tafiso daga wajensa kenan fiye da komai,tayi luf a qirjinsa tana murmushi tare da shaqar daddadan qamshin da bata taba jin makamancinsa ako ina ba sai a wajensa.

Mutum ne tsayayye dan gaske,wanda komai zaiyi baya daukarsa da wasa matuqar ya sa kansa,don haka sanda ya fara aikinsa ya bashi muhimmanci qwarai da gaske,abinda ya jawowa shaheeda samun qarancin kulawa,tana jin babu dadi amma ta danne,taci gaba da haquri dashi da kuma dukka abinda zai taso,a yawancin lokuta shi da kansa yasan tana buqatar kulawarsa,amma babu lokaci,hakan ya sanya shima yaqi dauketa daga cikin gidan nasu,saboda zamanta tare dasu anni xai rage mata kewa da zaman kadaici.

A haka shaheeda ta samu cikin twins,a lokacin laulayinta tasamu zama dashi sosai saboda hutun qarshen shekara daya fara yi,ya kuma dan dade.

Wata takwas da sati biyu ta haifa masa kyawawan ‘yan biyu dukkaninsu mata,ikon Allah dayar shi tayo,dayar kuma babanta sakkk,ya kashe kudi bakin iyawarsa,ya kuma gatanta,ta samu gift masu yawa daga gareshi.

Yaran yarane masu shiga rai kamar mahaifinsu,hatta da baban nasu wata iriyar soyayya yake musu ta musamman,a haka yara suka fara wayo,ya kuma koma bakin aikinsa.

Sannu a hankali yara suka fara girma,sunata wayo abinsu,har zuwa sanda sukayi shekara biyu,ya dauki hutu yazo dai dai randa su nadeeya suka hada musu birthday,akayi komai dashi,ya kuma cikasu da gifts ya koma aikinsa.

Kamar dai baya haka ya koma aikinsa ka’in da na’in,a wannan karon shaheeda kanyi qorafi lokaci xuwa lokaci

“Muna buqatarka,muna buqatar kulawarka,ba don ni ba ko don yaran nan” shi a kansa yasan da haka,don haka ya fara tsara musu yadda zasu xama kusa dashi ba tare da ya gaya mata ba,shi kansa yana kewarsu sosai.

*_MUTUWA rigar kowa_*

Tunda watan ya kama take masa complain din tana yawan jin ciwon kai,murmushi yakeyi yana tsokanarta,saboda yasan wani lokaci idan tana buqatarsa ko buqatar ganinsa da hakan take fakewa,har sai yabar dukka abinda yakeyi yazo ya gansu.

Wannan karon sai yake basarwa,saboda so yake zuwa qarshen watan yayi musu suprise ya debosu suzo suyi hutu tare dashi.

Sati kusan uku suna a haka,ranar wata alhamis……….

A ranar akwai jirgin da zai tuqa,awa daya saura su tashi sai ga kiran shahidan,tana shaida masa gata a qasar,da fari ya dauka wasa take masa,don last week sunyi hirar taji duka schedules dinsa na satin,amma daya duba number ya tabbatar ta qasar ce sai ya yarda da hakan,mamaki ya cikashi,da alama ta gaji da kewarsa ne ta biyoshi kenan,waya ya dauka yayi musu booking masauki sannan ya kirata yace su biyo cave ta kawosu nan,a marairaice tace

“Yanxu ko sau daya?,ko sau daya ba zaka iya qarasowa na ganka ba kafin ka wuce?” Agogon dake daure a hannunsa ya kalla,lokaci ya qurace sosai,bashi da zabi illa ya bata haquri,cikin karyayyar murya ta amsa masa da

“Shikenan……ga amna” murmushi ne ya wadata a fuskarsa,ya karba wayar sukayi magana sosai da yarinyar,don bakinsu dukka ya bude,abinda ya jawo ma kenan wayar ta katse sanda ‘yar uwarta amra ke shirin karba,yaso suyi magana da ita,don tunda suka fara waya da amnah take cewa ta bata daddy,zata bashi wani labari.

A sannan lokacin fara aiki yayi,ya kalli wayar yanason kira a bashi yarinyar amma ba hali,sai ya yanke bari suje sukai passengers,lallai a ranar zai dawo in sha Allah,cikin ransa ya dinga jin excitement na haduwarsu,ashe samun nasu da bazaiyi ba kenan saidai ya taras da gawar matarsa da kuma gawar diyarsa guda daya amra.

Lamarin yayi matuqar bugarsa da kuma gigitar dashi,don saura kadan ya zauce a sannan,bai taba kawo irin hakan a ransa ba,tun daga wannan lokacin komai ya tabarbare masa,ya tashi daga ja’afar akko ya koma wani mutum na daban,musamman lokacin da yaci karo da diary na shaheeda cikin kayanta,yadda take kewarsa da yawa da tarin qaunar da take masa, movement na yaransa a lokacin da baya kusa dasu.

Sosai depression ya sameshi,ya tattara komai nasa ya ajjiye,ciki harda aikin nasa da yake matuqar so,yace shine sila na faruwar komai,dukka qoqari anyishi kan jaafar don ya koma dai dai,amma inaa abubuwan sai a hankali,sai da aka tsaya da addu’a da roqon Allah sannan aka fara samun sauqi,amma sam ya canza totally,hakanan duk sanda abun ya motsa masa birkicewa yake gaba daya.

Sosai jabir ya taka rawar gani,saboda tsayawa da yayi akan jaafar din,da qyar aka sha kansa ya koma kan harkokinsa,amma piloting dai ya ajjiyeshi,ya zama wani mutum me zafin rai,miskilancinsa ya sake daduwa qwarai da gaske,babu abinda yake burgeshi a rayuwa,ya sake zama wani very careless akan sha’anin kowa,yafi ganewa kadaici,wanda kadaicin kuma illa ne tattare dashi,saboda shike tuna masa da shaheeda.

Wata irin soyayya yakewa diyarsa guda daya data rage wato amnah,wani irin gata yake mata,soyayyar mahaifiyarta da ‘yar uwarta duka sun dawo kanta,amma fir yaqi zaman nigeria duk da babban kamfaninsa anan yake kano gombe da lagos,dole don kada su matsa masa suka barshi,suke ci gaba da binsa da addu’a da kuma fatan Allah ya kawo qarshen komai.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram:

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply