Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 21


Gurbin Ido 21
Viral

21

“Kai…..kai,meye hakan?” Anni ta dakatar dasu cikin tsawa,ganin zasu fara sa’insa a tsakaninsu

“Ya zaizo ya samemu zaune,sannan kawai yace sai ta tashi ta shiga daki anni?,wannan wanne irin raini ne?” Khalid ya fada cikin jin ciwon abinda hisham yayi masa,yana jin ya disgashi abinda ba’a taba yi masa ba

“Anni,dawowarta kenan daga makaranta,da alama ko ke bakisan ta dawo ba,don nace ta shiga ta ajjiye qur’aninta sai ya zama laifi?” Shuru ne ya biyo baya,anni tana nazartar kowannensu cikin sakannin da basu wuce biyar ba,sai taji hankalinta ya dan tashi,zata iya cewa bata taba ganin irin wannan sabanin ba a tsakanin jikokinta,wannan shine karon farko da hakan fa faru,duk da tasan dama tsakanin khalid da hisham ba jituwa bace can can,amma kuma basa cecekuce,tabbas ya kamata ta yuwa tufkar hanci da wurwuri

“Wuce ciki maimunatu” anni ta bawa maimunatu dake daskare a wajen umarni,da hanzarinta kuwa qafafunta na rawa tayi ciki,kamar ta tashi sama haka takeji,har ta samu ta isa ga dakinta,ta tura qofar ta shige,ta zame a hankali a qasa ta zauna qafafunta suna rawa saboda tsabar tsoro,me ya kaisu fada a kanta?,shin wai basu duba kamanninsu da darajarsu ba da zasu tsaya suna fada a kanta?,kamar ita maimunatu?,wadda bata da komai?,bata kuma mallaki komai ba?,me yasa?,abinda ta dinga tambayar kanta kenan cikin mamaki da kuma tsoron abinda ya farun yanzu.

“Ku zauna” anni ta fada musu itama tana lalubar wajen zaman

“Ka zauna mana nace!” Anni ta fadawa khalid tsaye cikin matuqar bacin rai a tsawace.

Sun kusa minti biyu shuru kowanne anni tana karantar fuskarsa,kafin daga bisani ta kirayi sunan kowa a cikinsu

“Me idanuna suke gani?” Ta jefa musu tambayar da ba wanda ya shirya amsa mata,sai cin d’aci da kowannensu yakeyi

“Tun ina raye hakan zata fara faruwa ina ga ace qasa ta lullube idanuna?……to in sha Allahu wannan abun ba dai cikin ahalina da zuria’ta ba,haihata haihata,bazan lamunta ba kuji da kyau,na meye zaku dinga sa’insa akan maimunatu?,to dukkaninku ku dauketa a matsayin qanwarku,banason kowa ya sanya wani abu a ransa bayan wannan…….kuma inaso a yanzu yanzu ku baiwa junanku haquri”

“In sha Allah” kowa ya fada a cikinsu saidai murya ciki ciki,hisham ne ya fara bawa khalid din haquri,tunda ya girme masa da watanni kusan shida,shima khalid din ya maida masa,sannan khalid din ya miqe hannayensa zube a aljihunsa yana shaidawa anni zai tafi

“Aiba yanzu k saba tafiya ba,ko don na muku fada?” Kai ya girgiza yana duban agogonsa

“A’ah,dama da wuri naso na koma yau din,ina da abinda zanyi” tabe baki anni tayi

“Oho maka…..a sauka lafiya” qaramin murmushi ya sake ya juya yana ficewa daga falon,qasan ransa yana juya maganar anni da tace su dauketa matsayin qanwa kawai,shikam.dai Allah ya sani ya gani yana so,zai kuma yi duk iyakar bakin qoqarinsa,zai kuma fafata da kowa don ganin ya samu maimunatu,bawai ya haqura bane.

Sun fita sun bar anni ne da dogon nazari da tunani,tana tsoron kada abubuwa suzo su kwabe ba kamar yadda take shiryawa ba,tana hangen al’amura masu nauyi a idanun kowannensu tsakanin hisham din da khalid,wannan tunanin ya sanyata daga waya ta laluba number dr marwan,ta shaida masa idan ya shigo gida da wuri a yau tana son ganinsa,idan kuma bai shigo akan kari ba gobe da sassafe ya nemeta kafin ya fita ya amsa mata da to,saita maida akalar kiran nata zuwa number jabir.

“Me kuke har yanzu a qasar nan ne jabiru?” Ta tambayeshi kai tsaye ba tare data tsaya bi takan tambayarsa,sumarsa yaci gaba da tsanewa da towel

“For now dai ni na gama duk schedule din da nake nasu a turkey,matsalar tana ga mutuminki,sam bashi da sha’awa ko nufin tahowa” gyara zamanta anni tayi sosai

“Nan da yaushe kake ganin harshi xai iya dawowa gida?”

“Karshen watan nan nan da 2weeks kenan komai nasa zai kammala”

“To ka shaida mana,lalai dakai da shi din ina da buqatar dawowarku qasarku zuwa farkin sabon wata……kai kaga ma,hadani dashi a waya”

“Okay, hold on karki kashe” yayi maganar yana maqale da wayar,gami da ajjiye wandon hannunsa da yake da niyyar sanyawa ya fita a dakin.

Kofar dakinsa da sassanyar qamshin turarukansa suka kamashi ya tura,luf luf dakin yake,saidai bashi a nan,ya kalli a gogo,lokacin da yake shiga gym ne,tabbas yana can,don haka ya juya da ‘yar sassarfa yayi can.

Sanye yake da farin wando qal me ratsin green daga gefe da gefansa,iyakar wandon wasan gwiwarsa,hakan ya sanya sambala sambalan qafafunsa dake cike da gargasa suka bayyana,sai rigar kayan armless shirt,yana tsaye daga bakin window,hannunsa riqe da qaramin towel yana goge zufar jikinsa,idanunsa kuma na ga waje.

Duk da yaji sautin bude qofar amma bai juyo ba,haka ya sanya jabir din takowa ya iskeshi a wajen da yake tsayen

“Anni na magana” ya fadi masa a taqaice,kamar bazai motsa ba,sai kuma ya cilla towel din gefe yana juyowa duk da har yanzu idanuwansa naga wajen

“Duk randa mutanen can suka shiga gonata zasu gane shayi ruwa ne” ya fada fuskarsa na nuna alamu na bacin rai,wajen jabir yakai idanunsa,wasu ‘yan asalin turkey dinne,baisan me yasa mutanen suke da jin kansu da alfaharin su turkawa bane,ba yau ba sun saba wulaqanta baqar fata kamar yadda yanzun sukewa wasu,duk da laifinsu ne,yawanci suke zubar da kansu

“Kar ka fara,ka rufa mana asiri,a qasarsu kake fa?”

“And so what” ya fada cikin nuna halin ko inkula,kana ya miqa hannu ya zame wayar daga kunnen jabir ya maidata kunnensa,yana qara taku zuwa gaba gami da gaida anni.

Waje ya samu ya zauna bayan ya gama jin dukka bayananta,yatsunsa ya nutsa cikin lallausan gashin kansa,baisan me zai gayawa anni ta fahimta ba,kamar yadda ya rasa gane taqamaimen dalilinta na birkice masa,tare da bashi umarnin tahowa gida next month,bayan kuma shi bai shirya hakan ba,banda amna ma,baya tunanin xai koma nan kusa

“Zan duba,zanyi qoqarin zuwa” wannan itace amsar daya bata.

Sanda anni ta ajjiye wayar saita qwalawa tabawa kira

“Ina maimunatu ne?”

“Tana dakin karatu,kinsan lokacin karatunta ne yanzu,kin santa kuma da himma” murmushi anni tayi,ita kanta tasan yarinyar daban take cikin dukka yara data sani,ba sawa ba fitarwa ba,babu hayaniya hakanan babu hargowa,uwa uba bata dauki rayuwarta da zafi ba,har cikin ranta kullum kwanan duniya tana jin nutsuwa da kuma gamsuwar hadin da take shirin yi da yarinyar

“Kiramin ita tabawa,wannan maganar ce ta taso,inajin lokaci yayi da zata san da zaman maganar,saboda ta sama zuciyarta tun kafin qarasowarsa,bawai sai daga bisani taji maganar sama taka ba,uwa uba ina hango wutar rikici dakeson ruruwa,gwara na yima tufkar hanci” kai tabawa ta gyada

“Gaskiya ne wannan haj anni,ubangiji ya tabbatar mana da alkhairi,yasa komai yazo mana cikin nasara da sa’a,ya kuma sanya qarshen abun ne yazo” cikin jin dadin addu’o’in tabawa anni ta amsa

“Ameen,ameen ya hayyu ya qayyumu tabawa” daga haka tabawan ta juya ta fice.

Sosai yau din takejin dadin karatun,hakanan Allah ya sallada mata qaunar hadith,dalilin da yasa zaiyi wuya ayi musu qarin hadith bata haddace su ba,kamar yau din,saura guda biyu ta gama haddar qarin da akayi musu jiya juma’a tabawa ta turo qofar tare da sallama ta shigo.

Qaramin murmushi ya wanzu saman fuska da siraran labban maimunatun,ta rufe hadith din tana duban tabawa

“Yau ban shigo kitchen ba ko?,karatu ne ya tsaidani amma na kusa kammalawa” murmushi itama tabawan ta maida mata,maimunatu nada saurin shiga rai saboda sauqi da dadin mu’amalarta

“A’ah muna,bansan me yasa kike takura kanki ba wajen zuwa kitchen kullum”

“Bana takura baaba tabawa,inajin dadin zuwan sosai,na qaru da kalolin girke girken da bansan ana yinsu ba,ina kan qaruwa ma,hakan yana min dadi”

“Gaskiya ne” tabawa ta amsata tana murmushi,don ita shaida ce,tuquru maimunatun ke maida hankali tana koyar duk wani girki da tazo ta samu zasuyi,daga inda taga anyi sau daya a gabanta to tabbas ta haddaceshi kenan,idan ta maimaita irinsan kuwa zakayi mamakin yadda ya bada ma’ana,kamar wadda ta jima tanayi.

“Yanzun ma anni ce take kiranki”

“Tom,gani nan zuwa” tace da baba tabawan tana qoqarin ajjiye Hadith dinta a take,ta kuma miqe tabi bayan baba tabawa,suna dan zancan islamiyyarsu,har zuwa sanda suka isa qofar dakin annin

“Tana ciki,zan koma kitchen mu qarasa hada abinci,don yau anan Alhj Dr(haka tun da baba tabawa take kiran dr marwan) zaici abincin dare”

“Idan na fito zan sameki a can saimu qarasa in sha Allah” ta fada saboda gwada kyautatawarta akansu itama komai qanqantarsa

“To ba laifi” ta amsa mata tana komawa zuwa hanyar kitchen,ita kuma ta tura dakin anni ta shiga,bakinta dauke da sallama.

,kamar ko yaushe,cikin nuna matuqar kulawa ta amsa mata tana gyara zamanta

“Kinga miqon wancar jakar kafin ki zauna” anni tace da ita tana mata nuni da wata jaka dake gefan gadon,miqa matan tayi sannan ta zauna tana fuskantar annin.

Zuge jakar anni tayi,ta fiddo wani abu,sannan ta daga kai tana duban maimunatu tana sakin qaramin murmushi

“Yau hira zamuyi dake” murmushin nan nata dake nuni da nutsuwarta gami da kamun kai ta sakewa anni

“So nake naji samari nawa kika taba yi maimunatu,sannan a cikinsu wa kikafi so?,inaso kuma naji har yanzu kina sonsa?” Sosai maganar anni tayi mata nauyi fiye da zaton ita annin,taji kamar qasa fa tsage ta shige ciki,ta yaya zata fara irin wannan hirar da anni?,bayan ko dasu laila ba zata iya wannan maganar ba?.

“Uhmmm,ina jinki,ki bude baki ki gayan” sake daureta kunyar annin tayi,sai kawai ta hau kada kai a hankali,dan bata fuska tayi

“Kina nufin ba kowa?” Da sauri ta daga kai alamun eh,sai annin ta motsa tana ajewa maimunatu hoto a gabanta

“To ga jikana,zaki iya aurensa?” Kasa daga kanta tayi bare ta kalli hoton,tanajin kamar ta kulle idonta ta bude taga bata a gaban anni,kayan kunyar yayi yawa

“Da gaske nake miki maimunatu,zaki auri ja’afar?” Wannan karon sautin muryar annin ya fito da wani irin amo dake nuna babu wasa cikin maganganunta,abinda ya sanya maimunatu cira kai,a maimakon ta kalli hoton sai ta kalli anni,suna hada ido ta jinjina mata kai

“Inaso ki taimaki rayuwar ja’afar,ki aureshi,inajin qamshin alkhairi a tattare dake,bansan me yasa zuciyata take gayamin ke zaki fitar dashi ba” a nutse ta zayyanawa maimunatu waye ja’afar,ta koma dora da

“Kiyimin wannan alfarmar maimunatu,bansan me Allah yake nufi ba da yasa nakejin ke zaki iya…..”

“Kiyi duk abinda ya dace dani anni,don Allah basai kince neman alfarma kike daga gareni ba” maimunatu ta fada,dukka jiki da muryarta suna rawa.

Kai anni ta girgiza tana kallonta a nutse

“Aiba baiwa bace ce,’ya ce ke kamar kowa,don haka ya zama dole a nema daga wajenki cikin baki cikakken ‘yancin yin zabin eh ko a’ah,kije kiyi tunani maimunatu,na baki dama,idan har kikaji baki gamsu ba,ko ba zaki iya wannan alfarmar ba,kada kiji komai,ki gayamin kanki tsaye,ni kuma nayi miki alqawari har tsakanina da ubangiji na,zamu ci gaba da riqonki ba tare da komai ya sauya ba…..tashi kije” kasa cewa komai tayi,ta miqe cikin wani irin yanayi data gaza fassarashi,kamar anbi kowacce gaba ta jikinta an zare sinadarin dake bata kuzari,komai na jikinta yayi sanyi qalau,maimakon ta wuce study room ko kitchen kamar yadda ta tsara yi,saita wuce dakinta kawai,ta tura qofa ta kuma haye gado.

Inda batasan wace anni ba da sai tace wasa take mata,ja’afar dai da takejin sunansa a bakunan al’umar gidan nan?,koda batasan fuskarsa ba amma mutum ne da kowa ke ganin girma da kimarsa,kamar ita?maimunatu?,bafullatanar ruga ‘yar qauye?,ta yaya zatayi kan kan kan da mutumin da take da tabbacin a yanzu ma baya qasar nijeria?,ta yaya zata iya wanke wannan babban tabon daya nannade rayuwarsa?,kai tana ganin a rayuwar gida irin ta dr marwan,koda drivern gidansu darajane dashi,koda drivern gidan ya fita daban da sauran drebobi,koda shi aka ce ya aureta tana ganin kamar ya zarce mata,bare ace dan gida,dan gidan ma irin ja’afar dan gata ta kowacce fuska,anya kuwa zata iya?,idan ba zata iya din ba kuma zata iya kallon anni tace mata A’AH?,…..kalmar tayi nauyi da kuma muni da yawa,anni mutum ce guda har da rabi,wadda ‘yantata ta kuma maidata cikakkiyar mutum.

Ire iren wadan nan tunanukan su sukaci gaba da kassara maimunatu,suka kuma cika mata kwanya taf,ta rasa yadda zata sarrafasu su dace da hange da kuma fikirarta.

Ajiyar zuciya anni ta sauke bayan fitar maimunatu,fatanta daya komai ya daidaita,komai yazo da sauqi,don muddin maimunatu ta amince,to fa babu daga qafar da zata yiwa ja’afar har sai ta tabbatar komai ya kammala,wannan shine buri da kuma fatarta.

Wannan magana da sukayi da anni sai ta zamewa maimunatu kamar wani dabaibayi,dukka kuzari karsashi da walwalarta suka yi qaura sosai,duk da dama ita din miskila ce,wadda bata damu da hira ko hayaniya ba,tafi ganewa karatu,to shima karatun a dan tsukin nema yake ya gagareta,idan ta buda littafin sai ta tafi duniyar tunani,sai ta kasa qulla komai har ta gama zamanta ta tashi.

A wani yammaci ne,tana dakin karatun dauke da qur’aninta tana tilawa,saidai can tsakiyar karatun nata tunanin da ya zame mata jiki ya kutso mata kai,sai taci gaba da riqon qur’anin kawai ba tare data iya ci gaba da karatun ba.

A wannan lokacin baba tabawa ta shigo dakin,hannunta dauke da cup data cikashi da kunun gyada fari sol sai maiqo da qamshi gyada da yakeyi,daya daga cikin cimar da maimunatun keso kenan,tayi firgigit tana amsa sallamar baaba tabawa.gami da gyara riqon alqur’aninta,sai baba tabawan ta sakar mata murmushi tana miqa mata cup din,sannan ta zauna saman kujerar dake fuskantar maimunatu

“Na lura kwana biyu kin zama wata aba,don wannan kunun qilan saidao a zubda ba tare da kinzo kin dauka ba” dan murmushi tayi tana juya spoon din dake cikin kunun,cikin ranta tana ayyana yadda mutanen birni ke kashewa ciki kudi,suci wannan suci wancan

“Shawara nazo baki muna,don banaso kiyi asara har irin wannan a rayuwarki” daga kai maimunatu tayi ta dubeta cikin rashin fahimta,idanun baba tabawa cikin nata ta gyada kai tana tabbatar mata da duk abinda zata ji

“Maimunatu,tun zuwanki gidan nan naji kin kwantain,ina kuma qaunarki,maimunatu,naji na kuma san abinda ya sanyaki kika canza gaba daya,ba zancan ja’afar ba?” Tayi zancan da sigar tambaya,saita sad dakai,wato kowa ya sani kenan?,ya kuma fahimta?.

“Duk yadda zakiyi kada ki bari ja’afar ya subuce miki,duk yadda zakiyi kada ki soma wauta ko gangancin cewa baki sonshi,ja’afar yana cikin dai daikun mazan dake da wuyar samu duk da wahalar sha’aninsu,samunsa kuma sai mace mai matuqar sa’a kuma ‘yar baiwa,bawai don yana da kyau da kudi ba,a’ah…..yana da wata irin nagarta da kuma kebantattun kyawawan halayen da ba kowa bane ya sansu,ba shakka kowacce mace da tasan abinda takeyi zata yiwa wadda take so ko qauna fatan kasancewa da shi a mazaunin miji…..maimunatu,a shawarce…..ki aminta da maganar hajiya anni,ina mai baki tabbacin ja’afar gaba yake da nagartaccen miji idan ma akwai” shuru maimunatu tayi tana jujjuya maganganun tabawa cikin zuciyarta,tana ganin matsayinta baikai inda anni keson kaita ba sam

“Akwai abinda kike tsoro ne?” Tabawa ta tambayeta kai tsaye,a wannan karon batayi nauyin baki ba

“Bansan waye ubana ba,bafullatanar ruga nake,har na isa na hada kafada da zuri’ar anni?” Murmushi tabawa tayi

“Zallar karamci irin na hajiya anni babu abinda ba zaki gani ba,sa’annan ke din halastacciyar ‘ya ce,babu abinda ya nuna baki da.uba ne,ke koda haka ne,ina me tabbatar miki tunda hajiya anni tayu niyyar aiwatar da hakan,babu abinda zai dakatar da ita,ba kowanne mutum ke ganin baiwar da Allah yayi masa ba,kamar ke din,kina da wasu kebantatattun halaye da siffofi dani kaina nake saka ran akwai alkhairi me yawa a tare dake” shuru maimunatu ta sakeyi,tambayar qarshe kuma wadda take ta cin ranta

“Shi ya santa ne?,yana kuma sonta” maganar data fito sarari,sai murmushi kawai taga tabawa tayi

“Muna…..ke din ta musamman ce,hakazalika kina da tarin baiwar da namiji bai isa ya kalleki yace baiso ba,saidai idan wani abun daban kuma ba wannan ba” tabawa tayi matuqar sanyata cikin nazari,tana jin kokwanto tana kuma jin qwarin gwiwa,wanne zata rinjayar?.

“Anni ta damu qwarai,kin amince a shaida mata ko zata samu nutsuwa”
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram:

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply