Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 26


Gurbin Ido 26
Viral

26

Kulawa me kyau maimunatu ta dinga samu daga wajen yadikko matar kawu suleman,itace matarsa ta biyu,kuma tafi daada saratu quruciya,don haka ta zage da bawa maimunatu duk wasu kaye kaye irin nasu daya kamata ace amarya tayi amfani dashi,sannan ta zage ta dinga karantar da maimunatun mene ne aure?,waye miji da sauransu,abubuwan da suka sake fadada tunanin maimunatu,ta wani fannin kuma suka sake haifar mata da wani tunanin na daban

“Wannan shine aure?,irin zaman da zanyi kenan da mutumin da bansan waye shi ba?,shima baisan wacece ni ba?” Abinda ta yita juyawa kenan cikin ranta.

***********Zaune yake gaban laptop dinsa,ya baje takardu yanata shigar da wasu bayanai cikin system din,gaba daya hankalinsa kacokam yana kan aikin,wanda ya share kwanaki uku yana yinsa,burinsa ya kammale komai waje daya ya kuma gama da wannan aikin.

Wuninn ranar ko abincin kirki baici ba,sai uban coffee da yaketa danqara,lokaci lokaci kuma ya hada da cake,ko a yanzunma mug din daya sake tsiyaya coffee din na gefansa,ya dauka a hankali yakai bakinsa ya kurba ya maida ya ajjiye,dai dai sanda jabir ke qarasowa wajen,hankalinsa akan ja’afar,hannunsa kuma riqe da wasu rantstsun invitation cards,mamaki fal randa da zuciyarsa na yadda baiji ja’afar din yace komai ba kan yadda IV din nasu keta trending yana yawo tsakanin family and friends,duk da ya lura aiki yakeyi wurjanjan a kwanaki ukun nan.

Yaji isowarsa amma bai juya ba sakamakon shigowar wasu emails har kusan hudu a jejjere,sai yayi minimizing abinda yakeyi ya tafi kai tsaye ga email din,don dama yana jiran wasu bayanai daga secretary dinsa,yace masa a daren ya kammla su ya turo masa.

Maimakon secretary dinsa sai yaga saqon daga wajen hamza BBY yake,daya daga cikin abokansu tun na makaranta ake kuma tare har yanzu,budewa yayi gajeran rubutune da kuma hoto daga qasa sa bai budu ba

_Allah ya sanya alkhairi manya,da ba’a gaya mana ba JB ya gaya mana,Allah ya nuna mana lokacin big boos,i salute you🫡,biyu ka b’aro ashe_

Danna hoton yayi, within seconds ya bude, invitation ne dake dauke da sunansa,da sunan samiha da maimunatu,mutuwan zaune yayi,wani bacin rai yana ratsashi,ya dunqule hannunsa waje daya yana furzar da wata iska daga bakinsa,da gaske suke kenan,ba zasu fasa ba?.

Dai dai lokacin da jabir ya zagayo gabansa,yaja wata kujerar ya zauna yana zube masa IVs din a gabansa

“Ga hard copies” wani kallo ya watsama jabir din,wanda banda ya saba da irinsa ba shakka sai ya razana

“Are you in your sense?, what did you do?,su suna nasu kenan kai kana naka?,to sai kasan ya zakayi da mutanen daka gayyato da labarin qanzon kuregenka,don banga abinda zai kaini nigeria a yanzu ba bare na fuskanci abinda yake shirin faruwa” sai ya miqe ya fara tattara abubuwansa masu muhimmanci,huci kawai yake kamar wani maciji

“Da kaje da kada kaje babu abinda zai canza,so gwara ma ka nutsu ka karba abun hannu biyu,ka kuma fuskanci abinda ke gabanka dude” baiko daga kai ba bare ya bashi amsa,ya gama kwashewa ya wuce yabar masa wajen.

Dariya jabir ya saki yana kada kai,duk duniya su qalilan ne suka iya zama da ja’afar,cikinsu shi da shaheeda sun shiga ciki,shi yasa kowa yake jinjina mata har yau da bata raye,yana da murdadden hali da kuma wuyar sha’ani qwarai.

Sanda ya shiga dakin kasa ci gaba da aikin yayi,ji yake kamar yaci kansa,wani irin bacin rai ya dinga taso masa,yakai ya kawo yana jin wani huci na fita saman fuskarsa,idanunsa suka kai kan dan qaramin frame dake dauke da hoton shaheeda,sai ya qarasa wajen ya duqa

“Why did you go and leave me?” Ya furta a hankali yana kai hannunsa saman fuskarta dake qunshe da faffadan murmushin nan nata me sanyi,sai ya miqe da sauri da nufin yiwa zuciya da harshensa linzami,ya kuma ja da baya yana fadin

“Astagfirullah wa’atubu ilaika” yaqi yake da kansa ba tare da sanin kowa ba,bayason maida hannun agogo baya,bayason wannan mode din da yake zama out of sense,yanaso yayi nisa dashi,sai kawai ya fidda wayarsa ya duba cave mafi kusa dasu ya kirasu suzo su fiddashi,kayan jikinsa ya fidda ya sauya wasu ya jefa wayarsa a aljihu ya fito,jabir na zaune anan yana ta duba tarin saqonnin mutanensu,baice masa komai ba yadai bishi da kallo gami da tabe baki har ya fita.

Cikin mota kwanyarsa ta cake sosai,neman dukka hanyoyin da zai kaucema wannan auren yake,ana tsaka da wannan kiran wayar dr marwan abbi ya shigo wayarsa.

Sai daya sauke gauron numfashi sannan ya daga wayar,sallamarsa kawai dr ya amsa ya hau balbaleshi da fada,ta inda yake shiga ba ta na yake fita ba,maganarsa ta qarshe itace

“Duk abinda kakeyi ka barshi,kada ka sake jabiru ya baro turkey ba tare da kai ba,ka biyoshi ku dawo gida” daga haka dr ya kashe wayar.

Hannunsa guda daya ya sanya yana yamutsa sumar sa gami da kallon yadda suke wuce titi bayan ya sulalar da wayar gefansa,jin abun yake kamar mafarki,duk inda bacin rai yake ransa yakai nan wajen baci,zuciyarsa ta gaya masa jabir ne ya shaidawa abbi abinda yace

“I will deal with you jabir,definitely” ya fada cikin huci kamar jabir din yana kusa dashi.

********Kwanansa uku cur bai dawo gidan ba tun ranar daya fita,jabir yayi kiran yayi kiran har ya gaji,gashi dai kiran yana shiga,amma sai ja’afar din yayi rejecting,daga bisani jabir ya daina baiwa kansa wahala ya dakata da kiran nasa,don yasan tabbas a yanzun bazai daga ba,bazai kuma saurareshi ba.

A rana ta hudu ya iso gidan,tunda yayi knocking sau uku ya tabbatar jabir din baya nan,sai ya sanya key dinsa samfurin katin cirar kudi na atm ya bude qofar ya shiga.

Sai daya kunna qwai haske ya gauraye falon sannan ya wuce dakin baccinsa,yana tura qofar idanunsa suka sauka kan hoton shaheeda,sai yaji kamar ya jima bai kalli hoton nata ba,don haka ya qarasa a hankali,ya zauna gefan gadon nasa,sannan ya dauki frame din hoton.

Yadan dauki wasu sakanni yana kallon fuskarta,kafin ya ajjiye frame din bayan yayi kissing hoton,ya kuma karanta mata addu’a cikin ranta kamar yadda ya saba.

System dinsa ya dauko hade da charger dinta ya fito daga dakin,don dama kusan itace ummul’aba’isin dawowarsa gidan,sai kuma ya koma da baya,saboda tunawa da yayi da maganar da sukayi da abbi,ya buda wardrobe dinsa ya ciro passport dinsa ya sanya a aljihunsa ya dawo falon,ya jona caji a system din ya kunnata sannan ya wuce kitchen, fridge ya bude yana laluben abun sha,duk ya gama bulayin sa daga sama zuwa qasan fridge din amma baiga drink din da yayi masa ba.

Wani mix fruit ya dauka,saidai yana gama karanta rubutun jiki yaja tsaki ya maidashi,a qa’ida shan abun sha na kwalba gwangwani ko roba basu dameshi ba,yafison abun sha irin namu da gargajiya da za’a hada a gida,kamar kunun aya zobo da sauransu,daga qarshe ya dauki wani matstsen ruwan lemon zaqi hade da cup ya dawo falon.

Bai jima da fara aikin ba jabir ya iso,daga sallamar sa daya amsa bai sake bi ta kansa ba,shima jabirun sai ya shareshi,saboda ha fuskanci abun sai ‘yar tursasawa kadan ta shigo ciki,dole sai an ma ja’afar haka idan anaso rayuwarsa ta dai daita nan kusa,don haka shima sai ya wuce daki abinsa.

Sai da yayo wanka ya canza kaya sannan ya dawo falon,saman hannun kujerar dake daura da ja’afar din ya zauna yana fadin

“Ka gama yajin kenan kayo bikon kanka da kanka” maimakon ya amsa masa,sai kawai ya ciro passport dinsa ya cillawa jabir din.

Bin passport din yayi da kallo,kafin ya sanya hannu ya dauka ya soma budewa yana dubawa. Idanu jabir ya fidda waje sannan ya dorasu saman ja’afar din

“Over stay?” Kamar bazai amsa shi ba,sai kuma yace

“Yes” a daqile yana ci gaba da concentrating kan aikinsa,ajiyar zuciya jabir ya fitar yana daga passport din daga fuskarsa

“Ya Allah,why ja’afar?,kasan visa dinka ya qare amma kaci gaba da zama musu a qasa baka biya anyi expanding maka ita ba?ka sani turkey ba kamar kowacce irin qasa bace, you know how people suffer before they get the visa….shine ka samu suna baka whenever you need zakayi wasa da damarka?”

“I don’t like noises please,idan zakayi abinda ya dace kayi,if not ka ajjiyemin passport dina ka qara gaba ka barni naci gaba da zama,dama ban shirya tafiyar ba” gimtse dariyarsa jabir yayi,ya gano shi sarai,neman duk hanyar da zaya kubucewa komawa yakeyi

“Alright,sai kamin transfer abinda za’a kashe ta account dina,kasa dole sai na nema baaba ambassador” ya fada yana bata rai shima hadi da miqewa

“Bani dako sisi” ya fada kansa tsaye

“Kut!” Jabir ya fada yana fito da ido waje,dariya kuma na masa yawo can qasan ransa,lallai ja’afar din mugun dan rainin wayo ne,recently yaga amount din dake qaramin account dinsa ma,wanda shine baya ajiya kudi mai yawa a ciki,the amount is very huge,kamar yasan me yake tunani,sai ya daga kyawawan idanun nan nashi dake dauke da wani irin sinadari mi qarfi ya zubewa jabir su

“I mean bani dako sisin da zan batar don komawata gida,bcoz ban shirya ba” dole dariya ta subucewa jabir,cikin ransa yace

“Kayi ka gama,komawa gida dole,mu lafiyarka da hankalinka mukeso,tafi mana kuma komai”

“Okay,…..duk naji,but bani zan maka komai ba,you know,dole kaje da kanka,tunda kai mai laifi ne a wajensu yanzu” kamar bazai amsa ba kafin yace

“Naji” ciki ciki,kada kai jabir din kawai yayi yana nufar kitchen,cikin ransa yana fadin

“Allah ya shirya ja’afar,mai zama dashi sai ya shirya,zuma ga zaqi ga harbi ga kuma ba tsoro” .

Abinci ya shiryo musu,ya kuma kawo har nan inda ja’afar din yake,yanata wani ciccijewa da basarwa amma jabir yayi kamar bai gane me yake nufi ba,ya gama daagiyar duka ya sauko suka fara cin abincin.

Yadda jabir din yaga yana ci ya tabbatar masa a kwanakin da ya qauracewa gidan bai cin wani abincin kirki,dama can shi din irin mutanen nan ne da ba abincin kowa suke iya ci ba,sau tari sun gwammace su haqura da abincin,sai yaji tausayinsa ya darsar masa a rai,yaji har cikin zuciyarsa yana fatan wannan auren ya zame ma rayuwar ja’afar din wani babban sauyi da kuma ci gaba,suna gamawa kiran amaryarsa ya shigo,don haka ya miqe yabar wajen,jaafar ya bishi da tsaki da kuma harara,ganin yadda yaketa zumudin amsa kiran nata.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply