Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 32


Gurbin Ido 32
Viral

32

*WASHEGARI*

Tun sanda ta idar da sallar asuba bata koma bacci ba kamar yadda ta saba,tana ta azkar dinta,yayin da rabi da rabi na hankalinta ke kan tunanin yadda rayuwa zata kaya mata cikin gidan.

A hankali taji idanunta suna mata nauyi,gajiyar zaman mota daga gembu zuwa gombe ya sanya bata kai ga qarasawa ba bacci yayi awon gaba da ita,ba kuma ta farka ba sai wajen qarfe tara saura na safe.

“Hasbunallahu wani’imal wakil” fa fada s sauri hamma na qwace mata,ta miqe tana linke abun sallar data tashi akai,daga nan kuma fa zarce sa bubbuge bubbugen qura duk da dakin babu abinda yayi,ta kauda abinda yake zaune ba’a kan tsari ba,daga nan ta wuce toilet kai tsaye,ta hada ruwa tayi wanka.

Sanda ta fito hudubar anty maama da yadikko matar kawu sulaiman akan tsafta da kula da kanta,duk da cewa kwatakwata qazanta ba dabi’ar ta bace.

Cikin mayukan dake jere saman madubinta ta bude wasu ta shafa,sannan ta duba makekiyar wardrobe dinta ta jikin bango.

Tsaiwa kawai tayi tana kallon tarin uban suturun da a yanzu suke mallakinta,sai takejin kamar ta zurawa rayuwa jikinta da yawa,banda haka ina ita ina wadan nan kayan da batasan ranar da zata gama sanyasu ba?,haka ta dinga dubawa har zuwa lokacin da hannunta yakai kan wata atamfa,kalarta ce ta dauki idanun maimunatu,data gwada sanyawa kuwa saita amsheta,tayi mata kyau matuqa da gaske,batayi amfani da dankwalinta ba,a maimakon hakan sai ta nema qaramin hijab ta maqala a kanta.

Bakin gado ta koma ta zauna,ta rasa abinda zatayi,sai kuma ta fada tunane tunane,abubuwan da suka faru a rayuwarta,suke ma kan faruwar,tsakiyar haka taji kamar qararrawar falon nata neman dauki,hade da knocking,tayi kamar kada ta fita,amma jin baa fasa knocking din ba ya sanyata miqewa.

Cikin nutsuwa ta fita,qafafunta suna nutsewa cikin lallausan carpet dake malale a wajen har ta iso falon ta doshi qofa,dai dai sanda yake saukowa daga samansa,sanye da wata jallabiya saqar qasar morocco,ruwan a qasa da aka yiwa ado da wani zare mai dan kauri ruwan madara,yankakken hannu gareta,don haka dukka singalalinsa dake lullube da gargasa waje yake,sumarsa tadan hargitse kadan,haka nan fuskarsa na nuna alamu na jin bacci.

Idanunsa a kanta sanda ta bude qofar yana step na qarshe,ta gane fuskar matashin saurayin dake miqo mata kwanduna dauke da fulasai masu azabar kyau

“Daga gidan dr,amma ce tace a kawo muku” sosai taji dadin karamcin amman har cikin ranta,tasa hannu ta karba tana cewa

“Kayi mata godiya,Allah ya saka da alkhairi” sai ta maida qofar ta tura ta yadda take,ta kuma waiwayo don komawa ciki ta sama musu mazauni.

Karaf idanunta ya sauka a kansa sanda yake isa gaban babban freezer dake falon tamkar ma bai ganta ba,budeta yayi ya ciro babbar gorar ruwa guda daya,gabanta ke wani irin faduwa,tsoronsa dake shaqe a zuciyarta ya motsa

“Ina kwana” ta fada bakinta yana dan rawa kadan,tana jin kamar zai mata wani mummunan abu ne,banda alamun sauti da taji da sai tace bai amsa gaisuwar tata ba,kunnuwanta na biye da takunsa sanda yake shirin komawa saman,sai tayi ta maza tace

“Ga abinci amma ta aiko dashi” shuru na wasu sakanni suka ratsa yana ci gaba da tafiyarsa,kamar bazai ce komai ba sannan tayi yace

“Madalla,an gode” yaci gaba da hayewa saman,kunnuwanta dai na biye da sautin takunsa,takun da ake yinsa cikin wani irin salo da kuma tafiya wadda jinin sarauta ke yawo a cikinta.

Sai data daina jin motsinsa sannan ta daga kanta tana duban kwandon hannunta tare dason gane me madalla da yace take nufi?,ita yanzu ya zatayi da wannan abincin?,sai ta maida dubanta ga sassan unaisa dake a rufe,zuwa zatayi ta mata magana ko kuwa ta qyaleta?,kai ta girgixa,zuciyarta tafi karkata da ta qyalesu gaba daya,don haka tayi kitchen da abincin,ta ajjiye acan,bayan ta bude ta diba iya abinda cikinta zai iya dauka,wanda duka duka cikin plate daya ta xuba komai.

Tunda ta koma daki bata sake jin motsin kowa ba,don ko data gama cin abincin sake kwanciya tayi,ita ba gwanar kallo bace bare ta dawo falonta tayi,sai bayan kusan awa biyu taji tashin mota daga farfajiyar gidan,wadda batasan ta waye ba,saidai tana kyautata zaton tame gidan ce.

Qarfe daya da ashirin na rana tana fitowa daga alwalar sallar azahar taji knocking da ‘yar hayaniya,sake fitowa tayi falon,har yanzun kamar dazun dai babu kowa ba kuma motsin kowa.

Murmushi ya subuce mata sanda ta bude qofar,laila ce ita dasu hanne da hauwa,sai fa’iza da safina harda khadija,kusan dukkaninsu mutanenta ne,akwai sabo tsakaninsu sosai,abinda yasa ta sake jikinta ta kuma ji dadin zuwan nasu

“Ina fatan dai yaa ja’afar bai nan?” Fa’iza ta fada tana dan fidda idanu gami da watsa idanunta a babban falon gidan hadi da kallon stairs din,qaramin murmushi maimunatu tayi tana kada kai

“Ya fita” ta amsa musu kai tsaye,don motsin fitar motar dazun ranta yana gaya mata shine

“Na baroshi wajen amma ma fa sanda muke fitowa” safina ta fada tana zare mayafinta daga kanta

“Au to,dama wai don mufi sakewa ne” ta fadi tana dariya,ita dai maimunatu jagora ta musu zuwa sassansu,suna tafe suna gaya mata ba dadewa zasuyi ba,amma tace au dawo da wuri,kuma su hauwa da qyar idan ba anjima zasu wuce ba,zasu biya ta jalingo ne,akwai gaisuwar mutuwa da akayi da zasu fara zuwa sannan su wuce gembu.

Awa biyu kawai sukayi,amma sai taji kamar sunyi awa biyar,saboda yadda hirarsu ta dinga debe mata kewa,kowacce na qoqarin koya mata yadda zata zaun a gidan,ta kuma kama hankalin mijinta sannan ta tserewa kishiyarta,kasancewar dukansu sun girme mata,ita dai jinsu kawai take da kunne,hausawa sukace me daki shi yasan inda yake masa yoyo.

Da suka tashi tafiya sukace zasu leqa wajen unaisan su gaisa,cogewa maimunatu tayi har suka shiga suka fito,sannan tayi musu tattaki zuwa farfajiyar gidan,karon farko kenan da taga yadda harabar gidan yake,salmanu drivern abbi ne ya kawosu,tana tsaye tana binsu da kallo har suka fice daga gidan,sai ta sauke ajiyar zuciya tana jin tamkar ta bisu,cikin matuqar sanyin jiki ta dawo cikin gidan.

Tunda ta koma din bata sake jin motsin kowa ba,gaba daya gidan sai take jinsa wani iri,babu armashi babu kuma dadi,tana jin inama za’a maidata gidan abbi?,inama zaa maidata wajen anni,rayuwar can tafi mata dadi dari bisa dari.

UNAISA tun bayan tafiyar ‘yan uwanta da sukazo mata bayan sallar magrib ta shiga toilet dinta ta sheqa wanka,sunyi maganganu masu tarin yawa da anty talatu,wanda ta dinga qoqarin ganin tabi kowacce shawara da umarni da anty talatun ta dorata akai.

Cikin wasu azababbun English wears ta shirya kanta, straight leg jeans da rigarsa wadda tsahonta iyakarta cinya,ta zuba turare sosai a jikinta,ta kuma wadata fuskarta da powder da lip gloss da ya qarawa lips dinta sheqi,nails polish remover ta saka ta cire tsohon nail polish din,ta sabunta da wani da yaketa glittering.

Sai data tabbatar komai yayi,ta juya gaba da baya sannan ta dauki wayarta,already tana da number dinsa,saidai bata taba gigin kira ba,ta zauna gaban dressing mirror dinta ta kara wayar a kunne sanda take ringing,tana kuma kallan fuskarta,gabanta yana dukan uku uku,don batasan da wacce fuska zai tarbi kiran nata ba.

Dai dai lokacin da yake kashingide bayan motarsa suna magana da mr husain daya daga cikin manyan ma’aikatansa,kallo daya ya yiwa wayar ya dauke kansa ya maida ga maganar da sukeyi dashi cikin ma’ajiyar motoci ta kamfanin nasa,wanda ya budewa wuta yakeson ya dawo dashi.hayyacinsa,ya kuma ci gaba da aiki fiye da yadda yakeyi a yanzu.

Al’adarsa ce haka,ba kasafai yake daga baquwar number ba,don haka da ring din ya isheshi saiya maidata silent yaci gaba da uzurin gabansa.

Da matuqar sarewa ta sauke wayar daga kunnenta,kira uku kenan bai dauka ba,sai ta yanke ta tura masa gajeran saqo kawai,don haka ta batayi qasa a gwiwa ba ta senda masa

_hello hottie,it’s your wife calling you,i missed you so much today,please come back as early as possible,akwai abubuwa masu dadi dana tanadar maka….am waiting for you,urs…..unaisa_

Sanda saqon ya shigo wayar tana hannunsa yana duba wani verification code da wani company suka turo masa,zai bawa mr hussain,tsaki yaja wanda sai daya fito a fili,har sai da mr hussain ya daga kai ya kalleshi,saidai bai tambayeshi ba,shi sam yama mance dasu,tunda yasa qafa ya fice yau din duka aiki ya riqeshi,gaba daya hidimar company dinsa ne a gabansa,ko gidama da yaje amma kawai ya samu ya gaisar ya wuce,bai samu ganin abbi ba bare anni,saboda akwai sauran baqi,shi kuma bayason wannan wasan banzan da akema mutum da sunan abokan wasa.

Sai daya bawa mr hussain duk abinda zai bashin sukayi sallama sannan ya yiwa driver dinsa sign da ya shigo su tafi,sai daya tada motar suka fice a company din sannan ya tambayeshi

“where are we going sir?”

“Take me to the nearest restaurant” ya bashi amsa yana kara wayarsa a kunne,jabir ya kira,don tun dazun yaga miscalls dinsa,a sannan yayi calling urgent meeting da ma’aikatansa,daya fito kuma ya manta sai yanzu ya tuna.

Sai data kusa tsinkewa ya daga,cikin wata irin raunanniyar murya me cike da sanyi jabir din ya masa sallama,muryar data sanya ja’afar din tuno abubuwa masu yawa a shekarun baya wadanda suka shude masa,kamar shi a irin wannan lokacin da jabir din ya kirashi,da qyar ya samu ya daga,a sanda yake rayuwa da muradin zuciyarsa shaheeda.

Yayi kamar zai katse kiran,sai kuma ya dake,suka gaisa ya gaya masa uzurin da yasa ya kirashin

“Am sorry J,amma if possible please kayi postponing schedule din zuwa upper month mana,saboda ina tunanin tafiya honey moon ni da my fa’eem” wani dogon tsaki ja’afar ya sake a kunnen jabir,yana jin kamar ya raina masa wayau ne

“What nonsense are you talking about?,ina maka magana ne akan abinda ya shafi company kana min maganar honeymoon,if u r not ready to accept your vacancy shikenan fine,i can I can manage the company” daga haka ya katsr kiran cikin fusata,tamkar wani gagarumin abu jabir din ya gaya masa,yana furzar da wata zazzafar iska daga bakinsa.

Ko da yaje eatery din da drivern ya kaishi,ya kuma zaba abinda zaa kawo masan sai ya kasa ci,daga qarshe haka ya miqe ya biya abinda aka cajeshi duk da tsadar abinci a wajen ba tare daya ci wani abun kirki ba,yace su wuce gida kawai.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram:

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply