Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 33


Gurbin Ido 33
Viral

33

A hankali yake takawa zuwa cikin gidan,duka hannayensa cikin aljihun rigarsa,duk da yadda ya gaji amma sai daya daure ya biya ta store din gidan,ya duba kayayyakin amfanin da yace a zuba a ciki,ya tabbatar a saka komai da komai na amfanin gida na yau da kullum,sannan ya rufe,ya bulla ta qofar kitchen.

Dai dai lokacin da maimunatu ke cikin kitchen din,tana tunanin yadda za’ayi da abinciccikan da aka kawo na safe rana dana dare,tunda bai cinyu ba,daga qarshe kamar yadda taga acan gidan sunayi,saita kwashesu ta zuba a freezer.

Hannunta take daurayewa a bakin famfon dake cikin kitchen din,tana gamawa ta kashe ta juyo tana yarfe ruwan dake jiki,dai dai sanda yake fitowa daga store din,idanunsa suka sauka a kanta,cikin lausasan kayan bacci,doguwar riga baby pink da baby hijab light blue,kalar datayi masifar haskata,ta kuma fidda gewayayyar fuskarta dake nuna qarancin shekarunta,sam bata lura dashi ba,saboda idanunta yana kan hannayenta,har sai data zo gab sannan ta ankara da inuwarsa,taja baya kuwa da sauri gabanta yana faduwa,idanuwanta suka fada cikin nashi,zallar tsoron dake zuciyarta ya bayyana qarara cikin idanuwa da fuskarta.

Wani kallo yayi mata fuskar nan a dinke babu ko digon annuri,jinta tayi tamkar nutumin da zaki ya ritsa a tsakiyar jeji babu gurin kubuta,sai ta rasa me ya kamata tayi,cikin juriya da qarfin hali jajayen lips dinta suka motsa

“Sannu…..da zuwa” ta fadi a rarrabe,dauke idonsa yayi daga kan labban nata yana jan qaramin tsaki qasan ransa,yadda tayi maganar ma kawai zai gaya maka shes very young,ta yaya wai ma anni zata ce ya ajjiye kamar wannan a matsayin matar aure koda ya tashi yin auren?,wannan ba saidai a dauki buzunta ba duk sanda yace zai kaara jikinsa a nata?.

“Ungo nan” taji ya fada a maimakon amsa sannu da zuwan data yi masa,daga kai tayi a hankali tana duban abinda yake miqo matan,kafin ta saka hannu ta dauka a saman fridge din dake daura dasu,inda anan ya aje mata kafin takai ga karbar,sababbin kudi ne a daure a kyauro masu yawa,don ko da batasan adadinsu ba amma tasan cewa suna da yawa qwarai

“Idan kina da buqatar wani abu kiyi amfani dasu,banason ki nemeni,don banason damuwa da takura,take care” gyada kai tayi a hankali,sannan tace dashi sanda yake fita a kitchen din

“Allah ya saka da alkhairi” bata iya jin ya amsa ko bai amsa ba,itadai tabi bayansa itama ta fita bayan ta tabbatar yayi nesa da wajen,kudin na rungume a hannunta,saidai tana tsananin jin qyamar kudin har cikin ranta,itafa…daga randa ta ganshi yana zuqat taba shikenan kuma,bata masa kallon komai sai dan iska,mugu kuma azzalumi,biyo bayan abinda yayi mata,zuciyarta cike fal da tunanin mema zatayi da kudade haka?,me zafa buqata dasu?,da wannan tunanin ta fada dakinta ta kulle,ta isa gefan gadonta ta jawo side drawer ta jefa kudin ta mayar ta rufe.

Tunda taji motsi a sama ta tabbatar shine ya dawo,don haka ta sake duba kanta da kyau,sannan ta bude freezer dinta ta dauki sassanyan ruwa da lemo ta aza saman wani set din tray me hade da cups,ta yane kanta da wani dan yalolon mayafi,sannan ta fito.

Wani abu ya mintsini mai kama da kishi sanda idanunta suka sauka a sassan maimunatu,basu taba haduwa da yarinyar ba,basu taba gamuwa ba,ko yaya take?,tana ina yanzu oho?,taja wata qwafa kamar zata cire harshenta sanda zuciyata ta raya mata ace dai taje ta sameta tare dashi.

Har tsakiyar zuciyarta falon nasa ya tafi da ita,akwai wani yanayi na musamma tattare dashi,taci gaba da takawa a hankali ta nufi bedroom dinsa kai tsaye,saidai kuma kamar yasan wani zaya shigo masa,yana shiga kafin ya shiga wanka ya murza key,tana taba handle din ta gane hakan,dole ta koma saman kujerun alfarma dake falon,ta zauna ta dora qafa daya saman daya bayan ta kunna tafkekiyar tv dake falon,takuma canza tasha zuwa mbc Bollywood,ta samu kuwa suna wani film me kyau,saita maida hankalinta a kai,yayin da wani sashe na zuciyarta kuma yaketa wassafa mata yadda zai tarbeta,duk da tasa a ranta ba zata samu tarba me kyau dari bisa dari ba.

Cikin jallabiyya Morocco’s male abaya me ruwan gold mai gajera hannu ya shirya bayan ya fito daga wankan,duk da baici abinci ba amma sam baya jin yunwa,muryar amna yakeson ji,yayin da wani sashe na zuciyarsa kuma a yau yake cike da kewar shaheedansa,ya feshe jikinsa da lallausan turaransa bayan ya gama gyara sumarsa dake samun gyara na musamman,ya dauki wayarsa ya danna kiran number ammansa.

Bugu biyu aka daga,salma ce,ta shaida masa amman tana wajen abbi,sai ya nema ta hadashi da amna,ta kuwa hadasun,yarinyar ta dinga masa hira sosai,abinda yasa ya samu relief daga abinda yakeji kenan,yadan sake shima yana tayata.

Ya kusa minti talatin tare da ita,ya samu sauqi sosai cikin ransa,harma ya samu qwarin gwiwan jin son shan coffee,don haka ya diba takardun da zai duba da system dinsa ya nufi falon.

Janye idanunta tayi daga fuskar tv din tana sakin murmushi,jarumin film din yana mata mugun yanayi da J dinta,yadda ya iya soyayya ta tabbatar J zai iya finsa,saidai shawo kansa da qwato hankalinsa abune mai wahala ta sani kuma,dai dai sanda take shirin sake maida idanunta ga film din,sai suka sauka ga babban hoton shaheeda dake rataye cikin falon,zuba ma kyakkyawar fuskarta idanu tayi,murmushin da take a cikin hoton tajiyana tabata,sake waiwaya tayi wani sashe still hotonta ne ita da twins dinta amna da amra,daga daha bangaren kuma shi da ita ne,sunyi masifar kyau cikin qananun kaya,karon farko data fara ganin wani abu me kama da murmushi saman fuskarsa,yana rungume da ita ta baya,da gani ba’a qasar nan aka dauko hoton ba,yana sanye da uniform da matuqan jirgin sama,kyau iya kyau yayishi,uniform din sun karbeshi matuqa da gaske,hoton ya fusgi hankalinta,ya kuma saka kishin shaheeda mai yawa cikin ranta,har sai data miqe ta isa ga hoton dake can wani kusurwa na falon,ta tsaya a gabansa tana sake qare musu kallo.

Da farko daya fito bai lura da ita ba,sai daya kusa isa inda ya ajjiye na’urar hada coffe dinsa take,yadan tsaya kadan,kamar zai magana sai ya fasa,ya isa inda coffee maker din yake,ya soma hada abinsa,saidai abun mamakin har ya hada ya dawo ya zauna saman kujera bata ankara da wanzuwarsa,abunda yayi masifar bashi haushi,saidai zaiga iya gudun ruwanta da nata qwaqwqwafin da kuma sanya idon.

Hannu ta sanya zata daga hoton don ganin date din jiki sosai

“Don’t dare touch it” ya fada da kakkausar muryar data ankarar da ita yana wajen,tadan zabura kadan tana juyowa,idanunta suka sauka akansa, sipping coffee dinsa yake hankali kwance,idanunsa kan tv din daya sauya tasha zuwa ta news,kai baka ce da ita yake magana ba.

Wani mugun kyau yayi mata,sai ta dinga jin inama ace zai rungumeta,ko ita ya bata wannan damar?,qoqarin dai daita kanta tayi,sannan ta fara takowa cikin salo na canjin tafiya zuwa inda yake zaune

“Welcome home” ta fada tana sakar masa murmushi,saidai kuma abun haushin,baiko kalleta ba bare ya fahimci kwainanen da takeyi,hasalima tambaya ce ta biyo baya

“Who gave you permission to enter my room?” Tambayar data sanyata yin sak,kafin kuma ta saki murmushi tana ci gaba da takowa

“am your spouse fa,mene ne a ciki?” ta fada tana isowa dab dashi,shirinta shine ta zauna daura dashi din.

Idanun nan nasa masu matuqar nauyi da kwarjini ya daga ya watsa mata su,abinda ya sanyata tsaiwa ta kuma kama kanta,bata sake gigin yunqurin zama kusa dashi ba yadda taso a baya,kamar bai shirya yin magana ba,saidai zuciyarsa tana gaya masa,ita kadai ce a yanzu zata zame masa damuwa cikin gidan baiyi wasa ba,itakam waccan bashi da damuwa da ita ya tabbatar,don ya gama da babinta,unaisan ke kallon kanta a ta cika macen da zata kutso kai tayi tarayya dashi cikin rayuwarsa,abu mafi wahala da tsada da diya mace ke nema ko ta samu daga wajensa,yana jin komai nasa kebantacce ne na musamman

“Am warning you for the second time,stay away from me,banason kutse cikin al’amurana,Live your life,I live mine,banason kutse cikin al’amurana,ki kiyaye” ya fada da sautin dake nuna gargadi mai qarfin gaske.

Har cikin zuciyarta maganganunsa suka soketa,tanason ta maida masa raddi amma kuma ya mata kwarjinin da ko bakinta ta kasa motsawa

“Am saying in respect, get out of my room” ya fada with his husky voice.

Jikinta a sanyaye ta fara takawa zuwa bakin qofa,gefan ranta a quntace,sai ya ajjiye cup din idanunsa na sauka kan tray din data ajjiye,ya janyo wata qaramar dawer daga jikin kujerarsa,wadda ba kowa ne zai kula da ita ba,ya ciro kudi kusan adadin wanda ya baiwa maimunatu ya dora mata a kai,sannan yace

“Dawo ki dauke kayanki” cak ta tsaya,kamar ba zata dawo din ba saboda yadda qwalla ke neman cika mata ido,to amma ba zata iya tafiyar ba,saboda yadda muryarsa ke iya canza duk wani nufi naki,ta dawo ta dauka din kamar yadda yace sannan ta fice.

Cup din ya dangwarar a wajen,yana furzar da iska daga bakinsa,shi kansa yana jin baiyi dai dai ba,amma kuma hakan shine dai dai a wajensa,gwara tun wuri kowacce a cikinsu tasan cewa bata da gurbin zama cikin rayuwarsa,yafi kyau ya nesanta kansa dasu akan ya sake musu su sanya ransu a kansa.

Tun a falonta ta watsar da komai suka tarwatse sukayi nasu waje,ita kuma tayi daki da sauri tana sakin kuka,wayarta ta laluba,ta kuma kira anty talatu,kukantanya daga mata hankali sosai,don da qyar ta iya ta mata bayanin abinda ya faru.

Murmushi anty talatun ta sake,alamun hankalinta a kwance yake

“Hmmmm,yaro man kaza,ke haka kike unaisa?,baki da haquri?,ga shegen gaggawa?,daga fara wasan saiki saare?,waya gaya miki abu mai daraja da tsada yana samuwa ta sauqi haka?,in just a minutes amma kin gaza?,haka zaki nunawa kishiyar taki har ta fuskanci kema kin kasa?,to kiyita kukan,idan kin gama kya kirani na fada miki abinda zan gaya miki” sai ta kashe wayarta,itama bata sake kiran nata ba,sai data gama kukan nata,ta kuma huce sannan tayi kiran nata.

********Cikin kwanakin ya maida kansa busy qwarai da gaske,duk wani tunani nasa da kulawarsa na ga companies dinsa dake nan gombe kano da kuma lagos,kusan tun daga ranar yama mance dasu cikin lissafin rayuwarsa,basu kuma sake haduwa da kowacce a cikinsu ba,kamar yadda suma kowacce rayuwa take a sassanta ba tare da ‘yar uwarta ba,duk da cewa sau tari maimunatu takanyi kamar ta leqa su gaisa da unaisan,amma kuma sai taji tsoron yin hakan,musamman idan ta tuna da me gidan kansa

“Qila itama irin halinsa ne da ita” abinda zuciyarta take raya mata kenan,saita juya ta koma.

Daga gidan dr marwan ake kawo musu abinci kullum,safe rana dare babu gajiyawa,kullum maimunatun ke amsa,ta kuma barshi saman dining na main parlor na gidan idan ta diba yadda zai mata,wanda yawanci ma idan ta diba na rana ita shike kai mata har dare,bata sake neman wani kalar abincin.

Ba kasafai yake dawowa gidan da wuri ba,yakan kai tara ko goma,kuma daya dawo ya haye samansa yake rufewa,idan ba wani babban uzuri ba baya saukowa sai washegari,takwas na safe ya fice sabgoginsa,saidai lokaci lokaci yakan sauko ya duba cikin gidan ko akwai wata matsala,sai ya tabbatar da babu wani abu da ake buqata sannan ya sake komawa,a hakan suka kwashi sati biyu cur,a ranar suka tashi shuru babu saqon abinci,dama kuma maimunatu ta tsammaci hakan,don haka qarfe sha daya saura bayan tayi wanka,ta danyi gyare gyarenta cikin daki wanda basu da yawa,tayi wanka ta shirya kanta cikin wata army green din atamfa me maroon din ado saita fita zuwa kitchen don samawa kanta abinda zata saka a bakinta.

Ruwan tea ta dora,ta kuma hada kayan qamshi kamar yadda ta koya daga wajen baba tabawa,sannan ta juya ta laluba dankali ta debo bayan ta kwashe wadanda suka lalace saboda kwanakin da suka dan dauka ba’ayi amfani dasu ba,ta dauko qwai guda biyu ta fara aikinsu.

Tana aikin tana kuma tunane tunane,abinda ya zame mata jiki,a zaman kwanakin da tayi cikin gidan,zaman kadaici,da za’a irga adadin tunanin da tayi zata tashi wani dan qaramin littafi,ta saqa burika masu yawa da takeson cimmawa a rayuwarta,wadanda bata da tabbas din wanzuwarsu,tunda dai bataga hanya ko qofar da hakan zata kasance ba,nan din tana wani zama ne kwatankwacin zaman mutumin da aka kai prison.

Bata dauki lokaci ba,ta gama komai,tuntuni ta juyr tea din a flask,dankalin kuma ta zuba akwando don ya tsane,ta matsa gaba tana neman plate da zata xuba,tana ta kokwanton ma zata iya cinyeshi kuwa.

A dan hanzarce ta turo qofar kitchen din saboda wata mahaukaciyar yunwa dake sakadar cikinta,ta duba saman dining inda kullum take tadda abinci ta diba ba tare data damu da wanda ke girkawa ba.

Motsinta ya sanya maimunatu dake dauko plate dakatawa ta waiwayo,idanunsu suka hadu waje guda lokaci guda,lokaci na farko kenan da kowacce taga ‘yar uwarta,kuma kowacce a cikinsu jikinta ya bata.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: *HUGUMA*

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply