Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 46


Gurbin Ido 46
Viral

46

Tunda ya dawo gidan baba tabawa tasan ya shigo,ta kuma gayawa maimunatu a fakaice indirectly cewan ya dawo din,ta yita zuba ido taga ta fita yi masa sannu da zuwa ko wani abu makamancin hakan amma bata gani ba,tunda tasan unaisa bata nan,dazun da ta zaga baya tana tsinkar musu lemon tsami taga fitarta,babu kuma alamun ta dawo.

Abun nata cin ran baba tabawa,har zuwa lokacin da suka zauna cin abincin dare,ta dubi maimunatu

“Waiku kam…..haka akewa miji?,ya fita ya wuni fafutukar nema muku abinci,ya dawo amma ko arziqin sannu da zuwa a gaya masa bai samu ba?,sa’annan ace abincin da zaici ma a gidansa ya gagaresa a kasa sammasa?,anya kuwa maimunatu?,ta yaya zaki bata dukka yardar da anni ta baki?,ta dora duk wani fatanta da burinta akanki amma kina neman bata kunya?” Qasa tayi da kanta,tana jin kunya da nauyin suna kamata tun gabanin xancan ma yaje kunnen annin,tabbas tayi kuskure da gaske,to amma kuma shi dinne…..ba irin sauran mutane bane,batasan ta yadda zata fuskanci bahagon mutum irinsa ba,yau inda ace shi din kamar hisham yake to da da sauqi sauqi,amma…..he’s totally different from what they are seeing about him,ba abu bane mai sauqi tunkararsa

“Kiyi haquri baba,baice yana buqata ba”

“Kin taba nuna damuwa ko gwada kaiwar bare ki Fatima hakan?,bari na fito miki a mutum maimunatu” baba tabawa ta fada tana gyara zamanta,abinda ya sanya maimunatu tattara hankalinta waje daya

“Gaba daya na fuskanci inda zaman aurenki ua dosa,bansan na abokiyar zamanki ya yake ba,a gajarce zan gaya miki,ba’a yankewa mutum hukunci ba tare da ka ma’amalanceshi ba,ki sauya,ki zama kamar kowacce mace a gidanta,ki sauke naki hakkin da nauyin,ko meye zai taso a gaba….ko meye zai biyo baya zaki fita a ciki,kiyimin alqawari daga yau zaki canza,inason ganinki kamar kowacce macen auren maimunatu,ina miki sha’awar hakan,na san ja’afar,yana da zuciya me kyau wani abune daban ya canzashi,kuma ina kyautata zaton duk wanda ya aro wani hali da ba nashi ba,rabashi dashi abune me sauqin gaske,zaki canza maimunatu?” Kai ta gyadawa baba tabawa a hankali,tana sake jin nauyi,saboda tana ji a ranta da gasken butulci take son tayi,tana qasan inuwar alfarmarsu,ta samu rayuwa me kyau me cike da gata,sannan ta kasa ciyar da dansu abincin da shine ya siyo shi?,bayan duka duka bata zaman wata biyu ma cikin gidan?.

Da kanta baba tabawa ta shirya abincin cikin wasu sababbin warmers masu kyau

“Dauka maza kikai masa,daga yau babu ruwanki da abokiyar zamanki,duk sanda kika fuskanci yana da buqatar abinci kuma bata nan,bata kuma bashi ba,koda ba ranar girkinki bane dauka ki bashi,ke Allah zai bawa ladan”.

Daki ta koma,ta zabo hijab cikin hijabs dinta ta sanya,ba abinda hijab din keyi sai qamsin turaren wuta na kaya,ya kuma amshi fatarta qwarai,kalar blue black,da kallo baba tabawa ta bita sanda ta fito,kamar tace mata ta canza mayafi a maimakon hijab din,amma sai kuma ta canza shawara ta qyaleta.

A hankali ya sauke ajiyar zuciya,sannan ya tura hannunsa cikin sumarsa yana yamutsata,hakanan yaji kawai komai baya maaa dadi,sai yakai hannunsa guda daya ya rufe system din dake gabansa ba tare daya damu da yayi shutting down dinta ba,duk da muhimmancin hakan,sai ya koma a hankali ya jingina bayansa da kujerar da yake zaune,ya kuma hade yatsunsa waje daya yana lumshe idanuwansa.

Wani irin bugu zuciyarta take sanda takai step din qarshe na benan,tana ji kamar ta koma,amma kuma idan tayi hakan bata kyauta ba,kamar ta wofantar da maganar baba tabawa ne,ci gaba tayi da takawa cikin tsoro da fargaba,tana tafiya kamar ba zata kai qofar da zata sadata da ainihin falon ba.

Sanda ta isa qofar sai taja ta tsaya cak,ta runtse idanunta da qarfi,a karo na farko zata fara taka sassansa,batasan da wacce fuska zata kalleshi ba,tsoronsa yana nan fal cikin zuciyarta,tanason baiwa kanta qwarin gwiwa,ta dora hannunta saman handle din,ta runtse idanunta gami da dauke numfashinta sannan ta tura ta sanya kanta.

Daga inda yake zaune miqe da qafafunsa saman table din gabansa idanunsa a rufe yaji an motsa qofar,saidai duk da haka hakan bai sanyashi motsawa ko bude idanunsa ba,a zatonsa unaisa ce,wadda ta gaza haqurin zuwa wajensa da ziyartarsa lokaci lokaci,bayan ya riga daya tabbatar mata gaskiyar abinda ke ranshi gami da bata zabi.

A hankali sassanyan qamshin da ya hanashi sukuni wunin yau,ya kuma wuni dashi cikin jikinsa ya fara cika masa hanci,ya kuma gauraye da sallamarta cikin siririyar muryarta din nan mai dauke da wani amo na musamman,ba tare daya shiryama faruwar hakan ba ya soma bude idanunsa da suka sauya launi saboda mintunan da suka dauka a kulle.

Fes ya sauke idanunsa a kanta,cikin shigar da yawanci shaheedansa ke yinta,shigar da yakan tsokaneta da ita zamanin da suna raye

“I want to see my wife gani na haqiqa….. please madam, remove it” murmushi take jifansa dashi,sannan ta zare din tana fadin

“Am all yours,and belongs to you”.

Haka kawai ya samu kansa da gaza dauke idanunsa daga kanta,wani abu na masa yawo tsakiyan kai kamar ana yamutsa kwanyarsa,duk da cikin hijab take amma hoton dazu ke masa yawo cikin idanunsa,ya qureta da kallon dashi kansa yasan idan da ace ita din ba halaliyarsa bace ya kauceea koyarwar addini,baisan me ya sanya masa qulafucin kallonta haka ba.

cikin matuqar juriya da kuma dauriya take bawa kanta confidence,abun dazunke tabata,tana jin kakar qasa ta tsage mata ta shige,ko kuma tayi fiffike ta fice a dakin,ta iso gab dashi kana ta sulale a gabansa ta tsugunna,abinda ya bawa turarenta damar isa gareshi da kyau

“Barka da dare” tayi maganar da wani irin tune,sai ya tashi ya zauna sosai yana sauke sambala sambalan qafafunsa daga saman table din zuwa qasa

“Barka” ya amsata a taqaice,bata tsaya jiran cewarsa ko wani abu ba ta fara fidda warmers din,ya bude baki kaman zaiyi magana kiran jabir ya shigo wayarsa,sai ya maida hankalinsa ga amda wayar,inda ita kuma hakan ya rage mata wani mugun nauyi da takeji an aza mata tun farkon shigowarta falon,rawar da hannayenta keyi suka ragu,ta fidda koma ta kuma yi serving dinsa ta jera komai cikin nutsuwa,sai ta miqe ta fara takawa zata bar falon,cikin ranta cike da fata da addu’ar kada wani abu ya tsaidata.

Dan binta yayi da kallo kadan yana karantar tafiyartata duk da amsa wayar da yakeyi,tamkar wata me tafiya saman rairayi ko yashi mai laushi,duk da bai iys ganin qafafunta saboda hijabin da ya saukar mata,amma kuma yanayin tafiyarta kawai zai gaya maka qafafunta akan tsari suke,janye idanunsa yayi yana jan dan qaramin tsaki,tsakin da ya bayyanarwa jabir ta cikin wayar

“Lafiya?” Ya tambayeshi a taqaice

“No… it’s not a matter,ina jinka” yayi maganar yana sauke dubansa ga abincin,wanda tuni yaja ra’ayinsa,bai kuma iya gama wayar ba ya zamo a hankali daga saman kujerar,ya sanya spoon din data ajjiye masa ya diba ya fara ci.

Har cikin ransa yaji nutsuwa da abincin dari bisa dari,dama baba tabawa zabinsa ce akan abinci,don haka duk wani tsohon cinsa ya tashi,yaci abincin sosai fiye da kima,ya kuma kwantar da tsohuwar yunwarsa,haka nan ya dinga jin wata nutsuwa na saukar masa,ba shakka samun abinci gamsashe ma rahama ne,duk wata gajiya da kasala da yake ji fiye da rabinta ta kama gabanta,sai ya samu kuzarin yin aikinsa fiye da dazun,ya sake kunna system dinsa,yaci gaba da nazarin meeting dinsu na dazu wanda tuni PA dinsa yayi documenting komai ya aiko masa,ya dinga cire kusakuran da yayi a dazun,lokaci lokaci yana dan jan tsaki,baisan ya akayi gaba daya dan qanqanin abu irin wannan ya dagula masa lissafi ba,saidai duk da hakan a yanxun ma idan ya tuna sai yaji tsigar jikinsa tadan zuba,yakan dan lumshe idanunsa kadan kana ya bude ya ture komai yaci gaba da aikinsa.

Binta da kallo baba tabawa tayi lokacin da tayi sallama take shigowa falon,sai taci gaba da kallonta baki bude,har ta iso tana zubewa saman kujera

“Wash” ta furta ba tare da tunanin komai ba,ta fadi kalmar ne saboda yadda taji kamar an bubbuge mata gabbanta,uwa uba kuma gudun zuciyarta daya qaru wanda sai a yanzu take qoqarin sai saita kanta.

Hijabinta ta zare ba tare data lura da kallon da baba tabawa ke binta dashi ba,ta isa ga fridge ta bude,ta fidda ruwa me sanyi saboda yadda takejin maqoshinta ya bushe sosai,bata buqaci cup ba ta balle murfin ta fara sha a hankali,idanunta na hango mata shi cikin falon nasa da bai fiya haske ba,cikin wata abaya ta maza

“A haka he’s very calm and quiet,amma macijin sari ka noqe ne” ta fadawa kanta da kanta tana cire robar daga bakinta,ta dora ragowar saman fridge din sannan ta juyo.

Sai a sannan ta lura da kallon da babab take mata,ta kuma tsargu,amma kafin ta tambaya ita ta rigata

“Har me?,wai har kin dawo?” Kai ta gyada mata tana neman wajen zama,hannu tasa ta kama baki,sai kuma ta kada kai

“Nidai nasan ba’a ajewa miji abinci a taho a barshi dashi”

“Aiki yake baba,kuma waya ma yake amsawa,so yana buqatar space,may be wayar ta sirrice” ta fada har zuciyarta,saidai ita baba tabawan ta kalli hakanne da sunan bawa kai kariya kawai

“To Allah ya kyauta” yadda baban tayi sai duk maimunatu taji bata ji dadi ba,saboda itama baban kamar bataji dadin yadda tayin ba,to amma kuma ta yaya zata iya zama dashi a muhalli guda?,ko abincin data kai din kawai tasan karambani tayi da kuma bin umarni,tana da yaqinin zaiyi wuya yacu,ta fahimci kamar yana da jin kansa,izza da kuma qasaita,bai taba neman wani abu daga garesu ba cikin gidan dai dai da ruwan sha kuwa,sai taja wayarta kawai ta kunna data tahau sabon Whatsapp dinta,ta kuma fara da yiwa qawayen nata guda uku sallama.

Taci sa’a kuwa ta samu afrah a online,cikin mamaki take tambayar da gaske itace,sai suka zarme da hira,wadda ta daukesu lokaci mai tsaho,daga bisani sukayi sallama bayan ta bata labarin latest Korean dramas masu zafi da suka fito.

Kai tsaye ta wuce Vidmate ta saukesu masu yawan gaske,saidai tana tunanin yadda zata kallesu a nutse ba tare da sun hanata bitar karatuttukanta na makaranta ba.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram:

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply