Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 48


Gurbin Ido 48
Viral

48

Sai daya jima da barin wajen sannan ta tashi ta wuce dakinta,ruwa ta hada tayi wanka,sai taji dadin jikinta,kaya ta saka marasa nauyi cotton wanda bazasu takurata ba,komai takeyi cikin kasala take jinta,sai kawai ta haye gadonta,ta lumshe idanunta.

Fuskarsa da qamshinsa ne suka fara bijiro mata,the way daya dinga treating dinta,yana kuma watsa mata nauyin idanuwansa da suke da wani irin magnet a cikinsu me qarfi,wani juyi tayi,wanda cikin rashin sani ya sanyata danne hannunta dake dan zugi har yanzu,sai data ce wash Allah.

“Wai meye haka?” Ta jefi kanta da kanta da wannan tambayar,sai taja qaramin tsaki,ta miqa hannunta ta dauko wayarta dake saman kanta,videos din data dauko ta shiga,ta zaba drama daya ta kunna ta fara kalla.

Bata dauki dogon lokaci ba ta fahimci zaa buga soyayya sosai,abinda yasa ta tattara hankalinta akai,tana kuma biye dasu,lokaci lokaci tana sakin murmushi,a qalla tayi kusan awa uku sannan barci ya soma fusgarta,babu jimawa kuwa ya dauketa gaba daya daga duniyar nan zuwa tasa duniyar.

Sau biyu baba tabawa na leqota don taga ko lafiya?,duk sanda ta leqo din sai taga wayarta tana yi,sai ta koma ga zatonta idanunta biyu,kallo kawai takeyi.

Tunda ya fita yana masallacin,ya kuma samu gaba kamar yadda yakeso,a gabansa liman ya iso,ya gabatar da kuduba aka kuma tayar da sallar,sanda aka idar ya samu ganin abbi,saidai kuma yana ta fama da mutane,don haka ya masa sallama yace sa hadu a gida.

A harabar masallacin ya suka gamu da jabir,abinda ya sake tsaidashi kenan,ganin maganar tasu ba zata qare ba,sai ya kira driver dinsa yace yazo ya dauki motar suka wuce a motar jabir din.

Gidan mahaifin jabir qanin abbi suka fara zuwa,suka gaida uncle usman da matarshi,sun jima suna hira dashi kafin su baro gidan,suka wuce gidan abbi dr marwan.

Kamar ko yushe sassan ammansa ya fara shiga suka gaisa,ya taras da amna ta tashi a bacci,tana ta taba rigimarta,ganinsa yasa ta watsar da komai ta dafeshi tana fadin xata bishi,yarinyar nason binsa,shima kuma a duniya yafi kowa son kasancewa da ita a muhalli guda,to amma kuma idan yace zai dauketa wa zai kaiwa ita?,wa zai kula masa d ita?,ya tabbatar ba zata taba samun kwatankwacin kulawar da take samu ba a wajen su amma,bai amsata ba ya sabeta ya wuce wajen ammi suka gaisa,sannan ya wuce sassan mutuniyar tasa anni yana sabe da amnan yana mata tambayoyi da suka shafi karatun makarantarta,tana ta bashi amsa dai dai,abinda yayi matuqar faranta masa.

Da sallama a bakinsa ya shiga sashen,mutum uku ne zaune,anni jabir da ya riga shi yo gaba sai kuma hafsat,wadda sallamarsa ta sanyata rudewa gaba daya,ta kuma tattaro dukka nutsuwarta ta dawo da ita jikinta,gami da janye qafafunta data miqe a dazun tana kadasu,ta sanshi ta kuma san halinsa sarai,baya tolerating nonsense,har ya qaraso wajen tana satar kallonsa,tana jin kamar ta hadiyeshi,kishin unaisa da maimunatu yana saukar mata,kada ma unaisa taji labari,don ta samu labarin maimunatu ba mazauniya bace,makaranta take zuwa,bugu da qari tana ganin tayi qanqantar da zata bata wuya wajen shigowa gidan da kuma cimma muradinta.

Cikin salo iyayi da kuma kwainane ta gaidashi,kansa na wani sashen ya amsa mata,abinda yayi matuqar qona ranta kenan,saidai tayi biris taci gaba da zama a wajen ba tare data motsa ba,kunnuwanta duka suna ka maganganunsu su da anni

“Lallai da gaske anni tafison wadan nan guys din,kada ma wannan dan mulkin nata yaji labari” ta fadi a ranta,wanda a zahiran zaka dauka danna waya takeyi

“A zuba muku abinci” gyara zama jabir yayi

“Eh nikam a kawo,don nasan zaiyi wuya na samu idan na koma,don batajin dadi,banson cin kuma na yarinyar da aka kawo matan” sai da anni ta waiwaya ta dubi hafsat tace taje ta hado musu abinci a kitchen,ta kuwa miqe da hanzarinta tana aje wayarta gami da jin dadin wannan aiki da anni ta bata tayi kitchen din,sannan anni ta maido kanta ga jabir

“Jikinne har yanxu?”

“Wlh anni,yau da lafiya gobe babu”

“To Allah ya raba lafiya” murmushi yadan saki yana shafa kansa cikin dan jin nauyin annin,baki ta tabe

“Kaga dan nema,ja’iri,wai yau ni ake jin kunya” dariyar da yake riqewa ya qarasa saki,anni anni?,Allah dai yaja musu kwananta.

Kamar taa bar zanca sai kuma ta dubu sashen da ja’afar ke zaune,har yanzu amna na saman cinyarsa

“Allah yasa muji irin wannan labarin a gidan wancan kurman,kema yarinya kya samu kiga ‘yan uwanki ko maraici da kewar da kike ciki zata ragu” yi yayi kamar ba dashi ake maganar ba,kamar kuma baiji ba,duk da maganar ta tsaya masa a rai

“Ya jikin maimunatun?” Ta sake zungurarsa da magana ganin baice komai ba,dai dai sanda hafsat ke fitowa a kitchen din dauke da kwanukan abinci,gabanta yadan fadi,tana son jin qarashe zancen,kada dai ace ciki gareta

“Alhmdlh” ya amsa a taqaice

“Inaga kamar ya kamata tabawa ta dawo hakanan,dama tamin magana kan tanason tahowa” baiso annin ta fadi hakan ba yanzu,ko ba komai yana samun abinci kwana biyu yaci ya qoshi hankali kwance,ya rage zuwa eatery neman abinda zaici

“Ba laifi” ya amsawa anni,dai dai sanda ta iso wajen,ta fara ajjiyewa jabir,sannan ta qaraso inda ja’afar din yake,cikin salo ta duqa tana ajje masa nasa abincin,wanda zubin data masa ma daban yake,in a stylish way ta shirya salad din dake saman abincin.

Hannu ta miqawa amna

“Taho daddy ya samu yaci abinci ko?” Kafada ts maqale tana kallonta

“Ahaf…..wannan ‘yar wulaqancin fa sai wanda ta zaba,wuce ciki abinki” batas anni tafada haka ba,taso zama ne a wajen taci gaba da jin hirarrakinsu,ta kuma morewa kallon ja’afar din,don yau din wani kyau yayi na musamman,kayan sunyi matuqar karbarsa.

Dakin dake opposition da dakin ta shige,ta zare key din dake jikin qofar tana leqensu ta jiki,abun haushin duk yadda ta tsara masa abincin bata wani ga yaci komai ba a ciki,hasalima amna taga ta sanya cokali tana cin abinta,ruwan kawai taga ya dauka yasha,shima ba mai yawa ba.

Ana sallar la’asar daga masallaci gida ya wuce bayan sunyi sallama dasu anni,already dama yayi kiran driver,don haka kafin su idar ma ya iso,ya daukeshi suka wuce,yana mota yana tunanin amnan,duk sanda yazo gidan sai yarinyar tayi attempting din binsa amma tilas take sawa yace mata a’ah,to yau ka harda kukanta,abinda yasa kenan yayi deciding next month ya dauketa su danyi yawo kadan,koda zuwa lagos ne,yasan hakan zai mata dadi,zai kuma debe mata kewa.

Samansa ya wuce direct,ya bude dakin yana kallonsa,gaba daya it’s not in order,komai na dakin bai masa yadda yakeso ba,sai ya koma da baya ya bude daya bedroom din nasa ya sauka a can,kayan jikinsa ya sauya kawai zuwa wata farar jallabiyya ta maza mai sulbi da kuma wide neck,ya hada dukka aikin dake kansa wanda a qa’ida yau zaiyishi a office,amma yau din juma’ar qarshen wata ne,yana basu hutu yawanci duk qarshen wata,musamman idan akwai raguwar aiki sosai a lokacin.

Har zai zauna ya fasa,saboda cikinsa da yaji yana buqatar sanya masa wani abu,sannan kuma yanason jin ya hannun nata,don ya tabbatar a yadda yaji anni na masa magana a kanta yau,tabbas idan wani abu ya faru kai tsaye ma zata iya cewa shine ya qonata.

A nutse yake saukowa daga stairs din,duk inda ya gifta sassanyan qamshinsa yana biye dashi,rigar ta masa kyau ta sake maidashi cikakken mutum mai cikar kamala zati da kuma haiba.

Da tattausar sallama a bakinsa ya shiga falon,baba tabawan ce kadai xaune tana kallo,tana yi kuma tana duba girkinta dake kitchen,duk da abincin ma yau kusan ita daya taci na safen har na ranan,ta rasa wanne irin bacci maimunatun takeyi.

Cikin fara’a ta amsa sallamar tasa ta kuma yi masa maraba,ya tambayeta hannun nata

“Wallahi manya ban sani ba,tunda ta shiga ta kwanta bansan ma bacci take ba sai daga baya” baice komai ba ya miqe,hannunsa cikin aljihun rigarsa,ya nufa dakin nata.

A hankali ya tura qofar ya sanya jikinsa,kamar ko yaushe dakin gauraye da madaidaiciyar iska dake cakude da qamshi iri iri wanda ya bada wani scent na musamman,kasancewar yamma tayi dakin ya rage hasken dake akwai,yaci gaba da takawa zuwa inda yake hangenta a cure waje daya,saidai hasken wayar daketa aiki ta haske fuskarta sosai.

Gab da kanta amma ta bayanta,idanunsa suka sauka tun daga dogayen qafafunta dake harde waje guda,saidai kuma taba motsasu a hankali duk bayan wasu sakanni,da alama mafarki takeyi,don haka take dan motsa hannayenta ma,yawo yaci gaba dayi da idanunsa,yadda take kwancen sai yakega.kamar kwanciyar tata batai dai dai ba,sosai qugunta ya fita ta cikin rigar,sai ya dauke idanunsa da sauri ya saukesu kan screen din wayar.

Minti daya kacal ya tuna film din,one of the best dramas nashi,ya akayi ta nemoshi take kuma kalla?,hannunsa ya sanya ya zare earpiece din dake kunnenta ya maida a nashi kunnen idanunsa still suna kan wayar,lallausan murmushi ya qwace masa,abinda ya qarawa fuskarsa wani mugun kyau,abinda ba kasafai yake faruwa dashi ba kenan,ya tuna scene din,ya tuna wajen,murmushin yaqi daukewa daga fuskarsa,,ya tayar masa da wani tsohon memory da kuma wani sweet moment,sai yaji yana da sha’awan sake kallon drama din,ya duqa a hankali ta saman kanta da zummar dauko wayar ya kashe mata,abinda yasa yayi mata kamad rumfa a saman kanta.

Juyi tayi cikin hanzari tana sakin wata qaramar qara,abinda yasa ta bugeshi,ya kuma fada saman kanta saboda unexpected ta bugeshin,baiyi tsammanin zata motsa ha a sannan,qamqam ta riqeshi,tana tsamamnin cikin mafarkinta ne,saboda shine cikin mafarkin,ta kuma sake gasgata mafarkin takeyi jinsa a jikinta qamshinsa yana shiga qofofin hancinta.

A nutse ya zube idanunsa saman sleepy face dinta,karon farko da sukayi kusanci mai zurfi a tsakaninsu irin haka,har suna musayar numfashi,wanda yake fita da tare da qamshin jikkunansu,yayi gab da ita qwarai,kamar me shirin kissing lips dinta,sosai shagwababbiyar fuskarta ke shiga idanuwansa har yana ganin qananun gashin dake qasan hancinta wadanda suka sanya wajen danyi duhu kadan,cikakkiyar girarta da ta kusa hadewa da ‘yaruwarta,siraran labbanta da suke dauke da wasu irin Pink lips masu daukan hankali.

Wani abu ne ya motsa zuciyarsa,har sai daya saki wasu irin tagwayen numfashi guda biyu a jejjere kamar mai sheshsheqar kuka,yanason zame kansa data zagaye hannayenta dashi saidai ya fuskanci mafarki take,kamar ma kuka kuka,saboda yadda shagwababiyar fuskartan nan ta narke gaba daya,ci gaba yayi da kallonta,a hankali murmushi ya soma maye gurbin yanayin kukanta,ya zubawa dan qaramin bakinta daya soma motsawa idanu

“Kayi haquri…….”
“Yaa hisham” sunan ya fita can qasa,shi kansa motsi da dan qaramin fitar sautinta yabi ya fahimci me take cewa,mamaki ya cikashi,hisham?,hisham kuma take kira cikin mafarkinta?,for what reason?,fuskarta yaci gaba da kalla nasa yanayin na sauyawa ba tare daya sani ba,a hankali fuskarta ta koma normal mode na masu bacci,da alama ta gama mafarkin da takeyi kenan,sai ya zame hannunta daya nutse a qeyarsa cikin lallausar sumarsa,ya miqe tsaye yana ci gaba da kallonta bayan ya goye hannunsa a qirjinsa,kiran sunan hisham da tayi ya dawo masa,yadan rufe idanunsa sannan ya sake budewa,wani abu yaji yadan taba ransa,sai ya miqa hannu ya jawo hannunta dake boye a gefanta,zugi ya ratsa tsakiyar baccinta,abinda ya sanyata farkawa kenan.

Sai data bude ta kuma rufe idanunta sau uku don son tabbatar da cewa yanzun ma mafarki ne ko ido biyu,yaji alamun ta farka amma kuma baiko daga kansa ga dubeta,yana dai nazarin hannun nata ne,sai daya tabbatar batayi ko alamin tashi ba sannan ya sake mata hannun,a hankali kuma ya aza mata idanunsa masu nauyi da suka tilastata janye nata,ya basar ya kuma motsa kaman zai fita sai kuma ya dakata

“Karki qara kwanciya bakiyi addu’a ba,that’s why kuke rubbing mafarkai” yana kaiwa nan ya taka sannu a hankali ya fice.

Idanunta ta waro waje tana bin hanyar daya wuce da kallo bayan ta tabbatar da fitarsa,kada dai yana tsaye ta gama mafarkin da tayi yanzu,saita cusa kanta tsakiyar pillow tana son tuna me da meye ya faru cikin mafarkin,tsahon minti kusan biyar kafin ta sake daga kanta da sauri ta kalli agogo

“Kai” ta fada da sauri tana wantsalowa daga gadon,ganin lokacin salla ya qwace mata sarai.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram:

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply