Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 51


Gurbin Ido 51
Viral

51

Shuru ne ya biyo baya cikin motar,tsakanin unaisa da maimunatu babu wanda ya cewa da dan uwansa uffan,sai ogan daketa amsa waya cikin wani yare da dukkansu basu gane wanne ba,daga bisani unaisa ta fahimci turkish language ne.

 

Girman kai da shegen son girma yasa unaisa taji zafin yadda maimunatu ta shareta,a ganinta maimunatun bata isa tayi mata haka ba,yarinyar gaba daya nawa take?,sa’annan kuma wace da ita?,banda martabar aure da ja’afar din daya hadasu qarqashin inuwa guda,bata jin maimunatu takai koda matsayin ‘yar aikinta ma bare zaman kishi,amma zata nuna mata ita din ba komai bace,sannu sannu bata hana zuwa ai,muddin ta samu ja’afar a hannunta sai ta gane shayi ruwa ne.

 

Itakam maimunatu gaba daya hankalinta na kan wayarta,chart suke da afrah tana bata labarin ahmad dinta,a zahiri gwasale afran take,amma a badini yadda salon soyayyar tasu take shine yake burgeta,abinda ya sanya murmushi kenan saman fuskarta lokaci lokaci,har bata maida hankali ga unaisa dake gefe tana ji da girmanta ba,bare ja’afar dake amsa waya cikin yaren da batasan wanne bane,saidai lokaci bayan lokaci idan yayi wata maganar lallausar muryarsa na ratsawa cikin hankalinta da yayi nisa a wajen jin labarin da afra ke bata.

 

Karamin tsaki unaisa taja,har cikin ruhi da zuciyarta tana sake jin zafin shariyar maimunatu,gefe guda kuma yadda yarinyar ta canza ya tsaye mata a rai,ta lura idan ta tsaya wasa sai wankin hula ya kaita dare,dole tayi amfani da dukka wayewarta da kuma iliminta da kuma gogewarta tayi abinda take ganin shi ya kamata.

 

Qaramar ajiyar zuciya ta sauke sanda motarsu ta tsaya a babbar mashigar gidan dr marwan,drivernsu ya saki horn me gadi ya taso ya bude musu,cikin girmamawa yaja da baya kana ya rusuna musu har xuwa sanda motar ta qarasa shigewa yaja gate din ya kulle.

 

Tun kafin motar ta tsaya suka hangi abbi shi da ammi,tana riqe da briefcase dinsa da alama rakiya tayo.masa zaya fita,wannan kusan dabi’ar dukka matan gidance,girma ko shekaru basu sanya sun canza ba,abbi din yana riqe da hannun amna,wadda tayi kyau cikin dinkin atamfa straight gown,kanta babu dankwali saidai a taje yake cikin band da aka matse mata yalwataccen gashinta dashi,ta noqe kanta a kafada,da alama rigima take tabawa.

 

Dukka hankalinsa nakan yarinyar tasa,don haka yayi sallama da wanda suke magana a wayar ya kashe yana sanya wayar cikin aljihun rigarsa,dai dai sanda motar ta tsaya ya bude yana fitowa kamar yadda suma su maimunatu suka fito,dukka suka dunguma zuwa inda abbi da ammi suke tsaye,wanda hankulansu yayi wajen motar tun tsaiwarsu.

 

Idanu amna ta fiddo sanda ta hangi daddynta ta kuma hangi anty maimoon,da sauri ta zame hannunta ta manta da rigimar ma da take wa abbi ta nufesu da matuqar sauri,saidai tana isa dab dasu ta yanke ta nufi maimunatu wadda ta bude mata dukkan hannayenta fuskarta fadade da wata lallausar fara’a da murnar ganin yarinyar,ta dauketa cak suna dariya su duka

 

“To alhamdulillahi,shikenan rigima ta qare,an fansheni” abbi ya fada sanda suke sake qarasowa wajensa,ammi da maimunatu suka saki murmushi,banda ja’afar da ya dauke kansa daga kansu,karon farko da amna ta taba ganinsa ta wuceshi,koda waye ta gani kuwa shine mutum na farko da take fara zuwa wajensa kafin kowa,sai kuma unaisa da wani haushi ya saukar mata,wanda ya bayyana har saman fuskarta,ta kuma kasa danneshi.

 

Maimunatun ce ta fara isa gabansu,ta zube tana gaidasu,cikin nuna kulawa suka amsa,tadan miqe dauke da amna a hankali sanda ja’afar ya iso shima ya sunkuya yana gaidasu,bata tsaya jiransu ba tayi gaba abinta da amnan zuwa sashen amma,amna nata zuba mata zance yadda ta saba,ita kuma tana biye mata suna dariya,har suka isa sassan amma.

 

A falo suka gaisa da masu aikin amma cikin mutuntawa,suka shaida mata tana wanka,amma dab take da fitowa,sai ta zauna saman carfet tana dakon fitowarta.

 

Sallamar da akayi cikin falon ta sanyata daga kanta,hisham ne ya shigo,sanye da jallabiya, da alama yau din bashi da niyyar fita kenan,duk da ranar ranar aiki ce bawai weekend ba

 

“Matar babban yaaya” ya fada cikin dan zolaya yana wucewa gaban freezer din amma dake falon ya bude yana duba abinda ya shigo dauka din

 

“Barka da safiya” ta gaidashi cikin mutuntawa da kuma jin nauyi

 

“Barka kadai yayarmu…..jiki yayi sauqi kenan?”

 

“Alhmdlh ya hisham na warware”

 

“Allah ya qara afuwa……rigima’u,yau kuma me aka tashi dashi?,wa kike juyewa rigimar safiyar alhamis din?” Yayi maganar yana duban amna dake zaune gefan maimunatu,saidai ta kanainayeta gaba daya,duka gwiwoyinta na kan cinyarta,kamar jira take ta miqe ta isa gareshi,da niyyar fita ya shigo,amma dole amnan ta tsaidashi ya samu waje ya zauna a nan,ya ballowa kansa ruwa kenan.

 

Maimunatu na daga gefe tana murmushin jin yadda rigima ta barke tsakanin hisham din da amna,sauqin kansa da yadda ya iya tafi da rigimammun yara yana burgeta,gaba daya ya maida kansa shima kamar amnan,dai dai lokacin da ja’afar ya sako kansa zuwa falon.

 

Akan fuskarta idanuwansa suka fara sauka,fuskar dake cike da fara’a,jerarrun fararen haqoranta da suka bayyana,da wata lobawa ta musamman dake tsakiyar habarta,hasken fatarta ya sake fitowa sosai ta tsakiyar fuskar hijabinta,tana gab da dago idanunta don amsa sallamarsa ya kauda kansa,ya maida dubansa ga amna,wannan karon sauri tayi ta sabule daga gefan hisham da take zaune,ta nufoshi da sauri tana wara hannuwanta

 

“Dadddyy” tana isowa ya dauketa cak a hannunsa yana kallon fuskarta dake matuqar kamanceceniya da tasa,yasa yatsuntsa guda biyu yaja kumatunta,cikin low sound wanda ita daya zata jishi yace

 

“Naqi wayon,babu wani daddy,tun dazu ba’ayi welcoming daddy ba sai yanxu?” Wuta ta langabe masa fuskarta a narke

 

“Sorry….sorry dad” ba tare da ya shirya ba murmushin gefan baki ya kubce masa,yadda tayin sai ya tuna masa da maimunatu dake zaune a gefe,kamar ita,koda yaushe aka kamata ko ake tuhumarta da laifi ko aka ritsata haka fuskarta yake komawa,yayi kaman zai kalleta sanda yaji hisham na magana da ita amma sai ya dauke kansa,saidai kunnensa na sauraren hirarsu,yana mamakin yadda take dan sakin jiki haka da hisham din.

 

Yana qoqarin zama amma ta fito,maimunatu ta dubeta cikin girmamawa tana mata sannu da fitowa,fes ds ita cikin atamfa super exclusive,kai baka ce itace ta haifa kamar ja’afar ba saboda tsabar gayu da gyara.

 

Waje ta samu ta zauna lokacin hisham ya kama hanyan ficewa

 

“Me yasa ne baka tafi ba hisham?” Amma ta jefa masa tambayar tana zama,fuska yadan yatsina yana satar kallon ja’afar,suka hada idanu kuwa,ja’afar din ya watsa masa harara,sai yadan saki dariya hisham din,kafin ma yace komai amma tace

 

“Kada ka daka ta tashi,dama ka sani ba zuwa yake ba,tun can baya ma sai na matsa sosai yake zuwa,yanzun ma ya daina gaba daya” gyara tsaiwarsa yayi

 

“Taron family dinne anni….. sometimes kawai gulma ne da kuma daukan bangaranci,ga yarinyar can fawwaza…..ta cika naci wlh,idan ma naje ba barina zatayi na sake ba” ya qarasa maganar yana sanya kansa wajen,dauke dubanta amma tayi daga kansa tana cewa

 

“Allah ya kyauta” sannan ta maida kallonta ga ja’afar

 

“Ya kamata ku dinga daurewa kuna zuwa koda ba zama zakuyi ba,ba zai yiwu ace ko da yaushe saidai matan suje ba,nima banda yau na tashi banajin dadin jikina ai babu abinda zai hanani zuwa”

 

“Me ya sameki amma?” Ja’afar din ya fada da sauri cikin nuna tsantsar kulawa,tafin hannunta ta murza kadan

 

“Ba wani abu serious bane,kawai nauyi naji jikina yayimin” motsawa yayi yana miqewa

 

“Noo,bai kamata ace kin zauna ba bakiyi checking me yake faruwa ba,dauko mayafi amma muje a dubaki” qaramin murmushi ta sauke,ta jima da sanin irin soyayya da kulawa da ja’afar ke mata ta dabance ko cikin yaranta,shi yasa komai nasa itama ya fita daban cikin zuciyarta,duk da tana qoqarin dannewa

 

“Ba komai fa,jiki ne da jini,dama ba za’a yita zama haka ba ba’a taba lafiyarka ba,yanzu ba gani a zaune ba muna magana” duk yadda yaso suje amma tace masa aah,dole ya haqura ya zauna,saidai dukka hankalinsa yana kanta

 

“Ina fatan kuna lafiya” amma ta fada,tambaya ce guda daya,amma tana dauke da ma’anoni,kara ya hanata buda tambayar,kai maimunatu ta gyada kanta a qasa cike da kunya da kuma surukuta,yadan saci kallonta,yadda takeyi din kamar yadda shaheeda kema amman,can qasan ransa yaja tsaki,me yasa yake yawan kwatanta da shaheeda bayan ba ita bace?,sai ya miqe yana fadin

 

“Zan shiga wajen anni”

“To ba laifi,ki shiga ku gaisa maimunatu” ta fadi don tasan yawanci direct nan suke fara yowa sai sun gaisa suke wucewa sassan annin.

 

A hankali suke takawa zuwa sassan annin,yana gaba tana biye dashi a baya,tamkar wata maras gaskiya,jifa jifa take satar kallonshi,yadda yake takawa majestically,cikin aji da izza,ba zato taga ya ja birki ya kuma waiwayo,ta daga idanunta a hankali tana duban inda yake tsaye ba tare data iya kallon qwayar idanunsa kai tsaye ba,nuni yayi mata da hannu kan ta wuce gaba,sai ta tako a hankali tazo ta giftashi,ta wuce kamar yadda ya buqata,lumshe idanunsa yayi sanda iska ta kwaso masa qamshinta,wannan qamshin dake maqale a wani bangare na kwanyarsa tun a wancan lokacin,sai ya rufa mata baya,suna ci gaba da takawa daya bayan daya.

 

Yaso yima idanunsa shamaki amma hakan bai samu ba,qwayar idanunsa na biye da duk wani taku nata,ance ido guba ne,kuma dafi gareshi,koda bata waiwaya ba tasan kallonta ake,cikin jikinta takejin idanuwansa bisa kanta,abinda ya sanyata daburcewa gaba daya,ta kuma ji tana hardewa a tafiyar tata,saboda laushi da qafafuwanta sukayi,wannan ya taimaka wajen yin baya zata fadi lokacin da taci karo da wani dan qaramin dutse.

 

Baisan ya isa gareta har ya tallafota ba saida ta samu masauki a jikinsa,qamshinta ya cika masa hanci,fuskarta na kallon sama ne,yayin dashi kuma ya zame mata kamar rumfa,wannan ya sanya idanuwansu sukayi saurin haduwa wajen guda,sai ya zareta daga jikinsa da sauri yana hade ransa tsaf,kamar bai taba dariya ba,ya miqe da dukka tsahonsa ya tsaya sosai yana sake zuba mata arwa,sai ta rasa abinda zatayi,don haka ta bige da gyara zaman hijabinta tana bashi baya,kamar zaice mata wani abu kuma sai ya fasa,ya zarce da yin gyaran murya saboda yadda yaji muryarsa ta maqale,duk wani furuci da zaiyi ya kakare masa a maqoshi

 

“Thank you” ta fada tana daga qafarta zuwa next step,saidai wannan karon ta sanya idanuwanta ne a qasa,gudun maimaituwar faruwar abinda ya farun yanzun,tana shaqar iska me tsaho zuwa hunhunta wai ko zata rage kaifin qamshinsa daya cika mata hanci,wani irin scent dake haifar da wani yanayi me dadi a zuciya da gangar jiki,koda mutum baiso ba,ya kuma canzawa zuciya tsarin tunani,sai taci gaba da zuqar iskar tana fesarwa a hankali,qamshin yana sake yi mata yawo a hanci,yana kuma haduwa da iskar safiyar dake kadawa da wani irin yanayi dake nuna da gabatowar zafi.

 

Muryarsa cikin sautin sallama ita ta maye gurbin tata siririyar muryar,mutum biyu ne suka amsa sallamar,anni da hajiya munubiya(mahaifiyar hafsat),ta ukunsu unaisa ce,wadda a maimakon amsa sallamar tasu,sai ta bisu da idanu sanda suke shigowan.

 

Daga annin har haj munubiyan suma sai da duka bisu da kallo,saidai kowanne da irin kallon da yake musu,ta fannin anni wani farinciki ne ya tsarga mata,zallar dacewa ta hango mai yawa tsakaninsa da maimunatu,ganinsu tare kuma ya ninka kwadayinta nason daidaituwar al’amura a tsakaninsu,ya kuma sake saka mata kwadayin son dorewar alaqarsu,sannan kuma ta hangi wani haske a tattare dasu da take fatan tabbatarsa da kuma dorewarsa.

 

Haj munubiya kuwa wani abu ne yayi mata tsaye a rai mai kama da kishi qyashi da hassada,tun shigowar unaisan ita kadai ta fara jin hakan,a yanzun kuma ya sake qaruwa da shigowar maimunatu da ja’afar din,yadda taga ya sake fresh ya kuma qara haske ya tabbatar msta da gaskiyan labaran da suke ji a kansa na yadda yaketa samun budi,arziqinsa kuma ke dada ninkuwa,wannan shine dai dai lokacin da ya kamata ace diyarta ta kasance daya daga cikin jerin matansa,saidai sam bata mata sha’awar zama mace ta uku kwata kwata,inda da hali so takeyi ta zama mace qwalli daua tilo ga ja’afar din,to amma hausawa sukance da babu gwanda babu dadi,ya kamata tayi wani abu akai,ta kuma gwada sa’arta,koda basu zama du uku ba ya kasance su biyu ne,wannan tunanin yasa ta sake fuskarta sosai tana gyara zamanta gami da dubansu maimunatu tare da sanya baki wajen musu marhaba,tana kuma qara kaifin hankalinta da hasashenta akan fuskar unaisa,take ta fara shinshino al’amura,ta kuma fara kuma tunanin daga inda zata dasa harsashinta.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram:

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply