Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 53


Gurbin Ido 53
Viral

53

A tsaye ta taddashi,da alama anni ta gama tartsatsin nata,bata iya duban fuskarsa ba kamar yadda takejin ba zata iya hada idanu da kowa cikin falon ba

“A nan zaka barsu?” Annin ta jefa masa tambayar

“Driver zai maidasu gida, office zan wuce,akwai wadanda na basu lokaci zamu hadu qarfe daya”

“Ni gida zan wuce,ka saukeni mana” unaisa ta fada tana rangwada kai,zuciyarta fes,tana jin lokaci yayi da za’a kirata amarya da gaske,farincikin da take ciki yasa takeson komawa gida ta baje kolinta,sa’an nan ta fara shirin shiga turakarsa.

Ko kallon gefan da take baiyi ba ya soma yin gaba,don bayajin zai iya daukarta cikin motarsa,dukkansu sunzo masa iya wuya,daga yadda anni ke maganar nan ya tabbatar qararsa aka kawo mata,to amma wace a cikinsu?.

Maimunatu da bata son tafiya yanzu sai tabi bayansu tana son gaya masa a barta sai zuwa anjima,bata tsaya ga unaisa dake sallama da anni tana mata godiya ba tabi bayansa,saidai ta kasa bude murya ta tsaidashi.

Cak ya tsaya jin ana bin bayansa

“Don Allah……zan zauna zuwa anjima” ta fada da sassanyar muryarta dake cike da wani sauti na tsoro,idanunsa ya dan rufe kadan ya bude,har yanzu yana jin wannan zafin na tun dazu cikin ransa,kamar ya juyo ya rufeta da fada,sai kuma yaga fadan me zaiyi mata?,wanne laifi taqamaimai tayi?,yana da tabbacin wanda yakai qararsa ga anni cikin su biyun?,ko kuma itace ta kira khalid da har xai fusata a kanta har haka?,wannan dalilin ya sanya ya gyada mata kai kawai ya fara takawa zuwa parking lot na gidan,yana jin jiyo motsin komawarta ciki cikin murna.

Ran unaisa fes take takowa zuwa wajensa,har zata wuce parking lot ta sameshi,sai kuma ta tuna dazun bata shiga ta gaida ammansa ba,don haka ta juya akalarta zuwa sassan amman.

Tarba me kyau amman tasa aka mata a matsayinta na surukarta matar ja’afar dinta,wadda tayi zuwan farko cikin gidan tsahon aurensu shekara guda,saidai kuma gaisuwar ma a tsaitsaye tayi mata ita,ta gaya mata ja’afar din ke jiranta zasu wuce gida,bata wani tsawwala ba itama sukayi sallams ta fito tana duba agogonta,tasan tadsn bata masa lokaci,amma babu komai zata wanke kanta,wuyarta ta samu kansa daga yau gobe zuwa jibi.

“A’ah,badai har kun fito ba?” Muryar haj munubiya ta yiwa unaisa tsinke,ta waiwaya a hankali,hajiyar na biye da ita a baya kamar ma hanzari take ta cimmata,cikin murmushin yaqe kasancewarta ba wata meson jama’a ba tace

“Eh….”

“Shi yasa naga kinata sauri ai” ta sake fada tana jifanta da murmushi

“Eh,zai saukeni a gida ne”

“Ayyah,gashi kuma naga ya fita yanzu yanzu,dab da zaki fito daga gaida surukuwarki” idanu unaisa tadan fidda tana duban inda ya faka motarsa,wayam babu ita,ta dauke dubanta daga wajen,ranta na mata wata irin suya,da gaske tafiya yayi ya barta?.

“Indai ja’afar ne wannan ba komai bane a wajensa….amma kada ki damu,gidan surukan naki ai cike yake da direbobi” ta furta tana karantar fuskar unaisa.

Unaisan batace komai ba,sai ta sauke jakarta ta fara qoqarin fiddo wayarta

“Ba matsala,zanyi waya a kawomin motata” ta fadi cikin zallar bacin rai,tunda ya tafi ya barta ba zata shiga motar gidansu ko daya ba,don indai motace wannan tafi qarfin duk wata mota

“Uhmmm,ai dama shiryawa hakan akayi,shi yasa ita dayar tace ba yanzu zata tafi ba ai,kekam Allah ya baki wuyan dauka” haj munubiya ta fada tana motsawa gaba kadan kamar zata bar wajen,duk da ba ainihin hakan bane a ranta,tayi hakanne don jan hankali,taa kuwa jaa hankalin unaisan,don daga kanta tayi ta dubeta

“Kamar yaya?” Tambayar tazo ma haj munubiya a dai dai,abinda takeson ji kenan

“Ba zakiji mutuwar sarki a bakina ba,kedai kije kiyita haquri” yadda tayi maganar tana niyyar wucewa sai hakan yaja hankalinta,da sauri ta dakatar da ita,ta jima tanason sanin wasu abubuwa game da gidan dama ja’afar dinta,to amma bata saki jiki ba bare ta saba da kowa ballantana ta samu wasu labaran,sai a yanzun da hajiyan ta tareta da kanta

“Karki tafi,don Allah ki gayan abinda ke faruwa” jimm tayi kamar batason cewa komai kafin tace

“Banyi niyyar cewa komai dake ba,to amma kuma mahaifiyarki hajiya Aayag ta tabamin wani alkhairi da bazan manta dashi ba,shi na tuna a yanzu, shine kuma kawai zai sanya na taimakeki na shiga lamarinki”

“Uhmmm,ina saurarenki” ta fada cikin zaquwa da son jin abinda haj munubiyan zata fada.

Dan waiwaya tayi,tana duban gefe da gefanta,sannan ta maida idanunta ga unaisa

“Magana a nan ba zata yiwu ba,kizo gida ki sameni” kallon haj munubiya unaisa tayi,ta mance diyar wacece ita da zata ce taje gidanta?,lallai tayi araha da yawa,ya kamata ta dawo da girma martaba da izzarta da auren ja’afar yasa ta watsar,abinda yake ta yiwa mahaifiyarta haj Aayah ciwo kenan

“Saidai kizo ki sameni,bazan iya zuwa gidanki ba” murmushi hajiya munubiya ta saki,dama hakan takeso,batason karon farko tace zata je ne,kada ta zargi wani abu a ranta,ko kuma kimarta ta zube

“Karki damu,bana saka manta alkhairi ni din,zanzo in sha Allahu”

“Kamar gobe?,zan aiko da mota a daukoki?”

“A’ah,banason kowa ya zargi wani abu,mu barwa nan da kwanaki biyar ko zuwa rana ita yau,amma fa kafin sannan ki sanya idanu da dukka abinda zakiga ya faru,maganganuna zasu bayyana miki komai” kai kawai ta gyada,sannan ta buda jakarta ta ciro sababbin kudi masu dama ta miqa mata,da murmushi ta karba,ta lura kallon faqiriya take mata,batasan tafi qarfin dukka buqatunta ba,batajin cikin familyn khalid akko diyoyin anni akwai mabuqaci da baifinqarfi ci sha da suturarsa ba,gami da sauran buqatu na dan adam harda ra ra

“Bana buqatar komai a wajenki ‘yar nan,don Allah zan miki,da kuma qaunarki da Allah ya sakamin”

“Na gode” ta fada tana maida kudinta jaka.

Kasancewar bata samu number da take kira ba,tilas ta shiga motar gidan driver ya maidata gida,don ta qagu ta isa gidan suyi magana da anty talatu,sannan kuma ta fara tsare tsare da shirye shiryenta.

*_ADAMAWA_*
_RIGAR UMMARU_

A matuqar rude zaninta a hannu,tana tafe tana qoqarin maida zanin nata ta daurashi dai dai yana sake qwace mata,duk da hakan bata saurara da uban saurin da take zambadawa ba zuwa makwantar sabbin,inda take jiyo muryar laulo yana qwala mata kira babu qaqqautawa,ta kuma tabbatar ba lafiya ba,don dama duka kwanakin musiba da jarrabawa take.

Daga nesa ta tsaya cak tana bin dabbobinta da kallo,wanda da kadan da kadan sun zaizaye sun rame,dukka wannan cikar tasu kyau da kuma qoshin lafiya babu ita a tare dasu,kamar wadanda ake suda,ko kuma annoba ta fadawa.

Gabanta dukan uku uku yahau,ganin nagge guda hudu manya runtuma runtuma aqas babu alamun rai tattare dasu,tun kafin ta qaraso wajen ta dora hannayenta aka idanunta suka tara ruwan hawaye

“Yauwa inna,gasunan,nidai bansan me ya faru ba,ba zagaya zan kama ruwa,dana dawo na tarar babu gajee a wajen,dana duba da kyau kuma sai na samu wannan naggen guda biyar a zube a bakin ruwa,to guda daya ce me sauran rai,na ruga na kira na lami ya yankata ya siya,yace zai aiko miki da kudinki” sulalewa kawai tayi a wajen,tahau taba naggen daya bayan daya,batayi aune ba qwalla ta qwace mata,ta soma sharbar hawaye

“Wadan nan ne sukayi dakon jawosu,tunda kinsan anyi doka an hana yarwa,yana taba amfanin gonar manoma,saiki biyasu” daga haka laulo yayi gaba abinsa ba tare daya tsaya bi takan inna furera ba.

Kamar zata fadi haka don baqinciki,haka ta nufi shiyyar dakunanta ta dauko.musu kudin,qarta qartan samarin fulani ne majiya qarfi sun zuba mata idanu,banda haka bataga abinda zai sanyata biyan wadannan kudaden ba bayan asarar data tafka goma da ashirin.

Da qyar tayi sallar magariba ta hadeta da isha’i,tana zaune a wajen,ita ba addu’a ba ita bata bar wajen ba,sai qiyasta girman asarar da take tafkawa takeyi,tunda maimunatu tabar hannunta komai ya sake tabarbare mata,tun bayan tafiyarta take qunzuge kudaden da anni ke aiko mata,taqi daukan mai mata kiwon,ta tilasta gajee fita kiwo ita da laulo,da sunan gajeen takewa tanadin kudin daki dama na biki gaba daya,don tace bata ga abinda ubanta yake dashi ba da zai kai mata gidan aure.

To gajen dai ba’a son ranta ya fara fita kiwon ba,don dama gaba daya bata saba ba,a sangarce ta tashi,uwa uba kuma ita aure kawai takeso da himu,wannan yasa gaba daya ita da dabbobin suka shiga wahala,babu kulawa me kyau,a hankali suka fara lalure lalure,sai kuma haka siddan suka fara mutuwa,yau wannan gobe waccan,kudaden da taketa tarun su ta dunga diba tana musu maganu tare da karbo taimako na kambun baka da maita,waiko mayu ke kadar mata da garke,ita kuwa gaje ba abinda ya shalleta,idan suka fita kiwon sai tayi batan dabo,shi dai laulo baisan ina take zuwa ba,amma dai bata dawowa yawanci sai gab da zasu koma gida,tun inna furera bata gane meke faruwa ba,har ta gane,qaura wambai ta fadi ina take zuwa amma ta qeqashe qasa taqi fada,har inna ta haqura ta zubawa sarautar Allah ido.

A hankali ta bayyana wani baqon bafullatani take bi su fice daga shiyyar abinsu,haruna kyakkyawan bafulatanine wanda yake ruwa biyu,wani irin kyau ne dashi don hatta qwayar idanunsa launinta daban yake,idanun haruna a bude suke,sabida sunyi yawon kiwo gari gari qasa qasa,don haka babu wuya ya yaudari yarinya ta fada soyayya dashi,da wannan kyan nashi yake amfani,ya yaudari ‘yammatan dashi kansa baisan iya yawan adadinsu ba,da haka ya yaudari gaje ta fada soyayyarshi da sunan aurenta zaiyi,tana da son abu me kyau,don soyayyar himu fiye da rabinta kyansa ne yake janta,sai gashi ta samu wanda ya fishi.

Hankalin inna furera ya tashi qwarai,ta tashi haiqan don rabasu amma a banza,da sun fita kiwo suke jonewa,kuma gashi ta gaza hanata fita kiwon,saboda bata dame fidda mata dabbobin,daga qarshe ta yanke shawarar bari kawai ta samu daadar himu da maganar aurensu,gwara ayi a daura,duk tsiya idan tasan da igiyar wani a kanta kome zai yanke,shima harunan bazai bita ba.

Sai data gama maganarta tsaf sannan daadar himu ta watsa mata wani kallon banza

“An gaya miki shashasha nike?,ko ba’a cikin garin nan nake ba ai nasan kome ke faruwa,da farko kinso kai diyarki birni ki hana dana,saboda kina ganin acanne zata samu me arziqi,da hakan bai yiwu ba sai kika haqura,yanzun kuma diyarki ta gama lalacewa….ta gama bidar maza shine kikeso ki joganawa dana?,bazai yiwu ba,nima na fasa hadin,dana fita zaiyi duniya ya nemi arziqi kamar kowanne namiji,ko nima zan kere sa’a cikin rugar nan” sosai ran innafurera ya baci,ta dinga zage zage tana cewa daadar himu ta yiwa diyarta sharri,daga abun arziqi sai ya zama na tsiya?,idan himu bazai auri gaje ba ai basai ta hada da sharri ba.

To itama daadar ba baya bace,sai ta tasowa inna furera,suka fito har tsakar gida suna yi,yuuma na jinsu bata ce musu ta tafas ku sauke ba,sosai daadar himu ta tasar mata,har ta fara bankada sirrin inna fureran,da roqarta da tayi kan ta rufa mata asiri,shine silar alqawarin da ta yiwa daadar himu na bawa himu gaje don su samu suci dukiyar a tare asiri a rufe

“Barni yuuma,rabu dani na nunawa matar nan nima ba kanwar lasa bace” daada tace da yuuma sanda ta taso tana shirin kashe rigimar,saboda yadda suka fara tonawa junansu asiri,da qyar ta samu ta raba,bayan mutane ‘yan gulma sun fara marmatsowa,kowa yana son jin abinda ya shiga tsakanin tsaffin aminan,tun daga sannan sukayi baram baram,aka rabu dutse a hannun riga(dama duka tarayyar da babu Allah a ciki,to tabbas qarshenta kenan koma fiye da wannan).

Ajiyar zuciya inna furera ta saki,sai ta miqe tana zura takalmanta,ta kuma nufi turken dabbobin,tsaiwa tayi tana qare musu kallo,baqinciki na sake sudarta,wai me yasa komai yake shirin tabarbare mata ne?,watsewar wadan nan dabbobin dai dai yake da watsewar dukka farincikinta da kuma kima da daraja data samu a baya cikin qauyen ta dalilinsu,kuma hanya ce da zata bawa maqiyanta kamar su daadar himu damar yi mata dariya gami da zundenta,kai ta girgiza da sauri,ba zata taba barin hakan ta faru ba,ko ta yaya sai ta dawo da garkenta kamar yadda yake ada,amma kuma ta yaya?,ina taga kudin da zata sake siyan wasu dabbobin ta cakuda da nata?.

“Maimunatu” shine sunan daya fado mata,tabbas!,wannan itace amsa,tun daga kan kayan lefe sadaki da irin mutanen da suka je daurin auren yarinyar ta tabbatar ta taka wani babban shinge,kuma koda bata gani ba,jikan tsohuwa anni ai ba wasa bane,tunda tasan anni,sani na daga ni sai ke ba sanin shanu ba,ko daga motocin dake shigowa da ita garin da irin rabon da take zakasan ba qananun mutane bane.

Murmushin samun mafita ne ya subuce mata,ta saki ajiyar zuciya,hankalinta kuma taji ya kwanta sosai,dole ta nemo gidan maimunatu,tana da tabbacin zata samu dukkan kudaden data yanka mata,ai dai komai lalacewarta ita taci gaba da riqonta bayan bacewar ubanta da kuma gushewar uwarta daga doron duniya,idan ta kama ma sai ayi lissafin din abincin data dinga ci da ita har zuwa sanda aka aurar da ita,da wannan tunanin ta juya zuwa cikin gida,saidai abu daya da take ganin zai kawo mata tarnaqi shine,ina zata samu kwatancen gidan maimunatu,daga nan har garin gombe?.
“Yuuma mana” tsukakkiyar kwanyarta ta bata amsa,take kuma ta gamsu,don haka ta dage katifar ciyawa dake dakinta tana laluben sauran kudaden data adana,ta lissafa taga nawa suka rage mata?,tunda tun bayan auren maimunatun anni tace yuuma ta shaida mata,kudin aikatau an gama biyansu,tunda a yanzu tana gidabta tana zaman aure bautar Allah bata mutum ba,a ranta take qiyasta adadin kudin zasu kaita gwambe?,don bata tunanin kudin dawowa,tasan ko a jirgi tace tanaso a dawo da ita za’a kawo ta.

Barazanar daukewa numfashinta yake daga qirjinta sanda ta daga wajen ta kuma kakkabe katifar taga wayam

“Hukumullahu min zalika” ta fadi kalmar da ita kanta batasan cikakkiyar ma’anarta ba,yadai fadane kurum,gumi ne ya fara tsargo mata,ina kudadenta suka shiga?,cikin lokaci qalilan tayi gumi kashirban,ta koma bakin itacen gadon ta zauna tana sauke numfashi kuka kamar zai qwace mata,ta xurfafa tunaninta kan waye yabi dare yabi rana ya dauke mata kudinta?.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram:

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply