Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 56


Gurbin Ido 56
Viral

56

Dakinta suka wuce da amnan,ta ajjie lafayanta jaka da kuma takalminta,sannan ta sauya kayan jikinta zuwa wata doguwar riga

“Me zamu dafa amnee?” Murmushi tana fidda ido

“Kema irin na daddy?” Gira ta dage mata tana murmushi

“Eh yafi dadi ai” sai yarinyar ta saki dariya

“Nima nafi son shi”

“Yeah,me zamu dafa?” Dan daga idanunta tayi kadan

“Ummmm,daddy’s favorite” ta fada da sauri bayan ta gama tunaninta

“Me kenan?” Maimunatu ta tambyeta tana dubanta

“Sinasir funkaso or masa” ido ta zaro

“It’s late but I’ll cook it later,i promise”

“Yayi anty moon,i like it nima”

“Zan miki in sha Allah amnen daddy” ta fada tana jan kumatunta.

Tare suka wuce kitchen din da ita,tana aikinta ita kuma tana mata labari,tana ta biye mata,sai taji aikin yayi mata sauri,hakanan ranta fes,babu tunane tunane ko kuma jin kewa.

Soyayyiyar taliya tayi musu data wadata da kayan lambu,duk da haka kuma sai ta hada potato salad,sai kuma farfesun kifi ragon ruwa me kyau,wanda shima yaji kayan qamshi,kamar zata hada lemo taga aikin zai mata yawa,ga magrib an idar bata kuma samu ta sauke farali ba,don haka ta tattara komai takai saman dining,ta kuma gyare kitchen din,amna nata nacin ta bata ko mopping tayi mata amma ta hana,koda ta gama din tare suka wuce daki, maimunatu ta tube ta shiga wanka,bayan ta fito ta shirya cikin wasu white and soft fabric,skirt ne handkerchief style sai shirt off shoulder, design na rigar ya baiwa fararen kafadunta dake qyalli daman fitowa sosai,suka kuma fidda kyansu da kuma sigarsu,hakanan albarkatun qirjinta suka zauna daram daga qasan rigar,saidai ko yaya tayi sunkuyo za’a iya ganinsu saboda yanayin rigar,kayan sun mata kyau sun kuma amsheta,abinda ya bata sha’awa ta sanyasu ganin basu da nauyi ta kuma ji dadinsu a jiki.

Sai data yima anan wanka itama sannan sukayi sallah,suka fito cin abinci,hannun maimunatu ta kama ta riqe sanda take shirin serving nata

“Anty moon,daddy fa?” Kai ta daga a dubeta

“Me ya faru dashi?” Narkewa tayi tana duban qwayar idanunta

“Zaici abincin,yanason kifi” nauyi yadan kamata,to amma kuma jagwal zata ja mata,don ita bata shirya komai dashi ba,bata kuma shirya ganinsa ba bare ga tsareta da wannan kallon nata ya dagula mata lissafi ba

“Kinga baya nan ai,kuma baice yana jin yunwa ba”

“Please anty,zai dawo fa,he promised,kuma daddy na baya saba alqawari,Allah anty na tabbatar zaici,he like it” yadda ta riqe mata hannu ta kuma marairaice mata dole ta ajjiye serving spoo din tana sauke ajiyar zuciya,nan suka zauna jiransa,duk bayan mintuna sai amnan ta duba qofa,maimunatu ta biye mata ne kawai,amma ita ta sani ba shigowa zaiyi ba,tunda ba shigowar yakeyi ba,sai ta kunna musu mbc three daga nan saman dining din da suke ko zata ragewa yarinyar zaman jira.

A tashinta na karo babu adadi sai amnan ta fice ba tare da maimunatu ta lura ba,kanta tsaye ta haye stairs na ja’afar tana sauri sauri,ta wuce balcony ta tura qofar falon da sallama abakinta tana leqe leqe.

Yana tsaye gaban tv yana sauya tasha,bayan ya cika dakin da sanyin ac kaman babu gobe,hannunsa daga dauke da cup na black tea,yana sha yana tunanin abinda zaiyi order wanda zai dace da yanayinsa,yayu matuqar kewar tafiyar da baaba tabawa tayi.

Da mamaki a fuskarsa ya waiwayo yana dubanta,sai yadan sakar mata murmushi,ita kuma ta tsaya daga bakin qofar tana maqale wuya

“Daddy,your dinner is ready” idanu ya fitar alamun mamaki

“Who prepared it for me?”

“Anty moon ce,ka taho daddy please,munata jiranka tun daxun”

“Amneee…..zo kiji” ya fada yana ajiye cup din gami da yafitota,kafada ta maqale

“You promise fa daddy,kace zaka koma,please daddy let’s go” tayi maganar tana tahowa gami da jan hannunsa,idanunsa ya lumshe kana ya bude yana murmushi,baisan inda ta samo dan banzan wayo da kuma surutu ba,iya yau kawai ta sanya murmushi sau babu adadi saman fuskarsa,bashi da sauran zabi tunda yayi alqawarin illa bin bayanta da yayi.

Duka hankalinta ya dauko ga tv din,saijin muryar amna tayi tana rangada sallama,riqe da hannun mahaifinta tana gaba yana biye da ita a baya,sosai gabanta ya fadi,ya shiga tattare zamanta tare da gyara jikinta a fakaice,tuntuni idanuwansa suka sauka a kanta,idan yace ma batayi masa kyau ba lallai ya shimfidawa kansa qarya ne kawai,mutum ne shi ma’abocin son fararen kaya,don ko a yanzun moroccan abaya dake jikinsa fara ce sol da adon golden zare,sai ya maidashi tamkar wani basarake sak.

Kame kame ta shiga yi sanda ya iso wajen,yana daga tsaye idanuwansa akanta ya jama amna kujera daya ta haye,saita jaa masa itama kujerar dake kusa da ita,wadda daga ita sai wata empty chair sai kujerar da maimunatu ke zaune a kai

“Have a seat dad” ta fadi a shagwabe,baice komai ba ya sake janye kujerar ya zauna din,wanda a take qamshin turarensa ya mamaye wajen.

Ya tabbatar da cewa kallon da yake matan ya wuce yadda ya kamata,don haka yayi qoqarin tattara hankalinsa ga amna,yana saurarenta yana kuma lumshe idanu gami da gyada kai,kusan shine amsarta,don ya tabbatar idan yace zai biye ma surutunta zata bashi ciwon kai a daren,saboda hirar amna bata qarewa.

Cikin qoqari da jarunta ta tattara nutsuwarta ta soma serving dinsu,yana ankare da ita yadda take ta loda musu abinci a plate,caraf ya riqe hannunta ganin abincin yayi yawa kamar bata kula,a razane ta saki warmer din tana dubansa,wani abu tsarga mata tun daga yatsun qafarta zuwa kwanyarta,ya kumma kunno mood din da taketa qoqarin ganin ta danneshi.

Hannun nata ya saki ya sulale a hankali sannan yace

“Enough mana, yayi yawa” yayi maganar don baya tsammanin shi zai iya ci,baisan taste dinta ba,kuma bashi da tabbacin abincin zai dace dashi,duk kuwa da qamshin spices da ya cika wajen.

Sakin spoon din tayi,ta koma da baya a hankali ta zame saman kujerar,sai yaja plate daya,ya sanya spoon ya matsar gaban amna

“Uhnnn….bismillah” murmushi ta saka sanann ta dauki cokalin ta soma diban abincin tana kaiwa bakinta,wani murmushin ta kuma yi
“Yummy….” Ta fadi tana duban fuskar ja’afar

“Daddy,mucu, you will enjoy it over” murmushin gefan bakin dai ya kuma saki

“Ki cimin amnee,tunda ya miki dadi” qememe ta tubure kan shima fa sai yaci din,ta haura saman table din ta dauko masa wani spoon din,sanan ta tsareshi da idanu,tilas ba don yaso ba ya diba abincin dan kadan ya sanya a bakinsa yana taraddadin abinda zaiji.

A hankali dadin abincin ya fara zagaya harshensa ya kuma gauraye bakinsa gaba daya,sake diban second spoon yayi,sai ya kuma jin real taste din fiye dana dazu,sannu sannu sai gashi yana ta kaiwa cikinsa abincin yana kuma sauraren hirar amnan yana amsa mata da ka,kafin kace meye wannan sai ga plate din wayam babu komai.

Idanu amna ta fitar tana duban ja’afar

“Daddy,a qaro ne?” Kai ya girgiza yana shafa cikinsa,ta wani sashen kuma yana cika da mamakin yawan abincin da yaci,duk da dama shidin bamai wasa bane da cikinsa musamman idan ya samu abincin daya dace da taste dinsa

“No…..am full amnee, thank you”

“Thanks to anty moon,ga kifin dad” sai yayi kamar bazaici ba saboda qoshin da yaji yayi,amma shima yana tabin farko ya bude cikinsa yaci kifin sosai,har sai da sukaci kusan rabi,sannan ya dakata,ya yagi tissue ya goge hannunsa daya baci

“Anty bakici komai ba,ba kyau fa zama da yunwa” sai a sannan hankalinsa yakai kanta,ya kalli plate din abincin nata,kusan babu abinda ta taba a ciki

“Daddy kace mata taci” miqewa yayi ya zube hannayensa a aljihunsa,kana ya saukar mata da dukka nauyin idanuwansa yana kallonta

“Eat it” ya fadi a gajarce

“Daddy yace kici anty moon” saita jinjinawa amna kai

“Zanci amna” a hankali ya janye idanuwan nasa yana mamakin kansa,baisan me yasa ya maida kallonta one of his favorite thing to do ba a duk sanda zasu hadu a muhalli guda,bayason hakan ko kadan,sai ya kama hannun amna suka fice da sassan nata.

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana hade hannayenta waje daya da qarfi,abinda take ji cikin jikinta yana qara qarfi,tuni kowacce gaba ta jikinta ta fara amsawa,hakanan launin idanunta suka fara sauyawa,ko kusa ko alama babu wata yunwa da takeji,infact cikinta ma a cunkushe yake,sai ta tashi zuwa bakin fridge ta dauko sassanyan ruwa ta balle ta soma sha tana tsammanin ko zataji sauqin abinda takeji din.

*_UNAISA_*

Tun bayan sallar isha’i ta gama dukkan wani shiri nata na tarbar ja’afar,girke girke tasa aka masa har kala uku,ta kuma fece kwalliya bayan ta sallami dukka masu aikin nata,ta qwame tana jiran jin shigowarsa ko kuma wani motsi nasa.

Lokaci lokaci tana tana duban agogonta,har awannin suka fara nisa,ta fara debe tsammani da xuwansa,wani girman ksi hadi da maganganun da suka fara da haj munubiya suka sauko mata,suka sanya mata wani bala’e’en haushi da takaici,ta kuma shiga safa da marwa amma sai ta kasa daurewa,don haka taja wayarta ta kira anty talatu

“Karkiyi gaggawar zuwa wajensa,ki sake jira daga nan har xuwa sha daya ko sha biyu mu gani,duk wayon ango dai dole yazo hannu ai,yana zuwa hannu kuma ai ya gama yawo,da wannan ta koma din ta zauna tana kada qafa,idanuwanta a kan tv,duk da hankalinta ba’a kai yake ba.

Da qyar ta samu ta tsakura farfesun kifin,saboda abincin bata jin zai shiga cikinta,ta kwashe komai ta maida kitchen,ta gyara ta kuma wanke kwanukan,dukka a daddafe take komai,saboda zuwa sannan gaba daya mararta ta daure tamau,sai danshi da taji tana zubarwa,wanda tayi tsammanin ko period ne yake zuwar mata.

Bandaki ta shiga ta duba jikinta,saidai kuma ba period din bane,wani ruwa ne daban,tsarki tayi tana cije lebe ta fito ta baro toilet din tana takawa da qyar,kayan bacci ta canza tana duba kokaci,amna tana ranta,saidai tunda tasan tare suke da daddynta ba buqatar sai ta dami kanta,sai ta saita freshner din dakin sake fesa kansa da kansa duk bayan wasu sakanni,ta saisaita hasken wutar dakin zuwa dim light,sannan ta haye gadon a hankali taja duvet zuwa qugunta tana cije lebanta hadi da hade qafafunta waje daya.

Ajiyar zuciya unaisan ta saki sanda ta kalla agogo,qarfe goma dai dai na dare agogon ya buga,awanni biyu masu zuwa da anty talatu sai takejin sun mata nisa,ba zata iya bari ba,don haka ta miqe ta nufi bedroom dinta,ta fidda kayan jikinta ta wuce toilet don ta sake shiryawa,ta gama tsara cewa fitar zatayi ta taddashi a duk inda yake.

Hannunsa guda daya yana saman kan amna,yana shafa sumarta a hankali,yayin da dukka hankalinsa ke kan tv yana kallon news a tashar al_akhbaar,yaqe yaqe ne kawai ke tashi tako ina a duniya,abun akwai daukar hankali sosai.

Ajiyar zuciya ya sauke sanda suka kai qarshen labaran,ya janye idanunsa ya maida kan fuskar amna,kallonta yake,sosai take tuna masa da shaheeda,ta wani sashe tana dan diban kamanninta,duk da idonta lips dinsa da skin color irin nashi ne,sai ya tofa mata addu’a sannan ya sunkuya a hankali yayi kissing din goshinta sannan ya miqe ya sabata a kafadarsa ya taka a hankali yana ficewa daga falon.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram:

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply