Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 58


Gurbin Ido 58
Viral

58

Assalamualaikum

NAFISAT K ABDULLAHI
Is an actress in the kannywood industry

She’s a singer and can sing all types of songs

You can’t afford to miss her newly released song named *KADDARATA* part 1-4 on her YouTube channel *OFFICIAL FEENAT*

You can only click on this link and stand a chance to listen and watch her amazing video

Dont only enjoy the emotional video but also *SUBSCRIBE* to anable you to be notified when ever she upload another video

Like and drop your comment under the video to encourage her do more of that .

The only way you can support and encourage her is by *SUBSCRIBING* to her YouTube channel below

She is used to noticing those following and commenting on her videos .

*GUESS WHAT*?

Click and see for yourself
Thank you so much

________________________________

58

Gefe ya janye mata,abinda yayi mugun yi mata dadi kenan,ta kuma bawa kanta tabbacin akwai nasara kenan,sai ta fara takowa zuwa ciki tana kuma sauya salon tafiyarta cikin kwarkwasa da taku d’ai d’ai.

Dab da zata gotashi tayi rangaji ta kuma fada jikinsa,bai tarota ba bai kuma hanata ba,damar data samu kenan ta ruqunqumeshi gaba daya cikin jikinta,duk yadda taso ta daure amma ta kasa,sai ta fara masa wasanni cikin son shagaltar dashi.

Tabbas tayi nasarar sake kunnashi,tunda dama a kusa yake,saidai daga lokacin da ya jata ya fara nuna mata nata salon qwarewar sai al’amarin ya sauya,tun tana iya jurewa irin salon wasanninsa har ta fara gayawa kanta akwai matsala fa,tasan kanta,duk jarabarta akwai iya limit dinta,tana da matuqar rauni ta nan bangaren wanda ba kasafai ta fiya son a dameta ko a zurfafa ba,ko saurayi ne ka fiya nacin manne mata yau gobe jibi zata qara maka wuta,takan ce ita ba riga bace da za’a yita wanketa,daga dukkan alamu yadda yake aike mata da saqo cikin wani irin zafin nama kadai ya isa gaya maka wanne irin kalar mutum ne shi.

Tuni idanunta suka raina fata,ta kuma fara qoqarin guduwa,ta tabbatar ba zata iya ba,ba zata daukeshi ba,don komai zai iya faruwa,qarfinta tattara ta watsala qasan gado tana dafe da lips dinta dake mata radadi kamar zasu yanko su fado,yunquri yayi kamar xai bita abinda ya sanya babu shiri ta miqe ta lalubi hanyar fita da sauri.

Saman gadon ya zube yana fidda wani irin murmushi,shi ya sani ba kowacce irin mace bace zata iya daukeshi ba,ko shaheedansa tasha fama kafin ta saba,saidai da yake mutum ce mai juriya sai ta saba din a hankali,take kuma kula da duk hanyar da zatasan zata sama masa farinciki da nutsuwa.

Ko baya son mutum ba kasafai yake fidda hakan quru quru ba,amma baisan dalilin da ya sanya sam ko sau daya bai taba jin wani abu guda daya daya motsa zuciyarsa a kanta ba,a hankali ya saki tsaki yana saukowa daga saman gadon,sai yaji gaba daya yana qyamar jikinsa bawai don ya fitar da najasa ko wani abu ba,toilet ya shiga ya hada ruwan dumi sosai yayi wanka.

Abu kaman wasa sai gashi gaba daya daren yazo masa a wani irin birkice,sau biyu yana sake wanka,a wannan karon dai wankan ibada ne,tsakiyan dare da kuma kafin sallar asuba,me yasa mafarkinta ya hanashi bacci?,me yasa mafarkinta ya hanashi sukuni?,yana gaban mudubi a zaune yana lissafa tsaho shekaru da watannin daya dauka baiyi rayuwa da mace ba,sai ya furzar da iska daga bakinsa,tabbas wannan abun da ya farun yana da nasaba da dadewar da yayi da nisantar rayuwa dasu,bawai wani abu bane na daban.

Dab da liman zai tada sallar asuba ta buda idanunta,tana budesun abubuwan da suka faru a daren jiya suna dawo mata fes cikin kanta,sannu a hankali ta waarasu cikikin dakin,yana nan a yadda yake har hasken data kunna kafin ta kwanta,saidai sanyin dake busawa ya fara mata yawa saboda iskar asuba data gauraye duniya.

Hannunta ta daga tana shafa saman mararta a hankali,sakayau take jinta,babu wannan ciwon,hakanan babu feelings din gaba daya,sai ta sauke ta juya hannun damanta,idanunta suka sauka akan amna dake baccinta cikin kwanciyar hankali,hannunta ta dora kan fuskar yarinyar da wasu lokuta take mata yanayi da fuskan mahaifinta,batasan ya akayi murmushi ya kubce mata ba,sai ta miqe ta zauna sosai tayi kissing goshinta,sannan ta sake gyara mata kwanciyar gami da ja mata bargon sosai.

Bandakinta ta wuce,ita dinma sai da tayi wanka don bata yadda da kanta ba,sannan ta dawo ta saka prayer jilbab and skart da takanyi amfani dasu musamman a sallar asuba irin haka,ta tada sallarta.

Ko data idar qur’aninta ta dauka,bata wasa da tilawa ko don saboda haddarta,ta buda daga inda ta tsaya jiya ta dora,cikin qaramin sauti da kuma lallausar muryarta dake koyi da qira’ar shaik khalilul khusari.

A nutse ya turo qofar dakin a hankali,sautin karatunta ya baqunci kunnuwansa,sai ya maida qofar kawai ya rufe ba tare daya katse mata karatun ba,ya juya yana barin wajen,sautin karatun yana bin kunnuwansa har zuwa sand yayi nisa a wajen.

“Itama matarka ce” zuciyarsa ta raya masa sanda yake shirin wucewa zuwa saman sa ba tare daya biya sassan unaisa ba,wannan tunanin ya sanyashi sauya akala,ya isa qofar falon ya murdata,sai ya jita a kulle, knocking ya soma,saidai babu alamun za’a bude masa,mutum ne da bai fiya tsawaita abubuwa ba,don haka yana qara biyu ya juya yayi gaba,taku hudu cikin na biyar yaji an bude qofar,ya waiwaya a hankali idanuwansa a kanta.

Kana kallonta zakasan a birkice take,don hatta gashin kanta a hautsine yake,hakan na nufin a yadda ta shigo jiya a haka ta kwanta bugu da qari kuma har yanzun bacci take,bugunsa ya tadata

“Lokacin salla zai wuce” daga haka yayi gaba,ya soma haurawa zuwa saman,unaisan kuma ta bishi da idanu,abubuwa da yawa take rayawa a ranta,indai har shirinta na jansa zuwa gareta ya tabbata,to batasan yadda sauran abubuwa kuma zasu kasance ba.

Tana gama azkar dinta amna ta farka,sai ta rakata toilet tayi brush sannan tayi alwala,komai ta iya perfectly,da alama ta samu background me kyau.

Sallar ma sanda tana yi tana ankare da ita,gyaran dake ciki da kusakuran basu da yawa,ta jinjinawa amma sosai,ta kuma sake ganin kimarta da martabarta,hakan kuma ya tabbatar mata da cewa ita din uwa ce ta gari.

Basu koma wani baccin ba,ko surutu da hirar amna ma ba zata bari su koma ba,don haka ta jata kawai suka wuce kitchen.

Break fast me kyau ta shirya,wanda ya dauketa awanni kusan uku kafin ta kammala,har masu aikin unaisa suka gama hada nasu break din suka fice suka bata wajen,sau tari dama idan girki ya hadasu lokaci daya ita ke tsaftace kitchen din,koda sun gyara baya mata dai dai,saita shiga ta sake killace komai.

A dining ta shirya komai,kamar ita da wasu zasuci abincin,hakan kuma zabin amna ne,ita ta dinga dauko warmers din daga kitchen din tana ajewa saman dining din,bedroom dinta suka wuce ita da amnan don yin wanka.

Tun suna wankan ta dameta da tambayar daddynta,don haka suna fitowa ta fara shirya amnan,tayi kyau sosai cikin fara shirt da gray color din skinny jeans,ta hade mata uban sumarta tsakiyar kai,tana ta qamshi yarinyar ta cilla ta fice zuwa sassan daddyn nata,sai sannan maimunatu ta samu sukuni,ta zauna gaban mirror ta buda manta ta fara shafawa,ta shirya kanta cikin favourite shigarta na chiffon fabric,sun ray pleat design da rigansa drawstring data zauna mata a jikinta ta mata kyau sosai.

A jikinta dama taji sai amna ta jawoshi sassan nata,aikuwa tana tsaka da hade sumarta cikin band amna ta turo qofar da sauri

“Anty moon,daddy xai fita,kizo kiy serving dinsa,yace bai yarda nima na iya girki ba,wai ba tare mukayi ba” dariya ce ta kusa qwacewa maimunatu,ta cikin madubin take kallonta tana saka band din,sannan ta janyo siririn mayafin kayan ta yafa saman kanta ba tare da taji shakkan fita dashi ba,tunda babu wani abu a jikinta daya fito,dukka yanayin dinkin me sakin jiki sosai ne

“Muje in gaya masa,amna ta ta zama ‘yammata,she can cook” dadi ya cika amnan,ta saqale hannun maimunatun suka rankaya zuwa falon.

A tsaye suka sameshi,ya bawa qofar da zasu fito baya,hannuwansa cikin aljihun wandon suit dinsa,wata iriyan suit mai daukan ido da hankali,koda bakasan tsadan sutura ba zakasan taja kudi,komai nashi designer ne me tsada,duk da bata ga fuskarsa ba amma ta baya tana iya hangen sumarsa da tasha gyara sosai,qafafunsa dake saye cikin safa sun nutse a cikin center carpet din dake wajen

“Daddy ka zauna mana” amna ta fadi tana zame hannunta daga na maimunatu ta kuma nufeshi.

A hankali ya waiwayo,a kanta idanunsa suka fara sauka,haka ma ita,duk yadda taso ta zamewa kallonsa amma sai da idanuwansu suka hade waje daya,duk da haka tayi namijin qoqarin kau da nata idanun,wani irin nauyinsa yana cikata,abubuwan da suka faru a daren jiya suna dawo mata cikin kwanyarta daya bayan daya,sai taji ba zata iya ci gaba da tsaiwa ba, nauyinsa da kuma nauyin idanuwansa na sake qara mata kasala da kuma nauyi,duk da abinda takeji a jiya cikin jikinta babu shi a yanzu,amma har yanzu cikin jikinta tana jinsa a mace yayi wani irin laushi,sai ta zame saman one sitter din dake daura da ita ta zauna akai,tana kwaranyar da dubanta ga tv ba tare da tana fahimtar abinda ke gudana ba.

Yadda ta rage tsahonta ta hanyar zama haka ya bita da idanuwansa,kyakkyawar zagayayyar fuskarta da tayi wani iri garai garai ta kuma yi fresh ta fito tarwai a tsakanin duhun kalar vail din dake kanta,kamar yadda jajayen siraran lips dinta ke qyallin lips balm

“Ina kwana” ta gaidashi da sak irin muryar data dinga gigitar dashi cikin mafarkansa na jiya,sai daya lumshe idanunsa yana hadiye wani abu sannan ya motsa bakinsa

“Lafiya Lau” tayi tsammanin zai mata magana kan abinda ya faru da ita a jiya ko wani abu makamancin haka,amma sai taji baice komai ba,hasalima ya tattara hankalinsa ga diyarsa

“Fita zanyi amna,am late,ina da alqawari da mutane,banason na saba” ya fada with softness lokacin da amnan ta dage sai ya zauna yayi breakfast dasu,haka ya juya suka fice tare yana lallabata ita kuma tana tuburewa.

Baki maimunatu ta tabe,bata taba ganin mutum irinsa ba,idan komai ya faru ma yana iya nuna komai din bai faru ba,shariya ginshira da kuma izza,ita dama bata wani damu yaci din ba,banda amna ta dage ma ba nemansa take ba iyakar zamanta a gidan,sai taci gaba da zamanta a nan tana jiran dawowar ‘yar rigima anma suyi break din tare.

Ba’a rufa minti uku ba sai ga amnan ta dawo dauke da kwalin sabuwar waya

“Ga wayarki inji daddy……sannan yace na hada masa abincin a foldable basket,yau da girkina zashi office” hannu tasa ta amsa wayar ta aje gefe,tana dariyan maganan amna,tunda dai yau ta tayata yanka veggies ta damu kowa da zancan ita tayi girki,sai ta miqe ta shiga kitchen din,ta hada komai a basket din ta riqowa amnan,har zuwa dab da inda motarsa ke kunne yana jiran amnan.

Tana hangoshi yadda yake duba agogon dake daure ga tsintsiyar hannunsa,sai ta gyara tsaiwarta sosai,ta kuma tsaya a wajen data tabbatar bazai ganta ba,so take ta qare masa kallo irin wanda bata taba ba tsahon saninta dashi,tanason ta gano dame yafi sauran maza da yake da kwarjini izza da kuma qasaita har haka?,saidai tun batayi nisa da bin qwaqwafin nata ba ta fara ganewa cewa tabbas da bambanci,sai ta lumshe idanunta tana sauraren sautin bugun zuciyarta,ta cikin idanuwanta kuma tana hango wancan lokacin da ya sanya yatsunsa biyar saman fuskarta,ta bude idanunta da hanzari kamar a lokacin abun ya faru,ta saukesu a kansa sanda ya saki wani qasaitaccen miskilin murmushi yana jan kumatun amna bayan ya karba kwandon hannunta.

Qaramin tsaki taja tana kauda kanta daga dubansa,haushinsa yana saukar mata,sai ta juya a nutse tana barin wajen,ta tsani duk mutumin dake busa hayaqi qwarai,har batason hada muhalli dashi,batasan ya akayi take manta wannan a kansa ba.

Koda ta koma sabgarta taci gaba dayi cikin gidan ita da amna,bata tashi tunawa da wayar ba sai da azahar bayan ta idar da sallah amna tayi bacci, fiddota tayi daga kwalinta ta budeta,sabuwa ce dal,sannan daga gani ba qaramar waya bace,mamaki ya kamata,me ya sami tata wayar?,bata sani ba,iya abinda zata iya tunawa kawai shine sanda wayar ta sulale ta fadi daga hannunta sanda ya tareta ya sanyata a wata iriyar koma.

Baki ta tabe ta miqe ta jonata a charge,sannan ta dawo ta kwanta saman kujerar ta buda daya daga cikin novels din afra dake wajenta,wanda batasan ta hado dashi cikin kayanta na makaranta ba,sai yanzu data qarasa zazzage akwatin,don baifi kwanaki goma sha hudu suka rage musu komawa makaranta ba.

Guraren qarfe uku da rabi taji ana knocking sassan unaisa,sai ta gyara kwanciyarta bayan ta duna lokaci,taci gaba da karatunta,sosai littafin yake daukar hankalinta,batasan ya akayi ta qulla alaqa me qarfi da films na soyayya da litattafansu ba,zama da madaukin kanwa,afra ta koya mata qarfi da yaji.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram:

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply