Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 59


Gurbin Ido 59
Viral

59

Ya tadda schedules da yawa a company,don yana shiga kamfanin tun daga first floor PA dinsa ke biye dashi yana lissafo masa,yasan cewa laifinsa ne,tun jiya ya kamata ya buda email dinsa ya duna schedules dinsa na yau amma baiyi hakan ba,hakan kuma baya rasa nasaba da abinda ya faru jiyan,ya kuma tabbata da qyar ya tsallake rijiya da baya

“Finally…..you have a trip” dakatawa yayi daga zuba wayoyinsa da yakeyi a muhalli na musamman da aka tanada masa saboda ajjiyesu,ya waiwayo yana dubansa da shanyayyun idanunsan nan dake ma kowa kwarjini

“To where?”

“the construction work of the estate in lagos should be checked sir” juyowa yayi gaba daya yana dubansa

“Did something happen?”

“Kamar akwai qorafe qorafe sir….but sir Jabir will explain to you” shuru ya danyi kana ya kada kai

“Okay….you can go, I need thirty minutes to get ready before entering the first meeting, tell them,and…..send me Mr. Martin”

“Okay sir” ya amsa a ladabce yana juyawa dauke da project planning manual dinsa.

Iska ya furzar daga bakinsa yana murza hannayensa guri guda,yana son duk yadda za’ayi ya fita da amna zuwa wani guri da zai zame mata baqo ko na kwana uku ne,He promised her,kuma duk yadda zaiyi baya yadda yayi mata alqawari ya saba mata,bama ita koma waye zaiyi mu’amala dashi,amma kuma yaga alama kamar dama ba zata bashi damar hakan ba,sabbin sabgogi sai danno kai suke,zai yi qoqari ya duba,koda a wannan karon zata kama ya tafi lagos din da ita ne zaiyi wannan qoqarin.

Shigowar secretary dinsa ya katse masa tunani,dauk da basket din da shi sam yama manta dashi

“Sir,It’s your food,you forgot it in the car” duban basket din yayi yana shafa gaban kanshi,daya hannun nasa kuma riqe da biro,kallon saman ido yayi masa yace

“Drop it here” a ladabce ya qaraso ya dora masa shi saman table din nasa saidai kuma daga gefe guda,wai ko xaiyi abinda zai dan wanke kansa a wajensa,saboda yasan me laifi ne shi a wajensa,saidai har yanzu baice masa komai ba,shurunsa kuma bashi da sauqi sam a wajensu.

Dubansa ya sakeyi,kamar zai magana sai kuma ya shareshi yaci gaba da rubutu akan file din dake gabansa,ya danyi jim yaga ko zaice wani abu amma yaga baibai ta kansa ba,sai ya danyi gyaran murya

“Sir,akwai baqi dakeson ganinka….”

“Ka gaya musu,yau bazan samu damar ganin kowa ba,tell them in a polite way,they’re our client…..don’t repeat it again” J ya fada da kakkaurar muryar dake nuna gargadi da kuma jan kunne ba tare da an fito an maka filla filla da laifin da kai kanka kasan ka aikatashi ba.

A ladabce ya kada kansa

“I will not repeat it sir,am sorry” bai amsa masa ba yaci gaba da aikinsa,shi kuma ya juya ya fita.

Files din dake gabansa ya gama dubawa,wadanda zai sakama hannu ya saka musu,ya tattare takaddun da zaiyi amfani dasu sannan ya shige toilet din dake manne cikin office din nasa.

Yana fitowa jabir na shigowa office din,kai tsaye kamar kowanne lokaci da bashi da shamaki da shigowar

“Good morning” ja’afar ya fada yana sauke hannun rigarsa da yayi rolling up don kada ruwa ya taba

“Morning dude,mun tashi lafiya” jabir ya qarasa maganar yana zama saman kujeru guda biyu dake gaban table dinsa

“Alhamdulillah….ya jikin madam?” Goshinsa ya murza

“To,da sauqi,yau kam ko breakfast ban samu ba,,she can’t cook”

“Allah ya bada lafiya” ya fada yana dawowa mazauninsa.

Hannu ya miqa zai dauka wani file,sai ya ture murfin daya daga cikin warmers din,cikin qanqanin lokaci qamshi ya cika wajen

“Wow,wannan fa?,daga ina?” Jabir ya fadi yana leqa warmer din,tambayar ta dan ja hankalin ja’afar,ya daga kai yana kallon abincin shima qamshin na cika qofofin hancinsa,kafin ma yace wani abu jabir ya buda warmers din ya fara serving kansa tare da ja’afar din a different plates,ya kammala ya tura masa gabansa shima yaja nasa.

Ko sau daya jabir ya kasa riqe bakinsa daga yabon abincin,da gaske kuma yake,dadin abincin yakai masa ko ina,duk yadda ja’afar yaso basarwa qamshinsa da kuma yadda jabir keta santi akai yasa ya gaza daurewa,sai ya rufe file din,yaja abincin shima ya fara ci.

Loma biyu kacal ya yadda da abinda jabir din ke fada,saidai ya dake ne ba tare daya nuna ba

“U have a great cooker” jabir yayi furucin yana gyada kai

“what is happening with our Lagos contract?” Ja’afar ya kauda wancan maganar ya sako masa wannan,baice komai saboda yadda girkin ke dibansa,ya fiddo wayarsa yayi dan danne danne ya turawa ja’afar gabansa,sai ja’afar din ya bishi da kallo,ya fuskanci sosai yakewa abincin santi,kaman zai magana sai ya fasa,ya dauki wayar yana duba abinda yake son nuna masa.

Ya jima yana nazari bayan ya tsaida nashi cin abincin,har jabir ya gama ya wanko hannunsa a toilet ya fito

“Da zaka kyautamin yaa J ai da an samin kwano a gidanka kafin my fa’emm ta warware” sai sannan ya dauke idanunsa daga kan wayar,ya watsa masa harara

“Lokacin aiki ne wannan,ba zancan family ake ba yallabai”

“Magana anan fa ta zama dole,kana samun irin wannan kabakin ya kamata a ga canji a jikinka,kadan aje tumbi haka”

“Irinka ne ni da zan kwanta?,so kake wataran ka kasa aikata komai a gad…..” Shuru kuma yayi ba tare daya qarasa ba,kaman wanda wuta ta daukewa

“A gado ko?,kuma hakane fa dude,ku da yake expert ne ta wannan fannin zaku fimu sanin sirrin farin shiga” jabir ya fada dariya sosai na kubuce masa.

Karamin tsaki yaja yana tura masa wayarsa da qarfi gabansa,banda jabir din yayi hanzarin saka hannu ya tareta da babu abinda zai hanata faduwa qasa,har yanzu dariyarsa yake kafin yace

“Na duba mana ticket na tafiya lagos jibi in sha Allah”

“Hakan yayi” ja’afar ya fada yana miqewa tsaye don shima ya wanke hannun nasa,ya wuce jabir daketa qunshe dariya har yanzu.

Sai gab da la’asar sannan ya samu kansa,sanda ya dawo office ya taras da miscall har uku,bai iya biba sai daya dawo daga sallah,yana zaune daman cussion yana dan sauke gajiya yabi bayan kiran.

Sosai tayi zurfi cikin tunani lokacin da take kwaba qullin alkubus din data yiwa amna alqawarin yi yau,amna na gefanta tana faman zuba mata surutu kaman yadda ta saba,zaune saman sink daura da tap din dake kitchen.

Tabbas fuskar hajiya munubiya ta gani tana fitowa daga sassan unaisa,unaisan na biye da ita,amma duka ba wannan bane yafi tsaya mata ba a rai,maganganun da kunnuwanta suka jiye mata

“Duk sharrin ammansa ne d wannan makirar tsohuwar,na gaya miki kiyi da gaske,kiyi kamar kinayi,ki kuma zuba ido sosai,zakiga dukka abubuwan da na gaya miki” me amma ta tsare ma haj munubiyan?,me kuma anni itama ta tsare mata?,meye alaqarta da unaisa da har ta zabi ziyartarta a kebantaccen lokaci irin wannan?,bayan basu jima da haduwa a gida ba?,bama wannan ba duka,ame zata zuba ido?,kwata kwata zuciyarta bata kwanta da zuwan haj munubiya ba,duk da bata ganta ba amma ta fita daga gidan ba tare data nema kowa ba.

“Anty moon ana kira,Allah yasa daddy ne” amna ta fada tana tattara hankalinta,ko daya maimunatu bata ma fuskanci wayarta bane saboda sabon ringtone dake kai.

Dab da zata tsinke ta daga,saboda sai data tsaya ta dauraye hannunta ta kuma gogeshi

“Assalamu alaikumm” yarrr yaji tsigar jikinsa ta tashi,sai ya zame kadan yana sake jingina sosai da kujerar,ya kuma dauke dukka qafafuwansa ya dora kan center table din yayi crossing nasu.

Har zata sake maimaita sallamar tata jin shuru,sai tashi muryar ta ratso ta cikin wayar,ta kuma isar da saqo zuwa ga qwaqwalwarta cikin lokaci qarami,har cikin bargonta taji sautin nasa,tsigar jikinta ta zuba itama

“Wa’alaikumus salam” ya amsa mata muryarsa can qasa kamar wanda ya tashi a barci,a hankali ta cira wayar daga kunneta ta juya ta miqawa amna,idanunsa na a lumshe muryar amna ta maye gurbin tata muryar da yake sanya ran ji

“Daddy i missed you, please daddy ka dawo da wuri,anty moon tana maka favourite dinka,daddy zaka dawo?” Murmushi mara sauti ya kubce mata

“In sha Allah amnee”

“Thank you dad,daddy pizza please”

“Amnaaaa” yadan ja sunanta,da sauri ta tareshi

“Please daddy say okay”

“Okay” ya amsa mata kamar yadda taso,sai ta shiga murna tana masa godiya.

Duk yadda yaso ya daure amma sai ya kasa,hakanan ya samu kansa da cewa

“Bata wayar” da sauri kuwa amna ta miqa mata,saita tsare amnan da ido tana son bin ba’asi,murya can qasa da sigar rada tace

“Daddy” amsar wayar tayi,kamar zata sanya a kunneta sai kuma ta latse wayar ta ajeta gefe taci gaba da kwabinta,dubanta amna keyi cikin rashin jin dadi kamar zata saki kuka, murmushi maimunatu ta saki,yarinyar ba zata gane ba,matuqar zata ci gaba da jin muryarsa to akwai damuwa,har yau bata fita daga tarkon maganin data shama kanta ba,lallabawa take

“Daddy yana aiki,ba’a son a dinga disturbing nasa,ko kinaso yayi ciwon kai?” Da sauri ta girgiza kanta

“Okay,budemin ledar can maza a dafawa daddy abinci” sai kuwa ta hau bude mata fararen ledojin,saboda dasu xatayi amfani,cikin ranta tana mamakin tsabar wayo na yarinyar da har ta iya daukan wayarta ta zuba numbers din daddyn nata ta kira,wanda already ta dade da haddace ta.

Daga wayar yayi daga kunnensa yana kallo cikin mamaki,yaji sanda yarinyar ta bata wayar,it means kashe masa waya tayi?,sai yaji wani abu ya tsaye masa a rai,karon farko kenan da wata diya mace a duniya ta taba yi masa hakan,ransa ya sosu sosai,ya furzar da iska daga bakinsa

“me hakan ke nufi?,ta dauka shi sa’anta ne?,she doesn’t know who I am” ya fada yana jin zafi har cikin ransa(a hayye,mai yi ne yau akayi masa,ashe dai babu dadi😝).
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram:

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply