Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 60


Gurbin Ido 60
Viral

60

Cikin mamaki ta sauke idanunta daga fuskar laulo zuwa kan kwanon da laulon yake ajjiyewa a gabanta

“Gashi inji innarmu,tana gaisheki,wai kuma tana hanya” maganar laulo ta sake jefata a wani mamakin bayan wanda take ciki,duk da haka yuuma batayi qasa a gwiwa ba ta girgiza kai da dan guntun murmushi saman fuskarta

“Haii laulo,yau kuma tuwo ne a idanunka ka mance da dakin daada ka kawo aiken nan?” Kansa ya girgiza

“Nan inna tace na kawo,dakinki yuuma” mamakinta sake ninkuwa yayi fiye da dazu

“Ni kuma laulo?” Kai ya gyada

“Eh ke”, kafin ta sake samun damar cewa wani abu yaron ya juya ya five abinsa.

Har sai daya baceea ganinta sannan ta dawo da dubanta ga kwanon,lafiyayyen dambu ne daya wadata da kayan zogala da gyada,maida murfin tayi ta rufe kana ta matsar da kwanon gefe cikin tantama,zuciyarta na bata za’aje a dawo.

Tasan babu wani abu da ya hadata da innar da har zata nanngo abinci irin wannan ta kawo mata,tabbas laulo shirme yayi,zaya kuma dawo,da wannan tunanin ta tashi ta shiga sabgarta na kula da sanwar abincin daren data dora.

Dai dai sanda ta sallame sallar la’asar inna fureran ta kwada sallama a tsakar gidan nasu,gaba gadi ta kuma tako sassan dakin yuuma,ba tar data waiwaya ta kalli sashen daada ba.

Sauraren isowarta yuuma tayi,fuskar inna fureran fal fara’a tayi sallama ta danno kai

“Anata sallah hajiya yuuma?” Cike da qarin wani mamakin tace

“Eh la’asariya ce na idar,maraba furera” ta fada tana ware mata babbar lallausar daddumar dake gefanta,wadda duk cikin siyayyan da anni ke mata ne.

Zama inna fureran tayi tana qarewa dakin kallo a fakaice,wannan shine kusan karon farko data shigo dakin a lokaci irin wannan kuma a nutse tayi zaman dirshan, komai na dakin yuuma me kyau ne,batajin kaf rugar tasu za’a samu daki ya nata,babu ko shakka maimunatu nacan a muhallin daya kere wannan din,lallai ko zata samu kudi babu ko tantama a wajenta

“Barkanmu da almuru” yuuma ta fada ganin irin kallon da takema dakinta,sai tayi caraf ta amshe

“Barka kade yuuma,ina wuninmu?” Gaisawa sukayi,itadai yuuman nata saurare,saboda ta tabbatar ruwa baya tsami banza.

Shuru ne ya biyo bayan gaisuwar tasu,sai da yuuma tace

“Saiga laulo da dambu yayo batan kai dashi ya kawo dakin nan” bakinta har qeya tace

“Kai haba,ba batan kai bane wallahi,dai dai yayo,ke nace ya kawowa” cikin mamaki ta jinjina kai

“Ni kuma?,harda wahala haka furera?na tsammaci na daadar himu ne”

“Babu komai fa,banda abun yuuma ai mun xama daya,daada?,ai wata kusan tafi kusa,ai yanzu munfi kusanci da ita akan ke”

“Gaskiya ne,gashi kuma naga ta fita”

“Dama.ba wajenta nazo ba,wajenki nazo mu sada zumunta,tunda jininki ya auri jinina kuma ai yanzu dangi muke ni dake yuuma” inna furera ta fada tana ta gyara zama kamar wadda ke zaune akan qaya

“Gaskiya kam” yuuma ta amsa mamaki yana kasheta,kafin ta fita a wannan mamakin kuma sai taji inna furera ta fashe da kuka,cike da wani zallar mamakin da kuma tsoron kada ta qulla mata wani sharrin take kallonta

“Toooo…..subhanallahi, meye haka furera?, lafiya?”

“Dole nayi kuka yuuma,dole nayi kuka,kusakuren dana tafka wa yarinyar nan maimunatu,kiga yadda ta gujeni,aka dauketa daga wajena aka aurar da ita a wani waje daban,har yanzu bata waiwayeni ba,ni kuma bansan muhallinta ba bare naje na nemi yafiyarta” sai ta kama habar zaninta tahau fece majina.

Dariya hade da mamakin furera suka kama yuuma,saidai ta danne kawai taci gaba da kallonta tana cewa

“Allah sarki,ai sai a godema Allah da yasa aka gane kuskuren da akayi,alhamdulillahi,Allah ya yafe mana”

“Ameena….ameena” ta shiga amsawa tana sharce hawaye,wanda kusan hawayennata dukka akan naggenta da suka dinga mutuwa ne,asarar data tafka.

Sai data gama dukka koke kokenta ta miqe zata tafi sannan tace

“Umm….nace ba,ai sai a bani kwatancen gidan nata,can inda take a gomben ko?,sai a leqa aga dakin nata,a kuma nemi yafiya,bai kamata a matsayina na uwar riqonta ba kuma ya zamana bansan inda mazauninta yake ba”

“Tooo….anzo wajen” yuuma ta fada,ta shafa addu’ar da takeyi sannan tace

“Yanzu kam bana ce miki ga inda muhallin maimunatu yake ba,tunda ba zuwa nayi ba ko sanda ake bikin,ban samu na leqa ba” gaban inna furera ya fadi,har yanayin fuskarta yadan sauya

“To,ikon Allah,to kuma su can gidan surukan nata fa?” Kai yuuma ta sake girgizawa

“Shima bana ce ba,tunda nafi shekara rabona da garin gombe,sannan koda can ma kinsan ba ni nake kai kaina ba,yafendo ke aikomin da mota ta daukeni daga nan qofar gidan zuwan wancan” shuru furera tayi,ga qoshi ga kuma kwanan yunwa,yanzu ya kenan?.

“To ai inaga ta zo da sauqi ko,me zai hana ki waya da ita ki gaya mata surukarsu nason ganin dakin diyarta,idan yaso nima basai motar tazo ta daukeni ba?”. Binta da kallo yuuma tayi galala,sai kuma ta gyada kai

“Haba furera,dama dai na tashi zuwa ne”

“Zan iya jiran tafiyar taki indai ba zatayi tsaho ba”

“Allah ya bamu aron rai” ta amsa mata a taqaice,sabida takaicinta daya fara kama yuuma,murna ta cika inna furera

“To alhmdlh,don Allah a qoqarta muje anan kusa yuuma,na gode Allah ya qara zumunci” ta fita tana zabga mata addu’a tare da hango nesa a kusa,duk daba haka taso ba,so tayi gobe ko jibi ta dage.

A tsakar gida sukayi kacibus da daada,sai tabi fureran da kallo cike da mamakin abinda tazoyi gidan,harara suka zabgawa juna,inna furera tayi gaba tana yada habaici

“A hayye na gaba kam ai yayi gaba,na baya ko tsintar hula ba zaiyi ba,yo mu da muke jinin sa’a da nasara,haihuwa me rana,ta jefa mu gidan arziqi,ai an rabu ne kuma ba’a rabu ba,yuuma gidan karamci” sak daada tayi tana duban dakin yuuma,ta sani cewa yuuman ba munafuka bace,da sai tace wani abun suke qullawa,hakanan ta san yuuman bata daukar raini ko cin kashi bare tace zata je tayi mata tatas kan ganin furera da tayi cikin gidan,amma duk da haka sai ta kasa daurewa,ta ajjiye faifan dake hannunta ta nufi dakin yuuma.

Yuuman na tsaka da nade abun sallah daadan ta shigo,ta daga kai ta dubeta

“Mamaki nake yuuma da ganin fitowar furera a dakinki,me tazo yi?” Tambayar sai ta bata mamaki da haushi,salon yadda tazo mata da maganar mai kama da titsiye

“Kunfi kusa ai,nima tare na ganku,sai kije ki tambayeta ai” daga haka taci gaba da aikinta,shuru daada tayi,don bata da sauran ta cewa,sai kuma ta juya ta fice daga dakin sukuku,yuuma taja qaramin tsaki,sun dauka ita din sakarai ce da zata biyewa shirmensu daga ita har fureran?,kallonsu kawai takeyi amma tasan halin kowa.

A hanya fureran keta sumbatu ita kadai,Allah yasa dai kada yuuma taja mata lokaci ko kuma taqi zuwa da ita

“Idanma taqi idanuna zan murje na tafi gembu,nayi musu kwance kwance har sai na samo kwatancen gidan,don ko da tsiya koda arziqi saina fanshe wahalata,ato” da wannan tunanin ta koma gida hankalinta kwance.

********Tunda hajiya munubiya ta tafi take ta juya maganganun da sukayi da ita,ranta ke mata wani irin ciwo da suya,sadakarta aka bayar shine abu mafi ciwo da qona rai a wajenta,musamman da hajiya munubiyan ta gaya mata dukka familyn dr khalid akko kallon da suke mata kenan,zuwa yanzun ta soma gasgata cewa amma da anni basa qaunarta,don ta lura da wani kulawa da soyayya ta musamman da suke nunawa maimunatun tun zuwan da sukayi a shekaran jiya,sannan abubuwan da suka afkun da yadda aka turata kitchen hado masa abinci maimunatu na zaune, bayan itace qasanta,ta fita daraja ta fita mulki da kudi,babu ko tantama akwai abinda aka kitsa a shigarta kafin ta fito

“Bari na baki wani sirri guda daya,kinga wannan mijin naku,a gabanmu ya tashi,babu wani hali da dabi’arsa da bamu sani ba,bari kiji,indai kinaso ki tsira da mutunci da martabar ki,to karki ragawa kowa,ki tsaya a tsayenki sosai,ki nunawa kowa ke din daga madaukakin gida kika fito,shi kuma ja’afar,kada ki yarda ki bada kanki ta sauqi,mutum ne shi da ya tsani yaga ana nuna masa soyayya,ke ko matarsa data mutu wadda ya kusa zama mahaukaci a kanta ko nace yama zama…..don duka yake wani lokaci harda cizo idan ciwon ya motsa masa…..” tsoron da unaisa bata taba jinsa ba yanzu ya darsu a ranta,zancan da aketa fada wai wai yau sai gashi daga bakin matar qanin babansa

“Eh….Allah dai ya kiyayeku kawai ya tsare kada wata warana ya illataku…..ina gaya miki,ita kanta baqar wahala tasha a wajensa saboda nuna masa soyayya da tayi,to ki watsar dashi,kija girma da mutuncinki,ina gaya miki idan na rantse ko kaffara banyi,idan ya fahimci kedin babbace kuma me aji,da kansa zakiga yana shanshanarki,a nan zaki murza zarenki yadda kikeso” sanda ta yima anty talatu wannan bayanin cewa tayi

“Ban yarda da maganganun matar nan ba”

“Saboda me anty?,don me zata zo ta gayan qarya ko ta shiryamin zance?,bayan suna da alaqa dashi?,ita ba kishiyar babarsa ba bare nace qiyayya da kishi ya sanyata aikata haka ba,sannan ba mai jini a jiki bace bare nace sonshi take take shiryan gadar zare,hasalima ‘yarta daya kuma an sanya ranar aurenta,saura watanni biyu bikinta,bamu taba gamuwa ba sai ranar dana kai qararshi gaban anni, gida zata tafi amma saboda ni ta tsaya,da qyar ma nayi convincing dinta tazo gidana mukai wadan nan maganganun” wannan hasashen na unaisa ya sanya anty talatun itama hankalinta ya karkata

“Kuma gaskiya kika fadi,mu jarraba mu gani din”.

Ajiyar zuciya ta sauke tana komawa inda ta tashi dazun ta zauna,tana lissafa adadin kwanaki ko watanni idanma ta kama shekarar da zatayi kafin ja’afar yazo hannunta,tabbas zata tsaya akan kowa har sai sun fahimci girma da martabarta,amma batajin zata iya daukewa ja’afar qafa,babu tabbas.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram:

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply