Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 66


Gurbin Ido 66
Viral

66

*_Johannesburg_*
*_kemfton park,69 oleander avenue_*

( *Eagle rock executive guest house*)

Tun daga parking lot na guest house din maimunatu tasan wajen na dabanne,jabir da ja’afar suna gaba su kuma suna biye dasu,a hankali fatiman ke mata hira

“Zan samu na huta sosai gaskiya,wajen yamin kyua fiye da yadda sweetheart ya gayamin,anty moon,qilan fa ba zaki sake ganina ba sai ranar da zamu tafi” ta fada tana ‘yar dariya,murmushi maimunatun ta sakar mata ba tare da tace mata komai ba,don ita nata lissafin daban yake,batasan ya zaman zai kaya na kwanakin da zasuyi ita da miskilallen mutum irin ja’afar ba,sai kuma ta sake sakin murmushi da kwanyarta ta tuna mata da fuskarsa,ya yake iya rayuwa haka kuma yake jin dadinta?,kullum fuska a dinke?,zata iya rantsuwa bata taba ganin dariyarsa ba sai miskilin murmushin nan nasa,shima sanadiyyar zuwan amna ne.

A main entrance su jabir din suka tsaya,da alama sallama suke don yana karbar muqullin private entrance da kowanne apartment ke dashi,waiwayowa jabir yayi ya dagawa fatimansa hannu,sai ta dubi maimunatu

“Anty moon,Allah ya qaddara saduwarmu” murmushin ta bita itama dashi tana amsa mata,sannan ta taka zuwa gaba a hankali inda ja’afar din ke tsaye,ya fara gaba shima a hankali tabi bayansa.

“Bismillah” ya sake cewa bayan ya bude dakin,yadan dakata kadan yana karanto addu’o’in shiga sabin muhallin da ba naka ba,sannan ya sake yin bismillah ya shiga tabi bayansa.

Dakin ya tsaya yana qarewa kallo,na meye jabir zai kama musu daki irin haka,maganan gaskiya ya fara gajiya da kwanciya saman sofa,sauqin abun ma large bed ne dai dai kwanciyan mutum biyu,sai bed sofa.

Knocking akayi,sai ya bude,ma’aikatan gidan ne janye da luggage dinsa,ya karba ya maida qofan ya rufe,ya jawota tsakiyan dakin ya aje a gefe guda.

Fidda abubuwansa masu amfani ya fitar daga cikin jakar,sannan ya rage kayan jikinsa ya shige toilet.

Tana zaune daga kan bed sofa din tana qarewa dakin kallo,kadan kadan sanyin garin yana dan busata,da alama ba’a jima da dauke ruwa a garin ba,don ya dauki sanyi sosai,qofar toilet din taji an taba,ya fito daure da tattausar hoodie bathrobe,sai tayi qas da kanta,batason tayi wani motsi bare yace tayi ba dai dai ba zaiyi punishing dinta da kalar abinda ba zata iya dauka ba,tana jinsa ya gama shirinsa tsaf,qamshin turarensa ya gauraye dakin,qafafunsa ya zurawa wasu boots da suka dace da shigarsa sannan ya miqe yana dan dubanta kafin ya kauda kai

“Kiyi waya reception idan akwai abinda kike da buqata,za’a kawo dinner”

“A dawo lafiya” ta fada a tausashe,sai ya lumshe idanu yana jin yadda muryar ta sauka masa a kunnuwansa,ya juya a hankali ya fice a dakin.

Yana fita din sai taji kamar an zare mata qaya,batajin zata iya wanka a yanzu,don a haka ma sanyin ya dameta,sunci abinci cikin jirgi don haka bata jin yunwa,sai kawai ta gyara kwanciyarta ta fidda wayarta,tana kunnawa taga free wi-fi na guest house din,babu passcode,don haka tayi connecting hankalinta kwance.

Duk yadda taso sakewa dole ta dauko electric duvet ta yafawa jikinta saboda yadda sanyin ke qaruwa,bata jima sosai ba bacci yayi awon gaba da ita saboda gajiyan zaman jirgi.

Bata farka ba sai bayan sallar magariba sosai a can,ta fahimci hakan ta agogon dake dakin da kuma agogon wayarta data maidashi na can saboda gudun kubcewar sallah,tana miqewa ta fahimci akwai room heater,sai ta kunnata,cikin lokaci qalilan sanyin ya ragu,gidan shuru duka ba dadi. Tana niyyar shiga toilet don ta watsa ruwa ko zataji qwarin jikinta akayi knocking aka kawo abinci.

Ajjiyeshi tayi tayi sallah,sannan ta ware wanda zata iya ci,tana ci tana duba lokaci,duk sai ta fara jin wani iri babu dadi,ina ya tafi?,ya kuma dade har haka bai dawo ba?.tun tana dubawa har ta haqura,ta kammala tayi sallar isha’i,ta cire kayan jikinta ta shiga toilet ta hada ruwa me zafi tayi wanka.

Duka jakan kayanta ta zauna ta hautsina,sai ta dafe kanta,da alama musayar jaka tayi,ta dauki wadda tace a tafi mata da ita ta bada wadda tayi niyyar tahowa nan din da ita,sai ta koma ta zauna kamar zatayi kuka tana bin kayan da idanu.

Duk ciki bata ga wata suturar arziqi da zata sanya ba,daga night gown din har sauran kayan sawa dake ciki,ta dan jima zaune tana tunanin mafita,babu…..itace amsar,don haka ta maida hannunta tana sake daga kayan ko za’a dace.

Da qyar ta tsamo wata a ciki,wadda a ganinta tafi kowacce tsarki,Two pieces ce in da top,wine color,ta cikin siririn hannu gareta kamar na vest silk and satin,iyakarta saman gwiwa,ta saman kuwa zallar net ne,long sleeve ce ita,ta kuma sauko har qauri,gaba daya zare daya ne ya riqe ta saman wanda dashi ta daure gaban rigar.

Gaban mirror ta tsaya tana kallon kanta,iya kyau rigar tayi mata kyau fiye da kima,ita kanta taga hakan,saidai gaba daya babu sirri,kusan abinda ta rufe matan kadanne,sai tasa hannayenta tana jan top din zuwa qirjinta sosai,ko zata sake dan rufe mata wani abu,don gaba daya tudunsu ya fito sosai ta sama.

Dan qaramin tsaki taja ganin babu abinda zasu iya sake rufe mata,sai kawai ta yanke ta kammala duk abinda zatayi tayi hanzarin kwanciya kafin ya dawo,wannan yasa ta rage wutar dakin,tabar qwai daya,sai ta koma bandaki ta dauko hair drayer din data ganina ciki,saboda gashinta yadan jiqe sanda take wanka,batason kuma kwanciya da jiqaqqen kai.

Cikin gajiya jigata da kuma zazzabin da ya saukar masa ya turo qofar dakin a hankali,qarar hair drayer din ya hanata jin shigowarsa,uba uba kuma gaba daya ta sauke sumar tata zuwa gaban fuskarta,bata iya ganin komai sai gashin nata da yayi mata rumfa.

Cikin wata kasala fiye da wadda ya shigo da ita ya maida qofar ya rufe,idanuwansa a kanta,cikin wine color sleeping dress din da tayi masifar haskata,farin bayanta da fararen damtsenta ya fito ta cikin lace top din,hawan kalar jikin fatarta sai ya zama kamar wani ado na musamman,dumin dakin ya gauraye da qamshin hair mist dinta dake dai daita masa tunani a duk sanda ya shaqeshi,maimakon yaci gaba da shigowa sai ya kasa,gaba daya ya goye hannayensa a qirji,bayan ya taimakawa kansa wajen tsaiwa ta hanyar jingina da bangon dakin,yayin da idanuwansa suka ci gaba da sauka zuwa kowanne sashe na jikinta,daga bisani idanuwansa suka tuqe ga qugunta wanda yake daya daga cikin abubuwan dake daukan masa hankali.

Gaba daya ta kwashe gashin ta maidashi baya,tana hadeshi cikin dan mitsitsin robber band,tana cire drayer dinne taga kaman da mutum a dakin,a matuqar razane ya saki drayer din,ta kuma juya da sauri da niyyar neman mafaka ba tare daga gama tantance waye a tsaye ba.

Duk yadda yakejin kasala da mutuwar jiki taku uku ya kamota,da gaske ta tsorata sosai, saboda har yanzun dakin bashi da wadataccen haske,cikin wani irin coolness ya buda qirjinsa ya sanyata a ciki,ya kuma matseta gam,sannan ya dora habarsa a tsakiyar kan nata,tattausan qanshin turaren gashin yana shigar masa hanci,gami da aike da wani saqo mai nauyi a qwaqwalwa gangar jiki da zuciyarsa,ya kuma tadda mood din da yake ciki ya fara motsa abun.

“Relax……relax,it’s me,ja’afar ne” ya fada da wata karyayyiyar murya,kaman ba muryar captain ja’afar ba,mai yawan zafi da karsashi.

Ajiyar zuciya ta saki tana jin wata nutsuwa na saukar mata,ta sauke ajiyar zuciya tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa,dumin dake jikinsa yana ratsa sassalkar rigar jikinta zuwa fatarta,duk da batasan temperature na jikinsa ba,amma zuciyarta ta bata zazzabi yake,dukkaninsu sukayi shuru kowanne bugun zuciyarsa na daduwa.

Kanta ta dauke daga qirjinsa saboda yadda qamshinsa ke kashe mata kowacce gaba ta jikinta yana kuma haifar mata da wani irin feelings,tare da tuna nata waccar ranar da ta kusa hallaka yadda dumi da qamshin jikinsa ya bata nutsuwa,ta zame a hankali,sai ya sauke hannayensa a hankali wadanda ya zagaye bayanta dasu,saidai still idanuwansa dake a wani jirkice suna kallon fuskarta data yi wani fresh

“Don’t do this again,idan ka tsorata ambaton sunan Allah ake” kai ta gyada masa idanuwanta na qasa,gaba daya lissafinta a yanzu na yadda zata sutura jikinta ne,ko daya bata samu zaizo ya risketa a haka ba,tana tsoron duk wani acting a gabansa kada ya hukuntata kamar yadda yace,don ta karanci fada da cikawa ne shi din da gasken gaske.

Zamewa a hankali ta baya ya zauna kan bed sofa,yana jin wani abu na tsarga masa mai tsananin qarfi cikin kowacce jijiya da hanyar jini dake jikinsa,matsalarsa na shirin motsawa ta hade masa kuma da zazzabin da tun dazu yake faman son ganin ya kauda shi bai taba shi sosai ba.

Cikin dakiya da juriya data arama kanta ta juya ta koma bakin madubin,a matuqar tsarge take tattare kayan dake kai tana maidasu muhallinsu,duk da abubuwa da yawa batasan ma inda take ajjiyesu ba,batasan me yasa ba,amma gaba daya hankalinta ya dauku ga dumin da taji a jikinsa,wanda har ya fara jirkicewa izuwa zafi,ta gama ta juyo a hankali da nufin isuwa zuwa gado.

Ya fahimci abinda take nufin yi,amma shi idanuwansa basu shiryama hakan ba,bai taba jin wani abu da idanuwansa suka jarabtu da kallonsa ba irin maimunatu,tun yana tuhumar kansa da qaryata kansa kan cewa ba ita yake kallo ba har ya fara gasgata zaton zuciyarsa

“Hadamim coffee” ya fada yana sabule boot din qafarsa dama socks din gaba daya,lallausar qafarsa ta bayyana,ya sauketa saman rug din dake shimfide iya wajen,yana fidda wata zazzafar iska daga bakinsa

“La haula wala quwwata illa billah” ya furta a fili sanda ta bacema ganinsa zuwa qaramin falon dake manne da dakin,wanda acan aka kebance wani guri aka zuba komai na amfanin kitchen.

Wayoyinsa ya ciro da suketa kuwwa ya kashesu gaba daya ba tare da ya tsaya duba me kiran ba,ya cilla wayoyin gefan sofan da yake zaune yana jin yadda mararsa ke sake curewa waje daya tare da wani irin ciwo me suka,idanunsa ya runtse yana kuma cizar labbansa na qasa.

A hankali take takowa riqe da mug da qaramin farantinsa,rufe idanunsan da yayi ya bata damar kallonshi sosai,ba haka tasan shi ba,duk da rashin fara’a da walwalarsa amma yanayinsa ba haka yake ba

“Gashi” ta fada a tausashe tana miqa masa cup din bayan ta isa gabansa,a hankali ya bude idanunsa,suka fara sauka kan fararen cinyoyinta sa rabinsu ya bayyana saboda yadda rigar tadan tattare a jikinta,janye idanuwansa yayi yaci gaba da binta da kallo,har zuwa sanda ya isa ga qirjinta dake tsaye kyam,suka kuma cika rigar baccin sosai,duk da ta jawo lace top din ta daure da igiyar data riqe tsakanin daya gefen da daya gefan,saidai babu abinda ta qara rufe mata,illa ma sanyata da tayi tayi looking so sexy,lumshe idanunsa ya sakeyi,bugun zuciyarsa na sauya,daya tashi bude idanun sai ya saukesu kan fuskarta,wadda tadan ya mutse kadan saboda qosawa data fara yi da tsaiwar

“She’s your wife,halal dinka ne” wanin sauti mai kama da rada ya dinga gaya masa daga can qasan zuciyarsa,qoqari yake ya toshe qofar da maganar ke fita,saidai kamar qara mata girma ake a zuciyarsa,sassan jikinsa kuma yana dada bada goyon baya

Hannu ya miqa a hankali ya zare plate din dake qasan cup din ya ajjiyeshi gefe,ya maida tattausan hannun nasa ya dora saman nata,ya hada da cup din ya riqe gaba daya,kana ya janyota cikin wanin salo na bazata,bai mata masauki ko ina ba sai saman cinyarsa,tsoro da mamaki suka kusa sawa numfashinta ya dauke,sai ta tsaya cak kamar wadda jinin jikinta ya daskare.

Kaman bai aikata ba,yaci gaba da riqe hannunta,yana kai coffe din bakinsa da taimakon hannunta,tamkar dai ita ke shayar dashi,wani irin kurba yake masa,kamar baijin zafin da yake dashi,ga duk me cikakkiyar nutsuwa zai karanci kamar ba cikin cikakken hayyacinsa yake sipping coffee din ba,idanuwansa akan fuskarta data bayyanar da tsoro da razana,ko sau daya bai iya dauke idon nasa daga kanta ba.

Bai iya gama shanyewa ba ya zare cup din daga hannunta yayi wurgi dashi da sauran coffee din a ciki,kafin kwanyarta ta bata abinda ya kamata ta tuna sai taji hannayensa saman qugunta,taja numfashi mai tsaho,kamar ba zata sauke ba sai kuma ta soma fiddashi a hankali

“Har yau baki daina tsoro na ba,kuma har yau baki gayamin me kike tsoro a tare dani ba” yakai qarshen maganar yana dora hannunsa guda daya saman igiyar dake riqe da rigar cikin jikinta.

Bai bata damar bashi amsa ba taji ya ja igiyar kittt sau daya gaba daya ta warware,a hankali ya zura hannunsa a tsakanin rigar ya kuma tura hannunsa ta cikin long sleeve din,sosai tafin hannunsa ya sauka kan fatar damtsenta,taushi da dumin hannunsa ya tsarga mata,tun daga kan fata qashinta zuwa bargota,yayin da dumin nata jikin ya sake kassarashi,tare da yin gaba da duk wani sauran haquri da juriyar da yakejin yana da ita.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram:

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply