Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 69


Gurbin Ido 69
Viral

69

Ya tabbatar anni ba zata qyaleshi ba ba zata daga masa qafa ba,ko a yanzun ma baisan wanne kalar tijara zata masa ba idan ta fahimci abinda yake faruwa.

“Gaskiya kana sakani jin kunya wallahi” fatima ta fada tana jifan jabir da harara,ga mamakinta murmushi ne kwance saman fuskarsa,amma kuma hawaye ne ke shirin sauko masa,sosai hankalinta ya tashi

“Sweetheart…..menene?” Hannunta ya kama ya riqe gam yana duban fuskarta

“Real version na ja’afar dina ne ya dawo, alhamdulillah…….bansan wanne kalar godiya zan wa Allah ba,bansan wanne kalar godiya zan yima maimoon ba……jikina ya bani,sannan yanayinsa ya nuna tun daga yadda yake amsa wayata,my ja’afar has back” Sai siraran hawaye suka biyo gefan hancinsa,ajiyar Zuciya ta sauke,ta kuma riqe tafukan hannuwan nasa da kyau

“Alhamdulillah,ita zaka yita maimaitawa,sai kuma ka yawaita yima annabi salati saboda nuna zallar godiyarka ga ubangiji” kai ya jinjina yana sake qaunar matarsa,ko yaushe kalamanta akwai Allah a ciki

“In sha Allah,bansan da waa zan raba wannan farincikin ba bayan ke…..kinsan inda daa ne,ko uffan bazaice min ba,har nayi na gaji na gama,abinda bamu saba dashi ba kenan,duk miskilancin sa babu ni a cikinsa” kai ta jinjina,ita kanta taji dadin hakan sosai.

Wuni sur a dakin sukayishi shi da ita,shima kuma jabir bai sake namansa ba,sosai ta dinga dari dari dashi da kuma jin kunyarsa,don da daddare bayan ya sake sanyata ta gasa kanta,tana tsaye bayan ta fito amma taqi kallonsa,sai ya qaraso gabanta,ya dora hannunsa saman nata sannan ya dagasu ya dora kan kumatunsa na hagu da dama

“Me yasa bakison kallo na?,har yanzu tsoro na kike?,irin tsoron da nake gani a idanunki yanzu,irinsa na gani sanda hannuwana sukayi kuskuren marinki……na baki dama,ki rama marinki adadin yadda kikeso” zame hannunta tayi da sauri tana girgiza kai,ta kuma kasa ce masa komai

“Just do it….kar kiji komai” sake girgiza kanta tayi,bakinta yana rawa

“N……na yafe” shuru yayi yana sake zuba mata idanu,hannayensa zube a aljihun wandonsa yana kallonta,baya gajiya da kallonta kwata kwata,sai ya taka a hankali ya rungumeta ta baya,cikin wani sauti da yafi kama da rada ya soma magana

“Tun randa hannuwana suka kai kan fuskarki na gaza mantawa da abinda nayi mikin,nakeji ban kyauta ba,ban sani ba…..ko tun a sannan ubangiji ya zuba dukkan abinda zai zuba a tsakaninmu?,a lokacin da nake jin duk duniya ba wanda ya kaini rashi,na mareki ne a lokacin da nake cikin tsananin damuwa na rasa shaheeda da amra ta,bisa dukkan alamu Allah ya bani wata shaheedan……zaki samar min new amra?” Karon farko da murmushi mai cike da kunya ya qwace mata,sai ta juyo ta cusa kanta a qirjinsa tana murmushi,kafin kuma ta zare jikinsa a nata,binta yayi da kallo,baiso hakan ba,yaso ne su dan jima a tsaye ko hakan zai rage masa zafi.

°°°°°°°°°dukka kwanakin ukun da suka biyo bayansu kusan biqinta ya dinga yi,bai sake neman komai daga gareta ba,saboda ya tabbatar ta jigata a hannunsa,duk kuwa da cewa kawaici kawai yakeyi da kuma qoqarin kame kansa,amma yana ji a jikinsa,har yanzu bata sake masa jiki yadda yakeso ba,yanata qoqarin ganin yabi kowacce hanya data kamata da zai dasa mata soyayyarsa a ranta mai zafi,amma baiga alamun komai ba daga gareta,saidai shi din ya yadda da kansa,ya kuma tabbatar babu.macen da zata iya tsallake tarkonsa.

Shirinsa bai kammala ba,don haka sanya jabir ya gabatar masa da batun komawa sai ya dubeshi

“Wai nikam duka kwana nawa mukayi?” Cikin mamaki da dariyar yadda lissafi ya bacewa ja’afar din nasa yace

“Iya kwanakin da na gaya maka mana,har ka manta?”

“Gani nayi kamar bamu qarasa ba ko?” Yayi tambayar kamar yana kokwanto,dariya dai sai data zowa jabir

“Akramakallah mr ja’afar,kace kawai honeymoon yayi dadi” cikin basarwa ya dauke kai ya kuma sake hade fuska ganin jabir din yanason ramfoshi

“Mtsweew,matsalata dakai kenan,kawai akwai wasu ayyuka ne da ban kammalasu ba,banason kuma su zame min kwantai”

“Gaskiya ne yallabai…..saika bada himma,zaka iya kammalasu nan da yammacin gobe kafin tashin jirginmu ai,musamman idan ka samu network me kyau” kai tsaye ya fahimci inda jabir yasa gaba,sai ya shareshi kawai bai tanka masa ba.

Gyaran murya jabir din yayi

“Munata waya da anni ne,tana complain na an koma makaranta bamu dawo ba,maimoon din anata kira daga makarantarsu,har sunci satin farko”.

A sukwane ya waiwayo yana duban jabir din,sai da yaji zuciyarsa ta tsinke,tabdijan,ai shi gaba daya ma ya ma manta da wani batun makarantarta,ci gaba yayi da duban jabir din kamar wanda ke neman mafita daga garesa

“Yaya dai?” Ya tambayeshi yana dubansa,kansa ya dauke

“Nothing,kawai babu yiwuwar ta koma din”

“Banjin anni zata bari gaskiya,don tanata maganar kada a katseta”

“Eh,tunda ita ke aurenmu ba ni da ita?” Baki jabir ya bude dariya na matuqar cinsa

“Annin?”

“Eh maryam farouq kumo ba” idanu jabir ya fidda gaba daya sannan ya miqe shima kamar yadda ja’afar ya miqe

“Ah wallahi ka sha kaina,kafi qarfina,an tashi a wasan,zaka maimaita kuma a gaban wadda ka kama sunanta”

“And so what?” Ya fada cikin rashin damuwa,tunaninsa a yanzu shine kawai yadda zai fuskanci anni da maganar qin maidata makaranta,musamman idan ya tuna yadda kwashe dashi sanda take shirin hanashi kaita,hannunsa ya sanya ya shafi sumar kansa tare da furzar da iska daga bakinsa.

°°°°°°°°°°°tun saura awa guda jirginsu ya tashi zuwa nigeria suka isa OR tambo international airport din,don haka dole suka zauna a gates zaman jiran cikar lokaci.

Jabir da ja’afar gaba daya suna waje basu shigo ba,sai ita da fatima,jifa jifa suna taba hira da ita,saidai hankalinta gaba daya ya kasu kashi biyu.

Kashin farko yana ga qofa,tana duban ta inda ja’afar din xai bullo,yau kawai da suka dauki mintuna ba kusa da juna ba sai takejin kamar tayi missing wani muhimmin abu,daya kuma gefen hankalinta yana ya daukuwa ne ga wasu matasan yara su biyu,dayar a qalla zatayi shekara goma,yayin da dayar kuma takai kusan shekara sha biyar,tunda suka zauna a wajen take kallonsu,fuskarsu taketa kalla,sai take ji cikin jikinta da ruhinta kamar ta sansu,kamar ta taba rayuwa da ita,abu na biyu kuma mamarsu da tunda suka shigo wajen fuskarta na kallon babban glass dake wajen,wanda ta nan kana iya hango farfajiyar airport din da jiragen dake girke a wajen,shuru ita daya,bata magana da kowa,saidai lokaci bayan lokaci takan waiwayo tayi ma yaran dake amfani sa wata tab da alama game suke,ta musu magana ta sake maida kanta ga wajen,kamar wadda ke cikin wani zuzzurfan tunani.

A duk sanda tayi magana sai maimunatun taji gabanta yayi mummunar faduwa,saboda sautin muryar irin tata sak,kuma irin ta daadarta,saidai sautin yafi nata nuna shekaru,batasan mene yaketa fusgar hankalinta akanta ba,ta kuma gaza ganin fuskarta,sannan kuma ta gaza dauke idanuwanta daga kan ‘yanmatan.

Sau biyu babbar ciki na kallonta,itama sai ta maida kanta ga tab dinta,bata kuma sake dagowa ba,taso sosai ta daina kallon nasu don kada su tsargu,amma kuma ta gaza hakan,tana jin kamar ana fusgar idanuwanta ne.

Cikin haka taji maqogaronta ya dan bushe kadan,sai ta dubi fatima

“Bari na samo ruwa”

“Ehenn,ki tahomin dashi” a nutse ta miqe,ta fara takawa zuwa wajen dispenser dake girke a gefe guda,wadda daura take da matar da hankalinta keta daukuwa a kanta,dab da zata qarasa ja’afar din ya shigo wajen,da fari bata ganshi ba amma shi ya ganta,daga bisani ne taji kamar qamshinsa ya cika wajen,sai ta waiwaya,yana tsaye yana kallonta kansa tsaye,baya ko jin nauyin mutanen dake zazzaune a wajen.

Ta soma karantar da yawa daga cikin dabi’u da halayensa,murmushi yake mata,amma idan normal mutum ne ya kalleshi ba lallai kai tsaye ya fahimci murmushin ne,wani irin sirritaccen murmushi,sai ta dakata daga takun da take har ya cimmata,kansa tsaye ya saqalo hannunta cikin nasa,yadan ranqwafa kadan ya rage tsahonsa yakai.bakinsa ga kunnenta

“Banason ki dinga yawan zirga zirga,akwai idanuwa da yawa a nan,ina zaki?” Kaf yawun bakinta ya dauke,saboda yadda ya saukar mata da kasala,ya kuma aike mata da wani abu da ya sanya tsigar jikinta zubawa,musamman yadda yake murza tafin hannunsa cikin nata

“Ruwa zan sha” ta motsa labbanta ta fadi murya can qasa,bata ma zaci zaiji ba,sai taji yace

“Okay,muje na rakaki” tare suka jera suna takawa zuwa wajen,idanuwan mutane da yawa yayi kansu,musamman jajayen fatar dake wajen wadanda suka.kasa boye zalamarsu

“Nice couple,perfect match…..wow” sune irin sautukan da suka dinga fadi qasa qasa,duk wanann abun hankalinta nakan matar,har suka isa gaban dispenser din,ya dauki disposable cup din ya fara taara mata ruwan.

A hankali matar ta waiwayo tana duban yaran nata da idanuwanta dake nuna zallar jigata da damuwa irin wadda ke sanya idanu su xuge kamar ka shekara kana kuka

“Idan daddynku ya kira fa ku sanar mini” ta qarasa maganar idanuwanta na sauka kan fuskar maimunatu da ta waiwayo gaba daya zuwa gareta.

Cak tunaninta da kwanyarta suka daskare suka daina aiki na wucin gadi,kafin kuma su dawo dai dai,ta miqe tsaye zumbur tana duban maimunatu wadda ta zame hannunta daga na ja’afar,tanason qafafuwanta su dauketa su kaita inda matar ke tsaye amma sunqi mata wannan aikin

“Maim…. maimunatu ce?” Ta tambaya bakinta yana rawa don kawar da shakku

“Umma sa’adeee” ta fadi sunan da wani irin qarfi sannan ta kwasa da mugun gudu tayi wajenta,tana isa umma sa’aden ta bude hannuwanta ta kuma rungumeta da kyau,sannan dukkaninsu suka saki kuka a tare kamar ransu zai fice.

Kiran sunan juna sukeyi,kowa yana jin kamar a duniyar mafarki yake,yayin da yaran matar suka zubar da duk abinda sukeyi suka qaraso wajen,cikin tashin hankalin kukan da mamansu takeyi suka tsaya carko carko suna kallonta gami da kiran sunanta.

Tuni ja’afar ya riga jabir isowa wajen,shi da fatima na tsaye a bayansa shima cikin rashin fahimtar meke faruwa?,zaya matsa gaba kadan ganin yadda maimunatun sa ke kuka jabir ya riqeshi,saboda ambaton sunanta da maimunatu tayi ya tuna masa da ko wacece ita a rayuwar maimunatu.

Taga tagar da sa’ade zata fadi yasa maimunatu da yaranta tarota,ta samu ta tsaya sosai tana sake kiran sunan maimunatu,gami da dagowa tana riqe da fuskarta,wasu irin hawaye masu zafi suna mata zirya a kuncinta,tana kallon fuska mafi soyuwa a fuskar maimunatun,fuskar ‘yar uwarta qwaya daya tal data mallaka wato shatu

“Umma ki zauna,kinga shirin faduwa kike” diyarta ta fada cikin damuwa,sai maimunatu ta kamata da kyau suka koma saman abun zama suka zauna,tana riqe gam da hannun maimunatun kamar zata sake bace mata.

Sai a sannan idanuwanta ya hangi su ja’afar dake tsaye,suma sai lokacin suka ga fuskarta da kyau

“Momma?” Jabir ya fada yana dubanta

“Jabir?” Itama sa’ade ta fada tana kallonsa,sai ya matsa daga inda fatima take ya tako gabanta

“Barka da rana momma”
“Jabir barka kadai,kai da waye?,daga ina haka kake?” Ta tambayeshi fuskarta jiqe da hawayen da taketa qoqarin tsaidasu,waiwayawa yayi ya kallo ja’afar da dukka hankalinsa yake kan maimunatu,kukan da take yana ta tabashi,banda jabir ya hanashi da tuni ya isa gareta ya janyeta

“Dude” yayi kiran ja’afar a tausashe,sai a sannan yakai fuskarsa kansu,ya gane fuskar matar,matar baaba ambassador ce,kuma tamkar uwa take a wajensa,sign jabir yayi masa na ya matso,don yana tsammanin ja’afar din bai ganeta ba,saboda yasan ba shiga sha’anin mutane yakeyi ba,sai ya waiwaya ga fatima itama ya kirayeta.

“Ja’afar?” Ta kira sunansa shima sand ya iso din

“Nigeria zamu wuce,munzo hutu ne na sati daya,ga mijin maimunatu” wata ajiyar zuciya me hade da qwalla sa’ade ta sauke

“Allah kai ne Allah,Allah mai yadda yaso da bayinsa,Allah mai qaddara dukkan abinda zai afku,ubangiji kai kasan kalar abinda ka shirya har ka qaddaro min matsalar da bazan iya fita daga qasar daka ajiyeni ba tsahon shekaru,sannan kuma ka qaddaramin fitowa daga wannan qasar a yau,Allah na gode maka” sai ta rungume maimunatun sosai suna sakin sabon kuka.

Idanu ja’afar ya runtse kana ya budesu,bayason kukan da maimunatu take ko kadan,yana jinsa yana sauka can tsakiyar zuciyarsa,kiran da akema wadanda zasu tashi a jirginsu ya katse komai,saidai kuma sa’ade taqi rabuwa da maimunatu,tana riqe gam a hannunta,har zuwa sanda aka kammala komai suka shige jirgi.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply