Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 71


Gurbin Ido 71
Viral

71

Duk yadda ta zata zai barta ne ta huta ita daya hakan bai samu ba,don hatta da girki a ranar data musu na a abincin dare yana tare da ita a kitchen,waya ce a hannunsa yana duba saqonni,amma kuma ya kasa ya tsare da idanuwansa,gaba daya ya azata mata wani nauyi,baya minti uku cikakke bai dago ya ritsata da idanuwansa ba,duk sai tabi ta rude ta kuma gaza sakewa,dalilin hakan har ta yanke hannunta.

A razane ya aje wayar,ya kuma sauko daga saman cabinet din kitchen din da yake zaune a kai,ya riqe hannun da kyau yana kalla a nutse

“Hold on,ina zuwa” ya fada yana fita a kitchen din da dan sassarfarsa,babu jimawa ya dawo da first aid box

“Zauna anan” ya fada yana nuna mata inda ya tashi dazun,ba musu ta zauna,saidai yana bude akwatin hankalinta ya tashi,ta fidda idanu tana zaton ya iya allura,har ta kasa boyewa

“Don Allah……don Allah kada kiyimin allura” cak ya tsaya da neman cotton wool din da yake,ya daga shanyayyun idanuwansa ya zube a fuskarta,karon farko tunda suke dashi taga murmushi na zahiri saman fuskarsa wanda har yaso ya hadu da qaramar dariya,fararen jerarrun haqoransa suka bayyana,sai taji kamar jinin jikinta ya daskare a wajen

“Haka murmushi ke masa kyau?” Ta tambayi kanta da kanta

“Matsoraciya……kin taba ganin captain yayi allura?” Tambayar tadan sanya mata nutsuwa data tuna shi din ba likita bane,sai kunya ta kamata tayi qas da kanta,shi kuma ya janye idanuwansa yana ci gaba da neman audugar

“Ban san me yasa…..fillon da tayi kiwo da dabbobi masu yawan gaske cikin daji…..babu qawa babu aminiya amma take tsoron allura ba,kin bada fulani fa(niko nace yo dama ai sun jima da baduwa,muggan ragwage ne😏🤨🤨)” cike da mamakin maganarsa take kallon fuskarsa,saidai ko sake daga kai baiyi ba bare ya nuna yasan shi take kallo,maganganunsa sunyi kama da maganganun mutumin da yasan wani abu game da rayuwarta,bai sake tankawa ba haka itama,sai ya kama hannun nata a tausashe ya fara goge mata wajen yankan,ta runtse idanunta saboda zafin da ta danji,sai ya dakata yana duban fuskarta da rufaffun idanuwanta,yaga yadda ta kebe baki ta kuma bata rai sosai

“Na dade ina tunanin auta na aura ko diyar fari……shagwabarki tayi yawa,ashe dukka kika hada…..ga wautar dan fari,ga sakalcin auta” ya qarashe maganar miskilin murmushinsa na subucewa a labbansa.

Wannan karon dole ta bude idanuwanta tana sake kallonsa da kyau,yanata kasheta da mamaki,a ina ya santa haka,sai yayi kamar bashi yayi maganar ba,yaci gaba da wanke mata wajen,har ya gama tas ya bata pain killer.

“Abar girkin nan haka,nidai na yafe” ya fada yana rufe akwatin,sannan ya miqe tsaye,ya qarasa gaban gas din ya kasheshi,ta bishi da kallo,tana son gaya masa ya barta zata iya ta qarasa,amma sai ya tsaya gabanta yana bata hannunsa,dole ta miqa masa nata,ya jata jikinsa suka fice a kitchen din.

Duk yadda yaso dauriya daren ranar ya kasa,dole ya sake kai kansa gareta,saidai yadda ta dinga masa kuka cike da tsoro yasa ya haqura,ya sanyata a qirjinsa yana sauke ajiyar zuciya kamar zai shide,shi da ita dukka sun dauki dogon lokaci kowannensu baiyi bacci ba,saidai duk da haka ta rigashi yin baccin.

^^^^^^^^^Washegari kasa hada idanu tayi dashi,ko sau daya bata yarsa qwayar idonta ta shiga tasa ba,daren jiyan ba qaramin murzuwa tayi a hannunsa ba,duk da baikai ga gaci ba amma jikinta ko ina ciwo yake mata,har cinyoyinta ma basu tsira ba.

A haka ta dinga zuba idanu taji yayi mata zancan ta shirya komawa makaranta amma shuru,ko kadan shima bai sake tunawa da wata maganar makaranta ba,yana shiryawa zai fita gaida su amman wayar anni ta riskeshi,tace yazo shi da maimunatun takeson gani,amsa mata yayi da to,don bai kawo komai cikin ransa ba,gefe daya tun jiya zuciyarsa ke cike da mamakin unaisa?,ina taje?,ita dai ba qaramar yarinya ba bare ace bata tayi ko kuma an saceta,hakanan baiyi da ita zata fita zuwa ko ina ba,saidai duk da haka zaisa a bincika masa ko gida ta tafi.

Sanda yace ma maimunatu ta shirya zasu gidan muraran farincikinta ya gaza boyuwa,nan da nan ta buda kayanta na lefe,ta hada kaya sosai da zata kaima su annin da sunan tsaraba,ana zaune a mota yaga fitowarta,idanunsa suka dinga yawo a kanta saboda mugun kyan da tayi masa,yana zaune harta qaraso,sai ya bude murfin motar,ya zuro qafafunsa waje,ya kama hannunta ya jata zuwa ciki,bata musa ba tabi bayansa cikin fargabar kada dai yace an fasa zuwan,tuni ta narke fuska idanuwanta suka fara tara ruwan hawaye.

Closet dinta ya bude,ya fidda wasu kayan daban,sannan ya fara ware na jikin ta,hannunsa ta riqe gam tana dubansa,sai ya girgiza mata kai sannan ya zare hannunta.

Shi ya sake shiryata tsaf,ya isa da ita gaban mudubin yana tsaye a bayanta,dukkansu shi da ita suke kallon mudubin,ya sakar mata tattausan murmushi yana duban qwayar idanuwanta,yaso ya rage kyau da kaifin kwalliyar data yine,shi yasa ya shiryata da kansa,amma kuma ya gaza yin hakan,wani kyau na daban ta sakeyi.

Da wani irin zafin nama ya juyo da ita suna fuskantar juna,don har ta tsorata tana dubansa,hannunta saman kafadarsa, idanuwansa ya sauke kan jajayen lips dinta,wanda koda bata saka mishi jambaki ba iya man lebe ya wadatar ya fidda kyansa,miyansa ya tsinke,ya hadiye wani abu ta maqoshinsa,sannan yakai bakinsa saman nata a hankali yana lashe lips din nata hade da wani zafafan kisses.

Sai da ya gama kashe mata jiki gaba daya sannan ya dauke bakinsa yana sauke numfashi a hankali,sakinta yayi sai tayi taga taga kamar zata fadi saboda rashin qwarin jikinta,da sauri ya tallafe ta yana kallonta,a karon farko yaga yadda tayi laushi,don har ta cikin idanuwanta hakan sun nuna,sai ya ajjiyeta gefan gado sannan ya wuce toilet dinta a hankali.

Minti.biyu kawai ya fito yana goge fuskarsa,ya miqa mata hannunsa ta dora nata a kai sannan suka fice zuwa motar,cikinsu ba wanda ya sake cewa komai.

Yau kai tsaye sassan abbi suka fara dira,saboda khadim da suka hadu dashi yace amma da ammi duka suna can,tamkar ta nutse haka maimunatu ta dinga ji,sai take ganin kamar kowa yana karanto komai daga jikinta.

A matuqar kunyace ta gaida abbi sannan ammi,amma tana bedroom din abbin tana gyara masa gami da hada masa ruwan wanka,sai data fito ta gansu,sai ta shaidaws abbin ta gama tana qarasowa cikin falon.

Yau fuskarta dauke da wani irin murmushi da farinciki,ta qaraso tana amsa gaisuwar maimunatu gami da sanya hannunta dukka ta dagota,sai kawai ta rungumeta

“Ashe ke din jinin sa’adatu ce maimunatu?,na jima jikina yana bani kamar na sanki,kamar nasan wani da yake da.nasaba dake,ashe diyar matar dan uwana ce ke, alhamdulillah” ta qarashe maganar tana maimaita hamdalarta,yayin da kunya suka yiwa maimunatu qawanya.

Shiko jabir yana zaune qafafunsa harde da juna yana kallonsu,wani farinciki yana ratsashi,shaheeda ta tafi ga wata shaheedan,komai da yake qiyastawa na shaheeda wanda yayi missing nasa ya sameshi a wajen maimunatu,harma abinda ita din bata dashi.

Su laila nata kai kawo suna son samu space suyi hirar yaushe gamo da maimunatun amma kowacce idan ta shigo sai ta wayance da wani abun ta fice ganin ja’afar na wajen,sai da amma ta cikata da kayan ciye ciye a sassanta,amma ta kasa cin komai saboda kunyar amman da takeji

“Maimunatu,diyata ce ke yanzu ba surukata ba, maimakon ki sake sakin jikinki sai kuma ki sake dararewa?” Matsowa gaba kadan ja’afar din yayi,ya buda dukkan abinda amman ta ajjiye ya zuba mata,kafin ma ya gama amma ta miqe ta matsa a wajen.

Shanyayyun idanuwansa ya sauke mata

“Ko sau daya ban taba ganin kinci abincin kirki ba…..oya matso muci” ya fada murya can qasa,narkewa tayi kaman zata saki kuka,a shagwabe tace

“Nafa qoshi” idonsa ya lumshe yana cije labbansa,tana kasheshi…..har baisan iyakar illar da take masa ba idan tayi wannan shagwabar tata,tana jefashi a wani yanayi,har yana jin kamar bazai iya jurewa ba.

Kaman baiji me tace ba ya matso ya dauki spoon ya saka musu a ciki,ya tsareta kuma da idanunsa,dole ta dauka ta fara motsa abincin kafin takai bakinta,a spoon na biyu kuwa hannunta ya kama yakai bakinsa,idanu a waje tayi galala tana kallonsa,bayajin kunya ko tsoron kada wani ya shigo?,saidai shi ko a jikinsa,ci gaba yayi da tauna abincin,yana jin yana masa dadi a baki fiye da kullum,ko don da hannunta ta ciyar dashi?.

Wasa wasa sai gashi sunci abincin shi da ita ba laifi,shigowar anty maama yasa suka fara wucewa sassan anni ita da ita,kafin ya bisu a baya.

A nutse anni tayi mata kyakkyawan kallo guda daya,a take kuma ta fahimci komai ya kankama

“Anzo wajen,haka dama nakeso,zakaci qaniyanka” ta fada a ranta,tana amsa gaisuwa maimunatu,wadda ta duqa gabanta tana duban qafan annin data sake motsawa da ciwo,sannu take mata,tana jin ciwon annin yana taba ranta, tsohuwar nada kima da martaba a wajenta,sai ta karba man da take shafawar taci gaba da shafa mata,annin na tayata murnar na haduwarsu da sa’ade,da kuma maida zancan yadda abun ya kasance,anty maama na saka musu baki,itama har cikin ranta tana jin dadin kasancewar hakan

“Ni kaina na jima ina ganin yanayinta da anty sa’adah da fareeda,musamman fareeda,muryoyinsu kusan daya ne,duk sanda naji muryarta sai na tuna dasu,ashe jini daya ne”

“Ikon Allah kenan,ga abinda kaketa nema ashe yana kusa da kai baka sani ba” anni ta fada rana jin zuciyarta na mata dadi,abu daya ya ragewa maimunatu a yanzun shine bayyanar mahaifinta,wanda shima ta fara shirya yadda zata tunkari ja’afar da maganar,don ya kamata ayi wani abu a kai, lokaci yana dada ja.

Dai dai lokacin da yayi sallama ya shigo,kamar kowanne lokacin idanuwansa suna kan maimunatu,duk inda zaya shiga ita yake fara gani,muddin tana waje.

Qasan carfet yau din ya zauna,dab da anni da kuma maimunatu da jikinta yayi week tun shigowarsa,batason yayi wani abu da zai bata kunya a gaban anni,don haka tana gama shafawan ta ajjiye man ta matsa daga wajen.

Gaida annin ya fara yi yana mata sannu da jiki,ta amsa tana dubansa,kafin ta dauke kai tace

“Sannunku da hanya matafiya,ya gajiyar tafiya”

“Alhamdulillah” ya amsa mata hankalinshi kwance,kamar bai fahimci da gatse tayi maganar ba

“To ma sha Allah,ba wata doguwar magana bace,dama so nake na gaya maka,da Allah kayi da jiki ka maida yarinyar mutane makaranta,tunda dai amana na dauko,kai kuma alqawari ka dauka,to ya kamata ka sauke” ya manta rabon da yaji gabansa ya fadi sai yau,yadan lumshe idanuwansa sannan ya budesu yana duban anni

“Wacce makaranta?” Dubansa take saboda yadda taga zai raina mata hankali

“Makarantar da ubanka marwanu ya bude” dauke kansa yayi daga inda take,yasan anni,zata fadi fiye da haka ma,don haka ya fito mata shima a ja’afar dinsa sak

“Na cireta anni,wata zan canza mata”

“Dalili?” Ta tambayeshi harda riqe qugu tana qare masa kallo

“Kawai” ya amsata yana sassauta daurin agogon dake hannunsa,don a take yaji kamar ya matseshi ma.

“To uban maryamu,to billhuwallazi la’ilaha illa anta baka isa ba,uban kuturu ma yayi kadan ballantana na makaho,kaiiii ja’afaru,kayi ta kanka wallahi,bakasan wace maryamu ba hala,mu zaka mayar qananun mutane?,wanne irin zabine baa baka ba amma ka kafe can zaka kaita?,shine zaka tsire cireta a makaranta kanason yi mata walagigi da karatu?,to kayi qarya ka kwana da yunwa” boyayyar ajiyar zuciya ya saki,yana jin cewa ya shiga uku yau,tijarar anni ta dira a kansa

“Lemme explain you mana anni…..”

“Lamma ma taci qaniyarta,kayi ta kanka fa,idan hausa hausa idan fillanci fillanci” hannunsa yasa ya dafe goshinsa da kyau,anni bata da kyau idan ta tubure,gashi jabir baya kusa ballantana ya tayashi,shi kuma bai iya daukan hayaniya da yawa ba har haka

“Relax…..relax,ba daina karatu zatayi ba,inaso ta koma day ne,i mean jeka ka dawo”

“Baka isa bafa,ita ka fara zaba mata ita zata ci gaba da zuwa,idan kaga ta daina saidai idan itace tace bata so…..” Maida dubanta tayi ga maimunatu dake zaune,tayi shuru yana sauraren dambarwar tasu

“Ke maimunatu…..kinason komawa makarantarki……ko kin zabi dadi miji ya sauya miki wadda yaga dama?”….
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram:

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply