Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 75


Gurbin Ido 75
Viral

75

Jan files din da jabir din ya tura masa gabansa yayi ya fara budesu yana dubawa,tun baiyi nisa ba ya rufesu yana duban jabir din

“Wannan ya akayi haka?” Gyara zamansa yayi

“Kai za’a tambaya malam ja’afar,tunda dai duka sanya hannunka ne a ciki,Allah yasa banyi gaggawar yin nawa sign din ba,da asara zamu tafka ba ‘yar kadan ba” shuru yayi ya sake budawa yana kuma dubawa

“Duka cikin satin nan nutsuwarka ba’a jikinka take ba why?” Rufewar ya sakeyi yana sauke ajiyar zuciya,ya hade yatsuntsa waje daya,sai kuma ya sake warasu yana shafa sumarsa

“I’m not in a good mood jabir,anni tanason tayimin abinda zai sa na sake ajiye aikina gaba daya,very soon kuwa,idan ba haka ba zanyi ta shirme ne kawai” danne dariyarsa jabir yayi ya gyara zamansa

“Tun farko laifinka ne J,ba yadda ba’ayi dakai ba kada ka kaita boarding amma kaqi,duk abinda babba ya hango yaro bazai taba hangoshi ba”

“I made a mistake,what is the solution?” Shuru kadan jabir yayi sannan yace

“Yanzun dai kome zakayi anni zata gane setup ne kawai,so ka qara haquri ina ganin,zuwa sanda zasu gama exams su dawo gida hutu,daga nan sai kasan me zaka.shirya da zai hanata komawar” kai ja’afar ya fara girgizawa

“No… gaskiya,I can’t wait until they finish the exam,lokacin yayi tsaho”

“Okay,shikenan,do your worst……amma kasan anni dai”

“Wait…..wai ita kemin zaman auren?”

“A’ah,amma ita tayi maka auren” ya fada yana dariyar tsokana,sai akwai ja’afar din ya saki murmushi ba tare daya shirya ba yaja gajeran tsaki sannan a fili yace

“Rabbish rahli sadry,wa yassir ly amry” sai ya dauka correction fluid ya bude ya soma gyara inda yake da kuskure yana gyarawa,jabir na zaune suna tattaunawa akan kasuwancinsu.

Haka kawai ya samu kansa da yawo saman titi bayan an tashi daga office,jabir da ya dauko ya rakashi aka masa gyaran fuska ya dubeshi

“Ka yiwa Allah ka kaini gida,na gaji da wannan ragaitar,kada fa’eema ta dauka wani gun na wuce tayi fushi dani” harara ya waigo ya watsa masa,sai ya qarawa motar wuta

“Ni da kuka hada baki da anni kuka maida tawa makarantar kwana wato na mutu kenan?” Dariya sosai ya sake

“Wa ya isa ya daukar maka mata ya kaita can?,kai kakai kanka” shuru ya kasa na wasu mintuna sannan ya sauke ajiyar zuciya

“Abu daya zai hanani daukota yanzun,wannan aikin da nakeyi a kanta,amma da zarar ya kammala na daukota daga makarantar to ta fito kenan,ba ruwana da wata anni” dariya ya kuma yi,sai kuma ya katse yana cewa

“Niko kamar naji kace unaisa bata nan?,ina ta tafi?” Ajiyar zuciya ya sauke hade da wata zazzafar iska daga bakinsa,ba boye boye tsakaninsu da jabir,a nutse ya gaya masa komai.

Shuru jabir din yayi abun yana kadashi,magana ta Allah bazaiso ja’afar dinsa ya hada jini da unaisa ko ya riqeta amatsayin matar aure ba,shi kansa tun randa ya fara ganinta ya gane fuskarta,yayi shuru ne baice komai ba saboda baisan me Allah ya shirya ba,sannan kuma ma babu kyau mutumin da yayi tuba na gaskiya ka tona asirinsa,ashe da sauran rina a kaba.

Shawara ya bashi ta hankali,wadda ta kusan zuwa daya da abinda ja’afar din ya yanke,saidai shi yace ya sanar da abbi abinda ake ciki

“Ka qyaleta,idan baka iya kama barawo ba sai barawo ya kamaka,da kanta zata fadi me tayi da inda taje,idan tana taqamar gata sai gatan ya qwaceta” har suka isa gidan jabir din suna tattauna batun.

Babu yadda baiyi dashi ya shigo ciki suci abinci ba amma yace aah,ya kunna motarsa ya qara gaba,dama yasan mawuyacine ya shigo din.

Samun kansa yayi da kasa komawa gidan,saboda yasan idan ya koma din ma bawai zama zai iyayi ba,gaba daya both gidajen guda biyu babu wanda yake masa dadi,yaja tsaki yafi a qirga a saman titi,kafin ya yanke ya tafi gidansu kawai ko zai rage tsahon dare a can.

Ganin lokacin sallar magrib ya kusa sai ya sanyashi zama saman motar abinsa ba tare daga shiga cikin gidan ba bayan ya faka motar a parking lot na gidan,ya fidda wayarsa ya soma dannawa,kusan babu wanda yasan ya shigo idan banda ma’aikatan gidan.

Bai rufa minti ashirin ba aka sake hon,mai gadin ya tashi ya sake budewa,sau daya ya daga kai ya kalli motar,sai ya maida kansa yaci gaba da danna wayarsa,motar hisham ce,ta gangaro gefansa tayi parking.

Sosai abbi dake zaune gefan hisham din yadan kafe ja’afar da ido wanda.baima san waye da waye a cikin motar ba

“Miskili kafi mahaukaci ban haushi” abbaya fada yana murmushi yana duban fuskar ja’afar din,kallonsa hisham yayi shima yana taya abbi murmushin,ya karanci kamar akwai damuwa akan fuskarsa,amma ba wanda zai iya buda baki ya gayawa,yasan bazai wuce case dinsa da anni ba,ko kuma unaisa da yau minister ya kirashi ya gaya masa cewa ya turo ta gida ba tare da sunsan meye ya faru ba,bude murfin motar abbi yayi yana cewa hisham ya biyo shi da jakarsa.

Yana ganin abbi din ya ajjiye wayarsa ya duro daga bayan motar ya tako inda yake cikin girmamawa yana masa sannu da zuwa

“Yauwa ja’afar,ya gida ya iyali?”

“Alhmdlh abbi” ya fada yana shafa kansa

“To masha Allah,bari na shiga ciki na fito sai mu wuce masallaci tare ko?”

“Okay abbi” ya amsa masa,zuwa sannan hisham ya qaraso,ya miqa masa hannu sukayi musabaha yana gaida yayan nashi,sannan suka rankaya ciki suka barshi a wajen.

Babu jimawa abbi ya fito da alwalarsa,tuni shima yayi tasa a bayan gidan suka wuce masallacin.

Bayan an idar a hanyar dawowarsu abbin yake tambayarsa

“Me yarinyar nan unaisa tayi maka manya?,abun kuma har yayi girman da zaka turata gida?” Abbin ya fada a tausashe,duk da tsauri da zafinsa amma yana sauqin kai da kuma saurin fahimtar al’amura

“Abbi,tafi kowa sanin abinda tayi,ita ya kamata ta gaya musu da bakinta” kai ya girgixa

“Yanzun ai ni nake tanbayarka bawai su ba,me tayi maka,ka gayamin ko mene ne,sai asan yadda zq’a gyara abun” kai ya girgiza

“Abbi…..banajin zai gyaru”

“Meye wanda bazai gyaru ba?” A nutse ya gaya masa dukka wani abu daya taba sani a baya akan unaisan,da kuma abinda ya farun yanzu da binciken da yayi da hujjojin da ya samu.

Sosai abbin ya kadu,don bai taba kawowa yarinyar haka ba,duk yadda suke takatsantsan wajen samawa ‘ya’yansu maza da mata abokan rayuwa na gari,amma duk da hakan bai nunawa ja’afar din ba sai yace

“Ka barni da kaina zan sake bincike”

“To abbi” ya fada hankalinsa a kwance,tunda dai ya sani,koda abbin din zaiyi binciken zai binciko kwatankwacin abinda shi ya samu ne koma wanda ya fishi.

Zuciyarsa ce ta dinga raya masa ya yiwa abbi zancan maimunatu,sai kuma yaga bazai iya ba,don haka ya share batun,yasan dai akwai lokacin daya dibama koma meye anni ta shirya.

Sassan amma suka wuce shida abbin din gaba daya,saboda yace yunwa yakeji,yau da wuri zaici abincin darensa,baya wasa da girkin amman,saboda yadda ta qware sosai wajen sarrafa abinci,tarin masu aiki ko sarauta ko arziqin da take dashi baisa ta sako abincin mijinta ba hannun yara ko masu aiki,har yau har kwanan gobe ita keyi,saidai a tayata.

Amma na shirya musu abinci suna fira sama sama,bayan ta gama itama sai ta samu kanta da zama a cikinsu,abinda ba kasafai takeyinsa ba,duk da ita bacin abincin take ba,tana ta dai serving dinsu ne,daga baya saiga hisham ya shigo shima yayi joining dinsu, khadim ma sai gashi,da yake sau tari sai ya baro abincin ammi ya taho wajen amma ci,duk da itama ammin gwana ce,amma shi dan dakin amma ne.

Bai waiwayi sassan anni ba sai da ya dawo daga sallar isha’i ya kusa wucewa gida,tasan ya shigo gidan sarai,kuma batayi mamakin rashin shigowarsa ba,sanda ya shiga tana zaune a falo tana shan damammiyar fura data sha sugar,don annin ba daga nan ba wajen shan zaqi,kanta ta daga ta dubeshi sannan ta tabe baki ta maida kanta ga abinda takeyi,ya samu hannun kujera ya zauna yana gaidata,a yatsine ta amsa masa,yadan zubawa tv ido sannan ya miqe

“Wannan sugar din da kike yawan sha fa yana yawa,shekarunki sun ja” dama jiransa take,saboda haushin qin shigo matan da baiyi ba,saboda ta saba anan yake sauka ko yaushe bayan ya gama gaisawa da kowa

“Kai arcannnn…….kayi ta kanka malami,mu jikinmu ba irin naku bane, sugar abin banza ba abinda zaiyi mana,haka zamu mutu ras da lafiyarmu in sha Allah,damu da mazanmu ba irinku bane,wanda sai mace ta shekare a gidansu su kasa yi mata ciki sabodq tsabar raggwanta” dole ya dora idanunsa akan fuskar anni,tirqashi😂, abun yazo harda gori?,ya tabbatar dashi take,shi takema gorin baima maimunatu ciki ba,don yasan itace tata,da ita ta damu.

Murmushin gefan baki ya saki yana cusa hannuwansa a aljihun wandonsa,shima bari yayi mata ta ‘yan zamani

“Me kike ci na baka na zuba anni?,ba tsallaken shekara daya bane?,to itama za’a ciketa,ki rubuta ki ajjiye biyu xa’a baki ko uku,nex year mu sake maimaitawa” daga haka ya juya yana ficewa daga falon,sai ta bishi da kallo,tana jin sanyi qasan ranta tare da cewa

“Ameen ya hayyu ya qayyumu,’yan ameen su amsa ya rahman” can qasan ranta,amma a fili sai tace

“Ahhh waima,zamu gani”.

Yana mota yana tuna matter dinsu da anni,sai kawai ya samu kansa da sakin murmushi,tare da imagining diyoyi daga wajen maimunatu,wanne irin kyau zasuyi?.

Duk guje gujensa yau dinma sai da yasha baqar wahala kafin ya samu bacci ya daukeshi
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply