Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 78


Gurbin Ido 78
Viral

78

Wata shirt ta zaqulo,tana da dan fadi daban,dama irinta take nema,sai ta zura,tayi amfani da turarensa ta feshi jikinta,sannan ta dauki hair drayer dinsa ta fara busar da gashinta da ya dan jiqe,ta gama fa shafeshi da mansa mai qamshi,sannan ta dauki band ya fara kiciniyar daurawa.

Duk tsaiwarsa a dakin sai lokacin ya qaraso,sai daya iso dab da bayanta sannan yayi sallama,ta fito da idanunta tana kallon fuskarsa data sauya,daga fuskar da babu rahamar fa’a zuwa fuskar data saba da murmushi ciki yan mintuna qalilan,ya soma takowa zuwa inda take tsayen.

“wa yace ki sakamin riga?” Ya fada cikin sigar tsokana,amma kuma yana dan bata rai,narai narai tayi da idanu tana langabe kai

“Banga kayan da zan saka ba” kai ya jinjina yana isowa dab da ita,ya sanya hannuwansa duka biyu ya nade rigar sama ya riqe qugunta yana kallon fuskarta,tafin hannuwansa saman lallausar fatar jikinta yana kallon tsakiyar idanuwanta

“Gaskiya bazan iya baki aro ba,nima ita zan saka” yayi maganar yana tafiya da hannayensa zuwa sama,inda yake ta tsole masa ido tare da jan hankalinsa,narai narai ta sakeyi da ido,a narke tace

“Please mana,aro kawai?” Kai ya girgiza

“Bazan iya ba”

“Don Allah”

“Ok,but let me feel your…..” Sai maganar bakinsa ta.katse, numfashin sa ya fusga kadan,saboda tuni yakai.hannuwansa inda ya nufa,kafin tace komai ya tsugunna ta qasan rigar ya cusa kansa.

Fara qoqarin zamewa tayi amma inaa,ya saka dukka hannuwansa biyu ya riqeta sosai ta bayanta,cikin qanqanin lokaci ya fara birkita mata kwanya,saqonnin da yake aikema qwaqwalwartata sun girmama,ta fara tangal tangal zata fadi,sai ya zare kansa daga ciki yana dubanta da idanuwansa da suka sauya launi

“Please nima,ki sanmin dan kadan,i promise you wannan karon no more any pain…..i promise…..i promise angel” ya fada a dan rude saboda yadda hankalinsa yayi gaba.

Bata jin dadi idan taganshi a gabanta cikin kwantar da kai yana roqarta akan hakkinsa,a hankali ta gyada masa kai tana lumshe idanu,caraf taji ya sureta yana cewa

“Thank you angel moon, thank you” ya azata a tausashe saman gadon ya maye gurbin duvet yana sanyata tsakiyar qirjinsa gami da sake lullubeta da wata tattausar soyayya mai dimautarwa da kuma gigita hankali.

Kaman yadda yayi mata alqawarin kuwa babu wani sauran radadi data fuskanta,saima tarin kunya da ya barta da ita, saboda yayi ta koya mata abubuwa yana sanyata tana responding masa saqonninsa,abinda ya basu wani irin dare mai matuqar qayatarwa,daren daya sake.narkar da kowannensu,ya kuma sukurkutar masa da tunani,ya sake dasa musu so da qaunar juna mai tsanani.

Ko bayan komai ya kammala cikin jikinsa ya matseta tsam,idanunsa a rufe yake cewa

“Let’s make this lovely journey last for a lifetime,do not ever let me go,am yours as long as you want me to” wani irin abu taji yana sulalewa yana kwaranya a kwanyarta,ta gyada masa kai a hankali ta lumshe idanu tana jinta a wata duniya ta daban,dama haka soyayya take?,sai ta tuna da wani korean drama data gani,kamar haka a lokacin ta dinga imagining kanta,amma sai zuciyarta ke gaya mata it can’t,ashe zai yiwu,harma fiye da yadda take hasashe.

°°°°°°°°°°shi da ita dukkaninsu a shirye suke tsaf,ita cikin shirin komawa makaranta,shi kuma cikin shirin office,tsaye take shima haka,tana rungume tsakiyar qirjinsa suna musayar numfashin juna da kuma scents na turarukansu,kowannensu ji yake kamar bazai iya tafiya yabar dayan ba,cikin wata karyayyiyar murya yace

“Can we go?” Ta gyada masa kanta a hankali zuciyarta na karyewa kamar kuka zai subuce mata

“Okay angel…..but,inason naji kalma daya a bakinki,me yasa kikemin rowarta,baki taba gayamin ba” sai data daga kai ta kalleshi sannan ta tambayeshi

“I want you to say i love you ja’afar” murmushi tayi tana cusa kanta sosai cikin qirjinsa,kunya….kunya takeji wallahi,tun jiya ya gama sakwarkwatar da ita gaba daya

“Uhnnnn…. please,say it” ajiyar zuciya ta sauke,tana jin yadda zuciyarta keta azalzalarta kan ta fada din,cikin wata irin murya dake dauke da amo na daban ta fadi

“Ina sonka,ina qaunarka…..i love you”

“Da gaske daga zuciyarki ne?” Saita jinjina masa kai cike da qwarin gwiwa

“Ina nufin dukka abinda na fadi din,da gaske nake,daga zuciyata ne” zallar farinciki ya kamashi,sai kawai ya hadeta cikin jikinsa,ta sauke ajiyar zuciya tana jin dadin kasancewarta a qirjinsa,akwai wata nutsuwa mai tarin yawa tattare da gurin,har batasan tayi subutar bakin furtawa ba

“Hugging someone taller than you is the best feeling ever,bcoz you fell protected” wani murmushi mai dadi ne ya subuce masa,ya dagota yana duban fuskarta dake a kulle

“Really?” Kai tsaye ta gyada masa kai

“Zanci gaba da rungumarki har gaban abada,kuma.koda baki a jikina cikin qirjina kina zuciyata,and i will give you protection everywhere you go bakin rai bakin fama”. Da qyar suka yakice juna ya dauketa sai makaranta.

Ko cikin mota sai data kusa missing first period sannan ya barta,ta wuce dakunansu ta saka uniform ta koma aji,shi kuma yaje yayi confirming maidota da yayi yayi singing.

Tun a aji suka dameta da iskanci su afra,saita sharesu saidai tana ta smiling,saboda ita kanta tasan jiyan tabar mata abubuwa masu yawa da bazata.mance dasu ba,su afra kuwa haka ta haqura da tsiyar da suketa mata har sukayi haquri sukayi shuru.

Tofa captain ja’afar da maimunatu sun fasa dadin abun,kwana daya rak yaji ya kasa sukuni,da qyar ya raka zuwa qarshen sati ran Friday ya sake zuwa ya nema alfarma ya daukota,tazo tayi masa weekend,idan yaso Sunday da yamma ko Monday da sassafe ya maidota.

Wani irin weekend mai bada kala sukayi, weekend din da tunda yazo duniya baijin akwai wanda ya fishi dadi a wajensa,ran litinin kuwa basu samu fita daga gidan ba sai azahar,da qyar ya taushi kansa,yana da tabbacin ya kusa gazawa,haqurinsa ya kusa qarewa,don haka ya sama kansa more effort ya gama aikin da xai sanya ya fake dashi ya raba maimunatu da makarantar gaba daya ta silarsa.

K’arfe shida da mintuna ya shiga gidansu kamar yadda yawancin lokuta yake zuwa a yanzun,amma sai ya wuce sassan ammansa,ya sameta a falonta a zaune,ita daya saboda yaran basu dawo a islamiyya ba,duk girmanki a gidan dr marwan baki wuce zuwa islamiyya ba,har su salma ‘yan university da ake shirin aurarwa,kasancewarsa sanannen mai ilimin addini,yakance neman ilimi baya qarewa dan adam sai idan mutuwa yayi,akwai makaranta nan saman unguwarsu me special classes irin nasu.

Duqawa yayi nan gabanta ya gaidata,sannan ya zame ya zauna sosai yana jan fruit din dake gabanta hade da qaramar wuqa tana gyarawa,da alama zatayi fruit salad ne, murmushi ta bishi dashi,har yau baya ganin ya girma ko ya taka wani matsayin da zai hanashi kama mata aiki idan yazo ya taras tana yi.

“Manya,me yake faruwa tsakaninka da unaisa ne?” Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke,duk duniya baya iya boyema mahaifiyarsa komai,don haka ya labarta mata komai a nutse.

Sosai hankalinta ya tashi,amma kuma bata nuna masa ba

“Haquri ake da sha’aninmu,tunda ai bata taba aikata hakan ba,sai ka bata uzuri” kai kawai ya gyadawa ammansa,amma bayajin zai taba iya riqe unaisa,bayason suci gaba da zama yana zaluntarta Allah ya kamashi kan hakan.

Bai tashi a kai ba sai da suka gama aikin duka tare sannan ya daura alwala ya fice sallar magariba.

Daya dawo wajen anni ya wuce,itama tana falo baba tabawa na gefanta suna kallon musabaqar duniya da ake haskowa a wata channel,wata ‘yar nigeria ce ke karatun a yanzun,suna ta tattaunawa akai,saidai kowanne hannunsa riqe da carbi da alama basu jima da gama sallah ba. Baba tabawa ce ta miqe tana marabtarsa

“Barka da zuwa” ya amsa mata cikin girmamawa yana zama,sannan suka gaisa

“Ina uwar dakina?,tayi mana nisa”

“Suna makaranta”

“Uhmmm…. makaranta ko gantali daga wannan kwararo zuwa wancan?” Anni ta fada tana tabe baki,daga kai yayi ya kalleta,sai kawai murmushi ya subuce masa,shi qarfin halin anni dariya yake basa,batasan a yau idan yaso.maimunatu ta gama zuwa makaranta ba?,ya fita iya kwaso rigima sosai,amma tana da wani babban matsayi a rayuwarsa,sannan she deserved respect daga wajen kowannensu,don ta taka rawar gani a rayuwar duk wani ahali nata

“A daiyi haquri a sassauta”

“Yoni ai bazan dauki wannan iskantun ba,kowa ta kansa zaiyi ya shiga hankalinsa,bazan bari a haifamin jika tsakanin qarya da gaskiya ba”

“Kin samawa kanki sauqi” ya fada hankalinsa kwance yana relaxing cikin kujerun hadi da lumshe idanu,dariya taso qwacewa baba tabawa saita fice,yayin da annin ta watsa masa daquwa

“Kayi ta kanka ja’afaru ka kiyayeni fa?”

“Na kiyeyeki” ya fada ba tare daya bude idanunsa ba,don shi yanzunma weekend dinsu na baya yake tunowa yana sa masa nishadi,tare da shirya musu next weekend yadda zai wakana.

Kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai abbi ya shigo,cikin girmamawa ya miqe yana masa sannu da zuwa,bai zauna ba sai da abbin ya samu waje ya zauna nan kusa da tsohuwarshi

“Dama ina nemanka,naji dadi dana ganka” sai yayi bismillah yana zama

“Zauna” ya bashi umarni,ya aikata hakan yana tattara hankalinsa akan abbi din.

Maganganu ne duka kan unaisa,da yadda tace batasan wani abu daya faru ba,qarshe ma dai saita buge da fadin irin zaman da sukayi,shuru ne ya biyo baya,anni tana ta jeranta abubuwan cikin ranta,ita gaba daya yarinyar bata yi mata ba,sannan data sake kawo mata qara ta kuma kalli tsantsar idanunta tace mata ayi masa fada bata taba kwanan turaka ba saita qarasa sare mata a rai,babu kunya ko qanqani cikin lamarinta,sannan ita kanta ta sanya cikin jikokinta sun mata bincike,sakamakon ba mai dadi bane, saidai dan yau baka bashi qofa haka kai tsaye.

Shima abbi din kusan hakan take,amma bayaso lokaci guda ya bashi go ahead na aikata wani abu,saboda gudun halin dan yau,don haka yace dashi

“Ka samu lokaci kaje ku fahimci juna ka dawo da ita dakinta”

“Zan samu lokaci” yace da abbin kawai,yanayin fuskarsu kawai ya nuna suma akwai abinda suke dannewa.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram:

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply