Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 79


Gurbin Ido 79
Viral

79

Weekend na musamman suka sakeyi kamar yadda ya shirya musu,don wannan karon daga makaranta kai tsaye airport suka zarce,already ya siya musu ticket zuwa kano,akwai aikin duba ginin company dinsa da yakeyi,cikin ‘yan awanni ya gama dubawar suka sauka a Bristol palace,a nan suka more amarcinsu sosai,kwanaki biyun da sukayi ta sakar masa zuciyarta harma da gangar jikinta,wani sabo da shaquwa ne sosai suka shiga tsakaninsu.

Ta dauka Sunday ko Monday da sassafe zasu wuce,amma sai taji baice komai ba,itama kunya da nauyinsu take ji shi yasa bata tanka masa ba,ta fuskanci makarantar takai masa ko ina,kawai lallabawa yake yana ma anni kawaici.

Da wani yammaci tana zaune a balcony din dake gaban dakinsu,saman wani table dan qarami mai kujeru guda biyu,gabanta littatafanta data taho dasu saboda assignment da aka basu wanda yake a mazaunin test.

Sosai hankalinta yayi gaba tanata rubutu,yana tsaye a bayanta bata sani ba,hannuwansa cikin aljihun trouser dinsa,yana sanye da slim fit shirt mai gajeran hannu,wadda ta zaune ta lafe a jikinsa,ta kuma fidda qirarsa na cikakken namiji.

Murmushi yadan saka sanda ta daga hannunta tadan yarfeshi kadan,alamun ta gaji da rubutun,ji yake kamar ya dauketa.ya hadiyeta,wani irin zazzafan so ne nata yake shigarsa zuwa kowanne sashe na jikinsa,sai ya fara takawa sannu sannu har zuwa bayanta,ya tsaya sannan ya miqa hannunsa ta gefan kafadarta ya ranqwafa faffadan qirjinsa yana gogar bayanta,ya sanya tafin hannunsa ya rufe rabin littafin.

Duk sanda ya kalleta ya tuna alkhairin dake shirin fuskantar rayuwarta sai yaji wani madaukakin farinciki yana ratsashi,yaya zata dauki lamarin?,zuciyarya zata samu wannan juriyar kuwa?,wannan shine tambayar da yakema kansa.

Cak ta tsaya da rubutun,murmushi na tashi akan fuskarta,sai ga cira kai a hankali ta waiwaya tana dubansa,take idanuwansu suka sarqe waje daya, fuskokinsu gab da juna,numfashinsu ya fara gauraya waje guda,kusan lokaci daya kuma a tare kowannensu yadan lumshe idanunsa kana ya bude, ja’afar din baice komai ba,sai ya sanya daya hannun nasa ya zare biron dake tsakanin yatsunta ya aje,sannan ya saka hannuwansa biyu ya dagata cak ya ture kujerar ya kuma dorata saman table din,sannan ya sake jawo kujerar gabanta,ya zauna a kai,ya kuma matso da ita dab da ita kamar zai shige cikinta,ya kwashi qafafunta ya dorasu saman qafarta.

Da kallo yabi qafafun nata,farare sol babu digon komai a kai,sai na baqin lalle sidik sake saman faratan yatsun nata,wanda hakan ya zama musu wani ado na musamman.

Hannu yasa ya fara mata tafiyar tsutsa a qafar tata,sai ta qyalqyala dariya tare da qoqarin janye qafartata tana jin wani iri

“Ka bari……don Allah”

“Don Allah wa?” Ya tambayeta yana kallon fuskarta,wani irin murmushi mai cike da shauqi kwance saman fuskarsa

“Nidai don Allah”

“Nace don Allah wa ?,yau sai kin fada,idan ba haka ba?,……. tom” sai yaci gaba dayi,wannan karon har saman qafarta zuwa qaurinta

“Don Allah my baby,my hot baby……..my life line…..my hubby…..my other half…..my moonlight” dukka ta hada ta fada tana dariya tare da son ya cikata,cak ya tsaya yana lumshe idanu

“Wow……wow….. great!” Ya fada yana sakin murmushi sannan ya dubi idanunta da wani irin taushi

“Fantastic I really enjoy these names moon angel…….,you have the best gift ever let me give it to you” bata qara wani tunani ba ya miqe tsaye ya sunkuceta,ta cikin balcony din ya buda qofar Glass din suka zarce bedroom dinsu.

Wani irin hot romance ya dinga aje mata da wasu kisses masu zafi,wani saqo me nauyi da tsayawa a rai ya dinge ajema kowacce gaba ta jikinta,sun jima a haka kafin su nutsa duniyar ma’aurata,wadda suka jima da tsarata hadi da killaceta da wasu irin abubuwa masu sanya abokin rayuwarka ya tsaye maka a rai.

Tana saman mirror yana busar mata da kai da band drayer,daure take da towel wanda ya dan zame kadan yana nuna fararen qirjinta da kuma tudunsu ta sama,abinda yake yawan tafi da hankalinsa kenan,shima din towel din ne daure a qugunsa,yana busar mata da kan idanuwanta na saman gargasar qirjinsa da ko yaushe taje burgeta,tana daya daga cikin abubuwan dake sanya mata nishadi,tana da laushi sosai,hakanan wani qamshi take bayarwa na musamman

“Yaushe zamu koma,akwai assignment da yawa a hannuna a satin nan” ta fada a hankali da muryarta mai taushi,duk da can qasan ranta tana jinne kamar zai maidata kurkuku.

Ajiyar zuciya ya sauke,sai ya juyar da ita tana fuskantar madubi sosai,idanunsu cikin na juna,ya motsa labbansa a hankali

“Angel…..na tsani makarantar nan totally yanzu…… you are my perfect place to go when my mind searches for peace,ta yaya zanso rabuwarmu kota second daya?,…..you are my world angel,if i could have one wish…..i would wish to wakeup every day to the thousand of your breath on my neck,the warmth of your lips on my cheek,the touch of your fingers on my skin and the feel of your heart beating with mine,ba abinda yafi min wannan dadi a rayuwata” ya qarashe fada yana nutsa yatsunsa cikin gashinta don ya tabbatar ko.ina ya bushe, idanuwansa kuma cikin nata,sai taja numfashi sosai,ta kuma lumshe idanunta,hannayenta ta bude gaba daya,ya saki tattausan murmushi shima ya bata dama tayi huggin dinsa sosai,a hankali tace

“Ka sakani jin cewa ni wata mutum ce ta daban,ka saka duniyata cikin nutsuwa ka sani inajin cewa am protected tako ina kuma am loved,i don’t ever want to live my life without you by my side”

“Don’t kill me please babe” ya fada yana dariya

“Abun zaimin yawa,ga huggin da wadan nan kalaman masu zaqi?” Sai ya bata kunya ta cukuikuyeshi da kyau, shi kuma yana dariya abinsa,kafin a hankali ya rage sautin murmushin da yake yi din

“Oya,sauko ki shirya,don idan naci gaba da ganinki a haka komai yana iya faruwa,ni kuma so nake kiyi alwala.kiyi salla raka’a biyu,ki godema Allah,akwai muhimmin al’amarin da yake shirin tunkaroki” daga kanta tayi a hankali gabanta yana faduwa tana dubansa

“Menene?” Murmushi ya sakar mata saboda ya hangi tsoro da karaya a tattare da ita,sai yasa yatsansa ya lakace mata hanci

“Matsoraciya,khairan in sha Allah” shuru ta sakeyi,sai ya riqeta sosai

“Baki yarda dani ba?”

“I trust you”

“Oya…..do what I said to you” saita jinjina kanta,ya riqe mata hannu ta zamo a hankali qasan mudubin.

Duk yadda taso ta manta da abinda yace matan ta kasa,tayi sallar harma sun wuce raka’o’in da yace mata,haka kawai takejin kasala da mutuwar jiki,gefe guda kuma kamar zazzabi zai kamata.

Wayarta dake gefanta ce ta fara haske ba tare da fitar sauti ba,duk sanda suke a tare ita dashi irin hakan wayoyinsu dukka a silent yake sanya musu idanma anci sa’a bai karba ya kashe ba,yakance basa buqatar kowa basa kuma buqatar komai,daga shi sai ita,duniyarsu ce wannan so basason kutsen kowanne abu.

Dubawa tayi sai taga afra,ta shafa addu’ar da takeyi ta janyo wayar tana amsawa,bayan sun gaisa tace mata

“Kin ganni a hanyar gida daga makaranta,zanje na duba jikin daddy,jiya muslim (qaninta) yacemin basuyi barci ba,jikinsa ya motsa,wai amma hajja ke boyemin don kada nazo,ta yaya zan iya zama maimoon?,ko tsanani jikin yayi basu gayan ba oho” cikin sigar lallashi da kwantar da murya tace

“Kai haba,bana jin haka,ki kwantar da hankalinki ba komai.in sha Allah” ta bata qwarin gwiwa sosai kuma afran ta samu qwarin gwiwar,sannan sukayi sallama tana cewa

“Ki gaida hajjan da daddyn duka,Allah ya qara afuwa” jikinta a sanyaye ta ajjiye wayar bayan sunyi sallamar,aai tadan fada tunani kadan,kafin J ya shigo ya kore kowanne tunani da fargabar da taketa tsintar kanta a ciki.

Bayan sunyi sallar isha’i motar hotel din ta daukesu zuwa shoprite,yace tayi siya duk abinda take so,kusan su amna amma dasu anni da kuma su laila ta yiwa tsaraba,sai ya tsaya yana kallonta kafin yadan ranqwasheta a tausashe

“Kin manta dani?,su anni kawai kika sani?” Ya fada yana narke fuska kamar qaramin yaro,sai abun ya bata dariya har haqoranta suna bayyana

“Ta yaya zan manta dakai?” Ta fada tana janyo daya cart din dake gefanta.

Luxuries undies ne masu kyau da tsada na maza a ciki,handkerchief perfumes da pyjamas masu shegen kyau,sosai yaji ta burgeshi qwarai, sai ya danyi hugging dinta ta kafadarsa

“Thank you,thank you my angel moon”sai kuma yace

“Amma banga taki siyayyar ba da kuma ta baby na”

“Ka wadatani da komai,bana buqatar komai…..baby kuma wanne bayan amneee na?” Fuskarta ya daga da yatsunsa yana kallonta,kamar mai rada ya rage murya can qasa

“Baby unborn” ya fadi yana shafar cikinta da hannunsa,turesa tayi tana turo baki hadi da sakin murmushin jin kunya,dariya ya saki yana sake jawota jikinsa

“Am serious,bana aikin banza,jikina yana bani very soon amneee zata samu brothers and sisters” ido ta fiddo

“Bama brother ko sister ba?,harda qari?” Kai ya jinjina

“Yeah,i trust my self cikin ikon Allah bana bada iri guda daya,ga example akan amna…..niba rago bane,sannan Allah na na sona,yasan inason yara da yawa” dukansa ta soma yi cikin wasa tana sake tureshi

“Nidai ka daina fada please”

“Zaki sani ne,na riga na bada ajiya kuma an karba,so sai randa zan karba kayata in sha Allah kawai nake jira” ta fuskanci yau din yan tsokanar suna kusa,dibanta kawai zaiyita yi,dole ya haqura ta barshi kawai,saidai kuma maganarsa tayi ta sakata murmushi ita kadai

“Ni ba rago bane…..yes,ta shaida haka” ta fadi a ranta,sai kuma taji kunyar kanta da kanta,ta saki murmushi kawai.
[11/25, 7:22 AM] Safiyyatulkiram:

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply