Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 81


Gurbin Ido 81
Viral

81

Tare da anni da baba tabawa suka tafi,akabar ammi a nan,saboda baba tabawan zataje tayo girki sai ta dawo sannan ammi ta tafi,shima abbi acan suka barshi.

Suna hanya suna tattauna yadda abubuwan suka kasance,anni ta saki ajiyar zuciya

“Kaidai manya Allah ubangiji yayi maka albarka,ka gama min komai,abinda yake kullum cikin nuri da mafarkina yau gashi ga cikamin shi,na sake tabbatarwa na kuma samu nutsuwa kan zamantakewarka da maimunatu,Allah yayi maka albarka” murmushi kawai ya saki baice komai ba,yau anni ke magana dashi a haka,tabbas ba qaramin dadi abubuwan sukayi mata ba.

A reception ammi ta zauna ta bawa hajja da maimunatu waje,hajjan na zaune gaban maimunatu,hannunta cikin na maimunatun tana kallonta,tana jin kamar ta maidata cikinta,kota ina ka kalleta zaka san jininta ce ita,ta dauko wasu abubuwa nasu sosai,duk da kamanninta sunfi.rinjaye dana mahaifiyarta,wadda hajja bata taba gani ba sai a hoto.

Itama maimunatun kallon fuskar dattijuwar take,tana jin wani farinciki mara misaltuwa yana saukar mata,wai yau itace take da kaaka?,yau itace zaune gata ga mahaifiyar mahaifinta?,abun sai take jinsa kamar a mafarki,amma kuma tana mata yanayi da wata fuska data sani

“Sannu diyam,sannunki,ina mahaifiyarki?,ina fata batayi fushi da abubakar ba?,bata masa kuma mummunan fahimta ba?, jarrabawa ce ta samu abubukar,qaddarar rayuwa da kowanne bawa baya iya tsallake mata” hajjan ta fada tana share qwalla

“Daadata ta rasu” maimunatu ta fada muryarta a karye tana rawa,cikin kaduwa hajja ta kalleta

“Aishatu ta rasu?,wayyo abubukar,bansan yadda zaka dauki wannan qaddarar ba,ina dan uwa ko ‘yar uwarki da mahaifinku ya tafi ya bari da cikinsa?”

“Ta rasu wajen haihuwarsa” ta fada tana rushewa da kuka,sai hajja ta jata zuwa cikin jikinta tana tayata kukan,sosai maimunatu ta dinga jin wata nutsuwa da sukuni sanda take jikin hajjan,sai taji kamar wani sashe na mahaifiyarta ne ya dawo.

Sautin kuka suka fara ji daga bakin qofar dakin sannan kuma aka turo qofar,afra ce sanye da hijab har qasa,amma idanuwanta shabe shabe da hawaye.

Tashi maimunatu tayi daga jikin hajjan tana duban afra cikin mamakin yadda akayi tasan bata da lafiya tazo gurinta,yayin da afrah ke kallon hajja da maimunatun gaba daya,tana shiga zurfin tunani,sai hajja ta sauqaqe mata ta hanyar daga mata hannu

“Zo nan,qaraso ciki fannah(asalin sunan afrah,sunan mahaifiyar hajja), shigo kiga ‘yaruwarki da mahaifinku ya baro a gembu” idanu afrah ta waro gaba daya tana duban hajjan ta gani wai ko tsakanarta take?,waiko tasan maimunatu ido da ido,ta kuma san irin aminci da shaquwar dake tsakaninsu shine takeson tsokanarta?,to amma kuma ko daya bata ga alamun wasa a tattare da ita ba,take zuciyarta ta gaya mata babu ko shakka dai daine abinda hajja ta gaya mata,yayin da maimunatu ita kuma ta zubawa hajja ido cike da mamaki da son fahimtar zancanta,afreen dinta ‘yar uwarta ce ta jini?,kafin ta lalubo amsa afran ta sheqo a guje,tana isowa kuma ta rungume maimunatu a jikinta

“Da gaske kike hajja don Allah, maimoon dita ashe ‘yar uwata ce?” Kacamewa sukayi da kuka gaba dayansu,har sautin kukan nasu yaja hankalin alhaji mansur qani ga abubakar din.

Shi ya tsaya kansu yana musu fadan kukan kafin kowacce ta sassauta kukan,ya fice yana gaya musu kada ya sakeji.

“Nifa ji nake kamar mafarki,dama abbana abbanki ne?” Murmushi maimunatu tayi,ita daya daga ita sai ubangijinta ne kadai a yau suka san irin farincikin da take ciki,ta qagu abbanta ya farka akwai.maganganu masu yawa tasan da zasuyi

“Abbanki shine abbuu na da ya bata tun ina qarama,saidai bazan taba iya manta fuskarsa ba” hajja ce ta bata labarin yadda komai ya wakana,anan maimunatu taji cewar ja’afar ne yabi diddigi tsahon wata kusan biyu yana neman dangin mahaifin nata,ya baza cigiya daga gembu ya dinga bibiya har ya fahimci yana da nasaba da gombe,don haka binciken yazo masa da sauqi,har Allah yasa ya gano sunansa da komai nasa harda address,sanda yazo ma hajja da zancan batayi musu ba,don dama sunata neman suma su samu wanda yasan wani abu da zai zame musu haske zuwa ga gembu don binciko shatu da diyoyinta,da ja’afar ya samu goyon baya,don su tabbatar da zarginsu sai ya kawo maimunatu gidan wajen abbun,cikin hikimar Allah kuma hasashensa ya zama gaskiya,tunda gashi har abbun ya kirayi sunanta,sunan da hajja ke jinsa a bakin abbun kafin ya gamu da hatsarin motar da yasa yayi loosing memory dinsa,ya manta dukka wani abu daya faru a baya cikin rayuwarsa

“Afra ita kadai ce diyar abubukar har kwanan gobe,sai kuma dan uwanta musaddiq,kece cikon ta ukun” hajjan ta fada farinciki na sake kamata na bayyanar jikarta.

Su biyu suka zauna cikin dakin sunata hirarraki da suka shafi rayuwar,hajja na gaya mata tarin dangin da take dasu cikin gombe da maiduguri asalin mahaifar hajjan,da kuma ‘ya’yan qanne na mahaifin nata da rayuwarsa ta baya,abu guda ta gaza tambayar ta,yadda akayi abbun nata ya auri daadarta ba tare da kowa yasan garin ba har ya samu wannan matsalar data zama silar rabuwarsu dashi tsahon shekaru.

“alhamdulillah” abbu alhaji ateeq abubakar ya fada yana shafa addu’a,bayan ya idar da sallolin da suka kubce masa,jin kansa yake a yau sakayau,kamar yayi dogon bacci ya farka ne,kamar dukka abinda ya faru a sanda bai cikin hayyacinsa sun faru ne cikin mafarki

“Kaini wajen diyam”ya fadawa musaddiq dake zaune daura da mahaifin nasa,sai musaddiq din ya miqe

“Zauna abinka bari muje” alhj mansur ya fada yana miqewa tsaye

“Abba nima inason zuwa na ganta don Allah” musaddiq ya fada cikin kalar tausayi

“Bismillah muje” ya fada kana ya waiwaya ga abbuu

“Zan iya takawa da kaina,bana jin komai a jikina” alhj ateeq ya fada yana miqewa da karsashinsa.

Da sallama ya shigo dakin,hajja ta miqe cikin farinciki

“Ma sha Allah,Allah mun gode maka,Allah mun gode maka” ta fada tana qwallar farinciki,gaban gadon maimunatu ya nufa kai tsaye ya zauna yana dubanta,cikin qauna kunya da jin nauyi ta gaidashi bayan ta gaida yan uwansa da suke a matsayin kawunanta a yanxu

“Diyam ina shatu?” Itace tambayar farko daya fara mata,kamar ba zatace komai ba,saidai cikin raunin murya tace

“Allah yayi mata rasuwa ita da abinda yake cikinta”

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” ya fada sannan yayi qas da kansa,hajja da alhj mansur ke bashi baki,har zuwa sanda ya dago kansa

“Ina fata bata mutu tana fushi dani ba tare da tunanin guduwa nayi?” Kai ta girgiza tana hawaye

“Ko kadan abbuu,har ta mutu tana gayamin kai din mutumin kirki ne,ko guda bata taba ji a jikinta guduwa kayi ba,akwai gagrumin abinda ya faru dakai,ya kuma haneka dawowa zuwa garemu, kullum abinda take fada kenan” saita rushe da kuka,hakanan abbun shima ya kasa tsaida hawayensa

“Allahu akhbar,qaddara ta riga fata” alhj mansur ya fada,afra ma kukan take,yayin da musaddiq yaketa kallon yar uwar tasa,tausayinta yana kamashi,hajja ta jima tana gaya musu suna da ‘yar uwa,amma ba’asan inda take ba,yau gasu gata.

Wani zama akayi na gayawa juna abubuwan da suka shude,har zuwa sanda akayi kiran sallar magariba su abbu suka fita sallah,ita kuma ta yunqura zata bandaki saboda yadda cikinta keta juya mata,batakai ga toilet din ba wani irin amai mai zafi ya yanke mata ta dinga sharara shi hajja na mata sannu,afra kuwa gaba daya ta rude,sai data gama suka kira cleaners suka gyara wajen ita kuma suka maidata gado tana maida numfashi,dr noor suka kira,sai data idar da sallah sannna tazo ta sake dubata,tace babu komai,idan ta sake zuwa anjima su gaya mata

“Karki gayama j don Allah” maimunatu ta fadawa afra qasa qasa,saboda tasan idan ta gaya masan hankalinsa zai tasa.

Kwana biyu rak sukayi a asibitin aka sallamesu gaba daya,duka suka dunguma suka wuce gidan alhaj abubukar,duk yadda ja’afar yaso ya dauke matarsa saboda yadda yayi kewarta amma anni tace dole yayi dagin qafa,dole dangi suna buqatar ganin diyar tasu,haka tana buqatar lokaci ita da mahaifin nata suga juna sosai,hakanan ba don yana so ba ya barta,amma kwana uku rak yace ya bata.

To ita dinma kewarsa sosai ta dinga yi,batasan cewa soyayyarsa tayi mata mummunar illa ba sai a sannan,komai takeyi yana maqale a cikin ranta,duk da tarin dandaxon ‘yan uwa da kuma dangi daketa cika gidan kulli yaumin wajen ganinta,kuka ta dinga yi sosai,inama ace daadarta tana raye taga wannan ranar,kullum burinta shine ta sada maimunatu da mahaifinta,yau gata ga danginta tako ina,harda wadanda suke diban kamanni duka ta gani.

Kwananta biyu rak hajja ta hada gagarumar walima,dangi na kusa dana nesa kowa yazo,tace mata

“Naso ace ba’ayi taron bikinki ba diyam,taron aure nakeson muku na gani na fada,ku biyu kacal Allah ya bani mata a cikin jikokina,dukka maza ne,bugu da qari abubukar na musamman ne,yasha wuya ya gamu da jarrabawa,gashi a yau Allah ya yanke masa komai,aurensa da mahaifiyarki qaddara ce mai qarfi,ya boyemin batun auren saboda yana ganin kamar bazan amince ba,don a sannan matarsa nada tsohon cikin afra,bayan kuma an haife cikin sai ya kasa gayamin din,saboda ni da matarsa baisan wai yadda zamu dauki batun ba,a haka shekaru suka fara turawa har zuwa sanda Allah yayi nufinsa ya gayan,nayi masa fada sosai naji kuma.babu dadi,sannan na gaya masa a sannan ne matarsa zatafi ji ciwon abun,za kuma tace ya munafunceta,har gwara farko farkon abun,na masa umarni da yaje yazomin da ku,ya tafi zai taho daku sai kuma aka kirashi hauwa’u matarsa mahaifiyar afra ba lafiya,sai ya yanke ya taho shi kadai idan ta samu sauqi ya dawo ya daukeku ayi mai gaba daya,ashe ba rabon abun zai ritsa daku,ya samu mummunan hadarin daya kawo masa wannan matsalar,yana cikin jinyar kuma itama hauwa’u ta rasu,duk da na shaida mata komai,tace kuma ta yafe masa,ta shaidi halinsa,ba haka yake ba,ta tabbata qaddararsu ce tazo a haka,sannan idan ta dawo Allah yayi zamanmu tare ta riqe mata afrah da musaddiq,to ashe itama Allah bai nufi ganawarmu ba” shuru maimunatu tayi tana share qwalla,tun faruwar abun kawo yau ba ranar da bazataji wani abu daya motsa ranta ba.

A daren abbuu ma ya kirata,sun jima suna hira,bayan sun gama ne ya dauko wasu files da takardu a ciki ya miqa mata

“Akwai haqqoqinki a wuyana masu tarin yawa da ban samu damar sauke miki su ba,hakanan akwai alqawura da na yiwa mahaifiyarki saboda kyautatawarta gareni da haqurin zama dani da tayi,wannan takardun wani estate dina ne dake new GRA road,na mallaka miki su halak malak,sauran ‘yan uwanki dukkansu suna da kadara kwantankwacin taki” kamar a mafarki takejin abun,estate guda.abbun nata ya bata?,koda ta duqa zata masa godiya dagata yayi

“Ban biya shatu da komai ba akan soyayyar data nuna min,fatana kawai Allah ya hadamu a aljanna,ya sake tabbatar dani da ita a matsayin miji da mata”

Cikon kwana na uku ja’afar yazo da niyyar daukarta,amma saita mararaice masa,tana son binsa amma kuma tana buqatar lokaci sosai ita da abbunta,ga umma sa’adah ma tanata qorafin har yau basu zauna ba.

Da farko yaqi,amma da hajja ta saka bakin kan ya qara mata ko kwana uku ne sai ya tafi ba tare da yace komai ba,saidai ita maimunatun ta cikin idanunsa ta karanci bawai ya haqura din bane.

Cikin dare ta dinga jin zazzabi ta cikin qashinta,ta dinga juyi saman gadon,tana jin wata azababbiyar kewarsa,ta saba duk sanda take zazzabi irin haka cikin jikinsa yake boyeta,ba zata dauki dogon lokaci ba zazzabin yake rabuwa da ita,to amma yau din saboda babu shi a kusa da ita,sai takejinta kamar tsirara babu tufafi a jikinta.

Tun goma na dare da suka gama hira da abbu da hajja harda afra da musaddiq take kwance amma sha biyu saura idanunta a soye suke,hakan ce ta faru ga ja’afar,ya shiga ya fita tsakanin bedroom dinsa zuwa parlor ya kusa sau uku,ana hudun sai yayi zaune saman kujerar falon nasa,ya miqe qafarsa saman glass center table dinsa,ya dauki wayarsa ya fara laluben number dinta.

Cikin jikinsa yakejin idanuwanta biyu itama batayi barci ba,hasahensa ya tabbata kuwa,don ringing biyu tayi ta daga,nannauyar ajiyar zuciya ya sauke wadda ta ratsa har cikin kunnuwanta,saita damqe filon da take kwance akai da kyau saboda yadda tsigar jikinta ta zuba,shuru ya ratsa tsakani,dukkaninsu aka rasa wanda zai fara yin magana

“Lafiyar ki qalau kuwa?” Narke fuska tayi kamar yana gabanta sai tace

“Ummmmm” cikin shakku ya sake magana da wata murya mai taushi da dadin sauraro

“Me kikeyi har yanzu bakiyi bacci ba?” Kamar jira take ya tambaya kawai sai taji kuka ya tsinke mata da ‘yar sheshsheqa har ta cikin wayar

“Ya salam” ya fada yana sauke qafafuwansa qasa gami zama sosai

“Please my angel,please” ya furta a hankali yana rufe idanunsan

“Zuciyata na qara yawan gudunta,stop it please,ki gayamin menene?” Maimakon tayi magana sai wani kukan ya kuma qaruwa,haka kawai batajin dadin dukka jikinta,kuma ranta tana jinsa aquntace.

Shuru yayi tsahon minti guda yana sauraron kukanta,sai kuma a hankali yace

“Ok,am on my way” ya kashe wayar,yana miqewa cikin kuzari yayi bedroom dinsa.

Wayar ta zare daga kunnenta tana son tuna abinda yace

“Am on my way fa?,yana nufin gidan zai taho a wannan tsohon daren?,ta sani indai ja’afar ne zai aikata,don haka saita shiga kiransa da sauri don ta dakatar dashi kada ya biyo hanya a wannan tsohon daren.
[11/25, 12:59 PM] Safiyyatulkiram:

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply