Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 82


Gurbin Ido 82
Viral

82

Yana gaban closet dinsa yana sauya kaya yaga shigowar kiran nata a jejjere,da kamar bazai dauka ba saboda saurin da yakeyi,amma sai ya daga ya sanyata a hands free yana saurarenta,da narkakkiyar muryarta cike da sautin kuka tace

“Don Allah kada ka biyo hanya yanzu”

“Why?”ya tambayeta kai tsaye yana fesa turare a jikinsa

“Dare”

“Bana tsoronsa,nafi tsoron nisantarki akan dukkan wani abun tsoro,so get ready,i will call you idan na iso,ki zauna kusa da wayarki” daga haka ya katse kiran,ya dauki key din qaramar motarsa cikin motocinsa ya sanyama kansa wata hula ya fito.

Samun kanta tayi da zama daram tsakiyar gadon, idanunta nakan afrah dake bacci can nesa kadan da ita,da yake gadon yana da girma sosai,kamar wata me dakon jiran nasa haka ta dinga duba agogo,wasa…..gaske saiga kiransa bayan minti talatin,ta tsorata sosai da taji wai har ya iso,wanne irin gudu ya sharara haka?,saita miqe a hankali tana yaye window din dakin nata

“Ki fito ko na shigo” taji ya fada a tausashe,tadan tsorata kadan amma sai ya zura hannu ta window din ya riqe mata hannu yana kallon qwayar idanunta ta cikin hasken daya gauraye harabar gidan gami da zare hular kansa,mamaki ya kusa kasheta,duk security din gidan amma ta ina ya iya shigowa da daren nan?,kallon da yayi mata kadai yasa taji duk duniya bata buqatar kowa sai shi,sai ta zame hannunta sannan ta juya a hankali ta bude dakin ta fice,bata ko sauya kayan baccin jikinta ba,duk da akwai baby hijab a jikinta.

Tana riqe a hannunsa kamar zata bace har suka isa qofar gidan,sai a sannan ta lura da guard daya ne ya taso ya bude masa gidan,to ya akayi yasan da zuwansa?,wannan kuma bata sani ba,har ya bude mata motar ta shige ya shigo ya tayar suka bar layin tana kallonsa cikin mamaki

“Yanzu inda wani abu ya cutarmin da kai fa?” Ta fada da wata irin murya data sanyashi waiwayo wa ya kalleta,wani irin kallo take jifarsa dashi mai tsuma zuciya data sanyashi dan dukan sitiyarin motar softly

“Ba abinda zai cutar dani in sha Allah,bana jin komai inda zan kasance dake,ko meye zai biyo baya mai sauqi ne” sai ya miqa mata hannunsa ta sanya nata a ciki,ya hada ya matse gam

“Don Allah karki sake yarda kije ko ina ki barni….kiyimin alqawari” a tausashe ta gyada masa kai

“Nayi maka” cikin jikinsa ya dauketa tun daga harabar gidan zuwa cikin gidan,yana kallon fuskarta kamar ya riqo jaririya

“Jikinki babu qwari moon,banjin kina da cikakkiyar lafiya” ta bude bakinta zata amsa mishi wani amai me zafi ya taso mata,saita zille daga jikinsa da sauri ta dire ta sheqa zuwa toilet dinsa,baiyi qasa a gwiwa ba yabi bayanta,saidai garin rufewa ta kulle bandakin gaba daya,haka yayi tsaye gaban toilet din yana kiran sunanta.

Dukka abincin da taci sai daya dawo mata,sai data gama ta kuskure bakinta sannan ta fito tana takawa da qyar,riqeta yayi sosai ya samu waje nan qasan carfet ya zaunar da ita

“Na fada baki da lafiya daman,me yake damunki angel,menene?” Kamar tambayarsa na zuwa da amai,sake yunqurin tashi tayi don kada ta bata kyakkyawar farar jallabiyyar jikinsa amma sai ya riqeta gam,bata sa sauran zabi illa kwararar dashi a nan,ta dinga sheqashi kuwa,sai data wankesu tas ita dashi.

Sosai hankalinsa ya tashi,don a daren tayi amai ya kusa sau hudu,kafin gari ya qara haske ta galabaita sosai,qarfe shida na safiya ba tare daya damu da lokaci ba ya dannawa dr noor kira.

A sannan tanata shiri da sauri sauri akwai emergency C.S da zatayi,already tasan waye ke kiran,don haka ta daga kiran,yayi mata bayani gami da neman tazo ta dubata

“Karka damu,zan iso yanzu in sha Allah”.

Cikin mamakin yadda captain ja’afar ya koma gaba daya kalan tausayi take duba maimunatu,PT test tayi mata,saita daga kai da murmushi tana kallonsa,tunda ta shigo yake tsaye ya kasa zama,ya kafe maimunatu da ido kawai kamar zata bace,J mai tsauri da kaushi marason wasa amma gaba daya yayi laushi saboda ciwon matarsa,wacce irin soyayya ce wannan mai ban mamaki?,wadda sun fidda rai zai sake ma wata mace irinta

“Congratulations captain,zaka sake zama uba again in sha Allah” idanu ya zubewa dr noor,gani yake kaman tana masa wasa ne ko kunnuwansa basuji da kyau ba

“Really?” Kai ta jinjina masa tana tattare jakarta

“Da gaske nake,abu daya ya rage ka kawota nayi mata scanning don na tabbatar da lafiyar komai,watanninsa da kuma expected date of delivery dinta”

“Allahumma salli ala sayyadina muhammadin wasallim” ya fada da wani irin amo mai qarfi yana rufe idanunsan,sannan ya dora

“Alhamdulillah alhamdulillah” har kamar bazai daina fada ba sannan ya dubi dr noor

“Ki duba parking lot na gidan nan,duk motar data yi miki ki turo gobe a daukar miki ita,wannan shine tukuicinki”.

Sosai farinciki ya kama dr noor,dama qarshen satin nan take sanya ran sauya mota,sai kuma ga dama ta samu,godiya tayi masa sosai sannan ta juya ta fita.

Zamewa yayi a hankali zuwa qasa yayi sujudush shukur,sannan ya rarrafa zuwa gaban gadon maimunatu dake kwance,wadda tuni bacci yayi awon gaba da ita,hannu yasa yana shafar gefan fuskarta a hankali,wasu qwalla suna tarar masa a ido,ashe ita din ba gurbin ido bace,ashe ido ce guda,sai yanzu idanun suka samu gareshi,ita alkhairi ne masu tarin yawa tattare da ita,rasa me zaiyi mata yayi,kawai sai ya fara kissing duk inda bakinsa yakai very softly yadda bazai tasheta ba yana fadin alhmdlh.

Abinda bai sani ba tuni hawayen ya diga saman fuskartata,yana shirin miqewa ta bude idanuwan nata wadanda suka qara kyau da kuma haske,ta dubeshi cikin yanayi na masu barci,bakinta ya motsa kadan alamun magana zatayi,sai ta dawo gefanta ya zauna fuskarsa na fidda murmushi,ya taimaka mata ta zauna sosai ya jingina mata bayanta da filo

“Congratulations angel moon” binsa tayi da kallo kawai ba tare dafa fuskanci komai ba,a tausashe ya rungumeta cikin jikinsa yana jin yadda take sake mamaye rayuwarsa da duniyarsa gaba daya,hannunsa ya dora a hankali yana shafar cikinta

“Kina dauke da juna biyun ja’afar marwan khalid akko,zaki haifawa anni d’a,zaki haifawa amma jika,zaki kuma kuma haifawa amneee ‘yan uwa” mamamki ya kamata ta kasa cewa komai,jin shuru saiya daga kansa yana duban qwayoyin idanunta dake nuna tsoro,tsoron nan dake burgeshi

“Are you happy?” Qwalla ce ta subuce mata hade da murmushi,saita kifa kanta a kafadarsa tana jin kunyarsa,wai ciki?,ciki ita din?,yanzu kowa zai san abinda suke aikatawa ita dashi a boye kenan?,tunda ga ciki ya fito?.

Sosai ya dinga tsokanarta,tare da.lasafta mata burikansa akan cikin,burikan nasa masu yawa ne,har ta gaji da tayashi lissafawa,sun jima a jikin juna suna wata irin hira dake haifar da sabuwar soyayya da kuma shaquwa ta musamman,idan tayi magana sai yace dumin babynsa yakeji,babyn da ko gama sanin lokacin shigarsa da kuma adadin zamansa ba’ayi ba.

Sanda ya dauki waya yana niyyar kiran anni cewa tayi

“Don Allah hubby……kada ka gaya musu” dubanta yayi yana murmushi

“Why?”

“Kunya nakeji Allah”

“Kunyar me?” Cikin sakalcin dan fari da da wautar auta ta daga kai

“Kowa sai yasan me mukayi na samu ciki kenan fa?,Allah bazan iya sake kallon kowa ba” dariya irin wadda takan jima bataga yayi irinta ba ya saki,ya zame wayar gefe ya riqeta da kyau,ita kuma ta tura baki gaba kamar zata saki kuka,don kukan kamar baya mata wuya

“Ni baba tabawa zan kira a aiko,saboda banason ki sake komai,amma kuma kinsan halin anni,indai ta tsokaneni saina rama” kamar wasa sai ta sake masa kuka,yana tsokanarta ya dauka wasa ne sai yaga kukan take da gaske,sanyata yayi cikin jikinsa sosai,ya fara gaya mata wasu sanyayan kalamai,a hankali tayi shuru tana sauke ajiyar zuciya,zuciyarta tana yin sanyi,shima ajiyar zuciyar ya sauke, yaushe ta koyi rigima irin haka?.

Bugu biyu anni ta dauki wayar,abu na farko data fara fada shine

“Kai nake shirin kira yanzu,kai kaje ka sace musu yarinya cikin dare?” Sam sam ya mance daukota yayi ma daga gidan,ba wanda ya sani sai guard guda daya

“Sata ce wannan anni?,matata na dauko na gaji da kawaici,ko tausayina na lura anni bakiyi gaba daya”

“Kai ja’afaru ka fita idanuna……kayi ta kanka wallahi”

“Zanyi ta kaina……amma kafin sannan,ki turo baaba tabawa please ta kula da ita,bata da lafiya” wani farinciki ya kama zuciyar anni, ja’afar dinsu daya daina amsa kowa ya daina hurda da maida amsar magana yau shine ake kai ruwa rana dashi akan matarsa,tun baice komai ba jikinta ya bata mawuyacine a wannan karon idan ba abinda taketa addu’a bane ya samu

“Ahaf,wato daga daukota harka hadata da jinya ko?”

“Ba jinyar kikeso tayi ba?,ko bansha jinki kina roqa mata ita ba?” Idanu ta fiddo

“Kai ja’afaru,ni zaka yiwa sharri?…..” Sai kuma tayi shuru data tuna randa tayi addu’ar,a take farincikinta ya ninka,ta kashe wayar da kanta tun bai kashe ba,ta kuma tashi da kanta ta shiga kitchen kiran baba tabawa,wadda tana ganin annin tasan kiran mai muhimmanci ne,don ba shiga kitchen din take ba.

“Matar manya ce babu lafiya,zaki je ki zauna da ita……don Allah tabawa kiwa Allah kiwa ma’aiki ki kula da yarinyar nan da kyau,kada kice zaki yiwa manya kaara,basu da kunya ko kadan yaran wannan qarnin,ki kula da ita da kyau,kada wata matsalar ta afku a rasa cikin nan” guda baba tabawa ta saki,wadda ta jawo hankalinsu laila safina da salma dake falon annin suna hada wata game

“Alhamdulillahi, alhamdulillahi,Allah mun gode maka,ai zama bai kamani ba,Allah dai ya raba lafiya” take tahau shirin tafiya anni tasa aka yiwa driver magana.

Cikin lokaci qanqani labarin cikin ya karade gidan,wani irin murna da farinciki suka tsinci kawunansu,amma na falon abbi tana gyara masa laila ta sameta a can tana labarta mata,saita saki duster din da take goge kayan kallon falon,ta sulale ta zauna tana ambatar

“Allah na gode maka,Allah na gode maka” sai kuma hawaye ya biyo baya,ta debe tsammanin samuwar ja’afar din a nan kusa,sai kuma gashi bayan daidaituwar al’amuransa harda tagomashi na samun qaruwa.

Abbi dake daura links din hannunsa ne ya fito,yaji dukka abinda.laila tace,gaidashi laila tayi ta juya ta fice,shi kuma ya isa wajen amman,ya zauna a hannun kujerar da take zaune a kai,cikin kulawa ya fara mata magana

“Ci gaba zamuyi da godewa Allah da yawaita sadaqa,ubangiji ya sake tabbatar da dukka alkhairinsa a tarayyarsu” yayi maganar shi kansa farinciki yana ratsa zuciyarsa,kai ta jinjina tana share hawayenta

“Babu abinda zamuce da anni saidai Allah yasa ta gama da duniya lafiya,kaf rayuwarmu da alkhairi take binta,ko yaushe tunaninta yadda zata inganta rayuwar family dinta” kai ya jinjina yana jin dadin yadda ko yaushe tana gaba gaba wajen fadin alkhairin mahaifiyarsa gami da yi mata addu’a

“Ameen ameen” ya amsata sannan ya miqe,cikin salon tsokana kuma yace

“Ashe dai aishatu anason samun sabbin jikoki,wannan kuka haka?, ja’afar din dai shine na gaban goshin dai,ya kamata anni taji wannan labarin” kunya ce ta kamata sosai,saitayi qasa da kanta tana goge hawayen da batasan sun zubo ba

“Ayi haquri yallabai,kada na kasa hada ido da anni” ta fada tana miqewa don yi masa rakiya.

Tun ranar da baaba tabawa ta tafi gidan ta koma ‘yar kallo,hakanan ta dinga kame kanta waje daya,saboda gaba daya ja’afar din ya kunce mata tunani,ashe haka yake?,ashe lumbu lumbu ne?,wata irin wutar soyayya ke tashi cikin gidan,saidai cikin salo da ban sha’awa da kuma qayatarwa,ya dauki kulawar maimunatu gaba daya ya aza a wuyansa,abinda baaba tabawa kawai keyi kula da gidan da kuma girki.

Ta fannin maimunatu kuwa sai yanzu tasan meye ainihin ma’anar gata,gata mai sunan gata,tako ina lelenta akeyi,umma sa’adah nayi,su fareeda cousins dinta sunayi,anni nayi ammi da amma nayi,tsohuwa hajja nayi,umma sa’adah nayi,abbanta nayi,ga kuma afrah dinta data qeqashe taqi komawa makaranta,sai day abbuu ya maidata,wanda a yanzun itama ta koma ce masa abbuu,ya samu cikakkiyar lafiya ya kuma koma kan ayyukansa kamar daa,ya murmure fes dashi kamar babu wata jarrabawa data taba samunsa,a yanzun abu daya ya ragewa hajja shine ya qara aure,shi kuwa gani yake bazai samu mace kamar hauwa’u da shatunsa ba.

Ko yaya maimunatu ta motsa sai a kawo mata caffa,tako.ina gata da kulawa take samu,hatta su laila kaman zaayi musu haihuwar jikan fari,kusan ranaku d’ai d’aikune basa zuwan mata a yini ana hira,haka afrah itama fashin kwana daya ko biyu take,ba abinda maimunatu keyi saidai taci abinda ranta keso tasha abinda ranta keso,duk da cikin yazo mata da laulayi sosai,amma tana samun sauqi saboda akwai masu debe mata kewa.

Saidai fa duk yadda gidan yakai ga mutane,da zarar oga captain ja’afar ya dawo zai dauke abarsa ya wuce sassansa da ita,hidimarta kuma ta koma wuyansa,ita kanta maimunatu qorafi take masa ya dinga hutawa yaji da aikin office kawai amma yakance

“Da da hali zan ajjiye komai ne,nayita rainon cikin nan har sai randa kika haihu zan sake fita na barki” idan kun sake ganin maimunatu yana cikin gidan saidai idan wata muhimmiyar fita ce ta kamashi.

Tako ta ina babu abinda zata cewa rayuwa sai godiyar Allah,cikin dare daya Allah Almusawwiru ya canza mata rayuwarta gaba daya,bata da wani sauran qunci ko kuma damuwa kwata kwata,saidai lokaci lokaci takanyi tunanin inna furera,ko yaya take ciki?,me takeyi a halin yanzu,da gaske bata sonta don bata taba waiwayar inda take ba.

Abinda bata sani ba shine,inna fureran ta hadu da ibtila’i,bata da lafiya ta fita wani private asibiti da aka bude jikin rugarsu,bayan ta gama fadi tashin neman adreshin maimunatu har gembu amma kowa ya hanata,daga bisani kuma ta samu adress din,saidai har garin gombe ta shigo amma ta bace,tayita yawon neman gidan bata samu ba,qarshe ta hadu da ‘yan damfara suka karbe sauran ‘yan kudadenta,sai bara tayi ta hado kudin motar dawowa gida.bayan taje asibitin an gama dubata likitan yace

“Akwai wani aiki da mukeson bawa.mutane,aiki ne da yanzu yanzu zaki zama.shahararriyar attajira idan kinso” a yanzu ba abinda inna furera keso kamar wannan kalmar ta zata zama me kudi, kowacce hanyace tana jin zata iya binta,don haka tace

“Ko meye likita zanyi,zanyi wlh”

“Ba wani abu bane mai wahala,jini zamu diba leda biyu,zamu biyaki naira miliyan talatin” jin yawan kudin ya sanyata zamowa qasa,sai gata dabas zaune a qasa tana raba idanu,fillo yaji kudi sama ta ka ba tare daya siyar da kasanarsa ba😝😝😜

“Shin da gaske kake likkita?”

“Hajiya ba wasa a maganar nan,jinin muna kaiwa ana taimakawa marasa qarfi a cikin gari,saboda ku fulani kun fisu lafiya da yawan jini saboda yanayin abincinku da nasu ba daya bane”

“Aradu likkita ko yanzu ina iya kwanciya ka diba” ta fada jikinta na mazari,don har ta gama hango kudaden da abinda zatayi dasu idan sun samu,lallai magauta da maqiya ganin bayanta ba yanzu ba,ita din me sa’a ce,tayi musu shalll…..
[11/25, 12:59 PM] Safiyyatulkiram

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply