Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 87


Gurbin Ido 87
Viral

87

K’awataccen kitchen ne na wadanda suka samu duniya da kyau a hannunsu,iya tsaruwa ya tsaru,hakanan an wadatashi da dukkan wani nau’in kayan wuta,bedroom da kitchen dinta suna daya daga cikin muhallan da maimunatu bata wasa dasu,don duniyar gidan aurenta kenan,tana iya kashe ko nawa ne ta qawatasu,don faranta ran captain dinta.

Da sallama a bakinta ta shiga kitchen din a dan gagggauce,mutuniyar kirki baaba tabawa na tsaye tana aiki,yayin da yasira kuma ke zauna tana tayata suna hirarsu kadan kadan.

Da murmushi saman fuskarta ta waiwayo tana yiwa maimunatu sannu da zuwa,yayin da yasira ta miqe itama cikin girmamawa uwar gijiyar tata mai tsananin kirki da adalci itama tana mata barka da zuwa,gami da yunqurin karbar mayafinta da take qoqarin zarewa

“An karbo kambun andawo kenan?” Murmushi maimunatu tayi yana buda kwabin alkubus din da tayi kafin ta fita

“Mun dawo baaba,amma naso manyan naki yana kusa,shi yafi cancanta ya karba min” kai ta jinjina tana murmushi,yanayin soyayyarsu koda yaushe abar burgewa ce,kullum sake kusanci suke da juna

“Dake dashi din duk daya ne maimunatu,idan kaga zahra ai kaga wata,kema kuma kin cancanci ki karba,alkhairanki ga al’umma masu tarin yawa ne,Allah dai ya jiqan mahaifiyarki,ya raya miki zuriyarki,ya kuma qara danqon qauna tsakaninki da mai gidanki”

“Ameen baaba,na gode,Allah ya qara nisan kwana da lafiya me amfani”

“Ameen ameen” daga nan suka kama aikin gadan gadan,wanda kafin wani lokaci sunyi nisa a aikin.

Suna falo sunata hayaniyarsu,lokaci lokaci suna shigowa kitchen din,wannan ya kawo qarar wancan,wancan ya kawo qarar wannan,kasancewar gaaje ta fita islamiyya bayan dawowarsu,sai su kadai,asad dake ta aikin alqalanci ya gaji,shi kuwa as’ad dama ba kasafai yake kula fitinarsu ba,idan yayi magana daya biyu ana uku baka jiba jikinka ne zai gaya maka, maimunatu na yawan masa fada,shi yasa bai fiya zama cikinsu suna wannan shirmen ba.

Sai data tabbatar komai ya hau saiti sannan ta saki ajiyar zuciya tana duban agogon dake kitchen din,akwai sauran minti arba’in a gabanta,waiwayawa tayi ga yasira

“Nan da minti ashirin ko da biyar haka,don Allah ki kunna dukka burners din gidan nan a saka turaren wuta ko ina”

“To ranki ya dade,turaren wajen aisa?” Idanu ta fidda tana dubanta

“A yau din?,ai karkimin gangancin nan,turare idan bana hajiya na’ima ba banason kowanne a gidan nan”

“Gaskiya ne,na jima banji turare irin nata ba wallahi,kamar kyauta ake bata kayan hadin,komai a wadace kamar yayi.magana,rannan fa asad naga yana murza turaren a jikinsa,nace me ya hadaka da turaren icce?,wai qamshin turaren ne baya gajiya dashi” dariya dukkansu suka saka maimunatu ta fara takawa zuwa gaba tana cewa

“Kinsan qasan kwalaben iya ruwan turaren dake kwanciya ya isa azuba wani sabon turaren ya tsumu,kiyi a gida kiyi a kayan sawa gaba daya,gaskiya yanzun ban gane kowanne turare idan ba nata ba”

“Ai ta hadu wallahi matar” yasira ta sanya musu baki,don ita kanta tafi son maimunatun tace ta kunna turaren hajiya na’imar saboda yadda gidan ke daukan wani tattausan qamshi

(Tasted and trusted,ba biya tayi ayi mata talla ba,nayi hakanne don mata su amfana,saboda naga yadda yake zaunarwa da gidanki da jikinki qamshi,na tabbatar duk wadda tayi amfani dashi saita godemin,turaren wajenta shine turarena a yanzu,na bar amfani da turaren wutar kowa idan ba nata ba zaki iya tuntubarta ta wannan number (803 212 7953) if u are interested,idan kinji dadinsa kiyimin addu’a kawai).

Sai data fara komawa sassansa tayi masa barin turare sosai,ta duba lungu da saqo ta tabbatar komai yayi neat tun daga katafaren falonsa zuwa lafiyayyen bedroom dinsa,ta ajjye masa dukka siyayyar data yi masa kowanne abu a muhallinsa sannan ta wuce nata sassan.

Bedroom ne itama mai lafiya,wanda ya zamanka a ciki ya isa samar maka da nutsuwa, yadda aka shiryashi kadai ya isa gaya maka matar gidan tasan abinda takeyi,tasan kuma me ake kira da aure da kuma soyayyar miji,toilet dinta ta shiga ta fara shirya kanta.

Cikin minti talatin kacal komai ya zama ready,ba abinda jikinta ke fiddawa sai daddadan qamshin turaren hajiya na’ima mai taushi da sanyaya rai,cakude da wasu lausasan bidy mist.

Wani fitananniyar atamfa ta saka wadda aka yima wani zaunannen dinkin girma,da yayi masifar fidda haibarta da kuma kwarjininta,kallo daya idan kayi mata ba zakaso sauke dubanka daga gareta ba,don ita kanta data fito falo yaran binta da kallo suka dinga yi,duk da sun saba ganin irin hakan a tare da ita,amma kwalliyar yau din ta tafi dasu,gaaje ma sai data yi comment akai,saboda sosai gayun maimunatu ke burgeta.

Tana tsaka da musu fada akan rashin fita da abincin masu gadin gidan da wuri,sannan ta koma wajensu asim tana masa maganar yadda suka fidda dukka games dinsu suna bazasu a wajen qarar bude gate da shigowar motoci gidan suka baqunci kunnuwanta,sai ta lumshe idanu bugun zuciyarta yana sake daduwa,wanda ya tabbatar mata da dawowar masoyinta uban ‘ya”yanta kuma rayuwarta gaba daya zuwa gareta,ta sauke wani siririn murmushi dake dauke da tarin saqonni daga zuciya har zuwa saman fuska.

Tana jin nasma da nasim na rige rigen fita zuwa gareshi,saidai ta tabbatar kafin su isa ya shigo,kusan haka al:adarsa take,duk sanda yadda suke sauri wajen ganin sun cimmasa sai ya rigasu,don shima a d’okance yake dawowa kuma a qagauce da son ganin iyalin nasa.

Kamar yadda ta zata kuwa a bakin qofar falon sukayi clashing da yaran,the handsome and adorable captain ja’afar marwan khalid akko,cikin wata shiga data bayyana zallar izza kyau kwarjini da kuma qasaitarsa,sassanyan matashi wanda yake kan ganiyar quruciya kyau da kuma arziqi,wanda ya dace da macen qwarai haziqa daya tamkar da dubu irin maimunatu,wadda a kowanne mataki na rayywarsa tana biye dashi tana kuma riqe hannuwansa zuwa kowanne mataki a rayuwa,nasara ko kuma akasinta.

“Assalamu alaikun warahmatullah” ita ya fara fada hancinsa yana shaqar masa qamshin da yafiso a duniya fiye da kowanne qamshi,zuciyarsa na masa wani irin motsi tana tabbatar masa da wanzuwar mace mafi soyuwa cikin duniyarsa,wanda a duk sanda kusanci irin haka ya samu tsakaninsu sai sautin bugun zukatansu duka sun sauya.

A tausashe ya durqusa gaban yaran nasa saboda ya basu damar hawa jikinsa kamar yadda suke da buri,yayin da muryarsa ta aike da saqo zuwa ga zuciya da kuma gangar jikin maimunatu,sai ta gaza jurewa ma shigowarsa,itama tabi sahun yaran nata wajen yin tattaki zuwa bakin qofar.

Daraf kuwa suka hayeshi,ya miqe dasu duka su biyun,kowanne a hannunsa guda daya

“Banda kun samu qaqqarafan uba,ta yaya zai iya dagaku duka ku biyun?” Ta fada a ranta tana murmushi,saboda nasma da nasim din ba goyon da tayi sukayi qiba kamarsu.

Miqewarsa tayi dai dai da hada idon da sukayi dashi,wasu irin abubuwa suka soma yawo a qwaqwalwar kowannensu da kuma zuciyarsa,a tare suka aikewa juna saqon murmushi mai dauke da tarin ma’anoni

“Barka da zuwa,barka sa dawowa daddy” ta fada tana daurewa yadda ta qagautu ta jita cikin ingarman jikinsa da bata sake gasgata tayi kewarsa ba sai yanzu data ganshi a gabanta

“Barka kadai ummul aulad hayati baitiha wa zaujiha” murmushi ta sauke masa tana basarwa saboda asad da as’ad dake wajen,wadanda suka fita parking space dauko jakankunansa,tunda suka tasa suke wannan aikin,bai bari kowa ya riski inda iyalinsa suke.

Zama tayi daga hannun kujera tana kallon yadda ya sake yana wasa dasu,kai kace tsakanin sako da sako ne,wannan din ba baqon abu bane a wajensa,a waje ne da fagen aiki yake zaaki,amma cikin gida tamkar mage yake komawa da ‘ya’yanta,duk sanda ta zuba musu idanu tana mamaki yakanyi murmushi yace

“Khairukum khairukum li ahlihi,wa’ana khairukum li ahli(mafi alkhairinku shine mafi alkhairi ga iyalinsa “wanda yafi kyautata iyalansa kenan”,sai annabi yace nine mafi alkhairinku ga iyalaina)” takan sake murmushi tana jin dadi har cikin zuciyarta,lallai ya tabbata diyan Dr marwan babban limamin qasar gombe,hakan kuma yana qara mata nutsuwa sosai,tana ji a rai da zuciyarta lallai bata da haufi ba zata wulaqanta a hannun mutumin dake qoqarin koyi da sunnar ma’aiki ba.

Da taga abun nasu ya miqa saita miqe tayi daki,ya bita da kallo a sace yana jan numfashi,yaran sun hanashi motsawa kwata kwata,ruwan wanka ta hada masa,amma har ta dawo yaran basu barshi ba,har sai data fara masa sign sai yayi mata alama data wuce dakin gashinan zuwa,tana dan tura baki gaba alamun complain ta miqe ta wuce din,shi kuma ya saki dariya cikin ransa yana cewa

“Zakiyi bayani” .

Sai daya bude jakarsa dole ya fiddawa kowa tsarabarsa,sannan ya sanya asad ya tattara kan yaran yace su wuce dakinsu,nan da awa daya kowa ya daura alwala zai fito su wuce masallaci sannan ya samu kansa.

Murmushi ya saka sanda ya bude dakin,tana tsaye harde da hannayenta,ya taka a hankali yana jin shauqi yana dibansa tare da wani magnet mai qarfin gaske zuwa gareta.

A hankali ya isa bayanta,ba bata lokaci ya jata zuwa jikijsa a tausashe ya manneta da jikinsa,rigima taso yi masa sosai kan yaqi sallaman yaransa da wuri,amma kuma saita kasa,suka sauke ajiyar zuciya a kusan tare lokaci kuma daya,kowannensu yayi shuru yana sauraren bugun zuciyar dan uwansa

“Ya rabb,ka fini sanin yadda nakeson wannan halitta taka…..ka fini sanin girman kyautatawarta gareni…..ka fini sanin girman soyayyar da takemin……” Kafin ya qarshe ta datsi numfashinsa ta amshe addu’ar gami da juyar da ita kansa

“Allah ka soshi fiye da yadda yake sona,ya ubangiji ka faranta masa fiye da yadda yake qoqarin farantawa iyalinsa da sauran al’ummar annabinka,ya Allah…..ka ninka soyayyata a zuciyarsa” da hanzari ya juyo da ita suna fuskantar junansu,ya waro idanunsa waje,zubawa juna idanu sukayi kowa zuciyarsa tana narkewa,sai ya kama hannunta ya sanya saitin zuciyarsa

“Angel…..indai soyayyar da nake miki a yanzu akwai qarin wata……to inajin mutuwa zanyi,ko a yanzun nakan rasa inda zan sanyaki na boyeki a zuciyata,inaga idan soyayyar tafi haka?” A tausashe ta sakar masa murmushi ta zagaya hannuwanta a bayansa ta rungumeshi sosai cikin jikinta,duk da duka duka tsahon nata iya qirjinsa ne

“So nake kayita sona…..kayita sona…..kayita sona…..saboda ni ina da tabbacin bazan taba iya daina sonka ba”

“Nima da soyayyarki zan mutu angel,saboda ke aka halicceni,kamar yadda nake da tabbacin saboda ni aka halicceki…..” Yayi maganar yana yiwa bannunsa masauki a tsakiyar bayanta da ya zuge zip din rigar tata har zuwa qasan rigar,kafin ta samu cewa komai ya balle brazier dinta ya kuma soma zameta tare da rigar gaba daya sannan ya maidota cikin jikinsa ya manneta yana sauke numfashi da sauri.

Kisses masu zafi ya soma sauke mata,kamar zai cinyeta danya,babu inda bai sumbata ba a jikinta,kafin ya dauketa cak zuwa duniyar da kullum yake mararinta,yake kuma jin maimunatun tashi kamar ranar ya fara saninta,tana da wata baiwa ta musamman,wadda sai an tara dubunnan mata baa samu mai irinta ba,sai tsananin dace.

Anan suka taru suka lalace,har lokacin sallar magrib ya gota basu sani ba,tuni su asad suka daura alwala suka sanya asim a gaba suka fice masallaci ganin daddyn nasu bai fito ba,basu nemeshi ba suma,yaran nada tsananin hankali da kuma tarbiyya,nasma da nasim kuwa na wajen baaba tabawa da gaaje da suketa hira,tana bata labarin mutumin dake ta binbinin binta yana sonta

“Yuuma tanata qorafi dama,ya kamata ki bashi dama,bakisan abinda Allah zaiyi ba,ni zan shaidawa maimunatu da kaina” wannan karon gaajen bata musa,don tana jin ya kamata ta saukewa mutanen da suka dauki nauyinta nauyin dake kansu ta matsa zuwa gaba itama.

Wasu irin hirarraki suka dinga yi a tsakaninsu bayan kammalar komai,hirar dake ratsa zukatan masoya tare da kawo shaquwa a tsakaninsu,tana kwance a qirjinsa suna jin dumin fatar juna(skin to skin).

Ita ta fara zabura zata miqe ganin lokaci yaja,yayi caraf ya riqeta yana kallon qwayar idanunta,saita narke masa da shagwabarta wadda bata girma sam a wajensa

“Lokacin magariba ya gota hubby” sake tsomoshi tayi,sai ya lumshe idanu,ya motsa tausasan labbansa yana cewa

“Astagfirullah” ya sake bude idanuwan nasa a kanta,wani qawataccen qaramin murmushi na fita a fuskarsa.

Biye masa tayi itama tana kallon fuskar tasa,irin wannan yanayin koda baiyi magana ba idanuwansa kadai sukan isar da saqo zuwa ga zuciyarta mai dimbin yawa,irin saqon da fatar baki tayi kadan ta isar dashi

“Bana gajiya dake angel moon,wai meye sirrin?”

“Kaine hubby” ta fada tana zamowa daga gadon da hanzari,ta riga ta kubce masa,sai ya bita da kallo

“Zamuje mu gaida abbi amma da abbu da yuuma,don Allah ki gayama anni,tayi haquri,na tuba nabi Allah na bita,ta daina ce miki gurbin ido,idan ta fada kaman zan mutu nakeji” dariya ta tuqe maimunatu sosai amma ta cinye gami da bata fuska

“Ba ruwana,aikai ka fara sakamin sunan,donme zaace ta daina yanzu?” Zamewa yayi da gwiwoyinsa a gabanta

“Wallahi wallahi ba ma kinfi qarfin ido ma a yanzu bare gurbinsa,ke din fuskace…..ke gangar jiki da ruhi ce gaba daya” dole dariyar da take dannewa ta fito,ta shiga qyalqyala masa,yayin da ya bita da kallo yana murmushi dariyarta tana burgeshi sosai

“An daina fada tuni,kula ne bakayi ba,dama tana yine don ta tono ka”

“Na tonu kuwa sosai” saita tsaya gabansa tayi saluting nasa,kafin ta sauke hannuwanta yakai hannunsa saman qirjinta wanda kullum tsole masa ido yakeyi,cikin muryar rad’a yace
“please idan mun dawo a sake sanmin don Allah” ya fada yana narke mata,kai ta girgiza kawai tana dariya ta shige bandaki da sauru,sai ya boye fuskarsa a tafin hannunsa yana jin zafin sonta a ransa,daga bisani kuma ya yaye bargon da sauri ya sauko shima yabi bayanta bandakin fuskarsa ta gaza boye murmushinsa.

Yana daga tsaye tana hada musu ruwan wankan yana qarewa bandakin kallo,tunda ya shigo ya lura da yadda ta canza wasu kayyaki na dakin zuwa toilet din, maimunatu ta musamman ce,ta dabance,komai nasa mai muhimmanci da kima ne a wajenta,sai ya qarasa ya karbe lallausan sabon towel din da take shirin ajjiye masa a gefan bathtub,ya dagota yayi kissing goshinta

“Thank you,thank you my moon”

“For what?” Ta tambaya tana murmushi

“For loving me and for everything you do and everything that you are” bai bata damar tofa tata ba ya jata zuwa bathtub din,nan ma suka bata lokaci wajen wanka saida tayi da gaske.

Ko kanta bata tsaya busarwa ba ta zura riga sukayi sallah,sai da suka idar sannan ta dauki waya ta kira baaba tabawa tace yaran su shirya zasu fita,ta sauke wayar tana zame dankwalinta ta sauki hand drayer ta jona zata busar da gashinta.

Zameta yayi daga hannunta yana fadin

“Ya zaki shiga aikina bayan gani na dawo?” Kai tsaye ta miqa masan,don ya sabar mata da hakan muddin yana nan.

Yana busar matan suna sake taba hira,dalilin da yasa aikin ya daukesu tsahon lokaci,ya gyara mata tsaf,sai yaja da baya yana kallonta,tayi masa kyau matuqa da gaske

“Gaskiya da matsala,zamu ajjye yaran nan a gidan abbuu”

“Daka gama farantama khalipha(yaron da yuuma ta haifa da abbu)”

“Amma daddy wai baka girma ne?,next month fa amnee zatayi candy” murmushi ya saka,sai ya juyar da ita tana kallon madubi,shi kuma yana tsaye daga bayanta yana dubanta ta cikin mudubin

“Soyayya bata tsufa,koda masoyan sun tsufa angel,jin nakeyi kamar yau na fara ganinki cikin kayan saqi kina koro shanu,kamar yau na fara saninki diya mace a johannesburg….” Maganarsa ta qarshe ta bata kunya matuqa,har sai data sanya hannu ta rufe fuskarta,yana tayata dariyan yasa hannunsa ya zame hannun nata

“Banson wata kunya malama,johannesburg tana da kima da babban tarihi a rayuwarta,ki shirya bayan amnee ta gama exams dinta,za’a dauran auren gaaje da himu,na gama magana dashi tun ina can ya kuma amince,zamu wuce umra gaba daya da yara,harda baaba tabawa,daga can zasu dawo gida,mu kuma zamu sauka johannesburg,inason na sake dasa wasu ‘yan biyun a can” juyowa tayi tana qanqame shi,dadi yana cikata kamar yaune zuwanta umara na farko,saidai shi din wajene da dukka musulmi,gefe guda farincikin yadda burinta ya cika,himu ya yarda zai auri gaaje,ta tabbatar har yanzu gaaje nason himu,saidai tana ganin kamar ya mata nisa,sai gashi cikin haquri dattako da kyawun hali nasa ya amince zai auretan duk da abubuwan da suka biyo baya.

Hannuwansa dukka biyun ta riqe,tana sake jin duk duniya babu macen data kaita sa’ar miji,addu’o’i ta dinga jero masa,wanda ta kasa yankesu har sai da ya hade bakinsu waje daya,bada gangan yayi ba amma sai gashi sun sake rikita juna saida suka koma ruwa,sannan suka dawo suka sake sabon shiri,ita ta shirya shi tsaf da kayan da suka kasance zabinta kamar tadda ta saba masa,ta zauna a gefansa ta ci dashi ya qoshi,sannan suka fito.

Wani irin perfect match couples wanda duk wanda ya kallesu sai ya sake waiwayowa ya kallesu,saboda zallar dacewa da juna da kulawa da kuma soyayya dake fita daga idanun kowa zuwa ga dan uwansa,wani lokaci ba tare da sunsan suna aikata hakan bama,haka suka dauki yaran nasu,sunata hirarraki a tsakaninsu,hira dake nuna fahimtar juna da qaunar juna a tsakaninsu,asim nata murna zaije ya tsokani anni,ya boye dan qaramin qadangaren wasaya radawa asad a kunnensa

“Yau anni zatayi ta kanta,saina tsoratata,ladan tallemin qeya data yi rannan” karaf a kunnen maimunatu,ta waiwayo ta watsa masa daquwa

“Akul dinka da tabamin uwa,ranka zai baci,zakayi ta kanka ne indai naji labarin hakan ya faru” dariya suka sanya gaba daya,dukkansu suna qaunar tsohuwar,har yanzu rigimar nan tata tana nan,saidai kuma tana tsananin son jikokin nata,musamman ace an hadu gaba daya,yaran hisham salma laila safina da fa’iza,ranar bata da katabus sai nasu.

A motar kuma hirar sai ta koma ta anty amna,asad da as’ad nata hirar graduation party da suka shiryama amnan ba tare da amnan ta sani ba,ko maimunatu ma sai lokacin takeji, murmushi kawai ta saka tana jin dadin yadda Allah ya hade kawunansu,babu wanda zaice ba ita ta haifi amna ba,captain ja’afar kuwa hannunta ya lalubo kawai ya sanya cikin nashi,yasan ko mene yaran suka zama qoqari da jajircewarta ce,soyayyar data gwadama amanan tsahon shekarun da suke tare ko mahaifiyarta sai haka,yana alfahari da maimunatu matuqa a rayuwarsa,tayi masa komai,ta kuma zame masa dukkan abinda yakeson matarsa ta zama,tana kan zama din ma.

*Tammat bi hamdillah*

*A nan na kawo qarshen labarina mai suna GURBIN IDO,ina fata Allah yasa al’umma sun amfana,kura kuran ciki Allah ya yafe mana,ya bamu ladan ciki,abinda muka manta kuma bamu rufe dashi ba sai ayi mana afuwa,ajizanci ne*

*Masoya masu siyan litattafan mu a koda yaushe,bawai don baku da inda zaku samu ba,mun gode qwarai da gaske,ubangiji ya yalwata arziqinku,ya bar zumunci a tsakaninmu,muna matuqar godiya a gareku,haqurin da kuke damu Allah ya saka muku da alkhairinsa,Allah ya sadamu da alkhairin sa*

*ZAFAFA BIYAR NA MATUQAR GODIYA DA JINJINA A GAREKU*

*Subhanakallahumma wabi hamdika,ash hadu an la’ilaha illa anta,astagfiruka wa’atubu ilaika*

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply