Hausa Novels Raina Kama Book 1 Hausa Novel

Raina Kama Book 1 Page 10


Raina Kama Book 1 Page 10
Viral

…..Maman Fauziyya ce taga shirun yayi yawa narashin gittawarmu ta aiko Kamal yagani muna nan, dan ita azatonta ko mama Rabi’a tawuce damu gidanta ne.
Da gudu yakoma ya sanar mata gamucan babu lafiya a d’akinmu.
ai bata tsaya jin k’arshen zancenba ta garzayo, halin data iskemu aciki itama hankalinta yakai k’ololuwar tashi, takira baba k’arami a waya tana Sanar masa, duk da haushinmu dayakeji hakan bai hanashi shiga tashin hankaliba shima. atare suka shigo da dady, shima abbanmu sai gashi yashigo.
Duk kuma jikinsu sai yayi sanyi, aganinsu yakamata su sauraremu ajiyan, amma duk da haka babu iyayen dazasuga wannan abun hankalinsu bai tsashiba, garashi d’an manyan mutanene, nashi mai sauk’ine, amma mune awahale.
Haka aka kira doctor yaduba mu, yace damuwace ta haddasa mana zazza6in, sai kuma yunwa.
Da k’yar maman fauziyya ta taimaka mana mukayi wanka da ruwa mai d’umi, sannan mukayi sallar asubahi. tea ma dak’yar muka shashi sannan mukasha magani, still kwanciya muka k’arayi, nan barci ya kwashemu.

Dadyne ya kalli ‘yan uwansa, cikin damuwa yace, “yaya Auwal yanzu bazamuyi wani yunk’urin bincike akan lamarinnan ba? ni dai sainake ganin kamar yarannan bazasu aikata hakaba, tsawon shekaru muna tare dasu, bamu ta6a jin makamancin abinan ba daga garesu, sainake ganin bai kamata mu yanke hunci ba akan abinda bamuda tabbas kuma cikin fushi”.
“Hameesu karka goyi bayansu akan wannan lamarin, babu yanda za’ayi abuga labarinan alhalin bai faruba, kaduba fa shi yaron d’ane ga Sarki, shinema Galadima, kodan tsoron abinda zaije yadawo ai nasan gidan jaridarnan saji tsoron buga labarin”.
“hakane yaya, amma baka ganin mak’iyanshi zasu iya amfani da wannan damar domin 6ata sunansa? maybe kuma su yaranmu tsautsayine ya gitta akansu”.
“maganarka gaskiyane Jafaru, nima wlhy hakan nake tunani, amma yakamata mujira muji daga gidan Sarki, Dan inhar Dan 6ata sunan yaron akayi nasan bazasu k’yaleba, kuma zasu nememu”.
Ajiyar zuciya Abba ya sauke yace, “nidai koma minene gsky aure yakamata ayima Munaya, Dan nikam banta6a cin karo da abinda ya rud’ar daniba irin wannan, mahaifiyar yarannan wlhy batayi barciba jiya, kwana tayi kuka, kuna ganin dai irin cin zarafin da inna tadinga mata jiya a tsakar gida gaban kowa, shin minene laifin A’isha akan wannan lamarin? zata aiki su Munubiya ne akan suje su aikata hakan?”.
“kayi hak’uri yaya, lamarin inna sai hak’uri, kasan dai halinta ai”.
Haka sukaita tattauna yanda zasu 6ulloma lamarin.

 

?.?.?.?.?.?.?.?.?.?.?.?

Jiki a sanyaye ya danna kiran Momma, bugu biyu ta d’aga, cikin girmamawa ya gaidata, ta amsa itama cikeda kulawa kamar yanda ta saba. hakanne yad’an sakashi jin sanyi a zuciya, ya sauke ajiyar zuciya yana fad’in “Momma ya jikin Abie?”.
“Alhmdllh Moh’d. wani mummunan labari yanzu Ummu Erfaan takirani take sanarmin?, sai kuma ga mama Fulani ma takira tanata fad’a. yanzu kuma Sauban ya nunamin wasu pictures wai an turo masane”.
Rintse idanunsa yayi cikin k’unar zuciya, murya a sark’e yace, “Momma nima haka kawai nagani”.
“ban gane kaima haka kaganiba Moh’d, kagayamin gaskiya please, wannan ba k’aramin Abu bane bafa”.
Da k’arfi ya cije lips d’insa tamkar zai hudashi da hak’ori, cikin wata murya dake nuna k’ololuwar 6acin ransa yace, “Momma wlhy bansan komaiba, yanay idi tabbas munyi kayo da wata yayinya hay wayata tafad’i ta fashe, jiya kuma yayinya takusan fad’uwa a plaza nayi yink’uyin taimakon ta saima ALLAH yasa bata fad’iba, kuma ko ta6a banyiba, shine kawai yau gidan jayiday nan suka maida pictures d’in haka fa”.
Ajiyar zuciya Momma ta sauke, (dan tarigada tasan halin d’an NATA, duk da ba’a shaidar d’an yau musamman idan yabar gaban idonka) “Muh’d tabbas wannan k’ulline, amma kuma yarinya d’ayace ai”.
“haka nagani nima Momma”.
“yanzu mi sarki yace?”.
“Momma wlhy maganay babu dad’inji, hayma sun shiyya meeting a kaina”.
“Humm Muh’d wannan maganace mai girma, kuma tabbas domin 6ata sunanka ne da namu akayi, akwai kuma dalilinsu nayin hakan, ita wannan yarinyar kodai da saninta kokuma an shigo da itane saboda cikar manufarsu”.
“Momma su waye to?”.
“Masusan ganin bayanmu mana, sun biyo wannan hanyarne domin dak’ileka da ragema kaifi”.
Wani naushi ya kaima k’aramin teble d’in gabansa na glass, nan take ya tarwatse. bai damu da ciwon dayajiba, cikin k’araji yace, “tabbas kafin suga bayana nizanga nasu!!! rayuwar mahaifina bazata salwanta abanzaba!! Saina wulak’anta dukkan masu hannu aciki kosu waye su wlhy billahi Momma! numfashina fansa akan mahaifina!!”.
Dole Momma tacire wayar daga kunnenta saboda yanda Galadima ke magana cikin matsananciyar tsawa.
Saman kujera ya wurga wayar, batareda ya katse kiranba, afusace yafito daga 6angaren nasa, tsawa ya dakama dogaransa.
Gaba d’ayansu cikin rawar jiki suka nufi motocin da ke fake a wajen, ko jira abud’e masa baiyiba yabud’e yashiga.
Hankalinsu a tashe yake daganin yanayin shugaban nasu, sunsan tabbas ran ‘yan maza ya 6aci yau, Dan kowa yasan rashin son hayaniya irinta Galadima a masarautar nan.
Saida suka fito daga masarautar a d’arare sarkin mota yace, “ranka ya dad’e ina muka dosa?”.
Tamkar bazai tankaba, sai kuma can afusace yace, “plaza!”.
“angama Ranka ya dad’e, ALLAH ya huci zuciyarka ya shugabana”.
Banza yamasa bai tanka masaba, sai huci yakeyi yanna karkad’a k’afafu da taunar lips, idonsa yayi zajur saboda masifar 6acin rai.

A plaza ma tunda yashigo kowa ya fahimci yanda cikin 6acin rai, Dan ko kallon masu gaisheshi bayayi, mutane masu siyayya sai kallonshi sukeyi, dama wasu gulmace takawosu dansu k’ara ganema idonsu akan labarin da ayau yazaga ko’ina da ina. kai tsaye wani Office yashiga.
Cikin hanzari Wanda yake a office d’in yamik’e domin kwasar gaisuwa, sai dai yanayin ogan NASA yayi masifar rikitashi.
Bai saurari gaisuwarba yace, “inason ganin abinda yafayu a CCTV tundaga safiyay jiya hay daye”.
Jiki Na rawa guy d’in yace “angama ranka ya dad’e”.
Kujera ya jawoma Galadima ya zauna, sannan yagyra zaman computers d’in wajen sosai, tariyo wa yafarayi cikin nutsuwa, saida yadawo Sunday morning 6pm sannan ya saki, tundaga bud’e plaza har zuwa masu share-share da goge-goge dasukayi aikinsu, har lokacin da masu sayayya suka fara Shiga da fita a plaza d’in, har an wuce yace “dawo baya kad’an”.
A slowly yadawo bayan kad’an, har zuwa kan wasu samari biyu d’aya sanye da jallabiya d’ayan wandon Jeans da farar t-shirt.
“kayo zooming d’in yayannan dake tsaye sunan waige-waige”.
Zooming d’insu yayi, sannan yasanya play yanna tafiya a slow.
Samarin sunata ‘yan kalle-kallene, saikuma zuwa can d’aya yasaka waya a kunne yana magana da kallon cctv camera d’in dake hasko tsakkiyar plaza d’in Inda motoci ke Parking, saikuma ya janye idonsa ya maida kan motocin dakeJere a wajen. da ganin Kasan yana maganane, Dan d’ayan dasuke tare yanata gyad’a Kansa alamar gamsuwa da abinda d’an uwansa yake fad’a.
Galadima Na zaune shiru, idonsa nakan computers d’in yana nazarin gayun har aka wuce Kansu, baice uffanba yacigaba da kallon shigi da ficin jama har zuwa 8:11pm, daga nan Computer tayi d’iff.
Da Sauri Galadima ya kalli sarayin “mi yake fayuwane?”.
“Ranka ya dad’e wlhy nima ban saniba, amma bara Na duba”.
Danne danne saurayin yafara da ‘yan dube-dube, babu wata matsala daga nan.
Kallon Galadima yayi yace “ranka ya dad’e babu wata Matsala daga nan, sai dai Idan daga cameras d’inne”.
A tsawace yace “bangane mikake nufi daga cameyas d’inne ba!? Kenan hay shigowata jiya babu kenan!? kuma kana zaune a office amma bakayi complain ba tun ajiyan? mika aikata!!? mi suka baka ne domin tozarta ni!!? nace nawa suka baka Saleem!!!!?”.
Kusan duk Wanda ke cikin plaza d’inan a yau yaji wannan hargagin Na Galadima.
Jikin matashin saurayin ne yafara rawa, ya zube a k’asa gaban Galadima saboda tsabar tsoratar dayayi da yanayinsa, tunda yake aiki a k’ark’ashinsa baita6a ganinsa cikin wannan yanayin irin Na yau d’inna ba, duk da labarin abinda yafaru yazo kunanensu, sunkuma ganin a jarida da social media baiyi zaton lamarin zaiyi zafi hakaba.
“wlhy yalla6ai babu Wanda yakeda abinda zai sayeni na cutar dakai, Kaine ka ceci rayuwata daga garari, ka tallafi maraicina a lokacin da nake Neman lalacewa saboda rashin matallafi, kazama gatana nida mahaifiyata da k’annena, mizaisa nabiyema rud’in wasu akan 6ata maka suna….”
“ya Isa haka!!”. ‘galadima yafad’a cikin tsawa’.
Gaba d’aya Galadima ya birkice musu a plaza, yasa securitys d’in wajen da dogaransa sun kori dukkan masu sayya dake ciki, ya tartare ma’aikatan wajen a d’aya, ya tabbatar musu da in har munafukan cikinsu da aka had’a baki dasu basu fidda kansuba gaba d’aya sai sunyi dana sanin saninsa.
Kaf d’insu sun rud’e, sai rantse-rantse da k’ok’arin kare Kansu sukeyi, amma yak’i saurarensu, ganin zasu kuma dagula masa lissafi saiya basu suspension kawai aka rufe plaza d’in baki d’aya.
Motocinsa Na k’ok’arin barin wajen motar Muftahu tashigo.
Muftahu ya faka motarsa waje d’aya suka fito shida Harun, (shima Harun abokin Galadima ne makusanci, Dan zan iya cewama yafi sanin sirrin Galadima fiye da kowa a abokansa gaba d’aya, shi d’an waziri ne).
Tunkan su k’araso Galadima ya sauke glass d’in motar da kansa. kallo d’aya sukai masa duk suka tsorata, Dan basu ta6a ganinsa a irin wannan 6acin ranba, baice uffanba, sai nuni daya musu akan su shigo motar.
Basu musaba suka bud’e suka shiga, Muftahu a gaba, Harun yashiga baya kusada Galadima.
Bayan gaisuwa dasukayi garesa babu Wanda Yakuma cewa komai, Dan ko gaisuwar bai amsa musuba, hannu kawai ya d’aga musu.
Sun hau titi sarkin mota yace “Ranka ya dad’e ina muka dosa?”. ‘cikin girmamawa da taka tsantsan yay maganar”.
Murya a shak’e yace “gidan Jayiday”.
Sarkin mota bai fahimtaba, amma yana tsoron tanbaya, murya k’asa-k’asa ya tambayi Muftahu ”.
Murmushi kawai Muftahu yayi yana girgiza kai, shiya shiga yima sarkin mota kwatance har suka Isa…..

 

?.?.?.?.?.?.?.?.?.?

Muna tsaka da barci saboda allurar da doctor yamana Innaro tafad’o d’akin, babu ko tausayi tashiga tashinmu cikin d’ad’d’aka mana duka a baya da cinyoyinmu.
Dagani har Munubiya a firgice muka tashi zaune.
“kutashi munafukai, Ashe abin ba a iya runguma da kama hannu ya tsayaba harda ciki kuka kwaso mana?, tsinannun gayyar tsiya, wlhy dagaku har uwarku yau saikin bar gidanan, a yau d’inan idan ubanku bai saki uwarkuba kun tattara kun tafi saina tsine masa albarka, yazo yaza6a ko Ku ko ni yau agidanan. sai kuma tafashe dakuka, takama bakin zaninta datayo lullu6i tana sharar hawaye, “kai ni dai Malam ya cutar dani akan had’a wannan aure da d’iyar marasa asali, ai gashinan ta Haifa mana bala’i da masifa, shikuma yatafi yabarni da kunyata, Malam kacuceni katafi kabar mana baya da k’ura. Wlhy yau sai A’isha tabar gidanan itada gayyar tsiyar ‘ya’yanta, natsaneku daduk wandama zai soki A’isha, natsaneku wlhy, takuma fashewa da kuka.
Tuni matan gidanmu kowa yafito, wasu harsun shigo falonmu, wasu kuma Na daga k’ofar d’aki, harda tsirarin ‘yan biki da sukak’i tafiya domin tsayawa kallon kwaf.
Cikin matan gidanmu ne wata taje tasanarma innaro wai bamuda lafiya munata amai duk abinda mukaci, anakiran likita ya dubamu yace duk munada ciki wata uku-uku.

Ni da Munubiya mun had’e kai muna kuka mai tsuma rai saboda tozarcin da innaro kemana muda mahaifiyarmu agaban bainar jama’a.
Dady da Abba k’aramine suka shigo sunama innaro magana akan bafa haka zancen yakeba, babu Wanda yace munada ciki.
Hayayyak’o musu tayi tana zaginsu, wai k’aryane suna kare Innarmu ne, aida likitan bai fad’aba baza’aje a sanar mata ba.
Cikin 6acin rai baba k’arami yace, “inna waye yaje yafad’a miki wannan maganar to?”.
“cikin matan gidanan mana, kuma daga bakin wadda nasan bazataimin k’aryaba”.
Ran Dady ma a wannan karon ya 6aci, afusace yace, “inna wacece acikinsu? Wace ‘Yar isakar matace”.
Nanafa matan gidanan mu suka shiga raba idanu akan juna.
Innaro tace “karka kuma zaginta, idaba ayiba bazatace anyinba, kuma koma wacece bazan fad’aba, idan kuma ni kake zagi sainaji?”.
“ALLAH ya huci zuciyarki inna, ni yaza’ayi Na zageki”.
“kai dai kasani sakarai”.

Duk abinda ke faruwa Abbanmu da Innarmu Na saurare daga d’akinsa amma acikinsu babu Wanda yayi yunk’urin fitowa.
Kayanmu innaro tafara kwasa tana watsowa waje, wai saimun bar gidan.

“Innalillahi wa inna’ilaihirraji’un, wannan wane irin tashin hankaline?”. ‘innarmu tafad’a cikin matsanancin kuka’.
Rungumeta Abbanmu yayi shima yana k’ok’arin maida kwallar data cika masa idanu.

Ganin abin yana Neman wuce gona da iri baba k’arami yafita da hanzari, wani tsoho dake can k’asan layinmu yaje ya d’akko, tsohon abokin Malam faruku ne na k’ut da k’ut, shika d’aine zai iya takama Innaro burki kuma.

Aiko hakance ta kasance, tunda yashigo yay magana Innaro ta dakata da abinda takeyi tana huci da fidda numfashi.
Tsoho Malam Labaran yace, “haba innar jafaru, da hankalinki da girmanki kike aikata wannan abin Na yara a gaban sirikanki da ‘ya’yanki da jikokinki? Shin babu mai fad’a miki kijine wai kekam?”.
Cikin sassauta murya tace, “malam mai kanwa nasan bakasan ainahin abinda yafaru bane kaima, amma wlhy da dakanka zakace Auwalu yasaki marar asalinnan sukama gabansu itada ‘ya’yanta am…..”
Hannu ya d’aga mata, yagyara tsayuwarsa jikin sandarsa dake taimaka masa tafiya, naji komai innar jafaru, amma wannan hanyar da kuka biyo ba wai itace mai 6illewa ba, bincike yakamata ayi domin asan gaskiyar lamarin. dan haka zoki wuce gida, zuwa gobe zamu tattauna akan lamarin sannan kowa ya nutsu, mukuma jira abinda zai fito daga can gidan Sarkin”.
Badan innaro tasoba tafice, hakama matan gidanan mu basuso wasan yak’are iya nanba, sunso a yau Innarmu tabar gidan da saki, sannan mukuma mahaifinmu ya koremu. Kowa taja k’afa takoma d’akinta cikeda takaici da addu’ar ALLAH yasa daga gidan sarkin suma su d’auki mummunan mataki akanmu…..

Maman fauziyya Ce kawai ta nuna damuwarta akan lamarin

?.?.?.?.?.?.?.?.?.?.?

Su Galadima ma sun isa gidan jaridar *Manuniya* tun sanarwar isowarsa ta kad’a hantar cikin ma’aikatan wajen, musamman wad’anda basuda laifi akan lamarin, tirsasu akayi.
Shi kansa manaja d’in wajen a kid’ime yake, dukya rikice yarasa matsugunni har Galadima da gayyarsa suka iso office d’in bisa jagorancin sakatare d’insa.
K’asa yazube kawai yana kwasar gaisuwa wajen Galadima, ko kallo bai ishi Galadima ba, cikin daka tsawa yafara magana………..???

 

Tofa masu karatu, ko manajan jaridar MANUNIYA zai amsa laifinsa? Kokuwa zai fad’i wad’anda suka sanyashine inba laifinsa bane shima? to koma dai shima da had’in bakinsa?. Wane mataki masarautar su Galadima kuke ganin zata d’auka akansa? Shin ina ma maganganun Momma suka dosa ne? Miya faru da mahaifin Galadima har suka koma k’asar India da zama?.??

 

Kumuje zuwa my guys danjin yanda zata kaya. da amsoshin d’unbin tambayoyinkun nan.????????????????

_Naga mutane basa fahimtar yaren yarima??, yarima later R ne baidashi, bawai tsamin bakine dashiba fa, kun gane, naga wasu kamar suna zaton tsamin bakine dashi??._

_Ngd da comments d’inku, kuna sakani farin ciki sosai, kuyi hak’uri da rashin amsawa ta, kunada d’unbin yawane wallahi??????????. I love you wujiga-wijiga all?????._

 

 

*_Ya ALLAH ka gafarta ma iyayenmu_*??????
[4/16, 9:53 AM] +234 811 277 0720: *_Typing??_*

 

*_HASKE WRITERS ASSO…??_*
_(Home of expert and perfect writer’s)_

 

*_?RAINA KAMA……!!?_*
_{Kaga gayya}_

 

*_Bilyn Abdull ce????_*

__________________________

*_Naga idi????, Galadima fa ba tsamin baki bane dashi, Ku fahimta??, bashida (R) ne, amma gashinan nayi gyara, ina fatan yanzu zakuna fahimtarsa??._*

_______________________________

 

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply