Hausa Novels Raina Kama Book 1 Hausa Novel

Raina Kama Book 1 Page 11


Raina Kama Book 1 Page 11
Viral

???1?1?

………Ba manager kawaiba, hatta da sauran jama’ar dake gidan jaridar saida suka tsorata da tsawar Galadima, su Muftahu ma tsorone ya kamasu, sunsan irin wannan matsanancin fushin gareshi babbar matsala ce ga lafiyarsa.
Aikam sai gashi ya dafe kansa, saboda yay wani mugun sara masa, da sauri Harun yajawo kujera ya kamashi ya zaunar, har yanzu dafe yake da kan nasa.
Muftahu ya furzar da hucin, matsalar da suke gudun ta d’akko hanyar faruwa kenan. kallon manaja dake durk’ushe har yanzun yayi,
yace “tashi ka zauna”.
Mik’ewa manaja yayi jiki Na rawa yakoma saman kujera, Muftahu da Harun ma suka zazzauna.
Cikin tsare gida Harun yace, “manager ka nutsu, kabamu had’inkai wajan fad’ar gaskiya, inba hakaba wlhy zakayi nadama ne, ba kaiba hatta da ahalinka saisunyi nadamar kasancewarka acikinsu”.
Manaja yashare guntun kwallar dasuka taru masa a idanu, a nutse yafara fad’in “ai tunkan jaridar jiya tafita nake acikin nadama, nayi dana Sanin kasancewata ma’aikacin jaridar da aka ci zarafin d’an Wanda yay tushen kasan cewata a wannan matsayin danake, da ace remote d’in rayuwata a hannuna yake, dana tariyo bayana jiya bata shigo rayuwata ba, amma Na…..”
Muftahu ya katseshi cikin d’aga masa hannu “kaga manager, ba rayuwarka mukazo saniba, munason ka fad’a mana waye yasaka wannan aikin? nawa suka biyaka kamusu shi?”.
“wlhy tallahi yalla6ai basu biyani komaiba, kaga wacan jakar sune suka ajiye min ita, amma ko bud’eta banyiba. kuma babu wani ma’aikaci daya buga labarinan agidan jaridar nan da hannunsa. sune da Kansu adaren jiya sukayi komai, bayan sun had’emu waje guda da bindugu, kuma sunzo nannane dukansu fuska arufe, wlhy ko fuskar mutum d’aya bamu ganiba, yanzu haka sun kwashe muhimman documents dake ma’aikatar nan sun tafi dasu. kuma sunsan da zuwan yalla6ai gurinnan yau, Dan komai sunyishine a tsare kamar yanda mukaji suna hira a tsakaninsu” manaja ya fashe da kuka, sannan yacigaba da fad’in “saboda sunsan zakuzo nan yau, sunje gidana tun adaren jiya, sun kwashemin iyali da mahaifiyata, yanzu haka suna wajensu, sun tabbatar min inhar wani magana yafito abakina abakin ran matata da yarana hud’u da mahaifiyata sai k’anwata. wlhy ina cikin masifa, yau anan Na kwana, nakasa fita waje saboda banason jin 6atancin da jama’a suka gani a wannan safiyar akan yalla6ai. Wlhy Na rantse muku bansan komaiba”.
Tunda manaja yafara magana kowa yay tsit, Galadima bai d’agoba saida yaji manaja ya ambaci iyalansa Na wajen wad’anda suka aikata aika-aikar. Idonsa yakad’a yayi jazur, sosai manaja ya tsorata da idanun Galadima, haryana tunani a zuciyarsa anya Galadima shi kad’aine, bashida aljanu kuwa?.
Komai Galadima bai ceba, ya tashi dafe dakai yafice daga office d’in, ma’aikatan wajen sai zubewa suke suna kwasar gaisuwa, amma kallon kowa baiyiba yafice.
Dogaransa suna ganinsa suka mik’e da Sauri, Mota suka bud’e masa yashiga, suma su Muftahu suka fito da hanzari.

 

?.?.?.?.?.?.?.?.?.?.?.?

Tun daga fitar innaro sai gidan yay tsit, kowa ya kama gabansa zuwa d’akinsa, a can suka cigaba da gulmace-gulmacensu suda bak’insu.

Niko da Munubiya muka shiga raira sabon kuka, munubiya ta kamo hannuna ta rik’e anata.
“Munaya dan girman ALLAH kibarni Na kar6i hukuncin laifina, nice Na aikata bakeba, miyasa zaki cema iyayenmu kece? kibari nafad’a musu gaskiya please ”.
“A’a Munubiya, wannan laifin nawane, karki manta ta sanadina abinnan yafaru, da ace Fu’aad bai kaimu plaza d’innanba da hakan bata faruba wlhy, munubiya farincikina fansane agareki, har abada bazan iya juriyar ganinki cikin k’unciba, Dan Girman ALLAH koda da wasa kar wani agidannan yaji banice Na aikata abunnanba koda kuwa innarmu Ce, namiki alk’awarin zan jure duk wata fitina dazata taso, zankira Fu’aad yafito muyi aure, duk da naso ace rana d’aya aurenmu zai kasance, amma haka ALLAH ya k’addara mana”.
rungume juna mukayi muka kuma fashewa da kuka, cikin shashshekar kuka Munubiya ke fad’in “mi mukaima Wanda ya k’ulla mana wannan sharrin? mi muka tare masa agidan duniyarnan Munaya?”.
“ban saniba Munubiya, bansan waneneba? Amma nafi zargin gidan wannan jaridar, aganinsu sun sami babban labari, bara su buga suyi suna, Sun zaluncemu Munubiya, sun yad’a labarin abinda ba haka faruwarsa ta kasanceba, Galadima ko ta6aki baiyiba amma suka saka har yana kissing d’inki, wane irin zaluncine wannan? wlhy nima bai ta6a niba da mukayi karo a filin idi, amma ki duba hannunsa rik’e da nawa ajaridar, Munubiya banga laifin iyayenmu ba, kowanne mahaifa bazasu so ganin wannan mummunan abinba, kuma ko zamu kwana rantsuwa bakowa zai amince damu ba, INA tausayama innarmu, ada Yaya muka k’are ma a gidannan bare yanzu?, munubiya innarmu innarmu, banason innarmu tashiga mummunan hali akanmu, yazamuyi innarmu ta fahimcemu, koda ace kowa bai yarda damu ba inason innarmu fahimcemu munubiya…..”

“Na fahimceku ‘ya’yana, tabbas nashiga tashin hankali da ganin hotonku a jarida, kuma a yanayin da kowace uwa ba zataso ganin ‘ya’yanta a wanna halinba, kuma ace bazata shiga fiyeda yanayin Dana fad’aba, sai dai ni ba abinda naganine yasakani cikin rud’ani irin haka ba harna yanke jiki na fad’i, cin zarafin innaro ne.
‘ya’yana nasan bazaku aikata koda makamancin hakanba, dan naji ajikina sharri akai muku…..”
Da gudu suka sakko a gadon sukazo suka fad’a jikin innarsu suka cigaba da raira kuka harda ita kanta innar, saida sukayi mai isarsu sannan sukayi shiru.
Duk suka nutsu suka mata bayanin komai, har Munaya ta d’akko wayar da Galadima ya barta da ita a filin idi ta nuna musu.
Nanna INA ta kuma fahimtar akwai 6oyayyen al’amarin abinda basu saniba akan lamarin, kuma tafi zargin k’ullin Anma Galadima ne kawai, ‘ya’yanta k’addara Ce ta sakasu cikin sark’ak’iyar, itadai Addu’arta ALLAH ya fiddashi da ‘ya’yanta baki d’aya, saitaji yabata matuk’ar tausayima.
Suna cikin haka saiga mama Rabi’a dasu Ayusher, nanma aka kuma zaman warware zance, mama Rabi’a da inna suka kuma fahimtar komai yanda yake.
Nasiha suka Shiga yima ‘ya’yan Nasu mai ratsa jiki, sannan suka nuna musu illar biyema samari batareda wani dogon tunaniba, duk sai jikin su Munaya yayi sanyi, sun fahimci bin Fu’aad dasukayi plaza shine yazama babban kuskurensu.
Sun nemi gafarar iyayen nasu akan hakan dasuka aikata, daganan suka Shiga tattauna maganar Auren munaya da Abba yakafe akan nanda sati biyu.
Sun Yanke shawara akan akira Fu’aad, inhar da gaske yakeyi to saiya fito kawai.
Akan wannan shawarrar suka zauna gaba d’aya.

 

??.??.??.??.??

Har suka Isa cikin masarautar Galadima baiko motsaba, yana tangad’i da layi yashige 6angarensa, daga Muftahu har Harun babu Wanda yayi yunk’urin binsa.
Tunda yaje yazube saman 3seater bai sake sanin inda kansa yakeba saboda matsanancin ciwon kai dake damunsa, da k’yar ya iya gabatar da sallar magrib da isha’i a lokaci d’aya, a saman abin sallar ya kwanta rigingine dafe da goshi, yana kwance shiba mai barciba shiba ido biyuba.

8:30pm dukkan mai ruwa da tsaki a meeting d’in ya hallara, hatta da sarki gaba d’aya, sai dai kuma babu Galadima babu dalilinsa har mama Fulani tafito.
(Babbar magana ??) na fad’a a raina, saboda ganin tsantsar mulki da isa ajikin hamshak’iyar tsohuwa dazata iya kaiwa shekaru 77 a duniya, sai dai tsantsar hutu da gayu ya 6oye ziryan d’in tsufan nata, gata da k’aramin jiki kuma, daka ganta haka bafulatanar asali.
Tunda ta fito kowa a falon yamik’e tsaye saboda girmamawa a gareta, amma banda sarki, ya risinar da kansane kawai alamun girmamawa ga mahaifiyar tasa.
Saman kujera 2seater ta zauna cikeda izzar mulki, (saikace itace sarkin??????) sai da ta gamaima kowa dake falon kallon tsaf sannan takuma kamewa, cikeda k’asaita tace, “Shi yana ina? Ko raini. Hankalin nasane ya hanashi zuwa?”.
Kowa dake wajen yasan galadima take nufi, babu wanda ya iya cewa komai sai wani matashin saurayi dazasu iya zama sa’annin juna da galadima, ya gyara zamansa yana wani 6ata rai shima, “Granny kinsan halinsa aii, ba ganin kowa da gashi yakeba a masarautar nan mtsoww”.
Mama Fulani ta turo hanci ga bada, cikeda fushi ta bada umarnin a kira mata jakadiya.
babu dad’ewa saiga jakadiya tashigo, k’asa ta zube tamkar zatayi mata sujuda tafara fad’in “ALLAH yaja zamaninki ranki ya dad’e, kinga taki kinga tawasu, fatanmu kiga tawasun wasuma, Sarautar gagara badau a hannunki take, domin kaida kaya ai duk mallakar wuyane, duk mai shirin ganin barcinki ya tabbata shima bazaiyi nasaba, kece k’i gudu samaza gudu, jaruma mai dad’and’en tarihi, kin ajiye tarihin da babu wanda yake dashi a masarautar nan, koda kuwa mai martaba gagara badaune, ALLAH ya tsare gabanki ya tsare bayanki, mace mai kamar maza, mazanma a tafin k’afafunki suke ya uwar gijiyata”.
Sosai kirarin jakadiya yayima mama Fulani dad’i, takuma kishingid’a a kujerar, cikeda izza tace, “inason ganin Galadima yanzunan”.
Angama damusa k’i sabo, cika umarninki wajabtaccene a gareni ‘Yar sarki, matar sairi kuma mamar sarki, wata ran kakar sarki, ki huta lafiya babbar giwa”.
Fita jakadiya tayi.
Ta isa 6angaren galadima, inda sarkin k’ofa yashiga domin yimata iso, halin daya isake shugaban nasa ya razanashi, amma haka yadake ya isar da sak’on jakadiya.
Da k’yar galadima yay masa nuni akan yabarta tashigo.
Babu dad’ewa saiga jakadiya, ta rusina cikin girmamawa ta gaisheshi, bata damu da rashin amsawar tashiba ta isar da sak’on mama Fulani. hannu kawai ya iya d’aga mata.

Kusan mintuna 7 da fitar jakadiya yamik’e dafe da kansa dayakejin tamkar zai fad’o k’asa, jiyay falon na juya masa, ya dafe bango da gyar kusan 2munute sannan yad’an lafa, haka yafito yana d’an tangad’i, wajen mota yanufa, dan bazai iya zuwa sashen mama Fulani da k’afaba, saboda akwai tazara sosai a tsakaninsu.
Da sauri sarkin mota yataso ya bud’e masa, shima shiga yayi mazaunin driver, sauran dogaranma suka shishshiga mota.
Da k’yar galadima yafurta “sashen mama Fulani zamuje, sauran su zauna”.
cikin girmamawa sarkin mota ya amsa, sannan ya sanarma sauran dogaran.

dukkan jama’ar dake falon idanu suka zuboma Galadima daya shigo dafe da kansa, baima kowa magana ba yasamu can gefe ya zauna, har yanzu hanunsa na saman kansa, muryarsa a shak’e yace, “barkanku da dare”.
Hakan yayi masifar k’ona ran mama Fulani, saboda ma ya rainata tare zai gaidata da kowa? kuma bazaizo gaban taba ma yabata girmanta?.
A falonma wasu sun amsa wasu basu amsa mishiba, shi baima San sunayiba, ta kansa kawai yakeyi.
Cikeda izza mama Fulani tace, “to isashe, gaisuwar ma saina rok’a ko yaya”.
Dukda halin dayake ciki bai hanashi sakin guntun murmushiba, ya janye hannunsa daga goshinsa, idanunsa dasuke matuk’ar jajur yad’ago ya kalleta, ba mama Fulani niba kowama a falon ya firgita daganin idanunsa, hakan ya tabbatar musu da bashida lfy kenan.
Ahankali Yakuma furta “bagykanki da hutawa”.
“ALLAH yarabamu da bak’in hali” . ‘mama Fulani tafad’a batareda ta amsa gaisuwar ba’.
Baice uffanba ya maida kansa ya duk’ar, tareda kuma tallafe goshin yana ta6e baki.
Idanun Ummu Hasheem yacika da kwalla saboda tausayin Galadima, ko kad’an batasan bashida lafiya ba, dukda d’azun ta aika bayinta su duba matashi suka tarar yafita.

Mama Fulani kam baki ta k’ya6e tareda kuma hard’ewa a kujera, takai dubanta ga wani dake gefenta, Matawalle! ahad’amin video call da Zeenah yanzunan”.
“angama ranki ya dad’e” Dan danan yahad’a video call bayan yakira wata number, wata kamilalliyar matace ta bayyana ajikin System d’in, tana sanye cikin shigar kamala, kallo d’aya namata Na hango kamannin Galadima tartare da ita, dukda kamar tafisa haske, hakkane ya tabbatar min da Momma ce.
Cikin girmamawa ta gaida mama Fulani, ita kuma ta amsa cikeda k’asaita sannan tafara magana kamar haka.
“nasan kowa yasan miya taramu anan wajen?, bana buk’atar maimaita wannan shed’ancin a harshena, wanda kuma ya aikata yasan kansa, Dan haka hukunci biyune, yanada za6i aciki. Na farko tozarcin da yayama masarautarnan da zubar mana mutunci mun haramta masa auren kowacce yarinya data fito daga kowacce masarauta, na biyu ya gaggauta fidda matar aure acikin shekararnan kafin yaje yayma wata ciki a waje akawo mana d’an tsakar gida a masarauta, kokuma mu muza6a masa acikin bayin gidannan, hukunci na farko babu sasauci acikinsa kuma babu canji, Na biyu yanada za6i nemowa komu nema masa. Wannan shine tabbataccen hukuncin kotun fulani. Idan akwai mai abun fad’a sainaji?”.
Kowa ya girgiza kai alamun a’a, wasu hukuncin bai musu dad’iba, wasuko yamusu fiye da zaton mai karatu.

A hankali Galadima ya yunk’ura yatashi batareda yacema kowa uffanba yanufi hanyar fita.
“to fand’ararre, daka tafi ba’a gama magana ba ai uwarka zataji, mara mutunci mai bak’in hali”.
Juyowa Galadima yayi ya kalli mama Fulani, wani k’asaitaccen murmushi ya sakar mata sannan yay salute nata yafice abinsa”.
Mafi yawansu saida suka zaro idanun mamakinsa, dama Kowa yasan galadima baya tsoron mama Fulani a masarautar, duk masifarta saima yagadama yake amsata, gaisheta kam saiya zo k’asar yatafi ma bata ganshiba. Iya kacinta tayi masifarta da sababi ta hak’ura, babu yanda ta iya dashi.
Murmushi kawai shima sarki yayi baice komaiba.
Mama Fulani kam kasa koda motsi tayi a kujerar saboda abin kunyar da galadima yayi mata gaban kowa, ta tsani shed’anin yaronnan mai ido a tsaitsaye dabaya shakkar kowa. Kwafa tayi sannan tatashi tabar falon tana tafiya cikeda mulki da izza.
Gaba d’aya suke fad’in ALLAH ya huci zuciyar sarauniyar sarakuna.
Duk abinda ke faruwa Momma naji kuma tana gani, amma dayake Galadima yana bayan laptop d’in bataga miyayiba, hasalima bataji ko sau d’aya yayi magana ba, hakanne ya tada hankalinta, mama Fulani Na barin wajen ta katse call d’in, waya ta d’auka takira number Galadima, amma harta tainke bai d’agaba.
Kira Na biyu ta sakeyi, hakan yay dai-dai da shigowar Galadima falon dafe da kansa.
Da k’yar ya iya d’aga wayar, muryarsa a shak’e yace, “Momma zan kigyaki anjima” bai jira cewarta ba ya yanke wayar.
Hankalin Momma yakuma tashi, tasan ransa yakai k’ololuwar 6aci, da sauri ta danna kiran Harun, yana d’agawa ko gaisuwar dayake mata bata amsaba tace, “Harun maza jeka duba min Moh’d yanzunan”.
Yanda yaji Momma Na magana shima kansa saiya kid’ime…..

 

?.?.?.?.?.?.?.?.?.?

Ayusher tafita tasiyo min credit domin kiran Fu’aad.
Jikina a sanyaye nagama loda katin, tunani nakeyi shin Fu’aad zai kar6eni bayan yaji abinda yafaru a jiya zuwa yau? tunda komai akan idonsa yafaru. Na dad’e ina juya wayar a hannu kafin Nayi dialing d’in Number d’insa d’in, harta tsinke bai d’agaba, ban damuba Na sake kiransa da tunanin ko baya kusa da wayarne.
Bugun farko kuwa ya d’aga wayar………..???

 

Humm masu karatu, mi kuke tunanin zai faru tsakanin Munaya da Fu’aad a waya, zai kar6eta kokuwa sa6anin haka?.
Yaya zata kasance ga Galadima kuma?.

Wannan amsar tana a page 12 da zaizo muku ranar Monday??????.

 

Barkanku da juma’a.

Musha weekend lafiya????????.

 

Team *_INNARO & MAMA FULANI_*???????????????????.

 

*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu._*??????
*_Typing??_*

 

*_HASKE WRITERS ASSO…??_*
_(Home of expert and perfect writer’s)_

 

*_?RAINA KAMA……!!?_*
_{Kaga gayya}_

 

*_Bilyn Abdull ce????_*

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply