Hausa Novels Raina Kama Book 1 Hausa Novel

Raina Kama Book 1 Page 2


Raina Kama Book 1 Page 2
Viral

Raina Kama Book 1 Page2

………Zan iya ce muku fitinar gidanmu ta farone daga tushe, dan kuwa ginannen abune tun zamanin k’uruciyar iyayenmu…

Malam Faruku shine kakanmu, matarsa d’aya Marwa’natu (Innaro), ‘ya’ya hud’u suka Haifa a duniya, maza uku mace 1. Auwal, Hameesu, Saffiya, Jafaru.
ALLAH yayi Innaro mace mai mugun son abin duniya, arayuwarta tanason ace komai daga gareta aka fara ganinsa, kokuma wajen ‘ya’yanta, sun tsayama ‘ya’yansu duk sunyi karatun addini dana boko, sai dai Safiya iyakarta primary aka mata aure. Sukuma mazan duk sunkai matakin babar makaranta (jami’a). wannan yasaka Innaro d’aukar burin duniya ta d’ora akan ‘ya’yan, harma matan dazasu aura.
Auwal shine yafara kammala karatunsa, dan haka Malam faruku mahaifinsu yace ya fiddo matar Aure.
Bai wani tsaya Jan rai ba ya gabatar da Ai’sha amatsayin wadda yakeso.
Kai tsaye innaro tace sam bata aminceba, d’anta bazai auri d’iyar buzayeba kuma ‘Yar iska, Auwal yayi lallashin yayi rok’on akan fahimtar da ita sonda sukema juna shi da Ai’sha, amma Sam tak’i saurarensa balle ta fahimcesa.
Da farko Malam faruku yasaka musu ido, azatonsa innaro zata sakko cikin sauk’i, amma ganin yanda ta kafe akan bakanta saiya sanya baki da tambayarta dalilin k’in amincewar.
Kai tsaye tace batason su Ai’shar ne, Dan ba’asan asalin suba, sannan kuma ‘Yar iskace, shima kuma yasani ai. cikin hikima Malam yaso fahimtar da ita halin k’addara kowa da irin tasa, itama Aishar bayin kanta bane ba, amma tak’i saurarensa shima. ganin abin zai tasamma rashin mutumci yace to aure tsakanin Auwalu da Ai’sha kamar anyi an gama. A wannan lokacin ba k’aramin birkicewa innaro tayi musuba, amma Malam faruku yace tayi tagama, dan hujjarta batada muhimmancin dazai haramta auren Auwal da Ai’sha. babu 6ata lokaci kuma aka fara shirin bikin.

*Wacece Ai’sha?*
Ai’sha d’iyace gawasu buzaye ‘yan k’asar Niger wad’anda k’addarar rayuwa ta jawosu zuwa k’asar Nigeria, su biyu kacal iyayensu suka Haifa, Aisha itace babba, sai k’anwarta Rabi’atu, wurjanjan suka shigo k’asar Nigeria, sun fara rayuwane awata tashar mota, inda anan tsautsayi ya fad’ama Ai’sha wani mara imani yamata fyad’e anan cikin tasha da daddare, randa abin yafaru Malam faruku yaje tashar zai bada sak’o akaima wani d’an uwansa dake garin Maiduguri, ya taras anata cecekuce atashar, yayinda Ai’sha da iyayenta ke rungume da d’iyarsu sunata kuka da kururuwa.
Malam faruku yatambayi abinda ke faruwa daga wajen mutanen dasuka zagayesu suna kallo, babu 6ata lokaci matashin saurayi yafad’a masa komai.
Hankalin Malam faruku yayi matuk’ar tashi, danshi mutumne mai kishin al’umma, anan ya d’auki Ai’sha da iyayenta suka nufi asibiti, saboda jinin daketa zuba daga jikinta (Dan bazata wuce 15 ba sannan), duk wata kulawar da yakamata anbama Ai’sha a asibitin, har tsawon kwanaki hud’u tasamu lafiya sarai, kamarma komai bai faruba, sai dai tabo Na zuciya da aka bar mata itada iyayenta. tun suna zaman asibiti Malam faruku ya fiskanci iyayen Aisha basuda wajen zama, dan haka yak’udiri niyyar taimakonsu.
Akwai wani d’aki k’arami ciki da falo dake gidansa, saiya zagaye musu shi da Katanga yamasa gyara.
Tunda aka fara aikin innaro ta tada hankalinta, duk zatonta aure zai k’ara, ganin tana neman tara masa k’asa ya zaunar da ita yamata bayani dallah-dallah, maimakon ta kwantar da hankalinta tunda ba kishiyar bace saima takuma tadashi, tace bazata zauna da iyayen Aisha ba.
Malam faruku yace bata isaba, Dan gidansane babu mai hanashi ajiye Wanda yakeso akuma lokacin dayaso.
Dole badan innaro tasoba su maman Aisha suka zauna agidan, sai dai ko kad’an basajin dad’in zama da ita, kullum gori da cin mutunci take musu, su Aisha kam basuda sakat awajenta, saita koma sakasu aiki tamkar boyi-boyinta. Malam faruku ne ya koyama mahaifin su Aisha sana’a, har shima yasamu rufin asirin rik’e iyalensa dai-dai gwargwado, amma ko kama k’afar Malam faruku baiyiba, lokuta da fama ma shine ke taimakonsa dawasu abubuwan Na rayuwa, musamman d’inkin sitturar su Aisha da wasu matsaloli Na yau da kullum dasukan taso. tun zuwansu gidan Auwal yafara k’aunar Aisha, duk da mahaifinsu ya Sanar musu da komai akan k’addarar da ta fad’ama Aishan kuwa, shekararsu biyu suna soyayya, tun Aisha Na d’ari-d’ari dashi saboda tsoron abinda aka aikata mata har tazo tasaki jikinta dashi, sai dai babu Wanda yasan suna soyayyar sai Rabi’a k’anwarta.

Ana haka kuma Auwal yazo da zancen Aisha zai aura.

To haka dai akayi auren Auwal da Aisha badan innaro tasoba.
Wannan kuma yasakata d’aukar Karen tsana ta d’orama Aisha, kullum cikin zagi da cin mutuncin Aisha take, sosai tazamar mata Uwar miji mai kishi da sarakuwa, ga gorin datake mata akan ita ‘Yar iskace, babu wani fyad’e da’aka mata, taje tayi iskancinta an fake da fyad’e an dawo an lik’ema d’anta da asiri, tujara dai iri-iri dai ta innaro.
Aisha tanada hak’uri, ko kad’an abinda innaro kemata bai hanata girmamata ba da bata matsayi irinna uwa, amma innaro bata gani.
Watan aurensu 7 kacal innaro ta samoma Auwal wata yarinya mai suna Mero, mero d’iyace ga wani matashin d’an kasuwa, tun alokacinma ana lissafashi a masu kud’in yankin balle yanzu daya zama shahararre, Auwal bayason Mairo, amma dolensa ya aura saboda innaro tace zata tsine masa.
Shigowar Mairo Yakuma k’untata Aisha a gidan, dan tunkan ta shigo innaro tagama 6ata sunan Aisha dana iyayenta awajensu mairo, shigowar mairo da wata 1 kacal kuma tasamu ciki, wannan fa yakuma k’ara ta6ar6arewar al’amura, gashi sannan ALLAH ya yalwatama Auwal d’in babu laifi, harma yasayi wasu filaye uku shida ‘yan uwansa anan cikin anguwar kusada su innaro, amma ba’a ginaba, dan babu kud’in ginin lokacin.
A wannan lokacinne kuma k’addara ta afkama iyayen Aisha, ranar wata alhamis da daddare aka maka ruwa Na tashin hankali, Wanda yay sanadin fad’awar d’akin dasuke ciki suka rasu.
Aisha da Rabi’a sunshiga matuk’ar tashin hankali, hakama Malam faruku, innaro kam ko’a jikinta.
Rasuwar iyayen Aisha yasaka rabi’a k’anwarta dawowa hannunta da zama, akuma lokacinne Hameesu shima yace Rabi’a yakeso da aure. tashin farko innaro ta taka masa birki da kukarin zata tsine masa kuwa. dole yabar maganar auren Rabi’ar yasamo wata Ruk’ayya ya aura.
A lokacinne Mairo ta haihu namiji, zokaga murna wajen innaro da mairo, Malam ma yayi murna, hakama Aisha, dukda innaro tace Na munafurcine. ranar suna yaro yaci Abdulhameed, koda wasa mairo bata ta6a yarda Aisha ta d’auki hameed ba, dan innaro tahana, Auwal yayi fad’an shida Malam harsun gaji.

Rayuwa tacigaba da tafiya tsawon shekaru, zuwa sannan su Auwal sun had’a hannu sun gina filinsu, kowa da 6angarensa, gidanmu yafara yawaita da ‘ya’ya, dan matar Hameesu ma ta haihu Namiji Shafi’u, hakama matan gidanmu sun k’aru, dan jafaru ma yayi aure, hakama Hameesu yak’ara aure shima, ga iyayenmu sun kuma bunk’asa, dansu wuce buk’atun yau da gobe, dai-dai gwargwado akwai rufin asiri agaresu, alokacin kuma sai Auwal yakuma auro ta uku, auren iyayenmu yakoma tamkar gasa wajen za6o ‘ya’yan manya, dan kuwa Aisha ce kawai d’iyan talakawa acikinsu, tana zaunene kawai da k’arfin ALLAH dakuma Na Malam faruku, saikuma soyayyar mijinta Auwal, amma da dan ta innaro ne da tuni Auwal ya saketa.
Akwaima randa fada ya had’a mairo da Aisha akan Rabi’a ta doki hameed saboda yamata rashin kunya, dukan da mairo taima Rabi’a saiya sa Aisha kasa hak’uri a ranar ta tanka mata, nankuwa mairo tafara zuba mata gori da cin zarafi, da innaro tazo danjin ba’asin rigimar saitace dole Auwal yasaki Aisha, dukda kuma mairo ce mai laifi, Auwal yayta magiya amma innaro tace yaza6a ko ita ko Aishan, babu yanda zaiyi yasaki Aisha saki d’aya alokacin. Hankalin Aisha yatashi matuk’a, dan batasan inda zasu dosaba, tunda basuda kowa a Nigeria, ga innaro tsaye akanta tace atake saita bar mata gidan d’a.
ALLAH ya tak’aita abunne dai-dai sanda Aisha ke fitowa rik’eda hannun Rabi’a kuma saiga Malam faruku yadawo daga kasuwa, nanfa ya tambayi ba’asi, Aisha tasanar masa komai, maidata yayi gidan, yakuma saka Auwal ya maida aurensu atake awajen, sannan ya tabbatar masa ko bayan babu ransa yasake sakin Aysha bai yafeba, kuma inhar innaro tasake sakashi ya saketa itama abakin aurenta.
Wannan shine dalilin dayasa auren Aisha da Auwal bai sake rawaba. rayuwa kuma tacigaba da shurawa. Matan gidanmu 7.
Auwal matansa uku, Aisha (innarmu) Mairo (mama) Sadiya (gwaggon haleema)
Hameesu nada biyu, Ruk’ayya (umma) Hadiza (momy)
Jafaru Nada biyu shima, Suwaiba (maman safara’u) Hafsatu (maman Fauziyya).
Kowacce ta haihu acikinsu, amma banda Aisha, wadda saida sukayi shekara 20 da aure itada Auwal sannan ALLAH yabata ciki, zokiga murna wajen Auwal da ahalinsa, saidai banda matan gidanmu da innaro, dan aganinsu duk sunfi Aisha matsayi, (maman fauziyya) Ce kawai babu ruwanta, dan suna d’asawa da Aisha sosai, ita kad’aice bata raina innarmu ba, dan Yaya ma take cemata.
Babu irin wahalar da Aisha batasha agidanba acikin shekarunan, kullum cikin mata gorin haihuwa dana talauci ake, harma dana batada asali, tundaga kishiyoyinta har matan k’annen mijinta basu raga mataba, kowacce jitake ina wuta tasaka innarmu a gidan, dama ga d’aurin gidi daga innaro suna samu. innarmu bata cemusu komai, saidai tashiga d’aki tasha kukanta, ‘ya’yan maman fauziyya ne kad’ai ke shigowa d’akinta, amma sauran duk an hanasu, gashi ta aurar da Rabi’a tuni, itama harta haihu uku ma.
to saikuma ga Aisha da ciki rana tsaka, bayan tagama fidda ran haihuwarma gaba d’ayanta. cikin ikon ALLAH cikinta yakai haihuwa, ranar data haihu saiga ‘yan biyu k’yawawa kamarta duk mata, A zahiri matan gidanmu suna k’untatama innarmu ne saboda yanda innaro tagama 6ata Aisha awajensu, a bad’ini kuma suna k’in Aishane saboda tafisu k’yau da komaima Na halittar jiki, (dan cikakkiyar buzuwa Ce) mai k’yawu Na asali, dirarriyar macece doguwa, fara tas, gashin kai, idanu da komai ALLAH yabatasu. Sa6anin su daba haka sukeba. cikin ikon ALLAH kuma saigashi ta haifo ‘ya’yanta masu tsananin kama da ita.
Hassana (Munubiya) da Hussaina (Munaya) wad’anda suke matuk’ar kama da juna, kamar Munaya da Munubiya ta 6aci matuk’a, ko Aisha saitayi da gaske take banbancesu, saida suka fara girmanema ake d’an banbantasu tawajen halayya shima ba kowaba, amma Aisha ita tana ganesu kai tsaye a sanan.
Munubiya tanada hak’uri tamkar Aisha, duk wahalar dasukesha wajen yaran gidan bata iya ramawa, saidai tasha kukanta tashare hawaye. sa6anin Munaya da take fitinanniya, bata bari a cuceta, koda anfi k’arfinta saitabi tawata hanyar tarama kuwa, wannan yasaka matan gidan da yara sukafi tsanarta, sai dai kuma basa iya banbancesu itada Munubiya, sometimes Munaya takanyi laifi akama Munubiya a daka, itakuma Munubiya bazata ta6a fad’in ba itaceba.
Ganin hakan yasaka Aisha yima Munubiya shaida saboda aringa banbantasu, amma Munaya Na k’yalla ido tagani sai itama tayima kanta irin ta Munubiya komai da komai, idan sau dubu akama Munubiya shaida ajiki Munaya ma zataje taima kanta, hakama Munubiya takanyi idan anyima munaya, hakan yasa Aisha ta hak’ura kawai harma suka Shiga makaranta, nanma rikicin Munaya bai k’areba, dan saima abinda yay gaba, tajawo fad’a akama Munubiya adaka, hakan kuma bazaisa gobe ta fasaba.
Shekarar su goma Aisha takuma haihuwar ‘yan biyu duk maza, Aryaan da Aiyyaan, tundaga lokacin kuma bata sakeba.
Sai dai Munaya da Munubiya suna matuk’ar k’aunar junansu over abinma har saiya Baka mamaki, sannan suna k’aunar mahaifiyarsu da k’annensu, Munaya ce kan shiga idan ana cin zarafin mamansu, amma ita Munubiya saidai taita kuka.

Yanzu haka zancen danake muku shekarunmu 19 nida Munubiya, muna matakin farko a jami’a, munzama ‘yan mata, k’yawunmu da tsananin kamarmu da innarmu yasake fitowa, mun fita daban a gidanmu, dan mukad’aine kamarmu daban, Ayyan da Aryan ma duk Abbanmu suka kwaso, wannan yasaka suke kama da ‘yan gidanmu.
Tabbas bamajin dad’in zaman gidanmu, saboda k’unci da hantara damuke fuskanta muda mahaifiyarmu awajen Innaro da matan gidan, harma dawasu yaran gidan ‘yan uwanmu, amma wasu muna shiri dasu sosai, musamman ma mazan yayyenmu manya, dansu babu ruwansu da gutsiri tsomar cikin gidan.
Gidanmu gidane tamkar gidan hayar daya had’a k’abilu daban-daban saboda yawan rikici, kullum cikin fad’a muke, ba iyayenba ba yaranba, kai kace muna ganin hanjin junane.
Gwargwadon iko akwai hali a gidanmu, dan iyayenmu sun rik’e gidanmu sosai da buk’atinmu, dukda yawa da ALLAH yabamu, bamu rasa ci da sha ba da situra, hakama matsalolin karatunmu, dan kai tsaye zance gidanmu gidan ‘yan bokone, kullum cikin gasa da juna ake, burin kowa ace shine gaba, batun ilimin addinima kam Alhmdllh, dan tsaye iyayenmu suke akanmu, har gobe yaa hameed bai daina zama gaban malamai ba balle mu ‘yan baya-baya. ak’alla yaran gidanmu munkai mu 43 kuma.
ALLAH yayma Malam jafaru kakanmu rasuwa shekara biyu kenan, innaro Ce dai tana nan daram, al’amuranta sai abinda yay gaba, dan har gobe bata k’aunar innarmu, kuma bata daina cin zarafinta ba agaban kowa da mata gorin rashin dangi.
Hakan yasa kullum cikin buri da k’udirin binciko dangin Innarmu nake, ko itama zata samu ‘yancin kanta kamar kowa??.

Wannan shine labarin gidanmu, sai ahankali zaku cigaba da fuskantar ainahin halayen jama’ar gidanmu da aiyukansu, harma da sunayensu??………….???

 

To masu karatu, sai nace yanzufa za’a fara, saiku kasance dani danjin labarin *_RAINA KAMA…. kaga gayya_* dan akwai babban al’amari a gaba, bawai gidan su Munaya kawai labarin ya shafaba, akwai wani lauje cikin Nad’i daga d’ayan 6angaren labarin Na Raina kama…..?? suga gayya ba??????.

 

 

One luv??

 

 

 

*_ALLAH ka gafartama Iyayenmu??????_*
[4/16, 9:53 AM] +234 811 277 0720: *_Typing??_*

 

*_HASKE WRITERS ASSO…??_*

 

 

*_?RAINA KAMA……!!?_*
_{Kaga gayya}_

 

*_Bilyn Abdull ce????_*

 

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply