Hausa Novels Raina Kama Book 1 Hausa Novel

Raina Kama Book 1 Page 29


Raina Kama Book 1 Page 29
Viral

??2?9?

………..“Munaya taimakona nakeson kiyi akan mijinki”.
‘Dagowa nayi na kalleta cikin tsantsar mamaki, saina sinne kaina alamar jin kunyar ta, nace “Umarni zaki bami Momma, domin ke mahaifiyatace”.
Murmushin jin dad’i tayi kamfin takamo hannuna cikin nata, “Alhmdllh Munaya, nagode da wannan karamci naki, yanzu nakuma aminta Muh’d yasamu irin macen danake musu addu’a shida d’an uwansa, ALLAH yayi miki albarka. nasan dukkanin yanda aurenku ya gudana”.
Gabana yafad’i, a raina nace badai Na yarjejeniyar ba?…….maganarta ta katsemin tunanin.
“Mahaifina Sarki Abdul’fatah shine yasakashi aurenki saboda abinda yafaru daku, Wanda nasan k’addarar Muh’d ce kawai tashigo dake cikin lamarin. Kafin nafara neman alfarmar zan fara baki tarihin masarautar su Muh’d, da dalilin zamanmu wannan k’asar daba tamuba tsawon shekara 24 kenan”.
Kaina na jin jina mata, nace “to Momma”.
Zamanta ta gyara sosai yanda zataji dad’in fad’ar abinda ke a bakinta.

*_MASARAUTAR GAGARA BADAU A WASU SHEKARU DASUKA SHU’DE??_*

Masarautar gagara badau masarautace mai d’unbin tarihi, da mulkinta ya gudana hannun sarakuna masu yawa, a hasashen masana masarautar sarakuna a k’ala 51 ne suka mulketa harda Sarki na yanzu, wato *Sarki jalaludden Abubakar*.
Sunan masarautar awani shud’ad’d’en lokaci ba *gagara badau* ake kirantaba.
Tasamo sunan gagara badaune dalilin wani Sarki daya mulki masarautar a zamani mai shud’ewa.
Abaya mulkin masarautar basai ka mutuba yake barin hannunka, a’a, da zarar anyi yak’i kayi sakakin da aka ci masarautar tom dolenefa kayi murabus a nad’a wani kuma. kuma bawai cikin ‘ya’yankaba, saidai asamo wani hazik’i a masarautar a nad’ashi sarautar.
Tom alokacin Sarki Hameesu Alasan sai aka kawowa masarautar wani gagarumin hari dayaso girgizata. Sarki Hameesu yanada wani d’a da ake kira da suna *Barde* amma asalin sunansa shine Salisu. lokacin da aka kawo musu harinnan ba’a cikin shiri sukeba, amma haka Salisu barde yay saurin had’a mayak’a suka tunkari wannan runduna, bak’aramin gumurzu akashaba, sojojin masarautar Sarki Hameesu duk sun salwanta, amma hakan bai tsorata Salisu ba, yacigaba da bata kashi shida wasu ‘yan tsirarun mayak’a, ALLAH mai iko saigasu sunci wannan runduna data kawo musu hari.
Wannan nasara da Salisu yasamuce tasaka babansa Sarki hameesu sauka a kujerarsa aka nad’a salisu. tundaga ranar takoma *_MASARAUTAR GAGARA BADAU_* abin nufi annan salisu barde yazama gagara badau.
Bayan Sarki Salisu gagara badau sarakuna kusan goma sunyi mulki kafin Sarki *_ABUBAKAR_* kakansu Muh’d kenan, mahaifin su takawa.
Shima ya gaji sarautarne a hannun mahaifinsa Yusufa.
Rana d’aya aka nad’a Abubakar Sarki shida amininsa d’an sarkin kan karofi yarima Abdul’fatah, mahaifin Abubakar Yusufu abokine ga Sarki idres na ll, dan haka rana d’aya suka yanke shawarar yin murabus suka nad’a ‘ya’yansu.
Sannan aka d’aura musu aure kuma a ranar da matan da su Sarki Yusufu & Idres suka za6a musu.

Gimbiya Marawuyya (mama Fulani) d’iyace ga waziri Sama’ila k’anin Sarki idris, a masarautar Idrees kenan, Sarki idres bashida d’iya mace, dan haka ya d’auki mama Fulani d’iyar k’aninsa yabama Abubakar d’an Sarki Yusufu a masarautar gagara badau, shikuma Sarki Yusufu ya d’auki Khadeeja (inno) yabama Abdul’fatah d’an Sarki idres.
To Ashe ita gimbiya Marayuyya (mama fulani) tana masifar son yarima Abdul’fatah ne, kuma yasani, amma ya nuna mata shi dama gimbiya Khadija (inno) k’anwar abokinsa Abubakar yakeso.
Tun daga lokacin gimbiya Marayuyya (mama Fulani) ta tsani Khadija (inno), ko wani Abu yahad’a masarautunsu bata mata magana, sai zagi da habaici.
Sukuma iyaye basusan gimbiya Marayuyya nason yarima Abdul’fatah ba, sukayi wannan had’in aure. (Iyayen mama Fulani ma sunso ta Auri yarima Abdul’fatah d’in domin sarauta ta dawo tasu)
Gidan sarauta idan an shata layi babu mai k’etarashi, dan haka gimbiya Marayuyya da iyayen ta dolen suka hak’ura da auren yarima Abubakar (tunda acanma suna saka ran gadar sarautar) haka aka kawota gagara badau. ita kuma Khadija (inno) aka kaita masarautar su Mama fulani.
Kusan atare duk suka haihu, saidai Khadija (inno) namiji ta Haifa, yayinda Marayuyya (mama Fulani) ta Haifa mace.
Duk da ba masarauta d’aya sukeba hakan yasaka mama Fulani bak’in ciki, dan aganinta inno taje zata gaje musu masarauta, ita kuma bata samu damar gaje tasuba. A haihuwa ta biyu kuma sai inno ta Haifa mace, mama Fulani kuma ta Haifa namiji. Alokacin kuma duk mazajen nasu suka k’ara aure, daga Sarki Abubakar har Sarki Abdul’fatah. kamar atsare haka sukaita kuma aure har suka cika mata hurhud’u.

A masarautar gagara badau Mama Fulani na zuba mulkinta a masarautar, yanda kasan itace sarkin, dayake shi Sarki Abubakar yanada hak’uri da sauk’in kai.
Humm matan Sarki Abubakar duk basu haihuba, sai mama Fulani keta zubo ‘ya’ya. Saikuma amaryar Sarki ta uku ta Haifa d’anta namiji, kusan tare da mama Fulani a haihuwa ta hud’u, duk da mama Fulani itace da manyan ‘ya’ya mace 1 maza 2 hakan bai hanata shiga tashin hankaliba, saita shiga tsangwamar gimbiya bagobura da aibanta d’anta *Saifudden*, wani lokacin har shegantashi tayi, saida Sarki Abdul’fatah yazo har masarautar ya taka mata birki sannan.
Mama Fulani tasaka sauran matan Sarki Abubakar sun juyama gimbiya bagobura baya gaba d’aya, batada sakewa ko kad’an acikin gidan. Sarki Abubakar yasan komai dake faruwa a gidansa, amma saiyayi tamkar bai ganiba, bakuma Dan mama Fulani tafi k’arfinsa baneba, yadai zuba mata idanu kawai yaga iya gudun ruwanta.
Ahaka yaran suka taso, gimbiya bagobura ma bata sake haihuwa ba, sai mama Fulani ce takuma biyu, mace 1 da autanta namiji Hayatudden.
Saifudden da jalaludden sun tashine tamkar tagwaye, dukda Saifudden ya girmi jalaludden d’in dakusan 1½ kuwa. danma mama Fulani na hana jalaludden sakewa da Saifudden ne. Kokuma Kamaludden da Shamsudeen suyita dukan Saifudden idan sun gansa tareda jalaludden d’in.
Ahaka Saifudden yatashi cikinsu a tsangwame har suka girma suka zama manya.
Saikuma wani Abu tashin hankali ya samu, a time d’in da mama Fulani ke ganin sarauta zata dawo wajen ‘ya’yanta sai ubangiji ya nuna mata ikonsa.
Dan kuwa Shamsudeen da kamaludden sai sukayi had’arin jirgi zasuje umara duk suka rasu.
A time d’in a marine kawai ba a saka mama Fulani ba, amma hauka tuburan tafara a masarautar gagara badau. Saida aka had’a da addu’a sannan talafa, saita kullaci gimbiya bagobura, wai ita tama ‘ya’yanta asiri suka mutu domin d’anta Saifudden yagaji sarauta.
Gimbiya bagobura zata tada hankalinta Sarki Abubakar yace tama kwantar da hankalinta.
Bayan mutuwar su Kamaludden babu dad’ewa aka had’a auren gimbiya Zakiyya d’iyar Sarki Abdul’fatah da Saifudden aure, shikuma lokacin Jalaludden da Rafi’atu d’iyar wani Sarki.
Aikam sai mama Fulani ta hau bala’i wai munafunci aka shirya. Babu Wanda yabi takanta akasha biki.

Gimbiya Zakiyya da gimbiya Rafi’atu kusan atare suka haihu a time d’in, gimbiya Zakkiya ta Haifa d’iyarta mace, saidai tana haihuwarta ko ganinta batayiba takoma ga ALLAH??.
Wannan shine silar aurena dana Saifudden.
Dan bayan rasuwar yayata gimbiya Zakiyya da kwana 7 aka d’aura min aure da yarima Saifudden, domin nacigaba da rainon abinda tabari.
Banason Yarima Saifudden, domin ina masa kallon *Mijin yayata* amma banida yanda zanyi, dole na aminta da auren domin yima iyayena biyyaya.
Nasha wahalar zama dashi, saboda shi hankalinsa yana kan yayata ne marigayiya, silar soyayyar danake nunama Habeefa (aunty Mimi) d’iyar da gimbiya Zakiyya tabarine ya siyamin soyayyar yarima Saifudden, a hankali har shak’uwa tafara shiga tsakanina dashi. Soyayar dayakema ‘Yar uwata saita dawo kaina.
Sai daifa inashan wahalar mama Fulani, duk da kuwa itad’in (Gwaggona ce) tana amsa sunan k’anwar mahaifina, amma k’iyayyar datakema mahaifiyarmu gimbiya Khadija (inno) saita shafemu, duk da abaya tana ik’irarin son mahaifinmu Sarki Abdul’fatah kuwa. Kamar yanda yayata gimbiya Zakiyya tasha wahalarta a gidan nima hakane, saima tawa taso fin ta ‘Yar uwata, bansan dalilintaba, wai Ashe dan ina tsananin kama da inno ne??.

“Ina fata dai kina fahimtata Munaya” ‘Momma tayi maganar tana kallona dana rabga tagumi inajin cakwakiyar masarauta.
Kaina na jinjina mata cikin damuwa.
Saitayi murmushi tacigaba da fad’in.

Mama Fulani taso d’iayarta ta farko gimbiya Mansura ta auri yayanmu yarima Abubakar, Wanda babanmu Sarki Abdul’fatah yayma amininsa takwara.
To saikuma hakan bata faruba, dan ita tata dabarar itada iyayenta, idan Yayana Yarima Abubakar ya auri gimbiya Mansura sarauta takoma hannunsu kenan, tunda yarima Abubakar shine magajin masarautar mu, kinga ai d’ansa ne zai gajesa kenan, idan tahad’a auren kuwa yazama jikanatane da masarautar nan gaba.
To saikuma tsarin nata bai yuwuba, saima nida yayata mukazo masarautar gagara badau tushen mahaifiyarmu mukayi kane-kane, gashi kowa yana Saran Saifudden shine zai gaji masarautar gagara badau alokacin, tunda manyan ‘ya’yan Sarki Abubakar sun rasu, Saifudden kuma shine babba namiji a lokacin.
Shiyyasa takuma d’aukar karantsana ta d’aura mana muda gimbiya bagobura.
Bayan haihuwar Haneefa babu dad’ewa gimbiya bagobura ta rasu, rasuwar data gigita yarima Saifudden kenan da Sarki Abubakar har ma da jama’ar masarautar gagara badau, amma banda mama Fulani da sauran matan Sarki, dansu hakanma dad’i yamusu.
Sanadin rasuwar gimbiya bagobura Sarki Abubakar ya kwanta ciwo, sai yayi murabus yace a d’aura d’ansa Saifudden a madadinsa.
Wannan Abu yama kowa dad’i a masarautar, amma banda mama Fulani dakejin tamkar tamutu dan bak’in ciki.
Saidai batada yanda ta iya, tanaji tana gani yarima Saifudden yazama Sarkin masarautar gagara badau.
Alokacinne kuma akace dole ya k’ara aure, dan Sarki baya zama da mace d’aya, gashi kuma ni ban haihuba har lokacin.
A rana d’aya aka d’aurama Sarki Saifudden aure da mata biyu. Nanfa mama Fulani tashiga jansu ajiki wai dan a kuntatamin, tana kuma koya musu yanda zasu kuntatama shi Kansa Saifudden d’in.
Sarki Saifudden nada shekara 9 a karagar mulki ALLAH yayma Sarki Abubakar rasuwa, mutuwarnan ta girgiza mahaifinmu Sarki Abdul’fatah sosai, dan saida aka had’a masa a addu’a.
Tun daga wannan lokacin masarautar gagara badau takoma hannun mama Fulani, dan sai yanda tace tanaso Sarki Saifudden zaiyi, dayake shi mutumne mai sanyin hali, baya ta6a sa6a mata.
Duk da haka wannan bai ishetaba, hattada yanda za’a gudanar da mulki saita tsara.
Har lokacin amaren Sarki Saifudden babu wacce ta haihu.
Cikin ikon ALLAH sai gani da ciki, babu kitumurmurar daba aima cikinnan nawaba d’anya zube amma ALLAH ya k’addara mijinki *Muhammad Sameer* saiyazo duniya.
Lokacin Dana haihu shekarar haneef 10 cif a duniya.
Muhammad shine jika namiji na farko da aka fara haihuwa a masarautar gagara badau, dan kuwa matar Jalaludden ma mata taketa haihuwa.
Daga nan nima ban sakeba saida Muhammad yacika shekara hud’u, yanda Saifudden yasha tsangwamar mama Fulani haka Muhammad ma yashata tun yana yaro.
Shima Sameer hak’urin mahaifinsa Saifudden ya gado sosai, dan ko abu aka masa saidai yayi kukansa ya goge hawaye, koni bazai sanarmawa ba, saidai in wata baiwa tagani ko Haneefa (aunty Mimi) su sanarnin.
Da *Ciwon zuciya* na haifi Sameer, dan haka kullum cikin kaffa-kaffa muke dashi saboda gudun samun matsala ga lafiyarsa, da yawa jama’ar gidan sukan masa abune wai dan zuciyarsa ta buga?? ya mutu. sun manta rayuwa da mutuwa duk Na ALLAH ne.

Da sauri na kallo momma.
Ta d’aga min kai tana murmushin takaici, “hakane d’iyata, kullum burinsu kenan akan Muhammad tun yana yaro..

Ranar wata litinin da asuba Sarki Saifudden yafita sallar asubahi sai kawo manashi akayi cikin gida, wai yafad’i ana tsaka da sallah.
A lokacin kafafunsa ne kawai basa aiki, amma sauran jikinsa yana motsawa.
Nice naita wahalar jinyarsa, ga cikina yafara tsufa, sai jakadiya ke taimakona, amma sauran matan Sarki ko’a jikinsu.
A hankali ciwo yacigaba da girmama a jikin takawa, tun ana kafa har yadawo duka jiki, idonsane kurum ke aiki a lokacin.
A asibitin garinan muke jiyyarsa a time d’in, a asirce batareda jama’ar gari sun saniba.
Acikin wannan tashin hankalin na haihu Namiji, shine Abubakar (Sauban).
Nidai lokacin kawai ina rainon Sauban ne, amma rabi duk Haneefa ce (aunty Mimi) yayinda kulawar Sameer takoma hannun k’anwata Zaituna (mom), autarmu kenan, dan dole aka dawo da ita wajena tana taimakamin.
Na haifi Sauban babu dad’ewa aka maida sarautar Saifudden akan Jalaludden d’an gidan mama Fulani, saikuma lokacin jama’ar gari suka San Sarki Saifudden bashida lafiya ma.
Ko kad’an ban damuba, danni ta lafiyar mijina nakeyi ma.
A lokacin anta kananun magana akan zargin mama Fulani dawasu kuma manyan attajirai, dan akwai wani zaman sirri da sarki Saifudden yayi dawasu attajiran k’asar ana jibi abin zai sameshi, kuma anga yafito ransa a 6ace daga tattaunawar, alamar sun buk’aci wani Abu ya hanasu kenan. suma angansu ran nasu A 6acen. Nikam bamma maida hankali akan wannanba, mahaifina Sarki Abdul’fatah shine kawai tsaye akan ciwon Saifudden, saini kuma da jakadiya.
Masarautar kuwa ai duniya sabuwa. Matan Sarki Saifudden ma duk sun kama gabansu, sunce bazasu iyaba.
Shekararmu d’aya a asibiti babu wani canji, saima jikinsa dake neman fara ru6ewa saboda komai sai an masa. Baya iya d’aga koda d’an yatsane. (Tun farko likitocinmu na nan sun Sanar damu an masa allurar gubane, kuma guba mai had’ari, dan babu makarinta, itakuma tana sakar da jijiyoyin jikine su daina aiki gaba d’aya, wannan yasaka jikin Sarki Saifudden ya sandare??.

Wani amintaccen likitanmune yabada shawarar mu maidashi India dansu sunada kwararrun likitoci, kuma zaifi samun kulawa da tsaro a can.

Wannan shine silar dawowarmu wannan k’asa, da cuku-cukun mahaifina Sarki Abdul’fatah, dan komai namu mukam ya k’are, duk abinda Sarki Saifudden kedashi yagama k’arewa a neman Magani.
Tunda muka dawo India kuwa Sarki Saifudden yafara samun kulawa ta musamman, saidaifa maganar ta kud’ine. Wasu sarakuna da yawa sun bamu gudunmawa, wasuma suna akan bamu.
Sanin Zara bata barin dami, gashi kullum cikin buk’atar kud’i muke sai mahaifina yakafa wasu sana’oi da sauran kud’enmu, tanan muke samun kud’in shiga. Karatun Muh’d da Haneefa kuma Mahaifiana ke d’aukar nauyi..
Tundaga primary har jami’a anan Sameer yayi karatunsa.
Kiyayyar Saifudden kuma ga mama Fulani saita dawo jlkan Muh’d gaba d’aya, kokad’an bata k’aunar ganinsa, kullum tsakaninta dashi sai aibantawa da jifansa da kalamai masu had’ari ga yaro.
Tunda Muh’d yafara sanin Kansa, yaga halin da mahaifinsa yake saiya fara canjawa daga mai hakuri zuwa mai zafi.
Ga ciwonsa kuma, duk yabi yayta kuntata zuciyarsa akan ciwon mahaifinsa da burin d’aukar fansa.
Muh’d mai fara’a da barkwanci yakoma mutum marason magana da azabar rashin d’aukar raini, duk da hakurinsa nanan bai dainaba, dan zakata masa Abu ya shareka kamar bai ganiba, sai randa yazo k’arshene zaka gane kurenka a wajensa.
Mahaifina Sarki Abdul’fatah shine yamatsa tun Muh’d na secondary school dole idan akayi Hutu yazo najeria, dan acewarsa tahakane kawai zai fahimci sarautar gidansu.
Muh’d ya karanci Engineering ne, dama tun yana yaro kingansa kullum cikin son had’a Abu yake, shine tsinka wayar fitila tsinka ta redio ya had’a wani abun, tunma ina masa fad’a harna bari kawai. Ashe abincinsa awajen yake. Yanzu haka sunada Company na had’a wayoyi?? da Computers????, da sauran kayayyaki dai. Sannan yana wasu business domin dai muke samun kud’ad’en kulawa da mahaifisa da sauran matsalolinmu, dan babu mai kulawa damu a masarautar gagara badau sai Sarki Jalaludden.
Wani zuwa da Muh’d yayi Nigeria shine aka bashi sarautar *Galadima*, galadima Sarautace mai k’arfin gaske, dan sai d’a mafi soyuwa ga Sarki ko k’ani ake bamawa. Kuma akance batada banbanci da sarautar waziri, dan duk abinda waziri zaiyi Galadima ma zai iyayinsa. Akwai ma wasu abubuwan da daga Sarki sai Galadima kan yisu a fada.
Da da farko nace ya mayar musu amma sai mahaifina yace a’a, ai hakan da sukayi dai-daine.
Sharrin kuwa dakika sun masa, har tsautsayi ya jefaki a ciki, sunyine dan hankalinsa ya tashi, har takai zuciyarsa ta buga ya mutu sun huta.
Dan ayanzu ne suke ganin sunfa *kashe macijine basu sare kansaba* Galadima yazamar musu *RAINA KAMA…..*, basuyi tunanin zaikai tsawon rai hakaba, saboda Ciwo mai had’ari dake a tare dashi.

Shikuma Muh’d yafi karkata hankalinsa ga jama’ar wajene sukama mahaifisa haka, koda akwai jama’ar masarautar gagara badau to kalilanne, kuma mama Fulani kawai yake zargi.
Nikuma ba ita kad’ai nake zargiba, amma yakasa fahimtata gaba d’aya har kawo yanzun kuwa. Dagashi har Haneefa sunfi zargin jama’ar waje, don mutananen masarautar suna 6oye musu ainahin fuskarsu ta zalunci, mama Fulani ce kawai tata take a bayyane.
Wannan yasaka tun sharrin da akai muku nasaka amin bincike a kanki, Alhmdllh ban samu wata matsalaba a tarihinki,, daga nan na dukufa addu’a da neman za6in ALLAH.
bamma kai ga furtama kowa matsalata ba sai mahaifina Sarki Abdul’fatah (papi) yace Muh’d saiya aureki.
Nasan ba sonsa kikeba, amma ina rok’on ubangiji da yasa wataran kuso junanku, kinada tarbiyya da wayon da zaki iya canjamin Muh’d, dan banason hallayarsa ta yanzu, nafi son nake ganin walwala atare dashi a ko yaushe, ki taimakeni ki shiga rayuwarsa sosai, dan ke macece, sai kin fishi zama cikin jama’ar masarautarsu, zakuma ki fishi fahimtar halayyarsu, sannan kidinga bashi shawara akan abinda yadace dashi. Inaji a jikina zaki iya canjamin Muh’d, saboda kinada hankali. gudun kar wani yasakama zuciyarki tunani daban yasaka nace yakawoki da wuri, domin kisan yanda zaki rayu a masarautar, kafin kutafi insha ALLAH komai Na zamantakewar masarauta za’a koyar dake kinji”.

Kaina Na gyad’a mata, sannan a sanyaye nace “Momma namiki alk’awarin zai taimakesa akan matsalarnan, kuma zan bama rayuwarsa gudun mawa insha ALLAH, Sai dai Abu d’aya ne ban ganeba”.
“miye baki ganeba d’iyata?”.
“Abokinsa Muftahu, shima a masarautar yake?”.
Murmushi Momma tayi, tace “daga Muftahu har Harun duk ‘yan masarautar ne, Muftahu kakanni suka had’a dasu Muhammad, da kakan Muftahu da Sarki Abubakar kakansu Muh’d uwarsu d’aya ubansu d’aya, shikuma Harun d’an waziri ne na yanzu, kuma shima wazirin haifaffen gidanne, saidai inason sanin ko wani Abu kika gani tareda wani acikinsu?”.
Kaina Na girgiza alamar A’a.

Momma ta sauke ajiyar zuciya, “Munaya saikin dage kinji, domin Na had’aki da aiki mai wahalar gaske, mai kuma sark’akiya, musanman akan halayyar Muh’d, dan bai yarda da kowaba dakike ganinsa nan, koyaya Abu ya had’aku sai yayi zargin turoka akayi garesa, kuma zaka Shiga jerin wad’an da yake tuhuma. amma kekad’aice mafi kusanci da Muh’d yanzu, zakifi kowa sanin matsalarsa da wuri, saikuma kin fimu fuskantar tunaninsa, danni kinga jinyar mahaifinsa tasa banwani zauna dasu irin sosai d’innanba, yanzu haka kafin nasan matsalarsa ‘Yar uwata Zaitun (mom) tasani ko Haneefa (aunty Mimi), garama Sauban.
Nace “shikenan Momma ki tayamu da addu’a kawai”.
“insha ALLAH muna kan yimuku kullum, ALLAH yayimuku albarka, ya albarkaci aurenku da dukkan rayuwarku da abinda zaku haifa”.
Ban iya amsawa ba, kaina Na k’asa nikam, ko azuciya ma ban amsaba, dan nayi alk’awarin zai taimakesa kamar yanda ta buk’ata. Amma ina gamawa zan nemi sakina, koda nanda shekaru 2 ne kuwa, amma gaskiya Na tausayama Galadima, dan nakula yana cikin tsakkiyar mak’iyane masu fuska biyu. abinda kuma nalura da Momma bata ganeba shine Galadima bawai bai yarda ‘yan gidansu nada saka hannu akan ciwon babansa bane, baya dai nunawane kawai, sai dai bansan dalilinsaba.
CCTV camera d’in dana gani a d’akinsace tadawomin a rai, maybe ya sakatane domin sanin masu shiga da fita koda bayanan.
Haka Na kusan yini cikin damuwa da tausayinsa, dan duk saiya bani tausayi wlhy. shiyyasa zaka gansa kullum shiru-shiru, gaskiya 6angaren hak’uri Na yarda yanada hak’uri kam.

***********

Yau saida yamma mukaje muka duba Abie, mun iske Galadima baya asibitin, dama tun da rana yazo gida yay wanka yakuma fita.
Har dare muna a asibitin, saida Galadima yazo muka taho tare, ina gaba ni da shi da khaleel dake barci a cinyata, yayinda sauban da aunty Mimi da Samha ke baya.
Maganar da samha ta fad’amin d’azun a asibiti ta dawomin a rai, Ashe mahaifinsu ya rasu suma shekara 2 kenan, itace d’iyar Aunty Mimi ta farko, sai Hakim da suka rasu tareda babansu, saikuma khaleel auta. Suma a Nigeria da suke zaune, bayan rasuwar mahaifin nasune suka dawo nan india, duk da dangin mahaifinsu sunso kar6arsu papi yahana, babansu tsohon Governor ne shima, mutuwar tasa kuma akwai lauje cikin nad’i shima, dan ya tsananta akan binciken ciwon surukinsa Abie sosai, shiyyasama ake zargin an kasheshine saboda wani Abu daya gani.
Har muka Isa gida bansan hirar dasukeba a baya, dan shima Galadima baya cewa uffan.
Shine ya kar6i khaleel a hannuna, ya sa6ashi a kafad’a muka shiga ciki, har d’akinsa ya kaisa. ni lokacinma harna haye saman……….???

Barkanku da juma’a.

Zanyi last page gobe idan ALLAH ya kaimu da rai da lafiya??????????.

Network yanata min iskanci tun jiya shiyyasa kuka jini shiru?

*_YA ALLAH ka gafartama iyayenmu_*??????
*_Typing??_*

*_HASKE WRITERS ASSO…??_*
_(Home of expert and perfect writer’s)_

*_?RAINA KAMA……!!?_*
_{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdull ce????_*

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply