Hausa Novels Raina Kama Book 1 Hausa Novel

Raina Kama Book 1 Page 4


Raina Kama Book 1 Page 4
Viral

????4?

…….Daga ni har Munubiya babu wata kwalliya damukayi, hasalima ni ko mai k’in shafawa nayi, danayo wankanma sainayi kwanciyata na hau barci. sai wajen 1 munubiya ta tadani wai sun iso, dama lokacin duk fashin salla muke nida munu…. (zakusha mamaki idan nace muku dai-dai da prioud yakanzo mana rana d’aya nida hassana ta, kuma musami tsarki tare), tashinai ina yatsine fuska, dan naji haushin tadanin datayi, toilet nashiga domin kimtsa jikina, sama-sama nadinga jiyo maganar Ikram tana fad’in “Aunty wai innaro tace kuzo”.
Cikeda mamaki munubiya ta amsa da to. nima abin yabani mamaki, dan haka nafito da Sauri, “wai Munubiya minake jiyowa ina toilet? ”.
Maganarta d’auke da mamaki tace, “wai innaro ke kiranmu”.
“ni da ke? kokuma mu duka?”.
“wlhy ban saniba munaya, sai dai munje d’in magani”.
Innarmu tashigo d’akin tana cewa “waishin Baku naji innaro ta aiko kira bane?”.
Muka amsa da “eh innarmu, mune”.
“to mi kuke jira, kuwuce kutafi mana”.
Babu Wanda yay magana acikinmu muka fita muna mamakin wannan kira Na innaro.
Tun a k’ofar falon baba k’arami mukaga wasu k’yawawan takalma, ga wani k’amshi yacika wajen, wicewa mukayi batareda mun shigaba, dukda mun hango Zarah da Siyama da Fiddausi natahowa cikin matsanancin gayu, saika rantse fita zasuyi wani gagarumin biki.
A k’ofar gidama munci karo da motoci uku duk bak’ak’e wulik, sai dai ta tsakiyar tafi k’yau da d’aukar hankali, garadan samarine majiya k’arfi kusan su 7 tsaitsaye ajikin motocin, duk suna sanye da bak’ak’en suit, daka gansu kasan babu sauk’i, hakan yasa muka fahimci bodyguards d’in bak’inne.
Gida biyu ne tsakanin gidan innaro da gidanmu, dan haka muka Isa da wuri. a tsakar gida muka isketa tana shanyar lawashin albasa. muka gaidata.
Yanda ta saba haka ta amsa mana, amma tace mushiga ciki tana zuwa.
Kusan mintuna 40 muna falon innaro zaune, amma bata shigoba, hakan yasakani tunanin tabas akwai wani lauje cikin nad’i a kiran namu, tashi nayi nalek’a tsakar gidan ta window, amma bata nan. “Munubiya kinsan Innaro bata gidanan kuwa?”.
Cikeda mamaki tad’ago tana kallona, “kamarya bata nan?”.
“Munu… Wlhy ko rantsuwa nayi babu kaffara aciki, akwai dalilin kawomu nan”.
A sanyaye Munubiya tace, “karki damu Sweetheart, ko mai suke nufi ALLAH ya fisu, dama naga mamansu ya hameed tafito d’azu bayan mungama girki, ai d’an hakkin daka raina shike tsolema ido, *_RAINA KAMA KAGA GAYYAFA_* inji masu iya magana.
Hakane dear.
Daga nan muka zauna shiru kowa da abinda take tunani, har barci ya sace Munubiya, nukuma nahau chart kawai.

A gidanmu kuwa su Siyama ne suka fara Isa falon, tundaga k’ofar falon daddad’an k’amshin turaren bak’in yafara rikitasu, sun shiga da sallama, yayinda sukuma bak’in suka amsa.
Gaskiya masha ALLAH dan kuwa matasan samarine k’yawawa masu aji da gayu, suna kama da juna, hakan zai tabbatar maka da cewa jininsu d’aya. sunci ado cikin wasu rantsatstsun shaddoji gizna, sai maik’o sukeyi, d’aya yafi d’aya sakin fuska.
Su Siyama sun gaidasu cikin shauk’i da zumud’in fatan kowaccensu ta kasance abar za6i.
Sun amsa musu cikeda jan aji da nazartar su, ahaka Fauziyya da Safara’u da Haleematu suka shigo suma, suma dai gaidasun sukayi. Fauziyya da Zarah ne kawai sukayi hankalin tashi su zuba musu ruwa da lemo, sannan suka musu bismillar abinci.
Mai d’an yawan fara’ar ne yamusu godiya, sannan yace, “to ya sunan k’annen namune?”.
Cikeda yanga kowacce tafara gabatar da kanta agaresu, yayinda sukuma suka maida hankali sosai wajen nazartarsu, bayan sun gama suma suka gabatar musu da kansun.
“Ni sunan Sulaiman, brother d’ina kuma Sa’eed, munji dad’i kwarai da gaske Na tarbar damuka samu daga gareku”.
Murmushi duk sukayi suna nuna farin cikinsu suma, sund’an ta6a hira.
Babu Wanda yadamu da rashin ganinmu acikinsu sai Fauziyya, iyayenmu kuma basusan babumu ba, dansu suna falon Abbanmu suna hira.
Kusan awa d’aya sannan duk suka fito suka barsu dan sud’anci abinci.
Suna fita Sa’eed ya kalli Sulaiman a yatsine, “my man nida yaran nan nakula sunada rawar kai, garama mai farin kayannan naga kamar tafisu nutsuwa (Fauziyya)”.
“wlhy gskyarka bro… Amma Kasan dolenefa mucika umarnin dad, tunda yayi rantsuwa akan dolene muza6a acikinsu, kai wlhy mun jama kanmu, ni dama tun maganar farko da dad yamana Na maida hankali naza6o da duk hakan bata faruba gareni”.
Cikin ta6e baki Sa’eed yace, “wannan kuma kaika Sani malam. amma basuma 8 akace manaba?”.
“eh hakane, amma kamanta ance biyu acikinsu sunada samari”.
A nanma bakin Sa’eed Yakuma ta6ewa. sun d’anci abinda aka ajiye musu, sannan su Abba suka shigo suka gaisa, cikeda girmamawa suka gaida su Abba, hakan yayima Dady da baba k’arami dad’i, sun kuma tabbatarwa yaran sunada tarbiyya, dama basa kokwanto akan zance yayan Nasu.
An musu rakkiya duka Sassan gidanmu, sun Haida iyayenmu mata. ganinsu Yakuma rud’ar da iyayenmu, kowacce addau’arta ALLAH yasa d’iyarta aka za6a, yo wad’annan zuk’a-zuk’an samari haka, ga kud’i ga ilimi, kowacce saida suka ajiye mata kud’i suke fitowa, har innarmu ma.
Tun aiko kiranmu Innarmu taji ajikinta da biyu aka turamu can, amma baiwar ALLAH hakan bai dametaba, tasan dai wata bata aurar mijin wani, dan haka ko’a fuska bata nunama wani bama cikin wad’anda suka je wajen bak’inba.

Saida Innaro takusa awa d’aya sannan tashigo gidan, yinai tamkar ban gantaba, Munubiya kam tanata barcinta, itama sai bata kulaniba tashige bedroom d’inta.
Shigarta baifi da mintuna 3 ba mukajiyo sallama a k’ofar d’akin, nice Na amsa, Basheer yafara shigowa, sai kuma Sulaiman da Sa’eed, irin k’amshin damukaji a k’ofar d’akin baba karami yasani d’agowa dan jinsa anan, hakan ya tabbatar min da sune sukazo gaida Innaro.
Tunda suka shigo idonsu ya sauka a kanmu, sun kasa d’auke kai daga kallonmu.
Cikeda jan aji nace, “ina yininku”.
Duk suka amsa da “lafiya big girl”.
Basheer yace, “kai Aunty dama kuna nan Ku?”.
Kallonsa nayi nace, “eh, ana nemanmu ne?”.
“a’a, amma dai ba’asan badaku akaje wajen bak’iba”.
Hararsa nayi, saboda sanin halin shegen surutunsa, “malam kaje ka kira musu Innaro ka zauna kana zubama mutane shegen surutu uwa aku”.
Baki ya zum6ura sannan yanufi bedroom d’in Innaro.

Wanda tunda suka shigo yakasa d’auke kai daga kallona, saima zama dayayi kujeraf dake kallona yace, “ok dan bakwa buk’atar ganinmu kuka gudonan kenan? Sai kuma gashi ALLAH ya kawomu mun ganku, dama ance rabon kwad’o…… koko my man?”.
Murmushi Sulaiman yayi, yace “hakane wlhy bro, hakanma dasukayi yamana dai-dai”.
Magan ganinmu yasaka Munubiya tashi, Sulaiman yace, “sleeping beauty kin tashi?”.
d’an waro idanu Munubiya tayi, sai kuma ta kalleni dan neman k’arin bayani.

Innaro takatsemu da fad’in “toku kuna ganin bak’i basai Ku tashi Ku basu wajeba”.
“cikin tsokana Sulaiman yace, “a’a Granny idan sun tashi wazamu kalla? Sun gudo wajenki dan karmu gansu kuma sai gashi ALLAH ya kawomu har gida”.
Ba k’aramin k’ona ran innaro maganar tayiba (dama an kawomu nanne dankar bak’in su gammu balle su za6emu, amma kuma sai gashi sun gammu anan d’in. Anyi gudun gara kenan…..????).
Bamu tsaya sauraren abinda innaro zata ceba mukayi fitowarmu zuwa gida.
Su Sa’eed sun gaida innaro, anan take tambayarsu kosun za6a acikin wad’anda sukaje gaishesu acan gidanmu.
Sa’eed yace, “eh mun za6a Granny, amma wad’annan dasuka fita yanzu”.
Caraf innaro tace, “ai wad’annan anmusu miji shiyyasa su basujeba, sai dai cikin wad’ancan”.
Bahaka sukasoba, amma yazasuyi, sai dai har sukabar gidan basu sanar da wa suka za6aba.

Koda muka sanarma innarmu cewa tayi babu ko mai, karma hakan ya damemu.

 

????????

Har tsawon kwana 5 babu wata magana data fito akan suwa bak’in suka za6a, su Abba basuce da kowa komaiba.
Hankalin iyayenmu mata duk atashe yake, kowa takasa kunne taji wacece aka za6a, sai dai babu mai iya tunkarar iyayenmu maza da zancen, dan duk ba suga fuskar hakanba.

Satinsu guda da zuwa saiga bak’i sunzo wai an kawo kud’in aure.
Hankalin iyayenmu fa yakuma tashi, dan ganinsu wani munafurcin akayi shiyyasa aketa k’unbiya-k’unbiya. Nanfa suka shiga ‘yan tsugunne-tsugunne Na gulma irinta gidan yawa.
Kwana biyu dayin haka su Abba suka sanar da cewa nida Munubiya sukace sun za6a.
Innaro ce tafara k’aryatawa, sannan tace, Sam bata aminceba, ina jikokin talakawa ‘ya’yan bak’in haure suka kai matsayin auren ‘ya’yan babban mutun irin sanata halliru, ai k’aryane sannan munafuncine, agabanta su Sa’eed sukace Zarah da Siyama suka za6a. (Zarah k’anwar ya hameed Ce, babanmu d’aya, Siyama kuwa d’iyar momy Hadiza Ce d’iyar dady).
Jin wannan zance yasa kowa ya fahimci akwai munafunci a lamarin, kowa yasan yanda mamansu ya hameed suke da momy Hadiza a gidan, kansu had’e yake. aikam matan gidanmu suka harzuk’a sunata yada magana, harma abin yaso yazama fad’a, innarmu ce batace komaiba, ita cewama Abbanmu tayi dan ALLAH amaida zancen auren kansu Siyamar tunda innaro tace dama su suka za6a.
Banza abbanmu yamata dan yasan innaro tayi hakanne danta k’untatama innarmu, amma tabbas dabakin su Sulaiman sukace ‘yan biyunnan suka za6a, shin sai yaushene inna zata bar muzgunama Aisha da munanata a gidannan?, shekara kusan Arba’in ana Abu guda babu sassauci, tunda yake baita6a ganin rana d’aya da innarmu tama innaro koda kallon banzaba bare rashin kunya, sa6anin sauran matan gidan da basa kunyar ya6a mata magana koda ta habaicine.

Kwana kusan hud’u ana d’auki ba dad’i akan wannan zance, saboda akawo k’arshen maganar sai Abbanmu yace su Sa’eed suzo su nuna wad’anda suka za6a da kansu.
Hummm bamusan miya faruba, (konace mi innaro dasu momy hadiza suka k’ulla ba) munga dai sunta murnar zuwansu Sa’eed d’in, sai rawarkan had’a abincin tarbarsu sukeyi, dan ranar su biyu kacal sukayi, kuma abin mamaki wannan karon agidan innaro aka saukesu.
Bayan isowarsu dakamar mintuna 20 sunci abinci sai akace duk muje gidan innaro.
Su Haleematu duk sun rigamu tafiya, mune k’arshen zuwa muda Fauziyya, saidai muna shiga gidan Innaro ta samu mukabi ta k’ofar kitchen nida Munubiya kawai, Fauziyya kuma aka barta tashiga ta falo.
Yanda sukaita zumud’in kallonmu wancan karon a yau ba haka bane, gaba d’aya hankalinsu Na kan Siyama da zahra, abin ya bamu mamaki har sauran ‘yan uwanmu.
Tunda mukaga haka duksai muka fice muka koma gida, su Haleematu harda kukansu, mukanmu zukatanmu sun sosu, dan harga ALLAH Sa’eed ya kwantamin arai.
Wanan lamari saida yajawo gagarumin fad’a agidanmu irinma wanda ba’a ta6a yiba, dan saida takai matan gidanmu da ‘Yar tone-tone asirinsu yanda suke kulle-k’ulle wani lokaci akan innarmu da junansu.
Sosai ranar saida ran kowa ya 6aci, amma mamansu yaa Hameed da momy Hadiza su wasai sukejin kansu, koba komai sune a sama suke gani, ‘ya’yansu zasuje gidan Hutu.

Abbanmu yasamu innarmu yayta bata hak’uri, dan tabbas yanada tabbacin akwai lauje cikin nad’i akan lamarin, tunda su Sa’eed da kansune suka Samar masa za6insu, amma gashi a wannan karon since su siyama ne ba ‘yan biyu ba.
ALLAH sarki innarmu sarkin hak’uri, cewa tayi babu komai, dama can su Siyamar ne matansu, Dan haka tunran gini tun ran Zane, suma sauran ALLAH yabasu Na kwarai.
Sosai Abba yak’ara jin jinama hak’uri da tawakkali irin Na matar tasa, abin sonsa, wadda yakejin har duniya ta tashi k’aunarta dabance a ransa, yana sonta harma baisan yanda zai fassaraba, kullum cikin mata k’yak’yk’yawar addu’a yake akan ribar hak’urin datakeyi da kowa agidan har mahaifiyarsa. yana ganin Kimar Aisha sosai da girmanta, tunda suke babu rana d’aya dazaice gawani abun aibu data aikata masa, sai dai abinda ba’a rasaba saboda zomu zauna zomu sa6a, balle shekara kusan 40 ba wasabace.

 

???????

An tsaida bikin Siyama da Zarah dai-dai danasu aunty Hauwa’u, komai kuma ankawo, saura lefe da sadaki kawai.

Ahaka muka koma makaranta inata yak’in fidda Sa’eed daga raina, ALLAH ma ya taimakeni dama bawai yashiga irin cancikin nan baneba.

******

Yau lectures d’in safe garemu, dan haka mukayi shiri da wuri nida Munubiya, a tsaitsaye mukasha kunun da innarmu ta dama mana, Dan yau girkin mamansu ya Hameed ne, idan bata gadama ba sai takai 8 bata kammala ba, har yara saisun makara,
Aiyaan yashigo d’auke da lunch boxs nasu yana tura baki gaba. “kai kuma lafiya kake cuno baki uwa na agwagwa?”.
6ata fuska yakuma yi tamkar zai fasa kuka, ya zube lunch boxs d’in saman kujera “Aunty ba mama bace tace wai yau batayi abincin dazamuje dashi makaranta ba, hakama fa jiya abincin dare ta d’umama ta zuba mana, amma damukaje school saigashi a kulan Haneep Indomi ne da kwai”.
Aryaan ya kar6e da cewar “ALLAH kuma aunty namu tsami yayi kafinma muci, haka mukadawo da yunwa”.
tausayi yaran suka bani, Munubiya tace, “kuyi hak’uri kunji 2 d’in inna, watarana sai labari ai”.
Kansu suka jinjina mata sukace “to aunty”.
innarmu tana jinmu amma uffan bataceba.
Fita nayi batareda nacema kowa komaiba, wani shago dake can k’asan layinmu naje, nasiyo musu yoghurt da cake k’ananu, nahad’o musu da biscuits.
A harabar gidan Na iskesu harsun fito, sauran yaran sunata shiga school bos d’insu da ake kaisu makaranta. School bag d’insu nabud’e Na saka ma kowa nasa, sannan nace ayi karatu da k’yau kunji babys d’inmu”.
Cikeda jin dad’i suka amsa min da fad’in “to auntynmu”.
Kumatunsu Na sumbata sannan na taimaka musu suka shiga motar suma.
Ina shigowa munubiya tamik’e tana fad’in “wai ina kikaje? kinsanfa jarababben lecturer d’inanne zai shigar mana yau”.
“sorry sweetheart tashi muje”.
Dubu 1 innarmu tamik’o mana, kar6a mukai muna mata godiya, muka fito tana binmu da addu’oin fatan alkairi.
Mun lek’ama su Siyama, kowacce sai tace batada lectures d’in safe, fauziyya da Feedausi ce kawai muka tafi, dansu duk department d’inmu d’ayane……….???

 

 

 

One luv????

*_ALLAH ka gafartama iyayrnmu??????_*
[4/16, 9:53 AM] +234 811 277 0720: *_Typing??_*

 

*_HASKE WRITERS ASSO…??_*
_(Home of expert and perfect writer’s)_

 

*_?RAINA KAMA……!!?_*
_{Kaga gayya}_

 

*_Bilyn Abdull ce????_*

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply