Hausa Novels Raina Kama Book 1 Hausa Novel

Raina Kama Book 1 Page 5


Raina Kama Book 1 Page 5
Viral

??5?

………..Wajen 4pm muka fito daga cikin makaranta, mu 6 ne yanzu, sa6anin d’azu damukazo mu hud’u, bayan tahowarmu Safara’u da Haleematu suka taho suma, duk da mun rigasu gama lectures sai muka jirasu suka fito muka rankayo tare domin tafiya gida, bamu samu school bos ba, dan haka muka da6o sayyadarmu har zuwa babban gate, muna tsaitsaye abakin titi, tareda wasu daga cikin tsirarun d’alibai irinmu, tundaga nesa muka hango tahowar motocin da uban gudu, saika d’auka sukad’aine akan titin saboda gudun dasuke tsulawa tamkar zasu tashi sama. duk baya muka matsa, dan tabbas wad’annan suka sameka babu abinda zai hanasu takeka su wuce batareda sun damuba.
Tamkar wucewar iska haka suka dinga gittamu, jikake shuuuu!! shuuu!! shuuu!!.
Furicin wani mayshin saurayi dake jingine jikin motarsa yazo d’aukar wasu ‘yan mata biyu dake gefenmu ‘yan matan sunada jin kan masifa, ko’a makarantar bakowa sukema maganaba, department d’inmu d’aya dasu amma ko kallo basu isheniba, dan ko sallama bata ta6a had’ani dasuba..
Saurayin yabi motocin da kallo yana fad’in “tab ashe *_GALADIMA!_* yashigo gari kenan?”.
“Da gaske yaa Usman?”. ‘d’aya acikin ‘yan Matan tafad’a cikin matuk’ar zumud’i’.
Yace, “da gaske mana baby, baga motocinsa kuna ganin sun wuceba”.
Dan danan suka shiga murna, kai kace an musu albishir da aljanna ne.
Baki na ta6e inajan k’aramin tsaki. Fiddausi tace, “to waye shi galadima d’in?”.
“oho musu”, ‘cewar Munubiya’.
Budurwar dake tsaye d’ayan gefenmu itada saurayinta suna jiran abin hawa suma tace, “Galadima d’an Sarki kenan, *Yarima Sameer!”*.

“humm lallai kuce manyane, shiyyasa suke gudun da kosunbi takan talaka babu abinda za’ayi”. ‘cikeda 6acin rai nake maganar’.
Dariya su siyama sukayi suna fad’in “toke ina ruwanki?, k’asarfa tasuce, sai yanda sukayi da ita, tsakaninmu dasu saidai mu hangesu cikin mota ko ranar hawan salla”.
Dogon tsaki nakuma ja tareda kauda kaina daga garesu na maida hankalina wajen tare wata taxi dake gabatomu.
A motama firar dasu Haleematu sukaitayi kenan, ta Galadima ne ko uwarmi ne ma Na manta. nidai uffan ban kuma tofawaba, hasalima haushi hirar tasu takoma bani, dan mai taxi d’in yasaki baki sai wani basu labarin Galadima d’in yakeyi dakuma kwarzan tashi, earphone na jayo a cikin lady’s bag d’ina na manna a kunne danma nabar jinsu gaba d’aya.
Saida muka iso gida sannan Fauziyya dake kusa dani ta zungureni, d’agowa nayi Na kalleta sainaga duk sun fice, bance komaiba nafito nima.

Mun iske innarmu bata nan, saisu Aiyaan kawai zaune a falo suna kallo, shigowarmu yasasu tasowa da gudu suna mana oyoyo, muma mun taryesu da murnarmu, Munubiya tace, “Aryaan miyasa baku cire Uniform ba kukayi wanka?”.
“yo aunty mun dawo munga Innarmu bata nanane”.
Nace “innarmu bata nan? to ina taje?”.
“muma bamu saniba aunty, munje kuma kitchen bamuga abinci ba, kuma yunwa mukeji”.
Munubiya tace, “ya salam, kujira ina zuwa”.
Fita tayi, babu dad’ewa sai gata tadawo cikin damuwa, ina cirema su Aryaan Uniform, Na kalleta ina fad’in “mike faruwa Munu…? Ina abincinne?”.
Kwallar idonta ta share, ta zauna bisa kujera sannan tace, “naje mama tace wai innarmu ta d’auka abinci tatafi dashi hospital, dan haka shine rabonmu”.
Raina a 6ace na mik’e zan fita, da sauri munubiya ta ruk’oni, “please Munaya, kibarta kawai, yakamata mu kira innarmu muji waye a hospital? Inaga wannan yafi komai muhimmanci nake gani akan abinda mamar tamana”.
“Haba Munubiya, wannan wane irin rashin mutunci ne, wai mi Matan gidannan suke tak’ama dashine? Idan suna tak’ama da Ubanninsu muma ai nan gidan Ubanmune ko, yanzu ace yarannan kamar su Aryaan su dawo school tun 3 amma ahanasu abinci, wannan wane irin zaluncine? Kisakeni kawai naje naci kutumar uban matarnan munubiya, wlhy sai dai yau Abba yace nabar masa gidansa”.
“A’a munaya, duk hakama bata tasoba, idan hankali ya6ata hankali ke nemosa, bai kamata mutaru muzama d’ayaba mu da su. bara kawai naje kicin d’in Na dafa mana wani abun mai sauk’i, kiyi hak’uri dan ALLAH, kinga innarmu bazataji dad’iba idan tatarar da faruwar hakan”.
Badan raina yaso ba Na hak’ura, saman kujera nakoma Na zauna ina huci, nikad’ai nasan minakeji a zuciyata.
Munubiya tafita dan nema mana abinda zamuci, nikuma Na d’auki waya domin Kiran innarmu naji abinda tajeyi asibiti.
Harta katse bata d’agaba, nakuma kira akaro Na biyu sannan ta d’auka, gaisheta nayi da tambayar mitajeyi asibiti?.
Daga can tace min Nafisar mama Rabi’a Ce jikinta ya motsa yanzu hakama jini ake buk’ata amma an Gaza samu, gashi yaa marwan dayakan bata jinin baya nan yayi tafiya shida Abbansu.
Hankalina a tashe nace “innarmu ganinan zuwa yanzunnan insha ALLAH, kuna general hospital ne?”.
“eh muna nan”.
“ok insha ALLAHU ganina zuwa”.
‘Dakinmu nashiga da Sauri nad’an watsa ruwa a tsaitsaye saboda naji dad’in jikina, komai ban tsaya shafawaba Na zira doguwar Riga jallabiya Na fice da hanzari. A k’ofar fita falo naci karo da munubiya d’auke da babban faranti tazubo spaghetti tanata turiri.
namatsa baya da Sauri INA fad’in sorry, munubiya bara naje asibitin wajensu innarmu, wai jikin feena ne ya motsa kuma ana buk’atar jini, gashi yaa marwan sunyi tafiya da abba”. Munubiya tace, “toko Na juye mana abincin a kula mu tafi gaba d’aya?”.
Nace, “a’a munu… Ki zauna dasu Aiyaan bara naje ni kad’ai, baikamata mubar wajen ba kowaba”.
“to shikenan, yanda akayi ki ta6oni awaya, amma in kunkai dare zakuganmu muma, abincinfa?”.
“humm munu bar abincinnan, banida wata nutsuwar cinsa, saina dawo”.
Ban jira amsarta ba nafice. ALLAH ya taimakeni INA fita nasamu napep. Mintuna kad’an muka isa hospital d’in, kud’insa na biyashi nashige da hanzari ina k’ok’arin kiran innarmu.
Babu dad’ewa kuwa ta d’aga, nace mata gani acikin asibitin. Kwatance tamin na inda aka kwantar dasu 6angaren masu sikila.
A rikice na iske innarmu da mama Rabi’a, saboda jikin feena ya motsa mata sosai a wannan karon.
Nace, “mama yanzu mi ake cikine?”.
“Rashin jininne matsala yanzu Munaya, sunce kuma anemoshi da gaggawa, to dama can jinin Fadeel baya yimata shiyyasama ko gwadasa ba ayiba, Marwan dake bata kuma sunyi tafiya da abbansu”.
“mama ina zuwa, bani takardar da suka baku”.
Mik’omin tayi nafita da saurina. dukna rikice inata kai kawo dan ganin ansami jinin, amma har magriba ta rufa ba a samuba, saboda jinin feena yanada wuyar samu, ana cikin kiraye-kirayen sallar isha’i saiga Ayusher ta iso itama, dama an barta a gidane saboda babu kowa, to takasa hak’uri tabiyo sahu, da ita muka cigaba da shiga da fita, saida aka fito sallar isha’i ALLAH yasa aka dace da samun leda 1, saura 1, dama biyu suke buk’ata. ana cikin d’aura mata saiga Munubiya ita dasu Aryaan da kulolin abinci.
Koda aka gama sakawa sai muka koma Neman d’ayar ledar data rage, yanzu harda munubiya muke tare.
Muna a lab d’inne muna shawarar ko a d’iba namu jinin idan zaiyi babu damuwa. Takun takalman damuka jiyo yasamu juyawa harda likitan da maganarsa takatse bisa k’ok’arin bamu amsa dayakeyi. wani ni’imtaccen k’amshine ya iso hancinanmu tunkan mamallakin turarenma yakai ga isowa inda muke. d’auke kaina nayi na maida ga mai d’ibar jinin.
Likitan naga yafara gyara kujera yana fad’in “dama yalla6ai ya shigo gari yau? Ni nama manta yaune ranar dayake bada jini”.
Bai samu mai bashi amsaba a cikinmu har tawagar Wanda yakira yalla6ai suka iso wajen.
Munubiya da Ayusher suka matsa gefe saboda wata uwar tsawa da masu take masa baya suka daka mana, nikam koma motsawa banyiba bare nasan ALLAH yayi ruwansu awajen, saima baki dana ta6e na d’auke kaina daga saitin dasuke.
Bulala d’aya daga masu jajayen rigunan ya d’aga da nufin zubamun.
“Wanda suke kira Yalla6ai dake zaune a kujerar da doctor ya ajiye masa ya d’agamasa hannu da Sauri, alamar karya dakeni”.
Cikeda girmamawa yace, “angama zaki s………”.
Hannu Yakuma d’aga masa alamar baya buk’atar kirarin.
Baki nakuma ta6ewa sannan na ra6a ta gefensu nafice, banga fuskar Yalla6ai d’in nasuba, saboda ya juyamin bayane ni, sananan shima tunda yashigo bai kalli kowaba a lab d’in, yanata aikin danna wayarsa, kuma baiyi magana ba, ko doctor da Norse’s d’in da suka gaidashi hannu kawai ya d’aga musu, kuma ko d’agowa baiyiba yanata aikin danna waya kai kace zai danno hanyar zuwa aljannane aciki.

Waje na dawo nayi zamana ina cigaba da game a waya, su Munubuya dai suna cikin, bansan uwarmi suka tsaya yiba awajen.
Kusan mintuna 40 saigasu sunfito, takun takalmansu kawai naji, amma ban d’agoba, sai k’amshin turarensa daya cika illahirin wajen, saikuma gaisuwar da mutane keta faman zubewa sunayi masa, ko sau d’aya banji ya amsaba.
Tsaki naja inamaijin haushin wannan mutumin, to wayema shine? dayakema mutane wannan jinkan., motsooww aikin banza kawai.

Tabbas yaji tsakin da akayi, hakanne yasakashi d’ago k’yawawan idanunsa yakai duba saitin Inda yajiyo tsakin, akan *munaya* dake zaune bisa kujerun dake Jere awajen ya sauke su, sai dai baya ganin fuskanta sosai, saboda ta duk’ar da kai tana danna waya, kuma gyalen jallabiyarta yarufe mata Rabin fuska, ita kad’aice zatayi wani motsi awajen suji, dan tafi kusanci da Inda suke tsaye.
Janye idanunsa yayi kawai daga gareta, yay saurin d’agama bayin dake k’ok’arin tafowa gareni hannu. Cikin Wata tattausar murya mai aji dake cike da k’asaitar masu isa najiyo yana fad’in “Bayta kawai”.
Cikeda girmamawa bawan yace, “ya shugaba tsaki tayi fa”.
Shiru yay kamar bazai tankaba, saikuma najiyo yace, “kasan dawa take?”.
Bawan girgiza kai yayi alamar a’a.
Bai sake cewa komaiba yay gaba suka bishi a baya.
‘Dago ido nai nabi bayansu da kallo, sainaga sun nufi 6angaren mata masu haihuwa.
janye idona nayi ina fad’in “kadaiji dashi Malam, kana fama da Girman kai kamar wani Sarki? Abinma dariya ko (R) bai iyaba, wai bayta”.
Dai dai nan su Ayusher suka iso cikeda farinci, hannunsu d’auke da ledar jinin

Cikeda jin haushi nace, “wai uwarmi kuka tsaya yi acikin lab d’inne?”.
“Uwarmu ta gode”. ‘ cewar Ayusher’.
Munubiya kuma tace, “zaman namu aiko yayi amfani, tunda gashi mun samo sauran jinin ko”.
Na kallesu da mamaki, “ina kuka samo jinin kuma to?”.
“Galadima ya bayar”.
Cikin ta6e baki nace, “miye kuma Galadima? A inama kukaga wani Galadima kome ma kukace?”.
“wanda yashigo muna cikifa, ai Galadima ne (Yareema Sameer d’an sarki)”.
Ido na waro waje, “wai kuna nufin wannan mai shegen girman kai d’in dama shine Galadiman? kenan munu…. shine yawucemu d’azu munfito makaranta?”.
“kwarai kuwa sweetheart shine, kuma wlhy bashida Girman kai kamar yanda kike zato ko Sis.. Ayusher? ”.
“Wlhy kuwa hakane Munu…, ashe duk k’arshen ko wane wata saiyazo asibitinan yabada jininsa gamasu buk’ata, gashi jinin nasa mai irin wahalar samu d’inanne irinna feena, kai mutuminnan yayi wlhy, Sarauta ba karya baceba, danyau naga tsantsar sarauta da mulki da k’asaita ajikin Galadima, yanzu haka zai zagayane yaduba marasa lafiya”.
Harara na ballama Ayusher daketa zabga surutu uwa aku, na warce jinin daga hannun munubiya ina fad’in “idan kun gama shirmen kwa taho”.
Kallo suka bini dashi, Ayusher tace, “Anya yarinyarnan batada aljanu?, ke kowama bai mikiba?, yanzu nan duk had’uwar Galadima Munaya tana nufin bai burgeta ba kenan?”.
Dariya Munubiya tayi, sis… Ayusher har yanzu baki gama fahimtar Munaya ba na lura, kyagama abinda yafi haka indai daga wajentane. Yanzu hakama tunda kikaji tace haka ko sau d’aya bata kalleshiba wlhy bare tasanma kalarsa. kinga muje kinji.
“humm aiko wlhy inabata kalleshiba anyi babu ita kuwa, ruwa ta shata kuma, yo kobabu komai aina bada koda labarine nace nata6a ganinsa ido da ido ko”. ‘cewar Ayusher’.
Dariya kawai Munubiya tayi, taja hannunta suka tafi.

Sanda suka iso harma an fara k’ok’arin sakama feena jinin, dama wancan yak’are.
Duk muna zaune a k’ofar d’akin bisa kujerun wajen, Aryaan da Aiyaan duk suna jikin mama Rabi’a barci ya d’aukesu, fadeel na kusada innarmu yanacin abincin dasu Munubiya suka kawo, zama nayi kusada fadeel d’in na saka hannu nad’au cokalin dayake cin abincin ina fad’in bro… nimafa yunwarnan nakeji, rabona da abinci tun kusan 1 danaci a kafteriya na makaranta”.
Kallona yayi yana cewa “sannu da k’ok’ari sis…., shiyyasa gakinan tsula guda bak’ya gaba bakya baya keda munu….”.
Cokalin nakai zan kwala masa a kai ya kauce yana dariya, nima dariyar nayi na d’auki kular abincin na k’ara mana.
Muna cikin ci Ayusher ma tamatso tace zataci, munci mun k’oshi sannan muka gyara wajen, mama da innarmu ma sukaci, dan zuwa yanzu duk mun sami ‘Yar nutsuwa.
Kusan 10pm saiga Abbanmu shida baba k’arami, duk muka gaidasu suka tambayi mai jiki, innarmu da mama Rabi’a suka amasa musu da sauk’i.
Har d’akin suka shiga, suka duba feena daketa barcinta, sannan sukace muzo mu tafi gida, za’a bar innarmu da mama Rabi’a su kwana.
Saida safe mukai musu muka fito, Fadeel ya d’akko Aryaan, baba k’arami ya d’akko Aiyaan.
Saida muka fara sauke Ayusher da Fadeel gida sannan mukuma muka wuce.
Mun tarar gidan tsitt alamun duk anyi barci, saidai masu wayar dare da samari irinsu aunty Ramla, saikuma masu charts.
Abbanmu da baba k’arami suka d’auki su Aiyaan, har d’akinsu suka kaisu sannan suka fita.
Muma shirin barci mukayi muka kwanta cikeda kewar Innarmu, muna kwanciya muka kirasu da k’arajin mai jikin sannan muka tafi duniyar barci muma, dagani har Munubiya babu mai wani saurayin da zamu 6ata lokaci wajen yin hirar dare……………???

 

Kumuje zuwa my guys??????

 

Gobe idan ALLAH ya kaimu baza kujiniba, inada wani d’an uziri, sai Monday idan ALLAH ya kaimu kuma.

https://chat.whatsapp.com/K1qwmMusX7ILDLATGSvfHJ

*_RAINA KAMA…….. FANS CLUB_*

_Duk Wanda yasan yana karanta wannan buk d’in ya garzaya yanemi link Na RAINA KAMA FANS CLUB, a wannan gidan kawai zan dinga posting a halin yanzun, awannan karon bazan turama kowa buk ta PC ba, narigada nayi rantsuwa. Amma annan zaka iya samu da faro, sannan inhar ba’a tattaunawa akan novel d’in zanyi waje da mutum babu ruwana, kuma kar a turomin kowanne novels acikinsa Dan ALLAH, inba hakaba zan fidda mutum ko Yaya nake dashi????, nabud’e gidanne saboda anan kawai zan dinga posting yanzu, sai wasu groups dabasu wuce 3 ba._

Ina fata zaku bani had’in kai please, inba hakaba ALLAH zai koma Na kud’ine saboda tsaro ba tsoroba????

 

 

One luv????

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu??????_*
[4/16, 9:53 AM] +234 811 277 0720: *_Typing??_*

 

*_HASKE WRITERS ASSO…??_*
_(Home of expert and perfect writer’s)_

 

*_?RAINA KAMA……!!?_*
_{Kaga gayya}_

 

*_Bilyn Abdull ce????_*

_____________

*_ASSALAMU ALAIKUM_*

_Jiya da daddare akaita kirana mutane Na tanbayata Yaya jiki, tun ban fahimci maganarba hardai nafara tsarguwa nayi tambaya. Dan sai kira kan kira ake jeramin, wata take sanar dani taga wani posting ne yana yawo wai za’amin CS. babu shiri nabud’e data naga mike faruwa, group d’in farko dana bud’e sainaci karo da wannan posting d’in mutane nata comments, nabud’e nabiyu ma hakan dai._

*_Assalamualaikum Alaikum,Dan Allah kuyiwa billyn Abdul(ma rubuciyan RAINA KAMA. Adua’baby ya mutu a cikin ta zaa cire Mata Shi yanzu_*

_sai daga baya nakejin Bily galadanci ce batada lfyar, amma wata ta maida zancen haka saboda sunan namu yazo d’aya, to ALLAH yabata lfy itama._
_sannan ina shawartar jama’a Dan ALLAH kuringa nutsuwa wajen tantance Abu kafin Ku yad’ashi, domin wadda tayi wancan write up d’in ta zaunane ta tsara nata son zuciyar, wadda tayi posting d’in farko akan ciwon Bily galadanci sunan Bily tasaka ba nawaba, itakuma ta canja nata tsarin tashiga ya d’awa, ALLAH ya shiryar damu, yakuma bama marasa lfyarmu lafiya._

*banyi niyar posting ba yau, amma ganin wancan write up d’in yana cigaba da yad’uwa yasani dole yi Dan na warware muku zancen.*

______________________________

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply