Hausa Novels Raina Kama Book 1 Hausa Novel

Raina Kama Book 1 Page 9


Raina Kama Book 1 Page 9
Viral

??9?

…….K’yaleta nayi najuya sit d’in bayanmu Na fusge ta hannun wani guy, rubutun farko dage jikin jaridar a shafin farko na tsirama idanu.

*_BABBAR MAGANA, GALADIMA SAMEER RUNGUME DA MATASHIYAR BUDURWA A PLAZA ‘DINSA SUNA SUMBATAR JUNA!!_*

sai kuma hoton dake k’asan rubutun shima har kala biyu, Na farko abinda yafarune na fad’uwar Munubiya a birnin gayu plaza, har Galadima yay yink’urin taimakonta amma tadafe baskets ko ta6ata ma baikai gayiba, amma abin mamaki da al’ajabi a hoton galadima ya rungume munubiya ne bakinsa akan nata.
Hoto nabiyu kuma ni da shi ne afilin idi lokacin damukayi karo har wayarsa ta fad’i, ko kad’an bai ta6aniba, ko waya daya kar6a a hannuna hannuna danashi basu had’uba, amma anan an nuna hoton yana rik’e da hannuna duka biyu muna kallon juna.

“Innalillahi” nafara maimaita jikina har yana rawa, gawata uwar jufa data fara jik’a sassan jikina, lallai dolene duk inda muka gitta abimu da kallo.
Ju yowa nayi na kallo munubiya dake tsaye a bayana, itakam hawayema takeyi.
Jikina a sanyaye nakama hannuta muka fita daga cikin hall d’in, kallon da ake Manama ayanzu yafi na d’azun, Dan labarin sai kuma yad’uwa yakeyi yanzun.
Muna fitowa muka samu taxi sai gida.
Tunda muka sauka naga wasu gungun samarin dake layinmu a majalissarsu sun zubo mana idanu gaba d’aya, tuni zuciyata tafara tsitstsinkewa, kenan labarin harya iso nan?. Dagani har Munubiya jamukai muka tsaya, saboda ganin dukkan ahalin gidanmu tsaye cirko-cirko a tsakar gida, hardasu yaa hameed anguna, ga bak’i dabasu gama tafiyaba, innarmu kwance akan tabarma maman fauziyya namata fifita, ga Abbanmu kusada ita tsugunne yana shafa mata ruwa.
Jaridar dake hannun baba k’arami mukabi da kallo, bansan sanda wani kuka yatahominba nima, sa6anin da munubiya kawai keyin kukan.
Da gudu mukayi kan innarmu, amma sai yaa hameed ya daka mana tsawa, “karku sake Ku ta6ata wlhy, idan bahakaba jikinku kuwa saiya fad’a muku”.
Babu shiri mukaja burki, amma sai muka durk’ushe ak’asa muka fashe da kuka.
Innro tace, “kwayi kuka kuwa munafukai, ahiyyasa ai ANNABI yace a auri mace tagari, Dan ‘ya’ya susami uwa tagari, yo wannan aimu ba sabon abu baneba agaremu, tunda dama halin uwarku kenan, itama saida tagama tambad’arta a titi aka k’ak’abama d’ana”.
Rintse idanu nayi saboda yanda maganganun innaro ke sukar zuciyata. Dady yakatseta da fad’in “dan ALLAH inna kiyi hak’uri kibar maganarnan”.
“hameesu barni nafad’i gaskiya, wannan abin kunya har ina, wai jikokinane yau aka buga ajikin jarida namiji rungume da d’ayarsu a titi” ta face hanci tana share hawaye da bakin zani, “ALLAH ya wadaran irin wannan rayuwa taku kuda uwarku, kun jawo mana abunkunya, yanzu dawane ido duniya zata cigaba da kallonmu” feeet, takuma fyace majina”.
Mudai ni da munubiya muna durk’ushe rungume da juna Luna rairai kuka maiban tausayi dacin zuciya, yayinda ‘yan gidanmu da sauran ‘yan biki suketa k’us-k’us a tsakaninsu.
Isowar likita yasa aka kama innarmu aka maida falon Abba, a sank’ame take tamkar gawa….

 

?.?.?.?.?.?.?.?.?.?.?.?.?.?

*_GAGARA BADAU PLACE_*

Shirye-shiryen komawa India yakeyi hankalinsa kwance, Dan yau zai koma ga mahaifansa da ‘yan uwansa dake can, jirgin k’arfe 8pm zaibi.
Yana gama had’a ‘yan abubuwan dazai iya buk’ata yadawo falo ya zauna, sanye yake cikin farare k’al d’in kayan Adidas na training, dogon wando da Riga mai dogon hannu, yasaki hular abaya, kayan sun masa k’yau sosai.
Kallo d’aya yayma abincin dake kan center table d’in ya d’auke kansa, cikin k’asaitacciyar muryarsa mai cikeda isar masu mulki naji ya furta “Saykin k’ofa”.
Kai kace anmasa dolene saiyayi maganar.
Da hanzari sarkin k’ofa yashigo falon, ya zube a k’asa “barka da hutawa ya shugabana”.
Kansa kawai ya jinjina, sannan yace, “waye yakawo abinci nan ne?”.
“ya shugabana bansan daga ainahin wane 6angare bane, amma bayin dasuka kawo daga 6angaren sarauniya Zulfah ne”.
Baice komaiba ya d’aga masa hannu alamun yatafi.
Sai da yad’an rissinar da kansa alamar girmamawa sannan yamik’e, dokace agareshi shi bayason kirarin da akema ‘yan gidan sarautar. dan haka basa yimasa shi, Saboda gudun 6acin ransa.

zamewa yayi yay kwanciyarsa akan doguwar kujerar ya lumshe idanunsa batareda yabi takan abincinba.
Sallamar sarkin k’ofa tasakashi bud’e idanunsa akansa, ya amsa sallamar bisa la66ansa, sarkin k’ofa yazube agabansa, cikeda girmamawa yace, “ya shugabana yalla6ai Muftahu yace amasa iso gareka”.
Alama yamasa akan yabada izinin ya shigo.
Fita sarkin k’ofa yayi. babu dad’ewa saiga Muftahu yashigo da sallama, Galadima yabud’e idonsa yana kallonsa tareda amsawa.
Zama yayi kujerar dake kallon Galadima, yace, “yalla6ai barka da hantsi”.
Murmushi Galadima yayi, ya tashi zaune sosai yana fad’in “my man daga ina haka naganka ayikice? bakaje aikibane?”.
Ajiyar zuciya Muftahu ya sauke, yacije le6ensa na k’asa yana mik’ama Galadima jaridar dake hannunasa, “nafita wlhy sainaci karo da wannan jaridar data fito a safiyar yau”.
Cikin halin ko inkula Galadima yace, “Miye had’ina da jayidan to?”.
“Kayi hak’uri ka kar6a ka duba”.

A shafin farko yay karo da abinda yasakashi sake kallon Muftahu, kai Muftahu ya d’aga masa alamar yacigaba.

*_ANYI WALK’IYA…., GALADIMA DA AIKA-AIKA A FILIN IDI_*
https://2gnblog.blogspot.com/
cikin hanzari yabud’e shafin farko, nankuma an saka.

*_BABBAR MAGANA, GALADIMA SAMEER RUNGUME DA MATASHIYAR BUDURWA A PLAZA ‘DINSA SUNA SUMBATAR JUNA!!_*

sai hoton farko dana biyu, wad’anda suka d’aure kansa, danshi gaba d’ayama ya manta daduk abinda yafaru, tundaga na birnin gayu plaza harna filin idi d’in. d’agowa yay yakalli Muftahu sannan ya maida kallonsa ga dogon rubutun da akai akan sharhin hotunan. bazai iya karanta rubutun ahakaba, saiya fara waige-waigen neman medical glasses d’insa.
Fahimtar haka da Muftahu yayi yace, “ina yake in d’auka maka?”.
Da hannu ya nuna bedroom d’insa ba tare da yace komai ba.
Mik’ewa Muftahu yayi yanufi bedroom d’in, babu dad’ewa saigashi yadawo, ya mik’a masa sannan yakoma inda yake da ya zauna yana fad’in “ko ka kawo na karanta maka”.
Nanma baice uffanba yamik’a masa jaridar, kansa ya maida jikin kujerar ya jingina ya lumshe idanunsa.

Tiryan-tiryan Muftahu yafara karanto k’aryar da aka jera jikin jaridar, ko sau d’aya bai motsaba, amma yana saurarensa.
Muftahu yagama cikin sauke ajiyar zuciya, Amma tabbas wannan wata k’ullaliyace, ai ba abinda yafaru kenanba jiya a birnin gayu, ni nama rasa mizan cema wannan gidan jaridar wlhy”.
Galadima ya bud’e idonsa dake a lumshe, ya kad’a yay jajur saboda 6acin rai, akan Muftahu ya saukesu batareda yace komaiba, tuno abinda yafaru a filin idi yayi kusan sati 4 kenan, tabbas sunyi karo da yarinya, wadda ayanzu haka ko fuskarta bazai iya tunawaba, dan ko’a waccan ranar kallo d’aya yamata, a jiya kuma ko ta6a yarinyar baiyiba ALLAH ya kareta daga fad’uwar dazatayi. jinjina kansa yayi cikeda 6acin rai da mamaki.
Muryarsa a sark’e yace, “Muftahu imason bayanai akan yayannan najikin jayiday su duka”.
“ok yalla6ai, amma ai yarinya d’ayace duba kagani”.
Kar6ar jaridar yayi yakuma kallon hotunan, tabbas duk yarinya d’ayace, wannan ya sake tabbatar masa da an shirya masa hakanne.
Mik’ewa yayi yazari mukullin mota batareda yace ma Muftahu komaiba, ganin haka shima Muftahu saiya mik’e yabi bayansa.
Cikin sauri dogaren dake binsa inhar zai fita suka taso gareshi, amma saiya d’aga musu hannu.
yana k’ok’arin bud’e motarne Jakadiyya ta iso inda yake…
Cikin rissinawa tace, “barka da hantsi galadima”.
Bai iya amsa mataba, sai hannu daya d’aga mata kawai.
Kuma rissinawa tayi tace, “Galadima takawane yabani izinin in kirayeka”.
Kallonta yayi zaiyi magana saikuma yay shiru ya maida motar yarufe tareda cillama Muftahu dake bayansa kyes d’in.
Muftahu ya cafe.

Komawa yayi 6angarensa yashiga wanka, kusan mintina 40 sannan yafito sanye da bathrobe fara k’al, bai wani d’au dogon lokaciba yay shiri cikin k’ananun kaya, yayi k’yau sosai, ya feshe jikinsa da turarensa masu matuk’ar k’amshi.
Wayarsa ce tashiga ringing, baibi takantaba yacigaba da hidimarsa, dama tun yana bathroom yakejin ana kiransa.
ta baya yabi inda bayi bazasu isheshi da gaisuwa gaisuwa d’innanba, dayake sarki yana gida, yau ana hutun zaman fada saboda tunawa da abinda yafaru da tsohon sarki (mahaifin Galadima Sameer) duk ranar litinin tana zama ranar daba’a zaman fadane…

?.?.?.?.?.?.?.?.?.?

Kowa ya ganmu yasan muna cikin rud’ani, da k’yar aka samu innarmu ta farfad’o, sai dai an hanamu mushiga mu ganta.
Gidanmu kam abin nema yasamu, hakama cikin anguwa, saboda yad’uwar labarin a social Media.
Muna zaune a falo duk mun zabga uban tagumi dagani har munubiya, idanunmu duksun kunbura saboda kuka, Ni ba abinda yafaru a jaridar ne yafi damunaba, halin da mahaifiyarmu ke ciki shine babbar matsalata, bamuda kamarta duk duniya, bazanso wani Abu ya sameta asanadinmu ba, bayan bak’incikin datake k’unsa agidanmu kuma.
Kamar anjeho mama Rabi’a itada ya Marwan suka shigo falon. mun tsorata kwarai da gaske, cikin daka tsawa mama Rabi’a take tambayarmu innarmu.
Hakanne ya tabbatar mana da suma labarin yaje musu. munubiya ce tabata amsa cikin kuka, sannan tace “wlhy mama sharrine, ba abinda yafaruba kenan n……”.
Saukar marin datajine yasakata rufe bakinta 6am, kafin na tantance mai Marin nima naji saukar nawa.
Ko kad’an yaa Marwan baiji tausayinmu ba, saida yamana lik’is da duka, dak’yar Dady ya kar6emu a hannunsa, amma baba k’arami da Abbanmu casukai yama k’ara mana.
‘Yan gidanmu duk sunfito cirko-cirko a tsakar gida, kowa na tofa albarkacin bakinsa, gashi akwai sauran ‘yan biki dabasu gama tafiyaba.

Iyayenmu da yayinmu duksun taru akanmu, ana tambayarmu wacece daga cikinmu.
Kafin Munubiya tayi magana nayi saurin cewa “kuyi hak’uri iyayena, nice munaya a gaba d’aya hotunan, wlhy kuma tsautsayine, amma ba ainahin abinda yafaruba kenan”.
Munubiya zatayi magana nayi sarin rik’e hannunta alamar kartace komai, “karki d’aurama kanki abinda ba laifinkiba Munubiya, nice Munaya na aikata….”
Itama cikin kuka tace “wlhy bake baceba, nice, wlhy nice”.
Nima nace “wlhy nice”.. ….
Tsawa Abbanmu yadaka mana, atare mukayi shiru yace “nasan dama Munaya kece, Munubiya bazata aikata wad’annan abubuwan ba, dukda kema d’in nayarda da tarbiyyar dana baki, amma bansan miya kaiki ga aikata hakanba, shiyyasa ranar idi mukaita nemanki, Ashe kinacan kina d’akko mana magana, tunda aure kikeso zan miki, nabaki nanda sati 2 kacal, inbaki kawomin mijiba zan had’aki dadu Wanda nayi niya”.
Yana gama fad’ar haka yatashi ya fice, baba k’arami ma ficewarsa yayi.
Wani kuka mai tsuma rai muka kuma fashewa da shi, musamman ma ni danasan nasaka kaina a tarko, amma hakan shine dai-dai, bazan amince naga ‘Yar uwata cikin bak’in cikiba, insha ALLAH koma minene zan jureshi, muniya tanada hak’urin dazai iya cutar da ita akan wannan lamarin, gashi baba yafurta in ban fiddo da mijiba zai auramin Wanda yaso, to idan hakan ta kasance kan Munubiya wane hali kuke tunanin zata shiga? Musamna dabamusan gidan dazamu iya fad’awaba tunda nasan abinda Abba yafad’a tabbataccene, dan shi baya magana biyu.
Dady ne yashiga lallashinmu, tareda mana nasiha da nuna mana illar abinda muka aikata, musaman ma ni. ya Marwan kam sai antayamin harara yakeyi shida yaa hameed.

Yinin yau kam kuka muncishi harmun godema ALLAH, mu duka kwance muke rijif da zazza6i, har akayi isha’i bamu kumajin motsin kowaba, mukuma muna d’aki kwance mu duka k’udundune a bargo.
Su Aryaan sunacan nanuk’e da innarmu dake 6angaren Abbanmu har yanzun, dan haka 6angarenmu saiya kasance tsitt. a ranar dai haka muka kwana babu lafiya nida Munubiya, babu mai iya taimakon wani acikinmu, ga yunwa ga damuwa ga ciwo.
Zuwa asubahi ko salla kasa gashi muyita mukayi, dan k’arfinmu yagama k’arewa…??

?.?.?.?.?.?.?.?.?.?.?

Ya isa sassan mai martaba, bayan masu tsaron k’ofa sun gama kwasar gaisuwa suka masa iso.
Izinin shiga mai martaba yabashi.
Falone k’aton gaske, Wanda nikaina banmasan yanda zan musalta k’yansa da girmansaba, ga kujeru rukuni-rukuni, ko ina yagama d’umamewa da sanyin AC, gawani k’amshi na musamman.
daga can gefe na hango mai martaba kishingid’e bisa wani lallausan carpet da aka k’awata da tarin tum-tum, gabansa tirene dake d’auke da jug na glass cikeda zo6o, sai wani k’aramin kwano na tangaram Wanda bansan miye acikiba, saikuma k’aramar butar shayi awani tiren daban, da mug guda d’aya.
Fuskarsa d’aure take tamau alamar yana cikin 6acin rai, ga jarida a hannunsa.
Cikeda girmamawa Galadima ya zauna a gefen dardumar, ya tankwashe k’afafunsa sannan ya risina yana fad’in “barka da rana ranka ya dad’e”.
Mai martaba bai amsaba, sai ma cilla masa jaridar hannunsa dayayi.
Galadima yabi jaridar da kallo batareda ya d’aukaba.
“ka d’auka ka duba mana, dan inason sanin gaskiyar zancen”.
Kan galadima a k’asa yace, “takawa nima yanzu Muftahu yakawo min nagani, nama fito zanje ga gidan jayidayne kiyanka ya isomin, amma wlhy Abba ba gaskiya baneba, ka…….”
Da sauri mai martaba ya d’aga masa hannu cikin 6acin rai “mi kakeson fad’amin? kana nufin zasu buga abinda baka aikata bane? ai sunsan gidan daka fito, haka kawai bazasu maka sharri ba kodan gudun abinda zaije ya dawo. Sameer yanzun nan da mutuncinmu kaje ka aikata wannan son zuciyar domin ka 6atama wannan masarautar suna? Lallai kacika d’an halak, kuma kayi dai-dai, tabbas ka kafa tarihin dawani bai ta6a yin irinsaba a wannan masarautar, Dama Ashe kabud’e waccan plaza d’inne domin son zuciyarka? Yanzu da ace lafiyar Yaya k’alau wane irin hali kake tunanin zai tsinci kansa? Ina ganinka shiru-shiru Ashe kaid’in shaid’anine”.
Runtse idanu Galadima yayi zuciyarsa na k’una da kalaman mai martaba k’anin mahaifin nasa, amma yagaza furta komai, sai idanunsa daketa k’are rinewa zuwa jajazur.
Har mai martaba yak’araci fad’ansa yagama Galadima bai iya furta komaiba, kansa ak’asa ko motsi baiyiba.
“katashi kabani waje, k’arfe 8:30pm akwai meeting, saika jira hukunci daga mama Fulani ”.
Rissinar da kai Galadima yayi yace, “ALLAH ya huci zuciyayka, na bayka lafiya”.
Banza mai martaba yay masa, yatashi yafice shikuma cikin k’unar zuciya.

Yana fita wayarsa ta fara ringing, ransa adagule yacirota da nufin kashewa gaba d’aya, saiyaga *_My dear Momma_* rintse idanunsa yayi ransa nakuma suya, yasan tabbas labari ya Isa gareta kenan, wannan wace irin masiface, mahaifiyarsa dake wata k’asa har ankirata an Sanar mata, ko halin datake ciki baza’a kallaba?. Kasa d’aga wayar yayi harta tsinke.
Tabbas duk Wanda yake gidan jaridarnan saiyayi Dana sanin saninsa arayuwa.
Kiran Momma ne yakuma shigowa, yanzuma bai d’agaba harya k’arasa sashinsa.
Sai da ya zauna sannan yafara k’ok’arin nemanta cikin suyar zuciya data ruhi……………???

 

To masu karatu, ko wanene da wannan aika-aikar? tabbas yau Munaya tabani matuk’ar tausayi daga ita har munubiya, kai harma Galadima.??????

Kumuje zuwa danjin Yaya kuma zata kasance?????.

 

 

Yanzufa aka fara wasan?????????????????????????

 

 

 

*_YA ALLAH ka gafartama iyayenmu??????_*
[4/16, 9:53 AM] +234 811 277 0720: *_Typing??_*

 

*_HASKE WRITERS ASSO…??_*
_(Home of expert and perfect writer’s)_

 

*_?RAINA KAMA……!!?_*
_{Kaga gayya}_

 

*_Bilyn Abdull ce????_*

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply