Hausa Novels Raina Kama Book 3 Hausa Novel

Raina Kama Book 3 Page 1-2


Raina Kama Book 3 Page 1-2
Viral

Book 3~ ????1??2?

……………Saida suka fara tafiya sai Harun yafara jin tamkar k’amshin turaren Galadima yakeji, mamaki ya kamasa, ya kalli gaban motar yana fad’in “lawwali nikam kaji minakeji kuwa? k’amshin Sameer fa”.
Murmushi Galadima yayi, baice komaiba sai “Uhmm”.
Hakan yakuma d’aure kan Harun, kamar zai sake magana saiya fasa, ya d’auki wayarsa domin son kira yaji ina Galadima, yasan Abu dolene ke fiddashi da daddare daga masarauta, amma sai kira ya shigo a wayarsa, k’aramin tsaki yayi Dan ba’a ko’ina yake d’aga wayaba, ya yarda da lawwali drivern babansa waziri amma bakomai yake barin ya saniba, ganinfa an damesa da kiran saiya d’aga. Da sauri ya janye wayar a kunnensa yana lek’o kansa gaban motar danya tabbatar. shin ina tunaninsa ya tafi dahar ya iya gaza banbance lawwali da Sameer?.
yace “Sameer!”.
Galadima dake tuk’insa hankali kwance yana kuma sauraren wayar Harun ta abinda yasa akunne, saboda ya saita duk wayar dazata shiga ta Fita a war Harun saiya shigo wayarsa shima kota fita yace, “Uhmyim”.
A tsorace Harun yakoma baya ya bigi seat da k’arfi, babu abinda zuciyarsa keyi sai dukan 100-100, wayarsa ya jawo jiki Na rawa yafara k’ok’arin kiran wani.
Galadima yay murmushi, cike da izzar k’asaita yace, “bar wahal da kanka my dear friend, duk wata waya dazaka kira a yanzu wayata zata shiga”.
Harun yay jifa da wayarsa a kujera jiki yana rawa, batare da wani tunaniba ya mik’e kawai ya shak’e Galadima, da hannu d’aya Galadima yake driving, hannu d’aya kuma yana k’ok’arin kare kansa daga shak’ar da Harun ya masa.
Da k’yar yasamu ya gangara gefen titi, yasaka hannunsa d’aya ya bigi gefen cikin Harun daya samu damar shak’esa da k’yau, Dan numfashin sa harya fara fita afisge.
Dukan cikinsa da Galadima yayi yasakashi sakinsa da sauri, Galadima ya juya yakuma naushin bakin Harun saiga jini, dama bai gama dawowa hayyacinsa ba daga dukan cikinsa da yayi.
Harun ya fad’a saman kujera yana rik’e ciki da shafar hancinsa dayaji yana yoyo, kallon hannunsa yayi saiyaga jini, ya zaro ido cikin matuk’ar mamakin shi Sameer ya fasama baki, yo ko danbe zasuyi ai babu abin zai d’auka a jikinsa, (Dan shima Harun d’infa ba bayaba).
Galadima daketa huci ya dafe sitiyari da kife kansa ya kuma tada motar a harzuk’e ya fara tafiya cikin tsananin gudu.
Cikin hakki da fidda numfashi a wahalce Harun yace “Sameer n..n..ni ka daka? harda fidda jini?”.
Banza Galadima yamasa yacigaba da tuk’insa, Harun ya kuma yunk’urawa zai tashi amma saiya kasa, saboda ba k’aramin duka Galadima ya masa a gefen cikiba, wajen ya k’ulle, dole ya koma ya kwanta yana cije baki da matse ido, hannunsa rik’e da wajen har yanzu.

Suna isa inda ya nufa yay horn, saiga Nuren da kansa yazo ya bud’e masa k’ofa, a fusace ya shiga gidan, shi Nuren ma har yana tsorata.
Yana tsaida motar ko kashewa baiyiba yabud’e ya fito a harzuk’e, inda Harun yake ya bud’e ya jawoshi, yakuma kai masa naushi, shima ya kai masa dukda azabarda cikinsa ke masa.
Nuren da Muftahu sun iso wajen a hanzarce, Dan ganin danbe Na Neman hark’ewa tsakanin aminai guda biyu, Nuren yaja Harun, shikuma Muftahu Galadima.
“Waishin mikukeyi ne haka brother? Da girmanku da ajinku kuke danbe? danbe fa? Wannan wane irin kuma abin kunyane? Lallai da y’an jarida zasu samu labari gobe dasunci kasuwa sosai…..”
Hankad’a Muftahu Galadima yayi baya, yay taga-taga zai fad’i, bai kuma kallon ko wanne a cikinsuba ya nuna Harun da d’an yatsa, “Mara kwakwalwa kawai, kafin ni ka kasheni ninan zan kasheka daga kai har munafikin ubanka, dak’ik’i kawai”. yana gama fad’ar haka yabar wajen zuwa cikin gida, taku yake kamar wani bajimi ya fito za6en sarauniyar k’yau.
Daga Nuren har Muftahu da kallon mamaki suka bisa, shi kansa Harun maganar Galadima tasakashi girgiza, kardai guy d’innan yana sane da wanene ni tun tuni amma ya k’yaleni? da k’arfi ya fisge shima daga jikin Nuren yana kaima Muftahu duka, “Munafiki dakai zan fara”.
Saurin kare kansa Muftahu yayi, Nuren yakuma yunk’urin rik’e Harun, danshifa abin yafara d’aure kansa, kowa yasan Harun aminin Galadima ne Na kusa, yau kuma miya had’osu haka? harda zancen kisa? Galadima yanada matuk’ar zuciya, idan ransa ya 6aci babu ubanda ke gane kansa….
Fad’a dai Neman komawa yay ga Muftahu, saida su Ameer sukazo suka rirrik’e Harun, cak suka d’aukesa yana fisge-fisge da fad’ama Muftahu magana suka shiga dashi ciki.
Nuren ya kalli Muftahu dake murmushi yana gyaran kwalar rigarsa.
“Amma mike faruwa kuma haka? Yau Sameer ne ke fad’a da Harun?”.
Muftahu ya dafa kafad’ar Nuren, “’Dan uwa akwai abinda baka Sani bane, amma Na tabbatar yanzu zama sanshi”. Yana gama fad’ar haka yayi gaba abinsa, shima da kallon Nuren ya bisa, kenan shima yasan dalilin fad’an nasu ashe? jiki a sanyaye ya nufi wajen motar ya kashe sannan ya nufi gidan shima, a yanzu kam lamarin wanan case yafara rud’ar dashi, dan yanda Sameer keta abubuwa a tsakaninnan basuyi kama da nasa zarginba shi.
Galadima Na kwance cikin kujera doguwa, tunda ya shigo anan yazufe, duk yanda zuciyarsa taso 6aci sai kalaman Munaya su danne su (mata kunga amfanin hikimar zance ga mazajenmu ko), zantuttukanta suka shiga dawo masa a rai daki-daki, tabbas a yanzu ba fushinsa bane abin buk’ata, jarumtar hak’uri ce, kamar yanda ta fad’a idan kwallo ta 6ata ba daina wasa akeyiba, wata kwallon ake d’auka ayi da ita, cikin lumshe ido ya ciji lips nashi yana wani miskilin murmushi.
Daga Muftahu har Nuren dai ido suka zuba masa, ga Harun da aka saka a wani d’aki aka kulle sai bugun k’ofa yake yana fad’ar magana masu zafi akan Galadima.
Mik’ewa Galadima yayi yana gyara rigarsa, ya kalli su Muftahu yana cire safar hannunsa, “bara naje gida”.
Abinda kawai ya fad’a kenan yay ficewarsa.
Tamkar sokaye haka suka bishi da kallo, yana fitowa ya iske sarkin mota a waje yana jiransa (Ashe dama ya biyo bayansu) da hanzari ya bud’e masa motar ya shiga, Galadima ya zauna yana sauke ajiyar zuciya a cikin kujera. Har suka Isa masarauta babu Wanda ya iya tankawa.
Sarkin mota nayin parking baima jira an bud’e masaba ya bud’e da kansa ya fice, hadimai masu tsaron sashen Na masa barka da zuwa amma ko kallo basu isheshiba.
Kai tsaye sashen Munaya ya nufa, babuko sallama balle Neman iso ya danna kai cikin d’akin. Laraba da samba da yara duk sunyi barci, Munaya kam takasa hakan, sai safa da marwa takeyi tun d’azun, taje d’akin Galadima yafi sau 7 amma bai dawoba, hankalinta a tashe yake da tunanin ina yaje a darennan? shida idon mak’iya kullum a kansa yake, dama kad’an suke nema ta cuta masa?…..
Cak tunaninta ya tsaya lokacin da taji anyi sama da ita, zata fasa ihu yace, “yima mutane shiru”.
A hankali yayi maganar, Dan haka ta had’iye ihunta cikin sauri da mamakin abinda yayi, yana fitowa falonta ya ajiyeta yaja hannunta zuwa sashensa.
Babu abinda zuciyarta takeyi sai dukan 50-50, miye yashiga kansa haka wai?. Basu tsaya a falo ba sai bedroom d’insa, dama tun a hanya ya fara cire jacket d’insa, suna shigowa yana ida cirewar, yay wurgi da ita a tsakar d’akin yakuma d’aukar Munaya suka fad’a saman gado.
Tsoronsa yakuma shigarta lokacin dataji ya sakata jikinsa ya matseta, kaikace zai maidata a cikine.
Cikin matse baki da sakin k’aramar k’ara tace, “wai minene haka yalla6ai?”.
“shiiii!!”. Yafad’a yana d’ora yatsansa d’aya akan bakinta, batada za6in daya wuce tayi shirun, sai zuciyarsa dake wani irin bugu da k’arfi, hannunta ta saka a saitin zuciyar tana karanto addu’a.
Duk abinda takeyi yana jinta, hawaye masu zafi suna kwarara masa a ido, saidai tacan gefene shiyyasa Munaya bata saniba, tsawon lokaci muna a haka, har zuciyarsa tafara dai-daita bugawa, takoma normal, sai ajiyar zuciya da k’ok’arin dai-daitar numfashi kawai yakeyi, a haka barci ya kwasheshi, saida nabari barcin yayi nisa sannan nazare jikinna cikin dabara da k’yar nabarshi, Dan Dana motsa saiya k’ara k’ank’ameni, da k’yar dai Na kwaci kaina Na maye masa gurbina da filo, cikeda tausayawa nake kallonsa ina hawaye, a haka Na cire masa takalman k’afarsa, naja bargo Na lullu6a masa, addu’ar barci nayi Na tofa masa, gudun karna ta6ashi ya farka na tofa d’in, Na kashe wutar d’akin nabar da barci kawai na fice ina share sauran kwalla. ‘Dakin da Sauban yake kwance na kwankwasa, yataso cikin mayen barci ya bud’e, ganina yasashi watstsakewa babu shiri, “Aunty gimbiya lafiya kuwa?”.
“lafiya lau Yaa Sauban, cazan dama kaje d’akin Abban su Amaturrahman ka kwanta tare dashi, naga kamar bayajin dad’i, ba’asan mi dare zaiyiba”.
Kansa ya jinjina yace, “to aunty”.
https://2gnblog.blogspot.com/

Tunda na koma d’aki sai damuwa ta katantaneni, na dad’e ban barciba, daga k’arshema saida na saka karatun Qur’an da k’ara kad’an sannan barci ya saceni batare da na shiryaba.

https://2gnblog.blogspot.com/
*_Washe gari_*

Tunda asuba kasa hak’uri nayi na nufi d’akinsa.
Mamaki da kunya suka kamani, Dan ganinsa ragal ya fito wanka, gashi d’aure yake da towel, Sauban yafita saishi kad’ai.
Da sauri na juya da nufin komawa amma sai naji an rik’o hannuna, kasa juyawa nayi, yamatso dani ya saka a jikinsa, laimar ruwan da k’amshin sabulun sai suka sakani lumshe ido, ya d’ora hannunsa d’aya bisa cikina ya rik’e hannuna da d’aya, kansa a dokin wuyana yace, “Thanks matar Contract”.
Kamar bazanyi magana ba sai dai nayi, Dan karna barta ta kasheni, nace, “Tausayinsu Abie ya sakani, kaji mijin Contract”.
Murmushi yayi mai sauti yana shinshinar dokin wuyana, hannu na saka na ture kansa ina fad’in “ka dinga kula fa”.
Ya kuma maida hancinsa a wajen, cikin tura hannunsa a rigata yace, “Nida sadakina gwaggo tsiwa”.
Ban tanka masaba na fisge jikina, shima saiya barni yana wani bina da ido cikin k’ank’ancesu da miskilin murmushi. Saida naje bakin k’ofa na tsinkayi muryarsa yana fad’in “Kinzo kawai kin karyamin alwala”.
Babu shiri na juya Na kallesa, amma saiya basar tamkar bashine yayi maganarba, yama juya ya nufi hanyar bathroom.
Kwafa nayi na ida ficewa.

Bayan Galadima yakuma d’auro alwala ya fito saiya iske tea a mug da da cake a k’aramin bowl, ya d’anyi luuu da ido tamkar zai lumshe saikuma ya bud’e yana murmushi da shafar kansa. jallabiya ya saka yay salla a d’aki, bayan ya idar yazauna yasha tea d’in, dama jiya baici komaiba ya fita, yunwa yakeji, koda ya kammala saiya fice abinsa.
Sashen mai martaba ya nufa hadimai nata zubewa suna kwasar gaisuwa, sukan samu amsa iya kan la66a da d’aga hannu, da haka harya Isa.
Saida jakadiya tamasa iso sannan ya shiga, a k’aramin falon mai martaba dayake hutawa idan baya buk’atar ganin kowa har matarsa ya iskeshi, yayi mamaki kwarai, dan inhar mai martaba ya shiga falonnan kofa mama Fulani sai dai tayi hak’uri da ganinsa.
Yana kishingid’e saman tattausar darduma da aka k’awata da kilisa ta asalin sarakuna masuji da tsantsar mulki, ga tumtum da sauran kayan k’awa, an saka na’urar dake d’umama d’aki kad’an saboda yanayin sanyin safiya musamman na wannan lokacin da bazara take kunno kai.
Da hannu mai martaba yayma Galadima nuni da kusa dashi, Galadima yaje ya zauna yana tankwashe kafafu, cikin girmamawa ya risinar da kai yana fad’in “barka da asuba Abba”.
Mai martaba ya jinjina kai yana lumshe ido da amsa cikin fad’in, “barka dai yarona, ina d’iya ta da abokaina da amarya?”.
Murmushi Galadima yayi, kansa a k’asa yace, “duk suna lafiya Abba”.
“Masha ALLAH, yaya jikin naka to?”.
“Na warke ai Ranka ya dad’e”.
“To Alhmdllh, haka akeso ai, Yaya maganar tafiyar ita mai d’akin naka? duk da dai abin yazo da tsoratarwa yakamata a ayi yanda kowa yakeyi Sameer, ALLAH shine mai tsarewa, kuma zai tsaresu, domin ransu a hannunsa yake, idan an hanata zuwa an tauye hak’inta, zakuma ta iya ganin hakan kamar ita danba wata baceba, nagama shirya komai yau za’amata rakkiya kamar yadda akema kowacce mace dake aure a masarautarnan”.
Cikin had’iye yawu da wani Abu daya tokare mak’oahinsa yace, “to Abba, ALLAH yasa hakan shine mafi alkairi, nima zuwa yamma zan koma India, akwai abubuwan da zanyi na kwanaki biyu zuwa uku zan dawo”.
Mai martaba yay murmushinsu irin na manya, cikin jinjina kai ya ajiye k’aramin mug d’in hannunsa mai k’yau yana fad’in “ALLAH ya taimaka, Maybe kana dawowa nima zanje insha ALLAH”.
Galadima yace, “ALLAH ya kaimu”.
Daga nan sund’an cigaba da ta6a hira, a haka jakadiya ta shigo nemawa matawalle iso, yabada izinin a shigo dashi. bayan shigowarsa da yin gaisuwa sai suka d’ora hirar su uku gwanin sha’awa da birgewa. da Wanbai yazo gaida Sarki jakadiya ta sanar masa ai Galadima da matawalle suna ciki, shi komawa yay wai yafasa gaisuwar, jakadiya ta ta6e baki tana 6azgar goro da fad’in “kaikuma kasani gwandararren banza, kai koma y’ar k’autarnan ta jinin girma ba iyawa kaiba, dakasha kanu da sirrika a wajena wlhy”. duk a hankali take maganar yanda kowa bazai jitaba??.

Saida gari yay tangaran da haske sannan Galadima da matawalle suka fito, suka bar Sarki zaiyi shirin zuwa fada.
Koda Galadima ya dawo sashensa wajensu Munaya ya nufa, saboda jiyo kukan yaransa.
Ya iske Ashe wanka ake musu, Munaya kuma tana wankan itama, sai Samha da Sauban keta faman jijjigarsu a kafad’a, Abdurrahman kuma yana hannun laraba tana masa wanka. duk gaidashi suka shigayi, ya amsa musu cikin jinjina kai da lumshe ido, baki kam ko motsi bai yiba. Samha ta kawo masa Amaturrahman dake hannunta, bai d’auketa ba, ya dai shafa kumatun yarinyar yana murmushi, sai tayi shiru tana kallonsa kaikace tasan wanene.
Murmushinsa ya fad’ad’a yana jan d’an hancinta.
Samha tace, “Uncle Sam ALLAH Amaturrahman tafi su Abdurraheem wayo, shiyyasa nafi ji da ita”.
Murmushi yakumayi, ya shafi muskar Samha itama tareda d’an bubbugawa, hakan ya sakata fahimtar yau babu y’an maganar a kusa. Saima ya juya yay ficewarsa abinsa daga d’akin.
d’akinsa ya koma ya sake wanka da shirin fita cikin wani d’anyen boyal fari tas, anmasa surfani da golden color sai walk’iya yake da d’aukar idanu, takalmansa na ainahin masu sarauta half cover da lankwasarsu a gaba suma fari da kwalliyar Golden d’in, ya matsa gaban Mirror yana kallon kansa da d’aura a gogo, ganin komai dai-dai ya d’auki turarensa ya fesa kala-kala sannan ya zuba wayoyinsa a aljihu da d’aukar links d’in hannun rigar yafice yana k’ok’arin sakawa.
Da Sauban sukaci karo, yabisa da kallon birgewa, kai manyan kaya na matuk’ar k’awata k’yawun dirin yayansa, kuma sai akayi sa’a yana masifar sonsu, Dan ko’a India yakan sakasu fiyeda k’ananum kaya ko suit.
Zungurinsa galadima yayi yana fad’in “baka sanni bane?”.
Ajiyar zuciya Sauban ya sauke, yana sosa k’eya, “Yaa Sam please one pic.. Mana”.
Galadima ya hararesa zai cigaba da tafiya, da sauri Sauban yakuma had’e hannanyen sa alamar rok’o.
Galadima yay guntun tsaki, “kaiwai shin mikake da hotone? kullum baka gajiya da tarasu”. ya k’are maganar yana d’an dafe goshi.
Shidai Sauban ya marairaice, babu yanda Galadima ya iya dole ya yarda yamasa hoton, harda zuwa sukayi tare. Shidai Galadima ya girgiza kai kawai ya nufi sashen Munaya.
Ya isketa taci gayunta cikin doguwar riga ta popul d’in material, tayi d’as da ita, bazaka ta6a kallonta kace itace da yara uku ba, tana zaune tana bama Abdurraheem nono, sauran kuma suna hannun Samha, laraba tafita..
Zama yay kusada Munaya ya kar6i sauran yaran a hannun Samha, ya d’an rankwafa kan Munaya yana kama hannun Abduraheem data cire a nono ta gyara rigarta, da sauri ta d’ago tana kallonsa da mamakin koya manta Samha na d’akin dazai wani shige mata, shima kallonta yayi yana d’age gira d’aya fuska babu walwala.
Hakan kam saiya bama Samha damar yimusu hoto jiki na rawa, Dan ba k’aramin bada kala sukayiba??.
Hasken camera d’in ya saka su d’agowa duk suka kalleta, wani ta sake k’yastawa ta fita da gudu.
Munaya ta saka hannu tana toshe bakinta saboda dariyar dake Neman kufce mata, shikam kwafa yay yana fad’in “zan kamaki ne Dan k’aniyarki, yara duk sunbi sun rainani”.
Dariyar Munaya ta fito Dan takasa rik’eta, hararta yayi dukda dariyar tata tamasa k’yau, yad’an rankwasheta akai, “kece kika sakasu ko? dama ai Sauban shima titsiyeni yayi”.
Daina dariyar tayi ta turo baki gaba tana tsafa inda ya rankwasheta, “yoni mizanyi da wani hotonka malam”.
“waya Sani ko sokike ki mallakeni”.
Baya Munaya tayi tana kallonsa, ya wani basar tamkar bashine yay maganarba, ya hauma yaransa wasa dukda basusan mima yakeyiba.
Dan gwarar da Abdurraheem tayi gefensa tana mik’ewa, “Humm, ko inason mallaka bazan mallaki abinda bai minba”.
Yi yay tamkar bai jita ba, yabama yaransa gaba d’aya hankalinsa.
Munaya taji haushin k’in kulatan da yayi, yakai mintuna 30 a d’akin kafin yay kissing kumatunsu ya ajiyesu. inda Munaya take tsaye jikin mirror tana kallonsu ya nufa ta d’auke kanta tana maidawa gefe.
Gabanta ya tsaya daf har tanajin hucin numfashinsa, hannunsa duka cikin aljihun rigar boyal d’insa 3Quarter, “Na dawo gareki, idan kin Isa maimaita abinda kika fad’a”.
Tasan halinsa da makomar maimaicin, shiyyasa ta ta6e baki tana cewa, “aini ba’a sakani abinda ban niyaba”.
Bakinsa ya ta6e yana murmushin gefen baki, “matsoraciya kawai”. yafad’a yana juyawa zai fita, saida yaje bakin k’ofa sannan ya kalli agogonsa, “kuzama a shiri, dana dawo….”. Bai k’arasa ba yay ficewarsa.
Da mamaki Munaya tace “daka dawo? To daka dawo za’yi mi?”. Batada mai bata amsa dan haka ta share ta koma kusada yaran.

Da hanzari Su sarkin Mota suka mik’e, aka bud’e masa mota ya shiga, sashen da aunty Mimi take suka fara zuwa, ya shiga Dan yasan tana nan tanajin haushinsa akan fitar jiya.
Aiko a falo ya isketa zaune a dining tana breakfast, hadimanta nata kaikawon gyara 6angaren, dining d’in ya nufa yaja kujera ya zauna, idonsa a kanta, ta shareshi tamkar batasan dashiba, shima baice uffanba ya d’auki spoon ya saka a plate d’in da take cin Arish, harararsa tayi, shima ya rama yana ta6e baki da basarwa ya cigaba da cin Arish d’in hankali kwance.
Kallonsa ta tsaya yi kawai da mamaki, takai hannu ta daki damtsen hannunsa, shafa wajen yayi yana bud’e baki, saikuma ya kwa6e fuska alamar shagwa6a.
Dariya Aunty Mimi tayi tana sake dukansa da fad’in “kadai girma rigimamme”.
Yay Murmushi tareda kwantar da kansa gefen kafad’arta, a hankali yace, “kin daina fushin dani to? kinsanfa babbar ya uwa”.
Murmushi tayi itama, ta shafa kansa tana fad’in “bazan iya fushi da kaiba ai my k’ani”.
Yace, “Nagode Auntyna”. yafad’a yana tashi zaune sosai.
Mug d’in tea d’in hannun ta ta mik’a masa, ya girgiza kansa.
Tace, “miyasa?”.
Iska yad’an furzo daga bakinsa, yace, “K’anwarki tamin d’ura tunda asuba Dan mugunta”.
Aunty Mimi tayi dariya, “’Dan rainin wayo, inama laifin daka samu mai maka d’urar, kama tunamin, Yaya maganar tafiyarta gida?”.
Saida ya rage fara’a sannan yace, “mungama magana da mai martaba” ya kalli agogonsa da cigaba da fad’in “yanzu zand’anje wani waje, insha ALLAH zuwa 2 to 3 zan dawo, basai yamma bane?”.
“To Alhmdllh, naji dad’i da mai martaba yasa baki, dan da wannan taurin kan naka bazaisa ka saurari kowaba”.
Mik’ewa yay yana ta6e baki, tareda cewa nayi nan, saina dawo, kudai zama cikin shiri jirgin 7:30pm zamubi”.
“ALLAH ya tsare ya bada sa’a”.
“Amin” ya amsa yana ficewa.
Aunty Mimi tayi murmushi da binsa da kallo, tana tausayin k’aninta da gwagwarmayar rayuwa ta zauna jiransa tunkan yazo duniya, ALLAH dai ya kawo iyakar komai dan shima yasamu kwanciyar hankali.

Nace, “amin aunty Mimi mu??????”.

 

*******************

Koda Galadima ta fita waya ya kira, Wanda suke wayar ya tabbatar masa k’arfe 11:00 dai-dai Alhaji Shehu Darma zaibar gidansa.
Galadima yay murmushi, sannan ya kalli sarkin mota.
“Baseer!”
Sarkin mota ya amsa da “na’am Ranka ya dad’e”.
Kwantar da kansa yay jikin seat d’in yana cewa “Zamu banbanta tafiya dasu, dan haka a plaza zamu kar6i mota hannun Saleem, da ita zamu samu Shehu, itace irin motar dazai shiga”.
Cikin mamaki Sarkin mota yace, “Amma ranka ya dad’e ta Yaya? Kasanfa yanada bodyguards kuma masu had’ari”.
Murmushi Galadima yay yana d’agowa, yace, “Duk had’arinsu Muhammad Sameer Saifudden yafisu, kaidai yi abinda nace”.
Da to kawai sarkin mota ya amsa cikeda girmamawa…………….???

 

??????Galadima ma yazama kidnapper, readers saiku kiyaye???????????????????????????.

_Masu nemo picture’s d’in mutane suna cewa wane da wane canta matse muku, nidai banyi cover d’in RAINA KAMA ba, sannan ban fad’i kamannin mutum ko guda d’aya a buk d’inaba balle mutum yace na siffanta da Wanda kuke yawo dashi, naga wasu suna fad’ar duk maganar datazo bakinsu akan hoton babu taunawa, Ku kama kanku bansan rainin hankalinnan, yafara isata hakanan kuma, bazai yuwu kulum ina asarar data da lokacina ba sannan kuzauna kuna yankama mutane magana batare da kun duba cancantar fitarta ba, please ya Isa haka, ya isa Wanda bazai iyaba babu lali babu tilas, idan kungama wannan kunga batakai mukuba saikuma Ku tsokalo wannan, shin wane irin rayuwane hakan dan girman ALLAH??????, salon cikin Luke d’auka ko k’alk’yalin duniya?, bazaku ta6a magana akan Abu mai muhimmanci da amfaniba sai Mara amfani._

 

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*??????
*_typing??_*

?? *_HASKE WRITERS ASSO….._*

*_?RAINA KAMA…..!!?_*
_(Kaga gayya)_

 

*_Bilyn Abdull ce????_*

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply