Hausa Novels Sakayyah Complete Hausa Novel

Sakayyah 37


Sakayyah 37
Viral

SAKAYAH

 

37

 

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

 

 

 

Alamomin infection sune kamar haka. Rashin sha’awa. Ƙaiƙayin gaba Kiji idan ya fara miki ƙaiƙayi kamar zakiyi hauka. Warin ko ƙarnin wurin. Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su ɗan fetso ƙananan ko ƴan manya, melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin ni’ima. Buɗewar gaba, domin har budurwa infection na iya buɗata. Ciwon mara ko ciki mai tsanani yayi al’ada, rashin haihuwa, domin har baƙin mahaifa take toshewa. Ko kirinƙajin wani abu na miki yawo ƙasan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da kuma saduwa, da dai sauran abubudann ban  lissafa. Sune manyan alamomin infection.

Shin kin kuwa san illar da infection keyi miki, amman kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi bulum buƙui da ita a jikinki. To bari kiji illolin infection wato cutar sanyi.

Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin kina tare da ita baki da wata daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi bare wata ni’ima mai Taste, Kinga kenan shinfida ta lalace, in kuwa shinfiɗa ta lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole sunason wurin da kwaranya Zaki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata. Kinga duk tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki nemawa kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa.

KADA KUJI IYA WANNAN DOMIN AKWAI MUGUN INFECTION WANDA BAYA BAYYANA KANSA. Wanda kawai sai dai kijiki, kamar kwalta kin bushe ƙyamas ya dauke miki dukkan sinadaran ni’imomin ki, da sha’awarki, duk kayan matan da zakisha a wofi zadai kiji ƴan uwa da abokan arziƙi da ƙawayenki na yaba miki magunguna GARKUWAR MA’AURATA, amman ke in kinsha jiya I yau,  duk nacin oga da yi miki wasannin bazaki ji sha’awa ba, toh wlh muguwar infection ce, wacce bata bayyana kanta har sai ta gama yi miki rugu-rugu. Ta lalata miki zaman aure. Lokacin da zata bayyana sai kiji Doctor’s suna kira miki, ovarian cyst, ko kuma fibrod duk a cikin chronic infection ne yar uwa.

INFECTION set ɗinmu na kowa da kowane Mata, Maza, Bazawara, Budurwa, Maijego, Yara, Ke yar uwa Wlh har maiciki zatasha, bashi da matsalar komai na Gargajiya ne mai rakake INFECTION ya fito miki dashi, wlh duk nacin infection koda na cikin mahaifane bi’izinillahi ta’ala zaki rabu dashi, cutar infection cutace mai masifar naci, so yar uwa kana dole ki nace masa da maganin set ɗin na 10k ne kuma maganin kala biyarne nasha da kala uku na tsarki ɗaya na shafawa ɗaya. Yar uwa idan har kin saya to kiyi ƙoƙarin kisha da mijinki, in akwai abokiyar zama, kisa miji ya saya mata, domin ko kin rabu da shin dai ita tana dashi tofa kin kashe macijine baki cire kaiba, ma’ana zai sake dawo miki, idan kuna da yara suma a saya musu, domin tsoron kada ya riƙa a jikinsu musamman ya’ya mata ya buɗa miki ƴa tun tana ƙaramarta, ki aurar da ita miji na muku kallon lalatattun iyaye da baku iya bada tarbiyaba. Saboda yamayin garin yasa ina raba rabin set ɗin in sa miki komai rabi-rabi 5k amman set ɗin 10k ne. Idan kin san a shirye kike ga account number na nan 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, ki turo kuɗinki kafin kiyi min mgn ta WHATSAPP NUMBER’N na 09097853276 sai ki turo min shaidar biyanki, domin akwaishi Available ko yau kika tura kuɗinki, gobe kayanki zai taho, ina bada sari ko sayan ɗaɗɗaya. Farashin Sari da sauƙi daga kan mutum 3 ko 6 ko 12. Kai ko na mutum 24 kikeso in Sha Allah zaki samu. Please dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn ki bari sai kin shirya. Taku ce dai GARKUWAR MA’AURATA.

 

 

 

Khausar kuwa cikin sanyi da rauni tunowa da M Jameel da ya dawo mata sabo ahankali ta kife kanta abakin gado tafashe da kuka mai cike da fargaba da kuma tsoron Allah.

Kallonta Mommy tayi cike da tausayawa tace.

“Kiyi haƙuri ki daina kuka Khausar addu’a zaki yiwa  Jameelu sannan Insha Allah za acika masa burinsa da wasiyyar daya bari in Allah ya ya nufa”.

Ta ƙare mgnar tare da sauƙe numfashi.

Idanta ta tsaida kan Khausar da har zuwa lokacin kanta ke kife jikin gado cikin tausasawa tace.

“Amma kisa Aranki cewa haƙuri zakiyi da duk rayuwar da zakije ki tarar, sannan wasiyya zaki cikawa Jameel, sannan ki sani shi zaman Aure kansa Ibada ne, koda ana son juna wata ran akanji babu daɗi, bare ke da dama kin san matsayinki a wurin wanda kike ganin kina da ƙarfin guiwar zama dashi,

dan haka kisa Aranki cewa ba lallai ne kiji daɗin zama da Moddibo ba, amma tunda kince kinji kin gani zakiyi abinda Jameel ya buƙata kafin barinsa duniya zan biki da addu’a Ubangij ya tabbatar da al’khairi tunda har iyayensa duk ya gayawa kuma tuni suma sun sa baki a mgnar, kinga ni bani data cewa tunda kun mamayeni”.

Cikin rauni Khausar ta sake fashewa da sabon kuka tabbas gaskiya Mommy ta faɗa ba Lallai tayi zaman daɗi da Moddibo ba tunda baya sonta hasalima koda kallonta ne baya sonyi tuno da hakan yasa wasu hawaye masu masifar zafi suka zubo mata tama sani tabbas cikin uƙuba zata rayu dashi, to amman ya zatayi rayuwa Yah Jameel al’ƙawarin amincewa da batun auren Amininsa.

 

Cikin sanyin murya Mommy ta cigaba da cewa.

“Sanin bake kaɗai Jameelu ya barwa wasiyya ba yasanarwa da Kakar Moddibo sannan ya sanarwa Umminsa da kuma Abbansa nima da farko hankalina ya tashi.

Amma yanzu barina ɗakin Abbanku yake cemin shekaran jiya da daddare Abban Jameel da Malam Ahmad da malam Arɗo sunzo da batun, abinda yasa baiyi mgnar ba Hajja Nana bata bashi dama bane daya mata bayani”.

Wani irin rauni, Kunya,damuwa da rasuwar Jameel ne suka dawowa Khausar alokaci ɗaya.

Cikin sanyi jiki ta miƙe ta nufi ɗakinta tana shiga ta faɗa kan gadonta kana ta cigaba da kuka cikin rauni tasan dai iyaye keyiwa ƴaƴansu auren dole a tarihin duniya, sai gashi ita dai itace zatayiwa kanta da kanta auren dole bisa wasiyar Yan Jameel malami na musamman mai matsayin babban Yaya wanda ita dai da fari har ranta shi takeyiwa kallon mai iya jiɓantan lamuranta.

 

Washe gari da safe Misalin ƙarfe 8:00 Anutse Moddibo ya fito daga falonsa cikin wani ɗanyen Boyel Sky blue Fuskarsa tayi fayau manyan Idanunsa dake lumshe sun sake girma sabida ramar da yayi, sajensa ya sake yawaita yayi fadi da cika, yana kuma ɗan hargitse alamun an kwana biyu ba’a gyarashi.

Kafadarsa na dama rataye da jakar laptop ɗinsa daga zip ɗin gefen wayoyinsa ya zira, sai hannunsa dake riƙe da jakar kayansa, a hankali yake tafiya, yayinda jikinsa ke fitar da sanyayyan ƙamshin tularen sa.

Kai tsaye sashen Innayi ya nufa ahankali Innayi dake breakfast ta ɗago Kai ta kallesa Anutse ya ƙarasa tare da zama gefenta.

Da mamaki take Kallonsa ganin kamar alamar cikin shirin tafiya yake.

Cikin sauri tace.

“Aliyu”.

Kallonta yayi da sauri domin bata fiye kiransa da Aliyu ba sai da babban dalili.

Cikin sanyin murya yace.

“Na’am Innayi”.

Hannunta riƙe da kofin tea tace.

“Ya haka? ya na ganka kamar mai yin tafiya?”.

Kai ya gyaɗa mata tare da tanƙwashe ƙafafunsa kana ya fuskanceta cikin ƙoƙarin danne damuwarsa kana yana mai jin farin cikin zai bar garin Gembila haka nan ya tsinci kansa da jin farin cikin yau dai zai bar Jahar Taraba domin baki ɗaya garin ya fice masa arai cikin sanyin murya yace.

“Innayi ba kama bace tafiyar ce”.

Cike da mamaki ta ɗago kanta kana tace.

“Aliyu tafiya zaka yi amma ban sani ba sai dai in ganka kana fita da jaka haka?”.

Ahankali ya riƙo tafin hannunta acikin nasa cike da mmkia yace.

“Kiyi haƙuri Innayi tafiyar ce nima tazo min a bazata kuma  ba jiya Abban Jameel ya gaya mikiba”.

 

Kai ta girgirza tare da cewa.

“A’a bai gaya minba zakayi tafiya ba, ya dai cemin yana neman al’farma ni kuwa nace umurni kawai zai baka kamar yadda yake bawa Jameel ni na amince duniya da ƙiyama, ban bari yamin bayaniba sabida kar yaga kamar zan hanaƙa yaji ba daɗi. To waima Tafiya zuwa ina zakaje?”.

Cikin kwantar da murya yace.

“Tafiya zuwa Marocco!”.

Cikin tsananin kaɗuwa ta zaro idanunta baki ɗaya lokacin ɗaya ta ƙware tare da fara tari sakamakon ƙwarewa da tayi da dankalin dake bakinta”

Moddibo kuwa ganin yanda ta ƙware yasa yayi saurin daukan kofin ruwa ya miƙa mata tare da cewa.

“Sannu”.

Amsa tayi tasha amma still tarin bai tsaya ba lokaci ɗaya Idanunta yayi ja zufa ya shiga tsats-tsafo mata agaba ɗaya ilahirin jikinta shi kuwa Modibbo ido ya zuba mata tare da jera mata sannu da kuma ɗan bubbuga bayanta kaɗan-kaɗan yana mmkin wasu al’amuran a ranta domin ya sani tsawon zamansu da J ta hanashi zuwa Marocco wanda bai san me dalilntaba, kasancewar sa ba mutum ne mai yawan bincikeba yasa bai taɓa mata musuba ko bincike.

Ahankali ya ke mata sannu cike da tausayawa takai kimanin minti biyar kafin tarin ya lafa sannu Ahankali ta fara maida numfashi.

 

Tana sauƙe ajiyar zuciya ta juya ta kallesa kana tace.

“Marocco!!!! kuma Aliyu?”.

Jinjina kai yayi cikin sanyin murya yace.

“Eh Innayi Marocco zanje amma idan har kin amince, idan bakya so, bazanje ba sai in bawa Abba haƙuri”.

Ahankali ta gyara zama tare da fuskantar sa da kyau kana tace.

“Toh amma mai zakaje kayi a can?”.

Tayi tambayar zuciyarta na mai cigaba da bugawa da ƙarfi.

Lumshe Idanunsa yayi tare da sauƙe Ajiyar zuciya kana yace.

“Abba ne ya nemi al’farma da Inje in kula da Company’nsa sannan kuma jiya daya zo nayi tunanin kunyi cikekkiyar maganar ne dashi kafin ku shiga wurina, shiyasa ni ban faɗa miki ba, ya nemi taimako da Inje in taimaka masa akan batun Company sa buga Abaya, jallabiya, Carpet, Sallayu blanket’s da dai sauransu”.

Kallonsa kawai Innayi keyi yayin da take ji tamkar zuciyarta zai fito saboda yanda yake bugawa.

Cikin sanyi Moddibo ya riƙe Hannunta dake cikin nasa yace.

“Akwai sabbin injinan aiki da za’a sauƙe na Company,  sannan kuma za’a fara aikin dasa Injina  za’a kakkafa toh akwai ɓuƙatar sa ido da kuma kula da abubuwan,  amma Insha Allah bazan wuce wata biyu zuwa uku ba zan zo Innayi”.

 

Girgiza kai tayi tare da jingina bayanta da jikin bango ta lumshe Idanunta kana ta shiga maida numfashi.

 

Moddibo kuwa ido ya zuba mata kana Asanyaye yace.

“Amma Innayi idan har bakyason Inje zan kira Abba in Faɗa masa yayi haƙuri”.

Uffan bata ceba kana bata buɗe Idanunta ba daga ita sai Ubangiji kaɗai suka san mai take tunawa aranta takai kimanin minti biyar ahaka kafin ta ɗago Idanunta ta kallesa kana taja dogon numfashi ta sauƙe tare  da sakin Murmushin mai tarin ma’anoni  sannan tace.

“Bazan hanaka tafiya ba Aliyu, domin ko baka tafi yanzu ba, dama lokacin tafiyar ya ƙarato. na amince kayi masa duk kan abinda Jameelu zai masa daya kasance araye, domin hakan zai rage masa raɗaɗin ciwon rashin Jameelu”.

Kai Modibbo ya gyaɗa yana kallon yanayin fuskartar ahankali yace.

“Toh shikenan Insha Allah zanyi hakan”.

 

Innayi kuwa kallonsa tayi kana cikin sanyin murya tace.

“Amma yanzu-yanzu tafiyar kenan Aliyu?”.

Kai ya gyaɗa kana yace.

“Eh Innayi zanbi jirgi zuwa Abuja ne, in naga komai biza na ya fito zan wuce”.

Jinjina kai tayi tare da cewa.

“Shikenan Ubangiji Allah ya sanya alkhairi Allah ya tabbatar da alkhairi sai nazo”.

Saurin Kallonta yayi cike da Mamaki yace.

“Sai kinzo kuma?”.

Sunkuyar da kanta ƙasa tayi tare da Girgiza masa kai kana tace.

“Mantawa nayi sai ka dawo nake son cewa”.

A hankali ya zaro ATM ɗinshi na Zenith Bank daga al’jihunsa,  cikin tafin Hannun ta yasa matashi kana a hankali yace.

“Ga ATM ɗina na Zenith Bank, kin san pin number ɗin, akwai kuɗi a ciki kusan 5 Million”.

Da sauri tace.

“Ina ka samosu?”.

Gyara zamanshi yayi kana yayi mata bayanin yadda sukayi da Abba sannan ya ɗaura da cewa.

“Akwai wasu a wurina, wannan ki riƙe kiyi dukkan abinda kike buƙata kafin in dawo, in haɗasu muyi ƙoƙarin barin garin nan, domin ya fita raina”.

Yayi mgnar yana tuno kalaman Hajja Nana ita kuwa Innayi cike da sanyi tace.

“Uhmmm Aliyu in Sha Allah kamar ma mun barima ai kama barin kai kam”.

Cikin sanyi ya jinjina

Kai tare da miƙewa yace.

“Toh shikenan Innayi amma dai bakiyi fushi dani bako?”.

Da sauri tace.

“La la la Aliyu banyi fushi da kaiba”.

hannunta ya riƙo tare da ɗaurawa a kanshi kana yace.

“Toh kuma baki samin Albarka ba”.

Cikin sanyin Murya tace.

“Allah yasan ya Albarka Ubangiji ya tsare gabanka da bayanka Allah maidakai lafiya ya kuma tsareka da lafiyarka, Ubangiji ya rabaka da sharrin duk kan abin ƙi walau mutum ko aljan ko  wani irin abune ya *Tsareka da Tsoffin magauta ya hanasu ganeka bare cutar da kai kafin isarka tushenka”.*

Lumshe Idanunsa yayi kana yace.

“Ameen ya Allah Innayi ni zan tafi”.

Kai ta gyaɗa tare da cewa.

“Toh ka tsaya bari na zo”.

Kai ya gyaɗa sannan ya tsaya ɗaki tashiga ba daɗewa ta fito sanye da hijabi, suka nufi  wurin motarsa,

“Yau innayi zafa ki koma gidan Abba ko Ummi dan zamani ke ɗaya a nan bai minba”.

Cikin sauri tace.

“Eh toh gsky k nima ina tsoro Ni kaɗai a nan to amman, gsky gwara min gidan Ummin Jameel kaga ita kamar ɗiya take a gareni gidan Abba kuwa ba wani sabawa nayi da matansa ba, amman can zamu zauna ɗakin Asma’u nasam Malam Ahmad kuma baida matsala”.

Cikin gamsuwa da haka yace.

“Gsky kam hakan yafi, zan gaya Abban in kin gama haɗa kayanki Asma’u zata zo ku tafi”.

Kai ta jinjina cikin gamsuwa tace.

“Ba laifi”.

Jingina yayi da jikin motar bayan yasa jakarsa gefen mai zaman banza.

Ita kuwa Innayi a hankali ta matso kusa da marfin motar zira hannunta tayi ta ciki, zip ɗin jakarsa tabuɗe tasa jim kaɗan kuma ta maida ta rufe kana sukayi sallama ya mota ya tafi.

 

Kai tsaye gidan Ummi Moddibo ya nufa cikin nutsuwa yake Driving yayin da yake sauraran ƙira’ar Ahmad Sulaiman cikin suratul An’am yana isa gidan Ummi yayi Parking aƙofar kana ya fita ya shiga coumpund ɗin yana tafiya ahankali yana ɗaura ƙafarsa akan farandar sautin muryar Khausar ya ratsa Dodon Kukensa cikin sauri ya tsaya tare da rumtse idanunsa.

Sabida jin yadda tsikar jikinsa ya fara tashi tun daga tafin ƙafarsa har tsakiyar ƙwaƙwalwan kansa, ahankali ya jingina bayan sa da jikin bango yayin da zuciyarsa ta shiga bugawa da kaso Cassa’in da tara cikin ɗari.

Aransa yakeji kamar ya koma domin gaba ɗaya ya rasa meke sashi shiga wani yanayi da zaran yaji sautin Muryanta zaiji tamkar ana tsikara masa allura yama rasa ta wani irin yanayi zai misalta yanda yake ji akan yarinyar shin kunyarta yake ko kuma tsoronta yakeji, ko shakkarta shi kansa ya kasa tantancewa, taune Lip ɗinsa na ƙasa yayi da ƙarfi tare da buɗe idanunsa da suka sauya launi kana ya tura ƙofar falon tare da sallama yana mai tsare fuska.

 

Ummi dake zaune ta tsira masa ido tare da cewa.

“Babana har ka shirya kenan?

Kai ya gyaɗa tare da faɗin.

“Eh Ummi”.

Kana ya zauna agefenta ya zamana yana facing ɗin kichen.

Kallonsa Ummi tayi cike da kulawa tace.

“Amma dai ba kayi breakfast”.

Kai ya girgiza kana yace.

“Uhm-Uhm”.

Da Mamaki tace.

“Toh ya za’a ayi ka tafi da  yunwa ba zaiyu ba Babana ba zaka tafi da yunwa ba”.

Langwaɓar da kai yayi tare da Marerece murya yace.

“Ummi bana jin yunwa fa”.

Fuska ta ɓata kana tace.

“Bafa zaiyu ba Babana baza ka tafi da yunwa ba”.

 

Khausar na fitowa daga kichen ta girgiza kai tare da kallon Asma’u tace.

“Toh ni zan tafi sai anjima”.

Da mamaki Asma’u ta kalleta kana tace.

“Bangane ba kamar ya sauri kike?

Dama ba nan kika zoba ne?”.

Khausar kuwa kai ta girgiza tare da kallonta kana tace.

“A’a ba nan nazo ba dama gidan Aunty Ruƙayya naje to da naje sai na sameta tare da baƙi shine na kira Mommy nace zan ƙaraso nan mu gaisa.

Mommy kam  cewa tayi wai da safiyar nan zanzo”.

Moddibo kuwa tunda yaji sautin Muryanta akusa dashi ya kasa ɗauke idanunsa akanta duk da cewa kallon Kasan ido yake mata.

Cikin sanyi Khausar ta cigaba da cewa.

“Toh shine nace tayi hakuri ba daɗewa zanyi ba shine fa tace inzo amma kada in daɗe saboda mune da aikin rana zan koma in ta yata nazo muyi wata mgna ce, kuma nafasa”.

Da sauri Asma’u tace.

“Dan Allah muyita”.

Kai ta jujjuya tare da cewa.

“Ba damuwa in kin samu dama kizo zamuyita, yanzun sauri nake”.

Ta ida maganar tare ɗago kanta.

Idanunta ne suka sauƙa cikin idanun Moddibo.

Atsorace ta zira Idonta cikin nasa tare da juya su acikin nasa wanda hakan ya zama kamar hararansa tayi ita kuma cikin mamakin yadda ya rame ya wani zama shiru, ne yayi matuƙar bata mamaki da tausayi domin da dane da tuni ya danna mata harara.

Cike da tsoro ta janye kwayar idanunta daga garesa, tana mai mamakin sauyinsa rayuwa, cikin wani irin sauri ta nufi ƙofar falon yayin da jikinta ke tsuma Muryanta na rawa tace.

“Ummi ni na tafi”.

Kallon yanda ta nufi ƙofar Ummi tayi kana ta kallo Moddibo da har zuwa lokacin idanunsa ke ƙasa da mamaki tace.

“Ya da sauri kamar kinga Dodo?”.

Kai ta girgiza batare data juya ba tace.

“A’a Ummi nikam na tafi”.

Cike da kulawa Ummi tace.

“Toh ki tsaya Kiyi breakfast mana”.

 

Kai ta girgiza still jikinta na tsuma tace.

“A’a Ummi Allah Mommy na za tayi faɗa idan na daɗe”.

Jinjina kai Ummi tayi kana tace.

“Toh shikenan nagode  ki gaida Mommy ki gashi kin ki kitsaya kiyi breakfast”.

Da sauri tace.

“Allah Ummi sai da nayi breakfast agida kafin na fito”.

Kai Ummi ta gyaɗa kana tace.

“Ki gaida Mommy naki da Raudat dasu Haiydar”.

Cikin sauri ta fice daga falon bayan tace zasuji.

 

Moddibo kuwa ahankali ya jinginar da kansa da jikin kujeran tare da lumshe Idanunsa kana ya cije Lip ɗinsa na ƙasa, sai kuma yayi saurin buɗesu sabida ganin surar jikinta da yayi ziraran miraran.

Gashi  da zaran yaji muryan yarinyar zai riƙa jin wani irin abu mai wuyar fassarawa kana lokacin da ƙwayar idanunsu suka haɗu babu abinda suka hango masa face.

Ƙirjinta tamkar zasu tsole mishi idanu.

Asma’u Mommy tasa ta kawo masa ɗan waken da sukayi sai ruwan Tea ba laifi yaci danwaken da ɗan dama kana yasha ruwan Tea.

Malam Ahmad ne yashigo tare da yi masa addu’ar Allah ya tsare miƙewa yayi ya fita kana yaja tsohuwar motarsa zuwan gidan Abba yana isa yayi Hong mai gadi ya buɗe masa Parking Yayi aharabar gidan kana yashiga sashen Abba bakinsa ɗauke da sallama ya shiga falon Cike da kulawa Abba da Hajiya Turai dake zaune gefensa suka amsa masa.

 

Anutse ya ƙarasa tare da zama gefen Abba cike da kulawa Abba yace.

“Aliyu ka ƙara so?”.

Jinjina kai Moddibo yayi cikin sanyin murya yace.

“Eh Abba ina kwana ya ƙarfin jikin”.

 

“Jiki da sauƙi Aliyu”.

 

Bayan sun gama gaisawa Abba yayiwa Moddibo duk kan wasu bayanai kana ya bashi wasu takardu da duk wani abu daya kamata sai da Abba ya masa bayani.

Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe kana yace.

“Toh Abba ni zan tafi”.

Ahankali Abba ya sanya hannu a aljihu tare da ciro key mota sabo dal ƙiran PRADO  ya miƙa Masa tare da cewa.

“Ga wannan Aliyu za’a kaika Airport dashi, in Manu driver ya dawo kuma gidan ku zaije ya ajiye maka ita”.

Cikin sauri Moddibo ya ɗago kansa tare da Kallonsa.

“Abba mota kuma?”.

Kai Abba ya gyaɗa masa alamar eh.

Cikin sanyi Moddibo ya sake kallon key motar kana yace.

“Abba to ai ina da mota”.

 

Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe kana yace.

“Uhm-Uhm Aliyu kenan. Ɗan Allah kada kayi min gardama ka karɓa kawai ka sanya albarka aciki”.

Sunkuyar da kai Moddibo yayi batare da  da yace Uffan ba.

Kallonsa Hajiya Turai tayi kana tace.

“Ka karɓa mana Aliyu ai yanzu kam an zama ɗaya”.

Jinjina kai Moddibo yayi kana yace.

“Toh shikenan Abba Nagode Allah yasaka da Akhairi Ubangiji Allah ya mayar maka da dubunsa”.

Murmushi Abba yayi kana yace.

“Ameen”.

Nan take ya ɗauko takardun motar ya miƙa masa tare da cewa.

“Jiya mukayi magana da Alhj Abubakar nasa ya kawo min da yamma gatanan lafiyarta ƙalau anyi mata dukkan abinda ya dace”.

Jinjina kai Moddibo yayi kana yace.

“Nagode Abba Allah yasaka da alkhairi ni zan tafi”.

Ahankali Abba yace.

“Allah ya tsare Aliyu Allah ya bada abinda akaje nema”.

Ameen ya amsa kana ya miƙe Abba ya rakasa da kansa ya buɗe masa bayan motar ya shiga, sabuwar motarsa sosai motar ta burgesa duda bai wani damu da bakin abuba, amman collor bakin yayi masifar kyau dan sai sheƙin sabunta takeyi,

Manu ne ya shiga yaja motar suka fita.

Kai tsaye gidan Malam Arɗo ya wuce dashi bisa umarninsa.

Sallama yayi masa kana daga nan suka ɗauki hanyar da zata sadasu da cikin Taraba Jaligo ja gari na Baba Abasu babban birnin Gembila kenan wanda kuma tsakanin local government ɗin nasu zuwa cikin ƙwaryar birnin Taraban tafiyace ta musamman.

Koda suka isa cikin Taraba, basu tsayaba suka nausa hanyar Adamawa Yola.

 

Jauro yaya

Baffan Liman ne zaune agaban Hajja Nana cikin sanyi murya da ladabi yayi ƙasa da kansa tare da cewa.

“Hajja kiyi haƙuri bai kamata ace kina fushi akan abinda bai kai ya kawoba, wannan al’amari ba wani al’amari mai girma bane bai kamata ace ki ɗauki zafi akansa har haka ba”.

Kallonsa kawai Hajja Nana keyi tana girgiza ƙafa tare da girgiza kai.

Ajiyar zuciya Baffa Liman ya sauke kana ya cigaba da cewa.

“Idan kin lura Khausar fa jika ce agareki ba ƴa bace, kinga kuwa duk ikon ka akan jika yana zama mai rauni, bare wannan zamanin da muke ya bambanta dana baya dan Allah Addah Hajja kiyi wa wannan al’amarin Kyakkyawan fahimta”.

Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da fesar da numfashi kana tace.

“Na lura sannan na fahimci Liman da kai dasu Garga, Sadu, Jauro baki ɗaya bakin ku ɗaya akan al’amarin Khausar tun da haka kuka ce ni bani da abinda zance kuje kuyi duk yanda kuka ga dama”.

Ahankali Baffa Liman ya ɗago ya kalleta kana ya sake sunkuyar da kansa.

Cikin alamun ɓacin rai ta cigaba da cewa.

“Amma fa kusa ni ba zata Auri wannan yaron ba, tunda har ta iya buɗe baki ta kalli tsabar idona tace bata son. Aliyu jikina kuma ɗan Uwanta toni babu hannu na akanta kuyi mata yanda take so amma banda Auren mara tushe da asali”.

 

Gyaran murya Baffa Garga yayi kana yace.

“Dan Allah Addah Hajja kiyi haƙuri shikansa. Muhammadu Jimeta yace zai zo amma yafi so yazo ya sameki cikin farin ciki kada akan batun Khausar ranki ya dinga ɓaci abanza a wofi”.

 

Fuska ta ɓata tare da Kallonsu ɗaya bayan ɗaya kana tace.

“Idan yayi niyyar zuwa yazo idan kuma baiyi niyyar zuwa ba yayi ta zama tunda shi kansa bayanta yake bi, tun da wai har cewa yake bazai yi mata dole ba”.

 

Baffa Liman ya sake sassauta muryarsa yace.

“Dan Allah Addah Hajja kiyi haƙuri ki bi lamarin asannu da izinin Ubangiji komai zai dai-dai-ta amma bama son ganinki cikin damuwa”.

Haka suka riƙa Rarrashinta tare da kalamai masu kwantar da zuciya.

 

Acan ɓangaren Moddibo kuwa tafiya tsakanin  Taraba da Yola tafiya ce mai zaman kanta sai dai bata wuce awa biyu zuwa uku,  tuƙi Manu keyi cike da ƙwarewa ga samun sabuwar mota.

 

Shi kuwa Modibbo a hankali ya fesar da sassayan numfashi.

Sabida ji yake wani irin yanayi yana lullubeshi gaba ɗaya tunanin J ɗin sa ya dawo masa ji yake tamkar idan ya juya gefen damansa zai ga J ɗin sa, ahankali ya zira  hannunsa ya kara volume din ƙira’ar da yake ji acikin Suratul Nisa’i, sai kuma ya koma baya ya jingina bayanshi da jikin Seat ɗin.

Domin idan har ba karatu yake jiba ko kuma yake yi sam baya taɓa samun nutsuwa, saidai kuma ta wani ɓangaren haka nan  yake jin wani irin farin ciki da yabar garin Gembila, ji yake tamkar yabar wani yanki da yake da tarin ƙunci, ji yake tamkar yabar wani waje mai duhu da zafi ji yake tamkar ana zare ransa da ruhinsa daga waje mai ƙunci da azaba, kana kamar ana nufar dashi awaje mai tarin nutsuwa da salama yakeji.

Domin tun bayan rasuwar Amininsa garin Gembila tayi masa zafi da ƙunci kana tayi masa duhu baya kallon haskenta gaba ɗaya ya tsani garin, to dama Meya rage masa da garin Innayinsa ce kaɗai sai kuma Ummi dasu Asma’u.

 

Sai Misalin ƙarfe biyu da rabi ya shiga cikin Adamawa suna isa cikin  Adamawa.

Manu yayi Parking A dai-dai Masallacin jum’ae dake cikin Atiku Abubakar shopping mall ɗinsu nan  sukayi Al’wala sukayi sallar Azahar Kasancewar hanya zai kama, ɗan tafiya yasa a gaba shiyasa yayi niyar ƙasaru  ya haɗa da sallar La’asar domin karfe uku dai-dai jirginsu zai tashi.

Baya jin zai iya cin wani abu haka yasa ya kalli Manu cikin mutuntaka yace.

“Manu sannu da yunwa”.

Cikin girmamawa Manu yace.

“Laa ba komai ai kafin mu fito ma naci abinci”.

Kai ya jinjina kana yace.

“Muje ka kaini cikin Airport ɗin, sai kayi sauri ka juya, kada kayi dare a komawa”.

Cike da gamsuwa Manu yace.

“Toh”.

Daga nan ya kaishi Airport sannan shi kuma ya fito, ya ɗan samu abin da ya taɓa kana ya kama hanyar komawa Taraba, Gembila.

 

 

Ƙarfe uku Dai-dai jirginsu Modibbo ya tashi daga Adamawa zuwa birnin tarayyar Nigeria Abuja.

 

 

Alhamdulillah cikin kwanaki huɗu bizi’nsa  ya fito da yake business bisa ne ba wuya.

Alhamdulillah ranar Al’hamis da misalin ƙarfe biyu dai-dai jirginsu ya ɗaga daga Abujam Nigeria.

Zuwa Rabat babban birnin ƙasar Marocco kenan

 

A hankali ya fesar da wani irin zazzafan numfashi dai-dai lokacin da tayun jirginsu ke raɓuwa da ƙasar Nigeria, rumtse idanunsa yayi da karfi sabida wasu irin zafafan hawaye da yaji  suna tsastsafo mishi ta cikin dukkan jijiyoyin idanunsa.

Wani irin yanayin da bai taɓajiba duk tafiye-tafiyen da yakeyi yaji yana dabaibaye rayuwarsa haka kawai yakeji kamar ya bar kasar kenan bari na har abada.

Lokaci ɗaya tunanin Jameel ya dawo masa, wanda hakan yasa yayi saurin jingina bayansa da kujerar jirgin.

Yana mai jin wani irin sassayan kuka na taso mishi daga can cikin ƙahon zuciyarsa, hakanne yasa ya fara karatun Alqur’ani mai girma a hankali.

 

Yayinda mutanen cikin jirgin kuwa kowa keta hidimar gabansa.

 

Shi kuwa Modibbo tunda ya zauna bai ɗago kansa ya kalli kowaba.

Sabida yanayin da yakeji.

 

A hankali dai tafiya ta fara nisa, tuni sun kutsa cikin sararin samaniya jirgi ya kama hanyarsa.

 

Koda akazo tambayarsu me yake buƙata.

Cewa yayi baya buƙatar komai.

 

A ƙalla sunyi tafiyar awa uku a sararin samaniya.

Zuwa yanzu kam mafi akasarin matafiyan kowa ya nitsu hada-hadar ta ragu matuƙa, wanda zuwa lokacin kuma sauran musu 57 minutes su dira cikin birnin Rabat sabida daga Abuja zuwa can tafiyar awa uku da minti hamsin da bakwai ne cib-cib.

 

A hankali ya gyara zamansa tare da kallon farin matashi da ya zo ya zauna gefensa wanda bazai wuce sa’anan ba.

Murmushi matashin yayi tare da miƙa masa hannun yana mai mishi wani irin kallo mai cike da tambayo al’ajabi da kaɗuwa.

Shima ɗan murmushin yayi tare da bashi hannu sukayi musabaha.

“Jabeer bin Jabeer Joɗa. Wanda ya kira kansa da Jabeer ɗan Jabeer Joɗa ɗin ya kare mgnar cike da masifar mamaki da zurawa fuskar Modibbo idanu yana matuƙar mamakin kamanninsa.

Shi kuwa Modibbo cikin yanayin sanyi yace.

“Aliyu Youssef Muhammad Mouley”.

Cikin tsananin bayyanar mamaki ya zazzaro idanu waje tare da juyowa garesa da kyau cikin alamu rawan jiki ya juya harshe zuwa larabci yace.

“Yah Salam toh kuma yaushe kazo”.

Cikin ɗan sanyi Modibbo shima juya harshe ih zuwa asalin amintaccen larabci yace.

“Nazo kuma? Nida ƙasata, me zanje yi a Marocco dai zaka ce”.

Kai Jabeer bin Jabeer Joɗa ya jujjuya tare da juyawa yayi mishi mgn da hausa yace.

“Kamar yaya ƙasar kuma?”.

Ga mamakin Jabeer sai yaji Moddibon na bashi amsa da harshen hausa.

“Sabida ni ɗan Nigeria ne girman Nigeria”.

Da sauri Jabeer yace.

“A’a wannan ai ko makaho ya shafa yasan kai ba ɗan Nigeria bane kuma ma sunan da ka fadi ai ya isa shaidar inda ka nufa komawa zaka yi ba zuwaba”. Ya ƙare mgnar da iya haƙiƙanin gskyrsa da  rawan jiki.

Cikin ɗan ƙosawa da surutun sa Modibbo yace.

“To sabida me?”.

Da sauri Jabeer yace.

“Sabida kafi kama da Larabawa”.

 

“Toh gashi kuma kaima da larabawan kake kama”.

 

Gyara zama Jabeer yayi tare da cewa.

“Kuma ni dai ba fullatanine”.

A hankali shima Middibo yace.

“Minfu mi pullo”.

To zuwa yanzu kam mamakin Jabeer ya tsananta.

Ya buɗi baki da niyar zaiyi wata mgnar kenan aka kirashi a baya bisa dukkan alamu Kakanshi  ne da sauri ya tashi ya nufi can bayan.

 

Shi kuwa Modibbo a hankali ya fesar da numfashin gajiya da surutun da Jabeer ya sashin.

Tare da fara karatun Alqur’ani mai girma.

 

Jim kaɗan da tafiya Jabeer sai gashi ya dawo zama yayi bakinsa cike da tarin mgn to amman samun yana karatun Alqur’ani mai girma yasa dole ya haɗiye dukkan rogowar mgnarsa da tarin tambayoyinsa.

 

A hankali Moddibon ya ɗago manyan idanunsa tare da kallon taswirar kasar Rarat da suka iso tsakiyarta.

Wanda tuni an sanar musu.

Haka nan yake jin wani irin salama da kwanciyar hankali kana da nutsuwa tunda suka shiga yankin ƙasar Marocco yake jin wani irin sanyi da more happy Wanda har ya iya jure surutun Jabeer.

Numfashin mai sanyi ya fesar tare da ƙara ware manyan idanunsa yana kallon garin ta window’n jirgin.

Haka nan yakeji tamkar yabar damuwarsa baki ɗaya acikin Nigeria ya kuma saki dukkan ƙuncinsa a cikin Taraba.

Cikin nutsuwa da kwanciyar hankali yake bin tsarin dogayen benayen gidajen garin da kallo kana sassayan muryarsa na ratsa kunnuwansa yana jin sautin karatunsa da yakeyi jikin suratul Kahf.

 

Misalin ƙarfe shida saura minti uku rak.

Jirginsu yayi sauƙar angulu a cikin babban Airport dinsu.

Rabat Sale international airport.

Wanda dai-dai lokacin kuma ya dire ayar ƙarshe ta Suratul Kahf ɗin tuni kuma jirginsu ya dai-dai-ta da’irar tsayuwarsa.

Da sauri Jabeer ya kalleshi sai kuma yayi sauri ya mayar  kallonshi gefen damanshi ganin har an buɗe ƙofar jirgin.

Juyowar da zaiyi kuwa sai ganin Middibo yayi a tsaye yana jawo jakarsa daga drower dake samansu.

Da sauri ya miƙe shima, sai kuma yaji ana kiransa a baya, da sauri ya nufi bayan.

Shi kuwa Modibbo agogon dake hannunsa ya kalla, da ɗan hanzarin sa ya nufi wajen sabida ƙaratowar lokacin sallan magrib.

 

A hankali ya fesar da sassayan numfashi, dai-dai lokacin da ya taka step na forko wanda ya fito da kanshi sararin garin Rarat, duk da dai duk Arfica ne amman ƙasar Marocco sunyi mana rata zarrama mai girma, sunada ci gaba na musamman.

A hankali ya furta.

“Yah Salam”.

Sabida wani irin ni’imtaccen iskane mai cike da salama ke ratsashi yana shiga duk ta inda hudar gashin jikinsa yake.

Wani rin amintaccen numfashin mai cike da yanayin sauƙe ajiyar zuciya ya shaka, like ɗan da ya daɗe baiga mahaifiyarsa ba, kuma yayi kuka.

A hankali yaci gaba da taka steps din yana sauƙo ƙasa.

 

Wani saurin runtse idanunsa yayi lokacin da ya dire tafin ƙafarsa kan ƙasar Marocco cikin yankin Rarat.

Wani irin tsuma yaji naman jikinsa nayi tun daga can cikin jikinsa da zuciyarsa yakejiyo wani irin tsuma.

Wanda ya ta’allaƙa hakan da tsananin yanayin sanyin garin ne.

“Alhamdulillah!!!”.

Ya furta a saman lips inshi sabida, tunda Allah ya halicce shi bai taɓajiba irin yanayin da yakeji a yanzu, ko Saudia yaje bayajin yanayin nan.

 

Yana mai shaƙar sassayan iskan garin ya fara bin ayarin sauran matafiya.

Yayinda can gefen kuma manyan motocine na al’farma wanda bisa dukkan alamun wani babba akazo ɗauka.

 

Su kuwa a cikin yanayin gajiya suka ƙaraso inda masu tarɓarsu suke.

 

Ɗan dube-dube ya yayi.

Da sauri ya nufi wani Balarabe dake jingina da Taxi yana riƙe da ɗan allon tarba wanda aka rubuta Aliyu Youssef Muhammad Mouley.

Yana isa yayi masa sallama.

Cike da tsananin girmamawa Balaraben yayi saurin buɗe masa marfin motar tare da cewa.

“Marhababuka”.

Kai ya jinjina masa cike da gajiya da ƙosawa.

Yasan Taxi Abba ne ya turosa.

 

Da sauri shima ya shiga Taxi ɗin kana yaja suka fita daga cikin Airport ɗin.

A hankali yayi miƙa tare da jingina bayansa da seat ɗin dai-dai lokacin da suka ratso ta cikin unguwar Ben slimane.

Anƙuwace ta masu alfarma, haka yasa tsarinta na musamman ne.

haka nan yaji yanayin Weather yayi masa masifar daɗi da kyau.

 

Gashi yanayin damuna ne Iska mai sanyi da ratsa jiki na kaɗawa gashi duk ta inda ka wulga ido bishi yoyin dabinone masu kyan tsari ke rausayawa sunyi kore shar dasu iska na kaɗawa suna rangaji ga kasar garin ajiƙe yake alamun anyi ruwa.

 

Ƙarfe shida da minti sha biyar dai-dai mai Taxi ɗin ya juya hancin motarsa kan wani gini mai kyau da ɗaukan indo wanda a samansa aka rubuta.

Belere Hotel Rabat.

Kai da ganin masifar kyau da tsaruwan hotel ɗin kasan zaiyi masifar tsada.

Cikin taushin murya ya kalli Balaraben dake riƙon.

Tare dayin mgn da larabcin.

“Muje wani wanda bai kaishi ba”.

Cikin sanin darajar aiki mai Taxi ɗin ya ɗan kalleshi ta madubi tare da cewa.

“Toh”.

Daga nan ya juya akalar motar ya ɗauki hanyar da zata sadashi da unguwar Sidi bettache.

Tafiya kaɗan sukayi suka fito kan babban titinsu.

Da sauri Modibbo yace.

“Masha Allah”.

Dai-dai lokacin da

Idanunsa suka sauƙa akan tamfatsetsen masha’hurin hotel mai masifar kyau da tsari daga can sama tsololuwan ginin an rubuta.

Welcome to Sofitel Youssef Mouley hotel.

Da sauri yace.

“Tsaya mu shiga nan”.

Yayi mgnar still idanunsa na kan sunan hotel ɗin da yayi kama da sunanshi hakan don sunan hotel ɗin yaji yana son sauƙa a nan.

Murmushin mai Taxi ɗin yayi tare da cewa.

“Toh ai wannan yafi wancan tsadama”.

Da sauri ya gyaɗa mishi kai tare da cewa.

“Eh shi yayi”.

Ya ƙare mgnar da lumshe idanunsa jin sautin kiransan salla a masallacin dake cikin hotel ɗin.

Haka yasa shima mai Taxi ɗin saurin shiga.

 

Numfashi mai sanyi ya fesar tare da buɗe Idanunsa daya lumshe kana ahankali.

 

Wani irin hotel ne mai masifar kyau da tsari da girma duk da cewa a farfajiyar akwai masallaci sai dai ba wani Babba bane, amma farfajiyar babbe ne me kyau da tsari daga gefen dama wajen Parking din Motoci ne wanda aƙalla zai ɗauki motoci settu zuwa saba’in da biyar kana daga jikin doguwar kantamgar kuwa bishiyoyin kwakwane zagaye da ginin daga can gefe kuma wasu irin flowers ne dake wadace  da damshin ruwa haka yasa jikinsu sai sheƙi  kayi, tafiya kaɗan zaka samu side ɗin shiga Reception ɗin.

Atsakiya daga gefe da gefe kuma hanya ce kana daga baya wani ƙaton gardin ne wanda yana iya hango bishiyoyin dake ciki kana yana jiyo sautin kukan tsuntsaye kala da ban daban.

Ahankali ɗago daga jingina da seat din da yayi.

Yana Jin zuciyarsa na harbawa kaɗan kaɗan cikin sauri mai taxi ɗin  ya rufe marfin gefensa   cikin sassarfa ya zagoyo gefen da Modibbo yake tare da buɗe masa murfin motar kana fuskarsa ɗauke da murmushi yace.

“Lalle marhaba fatan an ka isa Marocco lfy”.

Cikin sanyin murya da tarin gajiya yace.

“Yawwa”.

Kana ahankali ya ziro ƙafafunsa waje ya sauke aƙasa.

Da sauri ya rumtse idanunsa tare da kuma buɗesu a lokaci ɗaya yaji wani irin abu mai masifar sanyi ya zira masa tun daga tafin ƙafansa har zuwa ƙwaƙwalwar kansa irin dai abinda yaji daya taka ƙafarsa a Airport. cikin sauri ya kuma lumshe idanunsa tare da furta.

“Yah Salam”.

Kana ya fito dai-dai lokacin da mai kira sallah a masallacin hutel ɗin yazo dai-dai wurin kalmar shahada.

 

Cikin sanyi ya fara bin kalmar shahadar, wanda hakan ya ankarar da mai  taxi dinma ya amsa, tare da bin addu’a’o’in da yaji Moddibon yanayi.

 

Cikin sanyin murya Mutumin yace.

“Sannu da zuwa”. Lokacin da yaga ya ɗan juyo ya kallesa.

Kai Modibbo ya gyaɗa masa tare da buɗe bayan motar ya ɗauki Breafcase ɗinsa tare da jakarsa, da sauri mai taxi ɗin yasa hannunsa ya amshi jakar kan nasa tare da kuma miƙa masa hannun zai amshi Breafcace ɗinma.

Kai Modibbo ya girgiza tare da faɗin.

“Barshi, zasu yi maka yawa ai”.

Cikin jin daɗi  yayi gaba tare da

cewa.

“Bismillah  kashiga ciki gashi ma Maghariba ta tayi”.

Cike da salama Moddibo yace.

“Bismillah”.

Yayi mgnar tare da nuna masa gabanshi alamun yayi gaba.

Cikin sauri  yashiga gaba kana Moddibo yabi bayansa.

Cikin hanyar da flowers ke ajere gefe da gefe sai ɗan mawadacin hanya dake tsakani sukabi.

Ahankali Moddibo ya taka step ɗaya biyu ana ukun ya hau kan barandar Kofar falon.

Ya sanya ƙafarsa na dama aciki tare da furta.

“Masha Allahu laƙuwwata Illah billahi”.

Sosai komai na hotel ɗin keda tsari na Muslunci da burgewa.

 

Cikin yanayin gajiya ya ƙarasa gaban ma’aikatan dake binsa da kallon ƙurilla.

Bayan sun gaisane ya kama ɗaki, cike da mutuntaka da martabawa suka gama komai, ɗaya daga cikinsu, ya amshi jakarsa dake hannun mai taxi ɗin.

Kana yayi gaba tare dace masu bismillahi.

Cike da gajiya yabi bayanshi.

 

Lifter suka shiga cikin minti biyu suka isa hawa na biyu inda na ɗakin daya kaman yake.

Ma’aikacin hotel ɗin ne da kansa ya buɗe ɗakin ya shiga kana ya shimfiɗa beshit tare blanket, kana ya wuce da sauran kayan kamarsu Towel da Bathrobe da makilin da Brush sabulu ya ajiyesu bathroom tare da feffesasa Air freshner kana ya fito tare da cewa mishi.

“Sir akwai abinda kake buƙatane?”.

Kai ya jujjuya mishi alamun a’a.

Ganin haka yasa ya fice.

 

Shi kuwa Modibbo cike da gajiya ya ajiye woyoyinsa yana mai shaƙar ƙamshin Roomfreshner tare da kallon tsarin komai na ɗakin, komai na cikin falon Ash & maroon colour ne mai masifar kyau kama daga Cottins carpet dama kujerun.

 

Cike da gajiya a shiga bathroom al’wala yayi tare da fitowa da sassarfa.

Lifter ya shiga ya sauƙa kana kai tsaye masallacin dake cikin hotel ɗin ya shiga da sassarfa jin an tada iƙama.

Ya samu tuni sahu forko da na biyu duk sun   cika sai ana uku suka tsaya

Suna shiga suka tada kabbara dai-dai lokacin kuma aka tafi ruku’un Farko.

Bayan anyi Sallah an idar Moddibo.

Yayi Adduo’insa na yau da kullum, ya kara da na neman aminci cikin wakilcin da zaiyiwa Abba tare da samun nasara da roƙon Allah yayi riƙo da hannayensa ya bashi ikon riƙe amana.

Yana so ya jira Isha’i amma saboda yanayin gajiya da yake ji bazai iya jira ba yana so yayi wanka duk da cewa garin akwai sanyi,

Amma yana son yayi wanka dan yaji daɗin jin kinsa da sauƙin gajiyar hanya.

A hankali ya yunƙura da niyyan tashi, cikin sauri ya juya bayansa tare da fito da Idanunsa cike da tsananin son tabbatar da ganinsa ya miƙa da sauri saboda gani fuskar da bashi da hauki ko kokonta a kai cewa fuskar J…!

 

 

*Littafin dai na kuɗi 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276*

 

 

 

 

 

By

*GARKUWAR MARUBUTA*

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply