Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 12


Sakon So 12
Viral

EPISODE 1️⃣2️⃣

 

Kowa na dakin hatta Lujain din dake kuka sosai dashi kanshi Abee saida yadago kanshi yakalli Gwaggo jin abinda tafadi, cikin tsantsan nuna seriousness Gwaggo tace “eh haka nafadi, nace saika auri jikata! Duk abinda babba ya hango karami bazai hango ba, wannan video dakuka nunamin kokun watsashi aduniya mutane ba yarda zasuyi ba bazai wankemin jikata ba, hanya daya zai wanke jikata tastas shine ace kaidin mijinta ne da aure tsakaninku, daga masu gulma dashi usulin algugumi dan wutan jahannama daya yada video dana tabbata baku ganshi ba haryau saisuji kunya kaga ko banza yay aikin banza, shi bazai sami miliyan darin ba shibai samu kampanin ba” hannunta Baba yakama zaiyi magana Gwaggo ta fizge hannunta idanunta sunyi jajir tace “wlh wlh duk wanda yace saija dani cikinku saina tsine mishi albarka ubanme zaka gayamin lokacin dazata mutu ma baka tsaya mata ba yaune da aka kirata da fasika zaka tsaya mata? Nine komin Lujain, nine uwarta, nine ubanta, nine kakanta, kamin shiru kawai, wlh wlh saiya aureta akan wani dalili zaija sunan diyata ya baci kuma bazaiyi komi ya wanketa ba, wlh saiya aureta inba hakaba wlh wlh sai hukuma tarabamu, marainiyan yarinya na eh ku jibeta fa abin tausayi ubanta bai damu da ita ba sabida yaga batada mahaifiya, inda yau mahaifiyarta na raye Kunsan kalan tashin hankalin dazata shiga kuwa? Bayan kunsan rayuwa yakoma yanzu iskanci ado ne wajen namiji mace ce rayuwanta zai baci har abada, yanzu awannan video banda bayanshi anga fuskanshi eh? Yar yarinyar nan dai akaga fuskanta har akaga tana gyara riga, idanba aurenta yayi ba koya wanketa wazai auri Lujain iyye? Kufadamin wani namiji ne zai aureta? Wasu iyayene zasu bar dansu ya auri yarinyan da video fasikancinta ke yawo a yanar gizo? Shi yanzu bashi kwana biyu anmanta dashi itako fa? Namiji mutane barasu iya taranka ma itako Yar yarinya mace halama saidai tadaina fita danta fita tareta za’ayi amata duka a titi, yakukeso tayi? Matar ubanta kuma dama ba sonta takeba kaga gwara ka aureta naga kanada hankali kanada yara dasunma girmeta zaka rikemin ita amana koyau na mutu banda nadama dama kullum tunanina wazan aura mata da hankalina zai natsu dashi ashe kai Allah zai kawo mata amman ta wannan kaddaran” Gwaggo tafashe da kuka muryanta kawai akeji a duka office din ganin yanda take kuka kuma su Baba sun kasa mata magana gudun karta tsine musu yasa ahankali Mustafa yaje inda take tsugunnawa yayi yakamota kaman yakamo mahaifiyarshi hannu yasamata a fuska yana goge hawayen datake yace “dan Allah Gwaggo kiyakuri kidena kukan nan dan Allah sabida ni” ahankali tahadiye kukan tana kallonshi cikeda lallashi yace “Gwaggo kinga nan office neko wannan matsalan kuma matsala ce daya kamata atattauna agida kibamu address din gidanku anjima da daddare namiki alkawari dukanmu shima harda iyayenshi zamuzo sai ayi magana da kyau Gwaggo kinji Gwaggo amman yanzu kutafi, itama ku kaita gida tacire kayan nan kar wani abun yasameta maganganun nan da ake agabanta bai dace ba, kuma babu kyau yanda kike kuka agabanta, kece karfinta, kobaki hakura kitafi dan kowaba kiyi dan ita naga yanda kike sonta” juyawa Gwaggo tayi takalli Lujain dake kuka sosai har lokacin taji barata iya musuba tace “gidan mu na nan kwanan tipa a Gwarimpa idan kun shigo gida na biyar mai gate mai ruwan goro” anatse Musty yace “zamuzo anjima da daddare” tashi tayi tadauki gyalenta dake kasa taje wajen Lujain ta lullubeta dashi ta kama hannunta tadagata tace “muje Allah natare dake, nima ina tareda ke” su Baffa duk suka tashi, Musty yace “kaisu ta back door bata gaba ba sabida reporters” binsu su Ibro da Hamza sukayi dan kaisu sannan ahankali Musty yazauna tareda sauke wani ajiyan zuciya yana kallon Abee, Harun yace “wlh wlh idan aka kamo yaron nan I will make sure yay rotting at the worse Nigeria prison” Abdul yace “the guy is evil” daidai nan wayan Musty yashiga ringing ganin Hajiya ne yasa yakalli Abee da kanshi ke kasa yace “tashi muje gida Hajiya is calling” batare daya kalleshi ba yana kokarin fara typing yace “ban tashi daga aiki ba sai 4, and this is just 12:54” shiru Musty yayi yana kallonshi Allah kadai yasan yanda yake hurting right now amman bazai taba nunawa ba, ganin bakinciki Abee zai cusamai yasa yajuya yakalli su Harun yace “kumuje” saikuma yajuya afusace yadauki wayan Abee dake kan table yace “shima ka kwace idan ka isa” yawuce yafita fuuu daidai Hajiya na kara kira dauka yayi kafinma tayi magana yace “Hajiya gani nan zuwa komi yazo dasauki kada kidamu kanki hawan jininki yatashi” katse wayan yayi suna fita suka shiga mota sai gidansu Abdallah da Kausar sun dawo daga makaranta dudda sunada lectures ganin videos dake trending na babansu, Zainab data tafi daga ita har mijinta sun dawo, kofar gidansu yacika kaman anyi mutuwa dayan anguwa babu wanda baya sonshi a anguwan dukansu sun karyata guards na estate dinsu sun hana ko reporter daya ya shiga saida su Musty suka fara gaisawa da mutanen waje sukace shairi akamai sannan suka shiga ciki bayan babban Liman na anguwan wanda yake matsayin ubansu yabisu zuwa cikin gida duk suka zazzauna a falo idanun kausar yay jajir taci kuka harta gaji na Abdallah ma haka amman shi baiyi kuka ba.

 

Hajiya kafin suyi magana tace “ina yake”? Musty yace “ai kinsan Imran da taurin kai yace aiki yake sai 4 yake tashi daga aiki munbarshi achan danko jawoshi zamuyi da karfi bazai tahoba amman Ibro da Hamza na chan tareda shi karki damu” tagumi Hajiya tayi Anty Binta ta bubbuga mata baya yace “dan Allah Hajiya kada kidamu kanki” anatse Hajiya tace “Meya faru Musty”? Ahankali yabasu labarin daga farko har karshe tsaf da yanda iyayen yarinyar sukazo da abinda sukayi kowa yay tsit adakin na kusan minti biyar sannan Hajiya tai breaking shiru takalli Liman tace “Liman kaine kake matsayin mahaifin yaron nan yakake ganin za’ayi”? Ahankali Liman yace “shi aure rufin asiri ne kuma sutura ne ga mumini, gabaki dayan mu nan munsan Imran bazai taba iya aikata wannan abuba abinda nakeso kuduba anan shine ayar dake tattare da abin nan inhar Allah ya shiryamai wannan kaddaran to da dalili, saikuma abu nabiyu shine inhar akabar zancen nan haka shikenan yabata ma ita yarinyar dashi Imran suna nan da gobe zakuji wasu sabbin labarai da kazafi da sauransu natashi indai mutane ne, saikuma sana’arshi da kampaninshi zai jijjiga that is idan hukuma bata shigo bama ta rufe company gabadaya ba, amman yanzu duk idan kuka ijiye sauran hujjojin nan kuka dauki hujjan farko dana kawo kaddaran suce Allah yaga dama yakuma tsara musu ita ahakan dan haka ayarda da auren amusu auren amusu auren asanara duniya su daman ma’aurata ne dan killace mutuncinsu hakan kadaine za’ayi ya wankesu shikuma yaron kubashi dududu satin nan dakanshi zai kawo kafanshi yanemi gafara zan nunamai ayar Allah ba wasa bane sannan Allah sarki ne tsarkakke Al Azza Wajal! Dan haka mu amince da abinda sukace mu kalli maraicin yarinyar”, dan hawaye Hajja ta share tace “nasan bazai taba yarda yay aure nan ba, babu abinda Abee ya tsana kaman aure, amman yau zan nunamai nine mahaifiyarshi, zan iya komi dan kare mutuncinshi aduniyan nan” sallama Liman yamusu yatafi sukuma kowa yay zugum falo saida aka kira la’asar ne ma su Musty suka tuna ko azahar basuyibasuka wuce.

 

Biyar daidai on the dot Hamza da Ibro suka shigo office din yana zaune akan kujeran su kallo daya yamusu yadauke kai anatse Ibro yace “Yaya Imran is 5 mutafi gida” dago idanunshi yayi yakalleshi ahankali Ibro yasauke kanshi kasa dan gabaki dayansu babu mai iya jure idanun Ya Imran akansu kwarjininshi is way to much, kaman daga sama yace “yaushe nida ku muka fara barin office tare?” Da sauri dukansu suka dagakai suka kalleshi karamin Mac book dinshi da yan kananun abubuwanshi yashiga hadawa batare daya kallesu ba babu alamun wasa akan voice nashi yace “ku kama gabanku” daidai yatashi daga kan chair din tareda daukan Car key nashi laptop dinshi a hannunshi yafito wuce su yayi duk suna tsaye suna kallonshi yabude kofa yafice dasauri suka fito Ibro ya tsaya yana kulle office din ganin yayi hanyar dazai kaishi main entrance suda sukeso yabi ta kofan baya dan reporters har yanzu na main entrance yasa aguje suka bishi yana jinsu amman ko juyowa baiyiba yakallesu anatse yake tafiya one after another kaman mai sarauta har zuwa gate din suma security nashi daga gaban entrance din ganin Oga yasa sukaji kaman sucemai yajuya yakoma ta dayan exit din amman shakka da tsoro yahanasu, budemai kofa sukayi yafice reporters na ganinshi suka taso aguje ana binshi kowa da kalan tambayan dayake watsamai koransu security nashi suka dingayi suka rike hannu suka taresu shikuma yay wajen motanshi yabude laptop dinshi ya ijiye a dayan sit na gaban sannan yashiga yarufe kofa yatada motan yafice, su Hamza ma suka shiga motocin su suka mar mishi baya.

Agaban estate nasu wasu reporter yagani but anhanasu shiga dayake motarshi tinted ne basusan shibane aka budemai gate yashige abinshi yan jama’a yagani akofar gidansu ciki harda Arif dolenshi ya tsaya akofar gidansu yasauke glass batare daya sakko daga motan ba, chaaa jama’an anguwa sukamai akai suna Allah kyauta Alhaji duk mai nufinka da shairi Allah ya maida musu Liman yamana bayanin komi Allah natare dakai kuma zamu nunama mutumin ayar Allah ba abin wasa bane wlh saiyazo harnan anguwan dakanshi yabada hakuri dan murmushi yamusu yace “nagode” hakan yasa suka watse saura Arif kadai da idanunshi sukai jaa yataho wajen motan ahankali zubamai idanu Abee yayi kaman babu wani abu yace “what are you doing here kabar Amarya”? Kasa magana Arif yayi but kana ganin hankalinshi kasan atashe yake, dan murmushi Abee yamai kadan yace “wuce ka koma gidanka” gyadamai kai Arif yayi ahankali babu musu yakoma yashiga motarshi shikuma Abee yatada motanshi aka budemai gate yashiga cikin gidansu.

You can read EPISODE 13 a IG💃

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply